Maleeka Malik – Chapter Nine
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“Tana Shiga Falon ta tarar da babu kowa ciki sai wasu baki goggoninta na malumfashi dasuke zaune bisa lumtsuma lumtsumar kujerun Falon suna hira…
Kallo Daya tayi musu ,bata kara ba bayan taja musu uban dogon tsaki ba wanda tacema kala ta tsallakesu zuwa bedromm din Daddynta tana kwalamai kira,anan ma wayan Fitowa tayi a hargitse daga Falon tayi Falon kasa bibbiyu take hada Steps saboda yadda Ranta yake amatukar bace,gana Abunda tagani ga kuma na ganin wayanan zugan yan kauyen da suke zaune musu agida basu Tafi ba.
Tana saukowa Falon Tashiga kwalama Hajiya kira muryanta akaushe…”Hajiya…?Hajiya…? Take Fada tana takowa zuwa tsakiyar Falon Fuskarta babu Annuri tana bin mutanen dake zaune da wani wulakatattacen kallo….
Joda ce ta Fito daga dakin Hajiyar tana Fadin”Anty Malika lafiya,…? Kallonta tayi tana wani mele baki a sangarce tace”Bai shafeki ba,juz ina hajiya…? Ta bude baki tayi mgana sai ga Hajiya ta Fito daga wani bangare na gidan tana Fadin”Lafiya malika,ina wanan kiran fa..? Baya taja tana Fadin”Ina Daddy shi nake nema banganshi ba…?
Kada kai Hajiya tayi tana karema malikar kallo,da ita da rigar jikinta tace”Bayanan ya tafi daurin aure,ammh nasan yana bisa hanyar dawowa..”yamutsa Fuska Tayi kan tajuya tana kallon mutanen Falon tana fadin”Toh su kuma wadanan me suke jira basu tafi ba,sun zo sun share kafa kamar wadanda aka gayyata wani sha’ani plz nidai su tararra su Tafi ko ni na bar musu gidan…
Wata goggon Alhaji Abdulmalik dataji haushin mganarta kai tsaye tace mata”,Mu tafi ?muje ina Amarsu ta ango? ai muda tafiya sai mun mika ki gid…”Kai Goggo Baraka don Allah kiyi Shuru…”
Hajiya ta katseta da hanzari jikinta na rawa,domin Alhaji Abdulmalik sai da ya gargadeta datayi taka tsan – tsan ko Malika ta Fito kada ta kuskura tabada damar da zata Fahimci Abunda ke Faruwa,shi zai sanar da ita da kanshi,to gashi goggo Baraka Tayi baram barama.
Malika dataji mganar bata maida kai ba,Saima mele baki datayi wanda ga duk alamu ya zamanto mata jiki,ta juya gabadaya duwawukanta na wani rawa ,da alama ma ko pant bata saka ba,ammh sai me Abun ne ya shiga mata yawo akunne _Mu tafi muje ina Amarsu ta ango? Ai muda tafiya sai mun mika ki gidan ki.._ Toh me hakan ke Nufi..? Tafada tana kara kallon hotunansu dake yawo A Twitter,da sauran sakonnin Jama”arta.
.
Hajiya binta harta Fara murna,sai kawai taga Malika ta juyo cikin mamaki tana kallon Goggo baraka kafin tace”Kikace me? sai naji kamar kin ambace ni da Amarsu….? Tafada tana kure ta da ido,Tuni Hajiya binta tayi saurin tarewa da cewa”Tafiyarki Malika bada ke take ba,kawai tana zencenta ne…”Tafada bakinta na hardewa saboda tsoro.
Malika bata samu zarafin mgana ba mazan yan Daurin aure suka fara Shigowa,wani kawun Alhaji Abdulmalik ne ya Shigo yana Fadin”Kai yau naga jama”a Bura ube,😂alqur”an harda wandanda banta tsammani ba,duk na gansu,yau gani ga Shugaban yan sanda na kasa gabadaya mukayi hannu dashi duk dalilin Auren Malika,kai babu Abunda zance sai Allah ya basu zaman lafiya kawai mallam”.. yafada yana saba babban rigarsa bakinsa har kunni.
Turus kowa yayi domin Tundaga shigowarsa har mganarsa Kaf akunnan Malika,wacce Tunda taji zencensa lakkan jikinta ya saki tayimai kuri da ido tana binsa da kallon mamaki,shi da fari baima Lura da ita ba,sai da yaga anyi Shuru ana kallon barayin datake kana ya kallah,ganinta tsaye yasa ya nufota yana Fadin”Wai ga yar cin Durin uwa”Wani irin banzan dabi”a ce haka kina amarya ammh babu wani kwalliya,sai Fito da wannan banzar Shigar,ke binta kuna me baku Shiryata,ayi amikata gidan mijinta Tunda An Daura aure kuma ai babu jira…”Yafada yana kallon Hajiya binta wacce ta jike da zufa,Shiko ko ajikinsa domin bashi da masaniyar Malika batasan Abunda ke Faruwa ba.
Kawai bai ankara ba,sai ji yayi ta chakumo kwalanshi tana Fadin”Wata malikar aka Daura ma Aure…? take Fada idanuwanta sun chanza kala sun yi jawur,dayan hannunta kuma na rike da wayarta,yadda ta ci kwalan babban rigansa sai ka rantse wani sa”an ta ne nan ko ya haifeta ya juya uwa uba kanin kakartace,wacce ta haifi mahaifinta.
Gabadaya Falon aka saka salati daidai lokacin da Daddy ya shigo yana Tambayan meke Faruwa ne yaji haniya,ai ba”a bashi amsa ba yaga Malika rike da kwalan kawu Shitu,Zaro ido yayi kafin ya kirata cikin tsawa wanda Tunda aka haifeta baitaba mata makamancin irin wannan Tsawan ba.
“Malika….!! Yafada yana Kokarin saba babbar rigarsa wacce ke kokarin zamowa saboda tashin hankali,Jin tsawan da kiran sunanta alokaci daya shiyasa ta zabura ta sakeshi tayi baya Fuskarta tayi ja,ganin Daddyta tsaye yasa ta nufeshi da gudu ta fada jikinsa lokaci daya ta fashe da wani marayan kuka tanayi tana Shessheka.
Riketa yayi jikinsa yayi sanyi ganin yadda Malika take kuka,Rumgumeta yayi yana Fadin”Why Babby….? Dagowa tayi kafin tace”Daddy plz tell me d truth,da gaske an Daura min aure yau…? plz don”t say yes Daddy nasan cewa kai Uba ne mai Adalci kuma bazaka taba yimin Abunda bani so ba”?
Tafada tana kuka Kallonta yayi kai tsaye yarasa Abunda zaije mata dakyar yace”Injiwa…? waya sanar dake wannan lbrin ba gaskiya bane…”Yafada yana riko hannunta,Fizgewa tayi tana Fadin”,Gasu nan su suka Fada,Daddy kalli wayata kalli Abunda nagani,yana yawo mai zaka kira da hakan,kuma ma infact ma mai wannan taron jama”ar yake Nufi,nafara hango Kamshin gaskiya awannan zence,juz look Daddy ka kalli wannan Hoton ka sanar dani karya ne ba gaskiya bane…”Tafada tana haskomai hotonta dana Saleem da”aka hadashi waje daya.
Karba yayi yana kallo,gabadaya kansa ya kulle baida mafita illah sanar da ita gaskiya Dagowa yayi yana Fadin”,Comon baby taho muje ciki muyi mgana kinji…? Kallonsa tayi kafin ta ja baya tana Fadi cikin tsawa”Wlh babu inda zani sai ka sanar dani gaskiyan wannan mganar….”Tafada tana huci,Kallonta yayi kai tsaye bakinsa na Rawa yace”E…Eh…Gas…Kiyane,buh ammh bby ki tsaya ki…..”
“Ya isa…..”Tafada cikin dakamai Tsawa kamar wani tsaranta,Idanuwanta sun juye Shuru yayi yana kallonta,Wasu zafafan hawaye suka biyota,kawai sai ta nufeshi,tafara dukansa a kirji tana Fadin”Ka zalunci ne,Ka cuceni bazan taba yafemaka ba,i hate u…I hate Daddy….”Take Fada tana dukansa da alamar ta Fita da hayyacinta,kunya ne da nadama suka lullubeshi na Abunda malika takeyi riketa yake yana kiran Sunanta,ammh bata ko jinsa,illah dagewa datayi tana jifansa da duk kalmar datazo bakinta,harda cemin Azzulumi Ranshi yayi mugun baci baisan sadda ya daga hannu ya kwasheta da maruka har biyu ba, Dama da hauni,wanda sai da ta kife saboda zafin marin nan da nan bakinta ya fashe hancinta yafara habo,yana xubar da jini.
Tsaye yayi gabanta yana huci yake Fadin”Ba tun yau Nafara Nadamar sangartaki danayi ba Malika,Ammah yau na kara jadadda Nadama na,kuma na yarda Allah ne yafara nuna mim Isharata Aduniya,ina matsayin Mahaifinki,ammh kirika jifana da munanan kalamai,don kawai na aiwarta da Umarnin Allah,toh bari kiji daga yau na daina Saka rmiki kina Abunda kika ga dama,Tunda ke bakisan mutumci ba,kuma Auren anriga an Daura wlh ko zaki mutu yau nida kaina zan mika ki gidan mijinki,Allah barshi daga chan ki rataye kanki mutu karewar iskanci,Binta kamata ku Shiga da ita,ku shiryata a gaggauce nan da wani lokaci xan mikata gidan mijinta…”
yana gama Fadin haka ya wuce sama Fuu kamar zai tashi sama.saboda Fushi itako malika kasake tayi hannunta dafe da bakinta dake jini,Abunka da farar mace,nan da Fuskarta tayi jajir,ga shaidun yatsun nan sun bayyana,saboda bakin ciki da takaichi kukama ya kasa zuwa mata,kwanciya kawai tayi awajen hawaye suna kwararomata,bata ta zaton yau ita Malika malik,haka zai iya Faruwa da ita ba.
Tunda tataso wajen Daddynta banda soyayya da zallar kauna babu Abunda
yake gwadamata,bai taba saka hannu ya dake taba,kai ko Fada bai taba yimata,koda kuwa tayi ba dai dai ba,tsakaninta dashi sai lallashi da soyayyah,ammh yau na rana tsaka saboda Auren,Auren ma arasa waza”a hada ta dashi sai wani kazami kuchakin Dan sanda,kakin datafi tsana aduniya,tunda take gudanar da rayuwarta bata ta kawowa zata iya aure ta zauna karkashin wani abu,sai dai ko in ita taga kayimata,ta yarda ta aureka,randa ta gaji dakai ta sakeka,dama shirinta kenan koda Daddynta ya mtsamata tayi aure
Wani Siririn kuka take saki tana daga kwance,suko tsaye sukai suna kallonta,suna Allah wadai da ita,Hajiya binta ne ta karisa gareta tana dagota take Fadi”,Tashi tashi Malika kada ki zama wadanda Allah zaiyi Fushi dasu,ki bi umarnin mahaifinki don yana da hakki akanki,Ki biyashi shekarun daya kwashe yana gina rayuwarki da gata,baki taba neman Abu kin rasa ba,kullum Cikin Faranta miki yake baya son ganin bacin ranki,ke ko daidai da Rana daya baki taba Sashi Farinciki ba meyasa yau bazaki Sashi Farinciki ba,koda sau dayane arayuwarshi ya Tuna yau Malika tayi min Abunda nakeso batare da gaddama ba,haba Malika,don Allah bar kukan nan ki tashi,domin yanzu darajanki ta karu,igiya uku ke reto akanki,wanda bakowacce mace ke samun irin damarki ba…”Tafada tana rikota,haka ta data ita jikinta ya saki banda zubar kwallah bata komai,ga duk alamun mganganun Hajiya binta sun Shigeta,neman Faduwa suke gabadayansu saboda yadda Malika ta sakarmata Nauyinta,da Saurin wata kanwarta dake Malumfashi ta kariso zata rikota tayi saurin Matsawa alamar bata so.
Ganin haka yasa Hajiya binta ta yafito Joda da hannu suka riketa kowanne ya sagala hannunta daya bisa kafadansu,suka fara taku da ita zuwa sama,har dakinta suka kaita,Hajiya binta da kanta ta Shiga tiolet din ta hadamata Ruwan wanka,ita kuma Joda tana zaune kusa da ita tana Faman Sharemata hawaye kamar wata karamar yarinya,ammh ranta fal dariya,da sukace tashiga wanka banza dasu da tayi,sai ma saka baki datayi ta kira su merry da Dose sai gashi sun Fito da hanzari da hannu tayi musu mgana,Sai gashi sun dauketa cak sun Shiga da ita bedroom dinta.
Suna mata wanka tana kwance cikin bath din Idanunta arufe tana kuka ammh na zuciya,domin hawaye ne ke ta zubomata kamar an bude famfo,sukansu Dose sunji ba dadi,lalle Duk Abunda ya sanya Madam kuka bamai sauki bane,matar data ke jaruma isasahiya mai ji da kanta yau ita ke kuka da idonta.
Haka dai suka gama mata wankan suka Fito,da ita koda su shafeta da mayuka,tuni joda ta iso dakin dauke da wani Ubansu leshi mai kyau da yarari,kalan marun,and red,sai takalmin shi da jakarsa da wani katon mayafi red,ammh yana da santsi Kuma sharashara,yake yana da wasu duwatsu kanana masu kayyali ajiki,sai dan kunnen zinare guda daya Wanda mahaifinta yayimata domin zuwa gidan Miji dashi.
Mikamusu kayan tayi tana umartansu dasu sanya mata su,sake baki sukayi suna bin kayan da kallo,suna mamaki don dai su a iya tsawon zamansu da Madam bata taba sanya wani kaya ba,bayan Suit,ko kuma wando da riga ko Sikat da riga,ganin yadda suke mamaki yasa tayi musu mirmishi tace”Ur Madam she now a bride today….”Tafada kai tsaye tana kallon Malika wacce ke zaune kan Stool kamar mutum mutum banda kwararan hawaye babu Abunda takeyi,kuma bata damu data saka hannu ta share,ba in ka kalleta sai kazata kamar wata wacce tayi loosing din memary dinta,
Zaro ido sukayi cike da murna suka ce”Wow…Congratulation Madame…”,Suke Fada bakinsu har kunne,ammh kuma jikinsu yayi sanyi ,Ganin yanayin madam din,da alamun dai bata marada da wannan Auren,ahaka suka sanya mata kaya,Abun mamaki sai gashi tayi kyau cikin kayanmu na hausa Fulani Fiye da na Turawan data ke sanyawa,Joda ita tayimata Dan Simple make up,wanda anayi tana Batashi da hawaye,ahaka aka gama,Ko motsi batayi ba kamar wata waccce lakanta ta cire bata wani karkashi.
Suna gamawa sai ga Hajiya binta tana Fadin suma su merry su Shirya kayansu dasu Alhaji yace za”ta tafi,kuma su daukan ma malika duk Abunta mai amfani kama daga abubuwanta na Sirri,ammh banda kayanta jikinsu na rawa suka koma ciki suna hada kayansu,Itako tana Zaune kamar an Dasata,sai ga Alhaji Abdulmalik ya shigo har cikin bedroom dinta ganinta haka bakaramin sosaimai rai yayi ba,karisawa yayi gabanta ya durkusa yana riko hannunta yace
*MALIKA..*… Yakira sunanta cikin taushin murya,dagowa tayi tana kallonsa,ammh kuma hawayenta basu tsaya ba,Mikar da ita yayi tsaye yana kallon kwayan idonta yace”Ki yarda dani mahaifinki ne? kuma kin yarda ni bazan taba yin Abunda zai Cutar dake ba…? Zuru tayimai takasa mgana illah Kallonshi datakeyi tana zubar hawaye,Hannunshi ya kara mikamata yana Fadin”In har kin yarda da Soyayyar dani ke miki malika,ki saka hannuki cikin nawa kizo muje na mika ki gidan mijinki….”,Yafada yana mikamata duka hannuwanshi…
Wajen yayi tsit,ana jiran ganin Malika zata mika ko a”a,sai kawai tabama kowa mamaki,jikinta asanyaye ta mika hannunta cikin na mahaifinta,lokaci daya tana sanya hannunta danashi ta share kwallanta,kafin ta dago Fuskar babu fara’a ko kadan ballatana Annuri,Damke hannuwansa tayi kafin ta Furta murya shake”I Truth u Daddylove….and am very srry For wht i did…”,Tafada kai tsaye tana kara nuna dakewarta,jin dadin kalamantane yasa ya Rumgumota yana sakamata albarka,tuni Hajiya binta ta mikamai mayafinta ya saka mata bisa kai,shi da kanshi ya durkusa ya zuramata takalminta mai Dubu ya riko hannuwanta suka Fito daga bedroom din Joda da Hajiya na biye dasu abaya rike da jakar Malika,sai Su Dose da kowacce kowacce rike da jakarsu su murna ta ciikasu zasu koma new House.
Ahaka suka fito har zuwa falon kasa,Gabadayan matan dake wajen suka mike suna sakin guda,waje fa ya rude,haka suketa reramata wakan… _Ke kikace kina so,da baki ce kina so ba da bamu baki shi ba.._ Ayyiriri guda ga Amarya zamu kaita Gidan miji zata kwana,zamu je musa kida muyita Tsalle…_ Haka suketa rerawa suna rawa da guda,itako Maleka tana Rumgume da Daddy tana jin kamar ta farka ace mata mafarki take ba gaskiya bane.
Haka aka Fice da ita,motar Daddy vibe 2k19 ya saka Malika agidan gaba,shikuma ya shiga mazaunin Direba domin shi zai kaita da kanshi,Sauran jama”a kuma suka shiga sauran motoci domin suje suba idonsu Abinci,lokacin wajen shida ne na yammah ana gabda kiran sallar mangariba.
Motar Daddyce tafaryin gaba,sai na Hajiya binta wanda Joda ke ciki da wasu yan”uwa,dai sauran ayarin motocin wadanda sukayi combain,tare da excorts din malika da motocinta,duka domin Alhaji Abdulmalik yace da komin ta zata tafi,cuz bayaso Malika ta chanza,yarda take rayuwarta na baya haka yake so Ta cigaba.
_________________
Suko su Saleem suma koda suka koma gida ya dinke da jama”a anata hidima nan fa lbri ya tashi na irin Dukiyar da’aka narkama Saleem da kuma kyauttukan da Alhaji Abdulmalik ya bamashi saleem,din nan fa wasu sukayita mganganu,donsu harga Allah daga Saleem din har iyayan nashi suna musu kallon kwadayi ne ya kaisu.
Shiko Saleem Dakinsa ya Shige ya kulle kansa,saboda cigaba da Shirinsa,baifi minti talatin da Shiga sai gashi ya Fito,da makullanyen gidan,da Daddy ya bashi dana motar da”aka bashi,da kuma anihin key din motarsa,wacce yake hawa,agaugauce ya samu Abbi ya sanar dashi cewa yanzun nan ya samu waya daga chan headquatersu na zamfara ana nemanshi da gaggawa so yanzu zai tafi ne,Abun yabama Abbi mamaki wani irin neman gaggawa ne haka,bai musa mai ba yamai Fatan alheri,ammh sun rabu akan in komai lafiya zuwa gobe zai tafi katsina chan wajen Amaryan tashi,haka ya shiga wajen Ummi yamata sallama,ana ta mai tsiyan ango guda bazai tsaya agama shagali ba,Shidai yake kawai yake baya mgana.
Sanda Sadiq yaji tafiyan Saleem zamfara yaso ya bashi yaki bashi dama,dole ya kyaleshi ya Shiga mota ya kama hanya,ya bar garin Abuja yakama hanyar zamfara,bayan yakira wata nomba yana Fadin”Inspector Saleh,gani hanyata ta zuwa zamfara juz tell me,karfe nawa flight dina zai tashi…?Banji me aka ce mai naji dai yace “Ok mu hadu a Airport din kawai…”Daga haka ya yanke kiran yana wani killer smile bayan ya sakarma motar gudu.
Awa biyu ya dauka kafin ya isa zamafara saboda gudun dayayi ko headqutern nasu bai shiga ba gidansa ya Wuce,lokacin anata sallar mangariba amsallatai Shiyasa ya tsaya yayi wanka yayi sallah kafin ya chanza kaya zuwa Uniform dinsa,lokaci daya ya koma aninihin ACP SALEEM KABIR KUMO,madubi yake kallo sanda yake kafa hularsa bisa kai Fuskarnan babu Annuri ko kadan.
Cikin Sauri ya dauki wasu takardu,sai pasports dinsa da kuma Atm dinsa ma,’ajiyar kudinsa kenan sai kudi Dollarwanda ya dauka baisan ko nawa bane ya zurasu cikin aljihu ,bai dauki kaya ko daya ba,ya Fito a gaggauce ya kulle gidan,bai bata lokaci ba Shiga cikin headquater nasu nan naga yana ta sallama da ma”aikatan wajen yana barin musu sallahu,Abun da yabani mamaki office dinsa kawai ya Shiga ya dauki wata takarda sai Syestem din shi wanda dukkan Abubuwan aikinsa naciki,ga duk alamu dai kamar Tafiya ce mai muhimmaci Saleem Zaiyi daga yanayin yadda yake musabaha dasu na bankwana ne,suna fatan Allah yabashi sa”a kuma ya dawo dashi lafiya.
Koda yabaro zamfara 7 da wani Abu na dare bai yi wasa ba ya sakarma motarsa gudu yanayi yana duba agogon hannunsa,domin so yake ya isa Katsina kafin goma na dare,domin jirginsa zai tashi ne da karfe 3:30 na daren yau din,jirgin dazai tashi daga kano zuwa kasar CHICAGO dashi aciki,shiyasa yake komai cikin hanzari kuma yana Fatan komai yatafi kan tsari kamar yadda ya tsara.
Alhaji Abdulmalik da kanshi ya Shiga Da Malika har kayatattacen dakinta wanda ya Shiryamata ya kuma mata masauki bisa gadonta,Fuskarta na rufe,ammh kuma tana kallon komai saboda mayafin nada sharashara,kanta kawai ya dafa ya shiga sakamata albarka kafin yayi musu addu”an zaman lafiya hawaye ne yaji suna Shirin tahomai shiyasa yayi saurin Ficewa.
Kowa son barka yake da gidan suna jinjina dukiyar da”aka kashe babu wanda aka bari ya dade duka Daddy ya tararra su su koma gidanshii,Hatta hajiya binta bata dade ba tatafi Joda ne ma sai daga baya tatafi,aka bar malika daga ita sai merry da Dose sai su peter dake Haraban gidan suna mazurai.
Shiko Alhaji Abdulmalik bayan ya dawo gida ya kira Abbi yana sanar dashi amarya tana dakinta,nan Yake sanar dashi kiran gaggawan da Saleem ya samu da Wajen aikinsa,bai nuna damuwarsa ba,saima fatan alheri dayayi mai yace zai kirasa yanzu,bayan sun gama waya yayi ta kiran wayar Saleem bata shiga,sai yayi Tunanin kila network ne,bai san ko Tuni Saleem ya saka nombarshi cikin black list din wayarsa,domin game din ya kusa karewa.
Itako Malika tana jin Diran Fitan motocin gidansu tayi zumbur ta mike tana karema dakin kallo,kayan jikintane suka dameta tafara kokarin cirewa bayan tayi jifa da dankwalinta Merry da Dose take kwalama kira,wadanda ke Falo,da gudu suka Rumtumo suna rawan jiki,Jikinta ta nuna musu tana Fadin”Oy up dis Cloths now..”Tafada cikin Tsawa,jikinsu na rawa suka Nufeta suna kiciyar ciremata less din dake jikinta,tsab suka tubeta suka barta daga ita sai pant,da bra wardrope suka bude suka daukomata wata doguwar riga ta roba,wacce bata da hannu suka zuramata,nan da nan ta lafe mata ajiki,ajiyar zuciya ya ta sauke tana baza gashin kanta da hannu tayi musu alama dasu Fice su bata waje,da hanzari suka Fice jikinsu na rawa da sabon Halin Madam dinsu,Fuskarta kwata kwata babu rahama,duk da ada Bata da mutumci,ammh na yau yafi na kullum.
Karfe 9:40 Na dare Saleem ya zuba hon abakin get din gidan da”aka zana amtsayin mallakinsa,Megadi yana lekawa yaga Shine da hanzari ya budemai get din ya sulala ciki,Koda ya isa parking space baiyi mamakin ganin motocin Malika ba,Cike da wajen ba,gefe daya kuma Exscort din tane keta shawagi suna zaro ido,dariya yayi cikin ransa yana ayyana Abubuwa da dama.
Ya dade cikin motan kafin ya Fito cikin azamarsa na cikakkan Namiji kulle motarsa yayi yana saka duka hannuwansa cikin,aljihun bakin wandon dake jikinsa,taku ya farayi zuwa kofaar da zata sadashi da cikin gidan,ko kallon Su peter bai yi ba,wadanda suka kame gefe suna mazurai domin Tun Fitowarsa daga mota kwarjinsa da haibansa ya dake su,Baya su ja suna ayyana kila wannan ne mijin madam ne,balle yadda suka ga ya hade rai kamar an aikomai da sakon mutuwa.
Cikin takama da isa ya sa kanshi Babban Falon gidan yana bin ko”ina da kallo,gabadaya Falon ya cika da kamshin Turaransa na MAN, merry da Dose dake zaune sukayi hanzarin mikewa suna kallonsa,ammh shi ko inda suke bai kallah ba,kuma bai tankasu ba,Steps yafara hawa Still duka hannuwansa na jikin aljihun wandonsa,Har zuwa Dakin daya Haddace cewa Shine na Malika.
Tura kofar yayi batare da yayi sallama ba,har ya Rufeta batayi motsin da zan agane wani ya Shigo ba, dan makullin dake jikin kofan yayi amfani dashi wajen Kulle kofar dashi,gefe daya kuma yana Saka key din cikin aljihub wandonsa, yana juyowa Da Malika yafara cin karo wacce ke kwance bisa gado,Ta na kallon kofa ta baza gashin kanta,Har ya Rufemata ido daya bayan idanuwan nata na Rufe kamar mai barci,ga santala santalan Fararen kafafun ta nan awaje saboda yanayin yadda ta kwanta babu inda ya boye na jikinta.
Kuramata ido yayi yana jin Wani daci tare da bakinciki na zuwamai,nan da nan Abunda ya faru Shekaru biyar ya dawomai kamar yanzu komai ke Faruwa,cikin takun natsuwa ya isa gabanta yadauki kafarsa daya mai dauke da bakin Takalminsa Sawu ciki ya aza bisa gadon,yana girgizashi da kafarsa daya.
Kamar amafarki taji motsi bata bude ido ba tace”Who..? azaton ta su merry ne,ammh sai taji Shuru ranta ne ya baci ya sanya ta bude lumsassun idanuwanta tana bin bakin takalmin dake ijiye gabanta da kallo,kafin ta daga idonta zuwa bakin wandon jikinsa har zuwa rigar Uniform dinsa har zuwa saman kansa,Yadda suka hada 4 eyes cikin wani yanayi na tsana da tashin hankali Saleem ke kallonta yayinda ita kuma Abun yazomata abazata,ammh sai ta dake tana daga kwance tace”Who are u? waya baka damar shigomin gida…?
Baiyi mgana ba illah Saukar da kafarshi dayayi kasa yana kara maida hannunuwansa a aljihu zagaye gadon yafarayi yana Binta da kallo,itama tana kallonshi ammh kuma tana jin jikinta na rawa saboda yanayin yadda yake kallonta,Uwa uba kuma wai yau itace tsaye da mai sanye da Uniform din yan Sanda adaki daya? kai ina imforsble,tafada aranta kafin ta mike ta sauko daga kan gadon da hanzarinta sai gata agabanshi.
Baya yaja kamar yana jin tsoronta kafin yace”No ba yanzu ba Hajiya Malika juz wait nayi miki wani bayani mana…’,Karo na farko daya yimata mgana Zuru tayimai tana kallonshi daga sama har kasa,Zagaye bayanta yayi kafin ya takaro kafarshi da gado,shikuma yasata a tsakiyarsa kafin tayi wani yunkuri ya daga hannu ya zuba mata wani lafiyayye mari mai zafi da gigitarwa wanda sai da tayi luuu zata kife bisa gado yasa hannu ya Fizgota yana huci yace”Kai ne ko? kai kabasu Umarnin su tsaremin motoci ko? Toh daga yau bazaka kara saka atare motocin wani ba,balle motocin Malika malik…”Yafada yana fitar da hucin mganar bisa Fuskarta,
Itako Suman tsaye tayi,ayayinda jini ke biyo hancinta da bakinta saboda yadda marin ya gigitata,kalamanshi take son Tunawa,ammh kafin ta samu damar Sakasu Acikin kwakwalrta ya sake kifamata wani marin kamar Allah ya aikoshi wannan karon bai hanata Faduwa bisa gadon ba,ya barta ta Fada,rajab tana Dafe duka kumcinta saboda Taga gilmawan wasu taurari,bai barta tayi motsi ba ya sanya Kafarsa daya ya take mata dan yatsarta daya ya murje,sosai wanda sai da ta saka ihun azaba da kuka,Hannu ya sa acikin aljihu ya kwaso kudi dollars ya watsamata afuska yana Fadi cikin Tsawa…
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
