Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    “”Washegari da misalin karfe 10 da wani Abu na Safe Saleem yadau hanyar katsina bayan ya kira Abbi yasanar dashi,shikuma yakira Alhaji Abdulmalik ya sanar dashi ga saleem nan zuwa.

    Shi ya tuka kansa,shiyasa ya isa akan lokaci domin dama Saleem akwai gudu amota kamar zai tashi sama,koda ya shiga cikin garin katsina bai sha wahalan gane gidan ba,sakamakon gidan Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ba boyayye bane a katsina,cikin lokaci sai ga motarsa ta tsaya abakin makeken gidan,wanda yake kama da wata al’karya guda.

    Hon ya zuba Kafin megadi ya leko yana Tambayansa sunansa kai tsaye yace”Saleem kabir kumo…”Bai yi watawata ba ya wangalemai kofar get din motarsa kirar 4matic ta sulala ciki domin dama Tuni an san da zuwanshi.

    Aparking space ya Faka motarsa kafin ya Fito yana bin haraban gidan da kallo,wanda wasu tafka tafka motoci iya kallon ka mallam,sukama gidan kwanya gefe daya kuma excorts din Malika keta zagaye suna wani Mazurai Dan ware ido yayi yana bin benen gidan da kallo yana jinjinama fasahar bazanin da maginin harda wanda aljihunsa yayi kuka,domin duk Abunda yake zato,toh ya ganshi Fiye da Tunaninsa.

    Komawa yayi ya jingina da motarsa Yana wasa da key din motarsa,sanye yake da Shadda mai Ruwan kasa wacce taji yarari da maiko,dinki tazarce ne yayi matukar amsansa,gefe daya kuma ya dora wata hula zanna bukar itama mai alaman zanen Ruwan kasa,hannunsa sanye da agogon Fata na kamfanin Rado,shima mai kalan Ruwan kasa,bayan takalminsa shima Rufaffafe ne na Fatar damisa,shima kalan Ruwan kasa,kallo daya zakamai kaji kakasa kara kallonsa saboda yadda kwarjinsa da haibansa ke tasiri a idon wanda ya kallesa

    mace kuwa komin Girmanta da ajinta,da isarta da takamarta da duk Abunda take takama dashi,in ta kalli saleem sai taji ta raina kanta da duk Abunda ta mallaka.

    Bai Dade da tsayuwa ba,yaji muryan wata mace cikin hadadden Turanci wanda dagajinsa kasan mutum ba haye yayi ba,ya kware ne,daga gefensa kamar bazai daga kai ba,sai yadaga idonsa ya Fada kan Malika wacce ke Tahowa daga bayan gidan Daga ita sai wani karamin mini sikat,da wata riga kai breziya ce ma,domin banda kokon nono bata tare komai ba gashin kanta ajike yake da karamin Towel akanta tana gogewa da hannu daya,dayan hannu kuma tana mgana awaya,fararen kafafunta da cinyoyinta awaje suna kyalli,bayan kafarta na sanye da wani Takami flat mai taushi.

    Bayanta Merry ne da Dose,merry na Rike da robar Ruwansha,ita kuma Dose tana rike da wani karamin Towel din,dukkansu suna biye da ita kamar rakumi da akala,bai gama mamaki ba sai da yaga tabiyo ta gabanshi cikin wannan banzar Shiga ko ajikinta ta kuma ratsa ma,’aikatan gidan,wadanda suka kame mata kamar wata matar Shugaban kasa,Bayanta yabi da kallon Tir,yana jin wani takaichi aransa ganin yadda gabadaya idon kardawan arnan samudawan ke kan Hips dinta wanda ke Juyawa kamar wanda ake controle dinsu.

    Saurin Kauda kai yayi yana kiran Sunan Allah,wani Siririn tsaki yaja yana Fadin”Lalle yarinyarnan ta Wuce da Tunanina,ashe tsinanniyace ta karshe bansani ba….’Yafada yana rike haba,yana bin Kofar data bi da kallo,Bai gama mamaki ba,sai ga Alhaji Abdulmalik ya Fito da hanzari cikin Fararen kaya yana saba babban Riga ya kariso wajen Saleem yana Fadin”Am srry na barka awaje ko..?

    Yafada yana kokarin mikasa hannu ammh sai Saleem yaki bashi hannu sai ya rankwafa yana Fadin”Ina Wuni Daddy…”Yafada yana sadda kai,Dagosa Daddy yayi yana Fadin”Ash Tashi Tashi mana,Saleem ko..’,?Yafada cikin Fara”a,

    Gyada kai Saleem yayi yana Sadda kai,kafadansa Ya kama yana Fadin”Masha Allah…”Yana kallonsa murna da Farinciki sun cikashi ganin Saleem amtsayin Surikinsa koshi dayake Namiji kwarjinsa ya dakesa sosai,Yana Rike dashi Har zuwa Babban Falonshi na saukan baki,ya zaunar dashi bisa kujera,wanda Saleem din yayi saurin zamowa kasa yana dukar dakai.

    Yar Dariya Daddy yayi yana Fadin”A”a Haba Saleem,maza tashi ka zauna da kyau nan ma fa gidanku ne,nima Abbanka ne ko Kumo bai sanar dakai bane..?”Yana duke ya murmusa yana Fadin”Ya sanar dani Daddy kayi hakuri kabarni anan…”Dariyan Farinciki Daddy yayi yana Fadin”Toh indai ka dauke ni a mtsayin Daddynka toh na baka Umarnin katashi ka koma bisa kujera kaji..”ba yadda ya iya,sai tashi ya koma bisa kujeran yana Kallon Cafet din daya karama Falon kyau.

    Kallonsa Daddy yake ransa na Fari,Aransa yana ta Fadin masha Allah,waya ya daga ya kira Hajiya binta yace akawoma Bako Ruwa da lemo,ai ba’a dauki muntuna ba,sai ga Atika da Tire niki niki da lemuka da Ruwa ta ijiye gaban Saleem bayan ta duka ta gaisheshi,ya amsa bai kalli ma inda take ba idonsa na kasa.

    Mikewa Daddy yayi yana Fadin”Bari na barka kasha Ruwa ka huta kafin nazo muyi mgana ko..? Mirmishi Saleem yayi baice komai ba har Dadddy ya Fice daga Falon jikinsa na rawa,Da kallo mai kama da harara Saleem ya bisa kafin ya saka hannu ya dauki Ruwan swan ya tsiyaya akofi yasha,Ajiyewa yayi yana sakin ajiyar zuciya Lokaci daya yana bin Falon da kallo Yana mele baki

    Bai jima ba,sai ga Daddy ya dawo yana ganinsa yayi kasa da kai kamar wani na gari,nan ko zaginsa kawai yake aransa,domin hardashi abada Gudummuwar Wulakancin da Malika tayimai,kusa dashi Daddy ya zauna yana Dafa kafadansa kai tsaye yace”Sannu da zuwa,hop kazo lafiya..?

    Saleem ya amsa da cewa”Alhamdulillah..”Alhaji Abdulmalik yace”Masha Allah nasan dai mahaifinka ya sanar dakai komai ko..”,?Gyada mai kai kawai Saleem yayi,kafin ya cigaba da Fadin”Toh naji dadin hakan,yanzu Abunda nakeso dakai kamar yaushe ne kake bukatar ayi auren …?

    Saleem yaji ransa Fes,ammh sai ya basar yana Kara sadda kai yace”Daddy duk yadda kuka tsara ni awajena Daidai ne..”girgizamai kai Daddy yayi kafin yace”A”a ba ahaka Saleem ai kaine zaka zauna da ita,kai ya kamata ka sanar damu zuwa yaushe kakeson ayi komai agama..”Shuru yayi kafin yace”nan da Wata daya yayi Ko…,?

    Daddy yace”Yayi sosai ma,Allah ya nunamana yanzu kana wani aiki ne…? Saleem yace”Ina aiki a zamfara ne,karkashin wata headquter,a mtsayin Acp…”Washe baki Daddy yayi yana buga kafadansa yake Fadin”Wow Bravo…Ashe magajinn kumo ne,gaskiya am so happy to hear dat,Allah ya taimaka..”Yana mirmishi ya amsa da Ameen.

    Gyara zama yayi yana Fadin”Kana da muhallin ma”ana wajen da zaku zauna…? gyada kai Saleem yayi kafin yace”Eh inada dan madaidaicin gida anan zamfaran…”Shuru Daddy yayi kafin yace”Toh babu laifi,ammh akwai Abunda nakeso na sanar dakai,bawai don zaka auri yata ba A”a don kaima kana mtsayin Dana ne ko ba malika zaka aura ba,zan maka dukkan Abunda yakamata..”

    Saleem ya jinjina kai yana Fadin”Hakane Daddy…”Yace “Toh Abu na Farko Shine bani son ka kashe sisinka amganar auren nan bayan sadaki,duk wani Abun bukata,kama daga lefe da gidan da zaku zauna duk zan tanadar muku kaji..”Mirmishi Saleem yayi kafin yace”Ayi haka Daddy…’Kafadansa ya dafa yana Fadin”Karka damu Dukkanku ya”ya ne,so yanzu sauran mganr zamu tattauna da mahaifinka kaji ko,Allah yayi maka albarka yakuma baku zaman lafiya..”Afili ya amsa da Ameen ammh cikin ransa ba Ameen ba yake fadi ba,yana ayyana yadda rayuwarsa zata Cutu matukar Allah yabasu zaman lafiya da wanchan tantiriyar yar iskan.

    Mikewa Daddy yayi yana Fadin”Yanzu zaka Wuce ne,ko akirama ita ku gaisa ne?.”(Shima dai kawai ya Fadane kada Saleem din yagano ita malikar bata sani ba…) Saurin Girgiza kai saleem yayi yana mikewa yace”A”a Daddy rabu da ita,zan dawo insha Allahu,yanzu ma ina Sauri ne aiki yayiman yawa a office ni zan koma…”Daddy yace”Haba ka tsaya kayi lunch mana!Saurin girgiza kai yayi yana Fadin”ngd daddy…”

    Bai hanashi ba illah Shiga ciki dayayi ya kira Hajiya binta suka gaisa,wanda itama ta yaba da Saleem din,kuma aranta tana ganin Malika ta samu daidai da ita,har bakin mota Daddy ya rakasa yabashi rafar kudi yan Dubu ammh Saleem yaki karba sai da yaga ya nuna baiji dadi ba kana ya karba,har ya Fice daga gidan yana dagamai hannu da Fatan Allah ya kaishi lafiya.

    Saleem na tuki yana cin dariyan Ladabin karyan dayayima su Alhaji Abdulmalik,domin harga Allah baya wani ganin mutumcinsa,kawai yana mai na yan Duniya ne,ammh ina Abun girmawa anan wajen,yana babba ammh sam baida Tunani yabar yarinya na Abunda taga dama,ammh no wahala karshenta ya kusa zuwa,domin dama yace wata daya ne don ayi komai a Wuce wajen,Yaci burin yadda Adare daya malika ta chanzamai rayuwa,shima yayi al”kwarin chanzamata shi awannin goma ne bama sai an kai ga cikar dare ba,kudin daya bashi yake kallo yana harara,yana fadi afili,”Dole mana kabani kudi,Tunda za”a Tusa min Ragowar arna,yaga yaro shar zai makalamin tsohuwa,yo tsohuwa man wanda naba shekara daya,ai ta tsufa…”yafada yana sakin tsaki yana cigaba da hararan kudin kamar sune Alhaji Abdulmalik din.

    *

    Saleem bai kira Abbi ya sanar dashi Abunda ya wakana tsakaninshi da Alhaji Abdulmalik dan kasuwa ba,shi da kanshi ya kira Abbi ya sanar dashi komai kuma yana kara yabawa da Saleem din,Ada Abbi yaso yayi Turjiya game da Cewar dayayi sadaki kadai yake bukata,ammh sai shi Alhaji Abdulmalik Dankasuwa ya nuna daga Saleem din har Malika shi uba yake garesu,saboda yana da hakkin yimusu dukkan Abunda ya kamata,nan yake sanar dashi ya tsaida mganar auren nan da wata daya,.

    Abbi yaji dadin karamcin Alhaji Abdulmalik har ya nuna yana so yan”uwanshi baffanninshi da suka rage akumo zasu agabatar da neman aure,Alhaji Abdulmalik ya dakatar dashi da cewa basai sun zo ba ai duk Abun na gida ne,su bari Ranar daurin Aure sai suzo tare da Sadaki,babu komai shi ya riga yaba saleem malika har Abada,da wannan mganar sukayi sallama cike da Farinciki.

    Abbi baya da zabi illah sanar dasu Ummi halin da’a ake ciki,wanda Hajiya ce kadai ta nuna murnanta Afili ,ammh Saleema da Ummi Kamar su fasa ihu saboda bakinciki,Saleema ta bude baki tana Fadin”Haba Abbi yanzu Fisabillahi in yaya Saleem baida hankali da Tunani sai ka biyemai,yanzu don Allah duk matan Duniya yarasa wazai aura sai Wannan yar iskar…?

    Tafada idonta cike da kwallah,hararanta Abbi yayi yana Fadin”Kul na sakejin kina kiranta yar iska,iskancin me tayi miki toh zan sabama miki wlh in bazakima dan”uwanki Fatan alheri ba juz keep ur mouth shout tunkafin na saba miki wawiya kawai…”,Yafada cikin Fushi.

    Saurin mikewa tayi tana kuka ta Wuce zuwa dakinta,Ummi dake zaune batace komai ba,Hajiya ce ta kalli Abbi tana Fadin”Wai ni kabiru Meye dalilin da yaran nan basu son Auren nan,kodai ba diyar kirki bane…? Ummi tayi Saurin taran hajiya tana Fadin”Wlh bs diyar kwarai bace Hajiya,Yarinyar kwata kwata batayi kama da…”

    “Aisha…..”Abbi ya katseta da tsawa yana kallonta,shuru tayi da bakinta tana Jin wani daci aranta,Bai kara mgana ba ya tashi ya haye sama ammh daga yanayin kallon da yayimata Jikinta yayi sanyi,tashi tayi tabi bayanshi batare data kara cema hajiya komai ba,.

    Hajiya tabe baki tayi ta mike tana Fadin”Allah ya kyauta…”Daga haka ta shige dakinta Ranta fes Domin Dama babban burinta shine su Saleem suyi aure tagaji da ganinsu haka ba iyalai.

    Shiko Abbi yana Shiga daki sai ga Ummi ta biyo bayansa tana Shigowa ya tasomata yana Fadin”Haba Aisha meyasa kike haka? ke yanzu Abunda kikayi Yayi kama da Abunda uwa tagari zata aikata,kada kimanta kema kinada Diya mace,in aka aibatata zaki ji dadi? kada ki manta Allah shi ke shirya wanda yaso ya batar da wanda yaso,nasan kuma kina da sani kan hakan bayan karatunki na Shari”a low kina da karatun Addini daidai gwargwardo,why kika aikata haka?

    Yafada yana kallonta kur da ido ganin yadda jikinta yayi sanyi ne yasa ya juyamata baya yana Fadin”Kin bani mamaki Aisha,wlh ayadda na sanki mai hankali da hangen nesa banzata zaki ki bada goyon bayan Saleem yayi jihadi ba,baki Tunanin in ya aureta ya natsarta da ita,dani da ke dukkanmu munada lada? Gaskiya ban zan boye miki ba u already disoppoiting me Aisha…”

    Yafada Yana jadda kalamansa,Kukane ya kwacemata ta isa gareshi ta rumgumosa tana Fadin”Kayi hakuri yallabai,wlh nakasa sarrafa zuciyata ne na ganin Saleem ya auri yarinyar nan, da Duniya tagama saninta afannin rashin tarbiya da kamewa mezan cema yan’uwana da kawayena? wlh Abun kunya ne babban Amtsayinka na mai mutunci aji mun hada zuru”a dasu,sai ma afara zargin kila kwadayin Dukiyar mahaifinta ne ya Tsolemana ido…

    Tana Fada tana Sheshshekan kuka waigowa yayi yana rikota gefen gado ya zaunar da ita yana Fadin”kalle ni nan Aisha..”kai tsaye ta dago tana kallonsa hannunsa ya mikamata ta kama kafin yace”Tun sanda kika zamo mata nake mika miki hannuwa na domin ki kama,yazama bango da majingini gareki,kuma har gobe zan cigaba da mikamiki ,Toh yau gashi na kara mika ,mi ki ki kama ki damke yazama kariyarki har gobe kiyama ki kuma saka aranki indai Dan dani Kabir na haifa tare da Aisha ne bazai zamo gafalalle ba,sai da ikon Allah,na yarda da zencenki na za”a ce ko muna hangen Dukiyar mahaifinta ne,yes Alhaji Abdulmalik yana da tarin Dukiyar da baisan yawanta da karshenta ba,ammh wlh tallahi Aisha Dukiyarsa bata taba tsolenmun ido ba,mena nema na rasa,akwai Abunda bazan iya mallaka bane anan Duniyan…?Babu shi to kisa aranki Da zuciya daya na yarda da wannan auren,ki kuma toshe kunnuwanki daga zencen mutane,dama wasunsu dayawa basu son akullah alheri,ki kuma yi kyakyawan zato ga Danki,kinsan Abunda zai aikata da wanda bazai aikata ba,don Allah ki Cire wannan Tunanin azuciyarki kisama auren nan albarka kuma ki Rufe kofar da wani zai kawo kushen wannan Auren don Allah….,”

    Yafada yana kara damke hannunta hawaye ne suke shatatamata kawai sai tafada kan kafadansa tana Fadin”Na yarda kuma na saka musu albarka…Allah ya sanya alheri,ka yafemin yallabai,Akullum ina alfahari da samun miji gwarzo kamar ka,lokacin da na nemi kauce hanya sai kayi saurin dawo dani,Allah yabani ikon Yima biyayyah har karshen Numfashina,Allah kuma ya Shiryamana Zuru”a….”Da Ameen yayi ta karba bayan ya sanya hannu yana Sharemata hawaye yake Fadin

    “Toh bar kukan hakan,Fushi ya kare ko…”Yafada yana dariya Kirjinsa ta fada tana Rufe fuska wai ita kunya,yar dariya yayi yana Fadin”A’eesh dita har gobe bani da kamar ki AISHATUL HUMAIRA…”Yafada yana Mata rada akunne,Rumgumeshi tayi itama tana mai rada akunni,nidai nayi waje Tunda dai naga ma”auranta sun daidata kansu dole na ja Siraran kafafuna zuwa waje😂

    ____________________

    Tundaga Ranar Ummi ta fauwalama Allah komai ta karbi Auren saleem da hannu biyu,wanda harshi sai da takira tana mai Tsiyan yana Fushi da ita kwaso rantsuwa yayi yana bata hakuri,dariya kawai tayi tana sanyama auren albarka,aransa bai amsa da Ameen ba,don cewa yayi ai dama baki sakko ba Ummi,don ba auren gaske bane,na Ramuwa ne kawai na awannin kadan,ammh duk da haka bata makara ba😂

    Saleema ko kwana uku takara takoma mkranta bayan taga gidan gabadaya anhada kai babu mai goyon bayanta,Ummi ce toh itama yanzu tabi bayan mijinta,Hajiya kuwa batama sauraran mutum indai ta Fahimci zai kawo wata sukane game da auren Saleem,shiyasa ta tattarara kayanta Takoma mkranta,kuma tayi alqawarin ko bikin yatashi wlh bazata zo ba,indai da wannan Jinin Turawan ne.

    Ita ta kira ya marwan ta sanar dashi,wanda yaji Abun kamar almara,nan da nan ya hau Shafin instergram,ya bude shafin Malik malik,nan yaga badala kala kala nata,Tunda abokan aikinsa sunsha Tuka jirgin data ke ciki ita da Amintattun Escorts dinta,ammh shi bai taba katari da shegiya ba,duk da yasan lbrinta ba boyayyiya bace,anan nema yake ganin Jiya da misalin karfe 2:00pm jirgin daya tashi daga Abuja zuwa Amurka tana ciki wai tatafi tarin karama yan kasuwa sani da Duniya gabadaya ta Shirya akasar ta Amurka,irin hotunan data daura da shigarta Abun ba kyan gani,nan da nan zuciya ta debi Marwan ya daga waya ya kira Ummi yana Kumfan baki tana gani Saleem zai auri wannan Shegiyar yar iskan yarinyar.?

    Ashe Abbi na kusa yako karbi wayar yayima Marwan din Fata fata daga karshe ya bishi da Nasiha mai kashe jiki,shima din jikinsa yayi sanyi Domin yasani Shi da Allah ya Shiryar dashi bayafi sonshi bane,haka Allah yake Abunshi shi zai raya wanda yaso,kuma ya kashe wanda yaso,shi zai Shiryar da wanda yaso,Allah shike da ikon Umartan Faruwan Abu nan take kuma ya Faru ko ya kasance,ya sanar dashi ko ya manta kissan Annabin Allah Annabi Yunus wanda yayi Fushi da mutanensa ya baro garinsu zaiyi hijira ya Shiga jirgi sai aka ga jirgi na tangal tangal,nan masu jirgin sukace akwai wanda yayima Allah laifi acikin Jirgin,nan suka ganoshi suka jefasa cikin kogin,shikuma Allah nan da nan ya Umarci Kifi data hadiyeshi,ya sanar dashi Allah yace acikin alqur”ani mai girma ba domin Annabi Yunus yanemi gafarar Allah ba da ya dauwama acikin cikin kifin nan har ranar tashin kiyama.

    Hakuri yayi ta bama Abbi,domin Hakika duk Abunda ya Fada gaskiya ne, domin sau nawa zamu dunga aibata yan”uwanmu da jifansu da munanan kalamai a maimakon murika musu Fatan Shiriya tunda munsan babu mai batarwa,kuma ya Shiryar sai Allah,kuma hadisi ne ingantattace sau tari Mutum zai Fara aiki irin na yan Aljannah sai yana gabda mutuwa aikinsa ya juye yakoma na yan Wuta kuma ya mutu ya shiga Wutan,ALLAH YA KAREMU…Kuma sau tarin mutum yana ta aiki irin nan yan Wuta kwatsam sai yakoma aikin yan aljannah,kuma ya mutu alokacin ,sai kuma ya Shiga Aljnanah,to mai zamu ce da haka? musani Aibata wani mumina ba dabi”a mai kyau bane.domin babu wanda yasan tsakanin Ubangiji da bawansa…
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!