Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Sunan mahaifinsa BASHIR,Wanda ya kasance Lacra ne,a babban jami”ar gombe kafin Allah yamai Rasuwa ya rasu yabar matarsa *HAJIYA HAFSAT* da Da’nsa kabir,wanda yake aji uku ababbar jami”ar Usmam DanFodiyo Universtiy Sokoto inda yake karantan Sciology Sanin Hallayyar dan Adam kenan.

    Mutuwar mahaifinsa ta girgiza sa ammh haka ya fauwalama Allah komai ya maida hankalinsa akaratunsa,Shigansa jami”ar ne suka hadu da *ABDULMALIK SA”AD wanda shi yake karanta Business Admistration,ammh dayake hostel dinsu daya yasanya sukayi abota sosai Duk da shi Abdulmalik din dan jahar katsina ne akaramar hukumar MALUMFASHI.

    Kammallah karatunsu shiyayi sanadiyar raba zumuncinsu domin Shi kabir daganan Burinsa dama Aduniya ya ganshi yana sanye da kakin YA’N SANDA,nan da nan yasamu nasarar Tafiya *POLICE STAFF COLLAGE JOS PLEATUE* makarantace dake horar da manyan ya”n sanda mussaman wadanda aka dauka daga matakin Degree,shekara daya yayi ya Fito amtsayin *ASP*

    lokacin ne,kuma yayi Aure da yar”uwansa AISHA,Wacce ta kasance diyar wan babanshi ne uwa daya uba daya aka hadasu zumunci lokacin itakuma tayi candy,sai ya taho da ita nan ZARIA inda akayi posting dinshi,har yayimata cuku cuku ya sanyata a ABU Kongo,tana karantar Sharia Low,Shekaranta biyu tagama lokacin kabir yasamu chanji wajen aiki,zuwa kano suka tararra suka koma inda tadora daga Karatunta a low sch kano,Shekararta ta Farko Allah ya azurtata da ciki,inda ta Haifi danta na Fari Wato *MARWAN* Shekaran Marwan biyar Aduniya ta sake haihuwan Danta na Biyu Wato *SALEEM* Lokacin kuma Kabir yana matsayin *DEPUTY COMMISSIONER OF POLICE* Na jahar katsina.

    Sai da Saleem ya shekara Hudu Aduniya kana aka haifi *SALEEMA* wanda daga ita Allah bai kara bata haihuwa ba,kuma bawai don ta tsayar ba,Allah ne ya tsaidamata,Tunda daga ita har kabiru,suna bukatar ya”ya sosai atare dasu lokacin ta kamallah karatunta na low school ta Fito da sakamako mai kyau sai Kabir ya nema mata aiki ababban kotun jaha dake katsina nan da nan tafara aikinta amtsayin Lauyan gwannati.

    Tun Marwan na dan karami yake da sha”awan Zama matukin jirgin sama wato pilot,shiyasa yana gama secondry sch dinsa Iyayansa suka Turasa Kasar Russia,domin karantan Abunda yashafi Tukin jirgin sama,wanda zai dauki kimanin shekaru biyar achan,lokacin Saleem da Saleema,duk suna Nagerian Turkish Acadamy Abuja,Saleem na jss2 ne,Saleema na primary 4,ko lokacin tafiya Marwan Hajiya hafsat mahaifiyar Kabir taso ta nuna gaddama ammh iyayan suka lallasheta suka nuna,kamar yadda suka gini da boko to suna Fatan suma iyalansu sun san ilimin Addini hade dana boko,wanda malami na mussaman garesu,mai koyar dasu karatun Addini,Saleem dai ya sauke alqur”ani Tuni,Sauran littafai yake bita yayinda Marwan yasa wasa har kaninshi yazo yawucesa.

    Tun bayan haihuwan Saleem da tasowarshi mutum ne mai kulafuncin iyayansa,mussaman ma Abbansa,wanda suke kira Abbi,duk inda zashi yana makale dashi shiyasa dayawan abokan mahaifinsu sunfi sanin Saleem akan Marwan saboda shi nanike yake da mahaifinsa,shiyasa ko affice zashi dashi yake zuwa tun yana karami saleem yake jinjinama masu sanya kaki kowani iri,lura da ganin yadda mahafinsa ke kokari da fadi tashin kare hakkin al”ummah,Tun Abun na bashi sha”awa haryazo yana burgesa,ammh baitaba jin zai iya zama kamar mahaifinsa ba,shi arayinsa yafison zama *ENGINEARING*

    Lokacin dayayi Candy lokacin ne mahafinsa yazama Commissioner of police na jahar katsina,shikuma ashekaran ne yasamu addmission a ABU ZARIA inda yake karanta Chemical engenearing,Ammh duk sanda suka samu hutu yana dawowa gida ko kuma ya Wuce kauye kumo wajen Kakarsa wacce suke kira da Hajiya babba,ko yaje da niyyar yin sati,to dakyar zaiyi kwana biyu,ya wuce katsina saboda yadda basa shan inuwa daya da Hajiya babban,saboda sa idonta,shikuma tsokana da neman Fada itakuma ba hakuri sai suyita bugawa har sai ta gaji ta kira mahaifinsa awaya tana kuka tana Fadin ya kira dansa yasanar dashi ya barmata gida ko wlh ta fita ta kira samari majiya karfi awatsamatashi zuwa waje,Cp kabir sai ya hau bata hakuri nan da nan sai yakira saleem ya Rufeshi da fadan Maza yatattara kayansa yakoma mkranta,haka zai tatattara ya wuce katsina in ko taga yadade baizo ba ta dinga mita kenan tana cigiyarsa wai duk yafi iyayansa son zumumci.

    In yakoma katsina hutu duk inda mahafinsa zai sanya kafa,shima zai sanya,Hardai Abbansa ya bude baki ya tambayeshi koyana Sha”awar zama kamar shi ne”Girgiza kai yayi kafin yace”Ko daya Abbi,kawai kuna burgeni ne kona ce kuna bani sha”awa bama kuba,duk wasu masu kaki dake kokarin kare hakkin mutane da kuma martaba kasarsu,suna burgeni Abbi..”Tundayaji haka daga bakin dansa ya tabbatar da cewa Allah yabashi da mai hikima da kwazo,kuma yasa aranshi ko bajima ko ba dade,sai Saleem yazo yana sanar dashi ya sanyashi aikin dan sanda,saboda yadda yasan komai na mahaifinsa ya sanya ya saba da yawa daga cikin sargent da Inspectors din,wata rana ma in zasu pertrole yakan bisu,suje tare koda bazai yi komai ba,ya zauna amota yana charting Ko Vidion call shida ya marwan,wanda yake tsokananshi sa *INSPECTOR*

    Yana Final year dinshi Ajami”a Incident dinshi da *MALIKA MALIK..* yafaru,Wanda Ranar ana partrole ne atsakanin Titin shiga katsina zuwa Dutsenma,wanda ake binciken mota zuwa mota saboda masu Fitar da makamai ta bodar katsina,shine fa Saleem ya bisu lokacin yana da Shekara 24 Ne Aduniya,yazama saurayi sosai,duk da kana kallonsa zaka Fahimci alokacin yanada kurciya,Tunda ga lokacin da Abun yafaru Saleem yaji bakincikin da baita shiga ba,ya shigeshi dalilin mganganun Malika,wanda sune suka sauyasa daga yunkurin zama injiniya zuwa yunkurin zama *DA’N SANDA*

    Ko barci yake Abun na Fadomai arai,saboda yadda yasanya Abun ranshi,ko abinci kirki bayaci koda yakoma mkranta ga karatu ga Damuwa,duk sai kafin su kare Final exams,dinsu sai yayi rama daya koma gida haka iyayansa suka tasashi da tambayan meke Faruwa dashi ammh yaki sanar dasu komai,Lokacin daya je yasamu Abbi da mganar Shiganshi aikin yan Sanda,yayi Farinciki ya Rumgumesa yana murna da hakan bai tafi Police staff collage ba sai da yadawo service kan lokacin kuma ya sanya wani Dan sanda mai suna inspector sale,wanda yakasance ya yarda dashi sosai shiya sanya amtsayin wanda zai binciko masa lbrin malika malik,Tunda farko har karshe bayan nan,kuma yasakashi amtsayin wanda zai dinga bibiyan duk wani motsinta.

    Tafiyarsa police staff collage Jos,cike yake da jarumta da kuma buri,in akace buri toh ana nufin RAMUWA domin yayi alqawari sai yasaka malika kuka da idanuwanta,sai ya azabtar da ita,sai tayi kukan zuciya Fiye da wanda yayi sai ya nunamata cewa ba kudi bane kadai martaba Aduniya ba,Dan adam ma kanshi Abun darajawa ne,Saleem bai da aboki ko Amini,saboda shikanshi bai yarda dakowa bane,Duk duniya bayan iyayansa sai yan”uwansa bai iya zama yayi dariya dakowa ba.

    yana da taka tsantsan da Duniya,miskili ne sosai mara mgana da Fara”a,ammh kuma yana da barkwaci in yaso,musasaman shida sakonsa saleema,wanda in yadawo hutu,itama tazo andinga kwamawa kenan,har hutun ya kare kowa yakoma inda ya Fito Ummi kuwa har saita gaji da raba Fada kamar mayaka,ammh bai hana anjuma ka gansu tare,Ya marwan Ya dawo Nagaria,shekara biyu kenan,yana Lagos yana aiki saboda yanayin aikinsu ashekara baifi yazo gida sau uku ba.

    Shekara Biyu Saleem yayi yafito amtsayin ASP Lokacin kuma aka zana sunan mahaifinsa amtsayin *ASSISTANT INSPECTOR GENERAL OF POLICE* Shikuma Saleem akayi posting dinshi zuwa kankara dake garin katsina saboda yadda yake da kwazo baima shekara ba yasamu karin girma zuwa *DSP bai Rufe wata Shidda ba yasamu karin girma zuwa *SP* Wanda lokacin ne mahaifinsa shima yasamu karin girma zuwa * DUPUTY INSPECTOR GENERAL OF POLICE*,Suka tattara suka koma Abuja,duka iyalanshi harda Hajiya babba wanda dakyar ta yarda takoma don tace tafi sabawa da kumo.

    Yana da Shekara 28 Aduniya yasamu karin girma zuwa *ACP* akayi posting dinsa zuwa babban headquater yan sanda ta jahar ZAMFARA,wanda ko wata baiyi da samun karin girman ba,Allah yayima IGP rasuwa alokacin, nan da nan aka zama sunan mahaifinsa wato KABIR KUMO amtsayin INSPECTOR GENERAL OF POLICE* na kasa baki daya,inda suka tararra suka koma cikin katon gidansu mai kama da aljannar Duniya dake garki Abuja.

    lokacin ne kuma dukkan zati da haiba ta cikakken Namiji ta bayyana ga Saleem,wanda ya girma da buri da kuma Ramuwa ga Malika,shekaru biyar din nan duk yayi su ne cikin Shirye Shiryen Ramuwa ga Malika,kuma daman yanzu Ne lokacin daya dace ya aiwatar da kudirinsa,yasanar da kudirinsa gaban kowa da kowa ne,mussaman Hajiya babba,saboda Abbi yadauki Abun da muhimmanci,duk da shi Abbi yataba sanar dashi mahaifin malika tsohon abokinshi ne,zununci ne yayi Rauni tare kuma haduwa datayi Wuya.

    Ayanzu haka Saleema na aji uku a jami”ar Bayero University kano,tana karantar medicine tazama budurwa itama sosai,kuma Tana da Saurayinta *ABUBAKAR SADEEQ*Wanda ake cemai Sadiq dana ne ga wanda suke ya”ya maza da IG Kabir kumo,ammh mahaifinshi yadade da rasuwa kusan ma rikonsa Duk hajiya babba ce tayishi kuma duka wahalan karatunsa Abbi ne yayishi harzuwa yau dayake Matakin Controller,domin ma”aikacin costumer ne,yana Abia yana aiki shima bai cika zuwa gida sosai ba.

    Dashi ne kadai nasan Saleem nada kayakyawan alaka,sosai domim ko Hutu yazo daki daya suke kwana,ammh koda wasa Saleem baitaba sanar dashi Abunda ke ransa ba ko damuwarsa,duk sun shaku da juna sosai,sai dama Sadeeq din ya Furta soyayyarsa ga saleema ne ma yasa yadaina shigemai saboda gudun raini,dayake kuma shi Abun shi zuwa ne,Ranar dayake jin barkwamci kaf,gidan nan sai sunji ya gunduresu musssaman ma sufara tsiyarsu Shida hajiya wanda baya mutuwa kamar cin kwan makauniya.

    Tuni Sadeeq ya Fahimci Saleem nada damuwa,yayi tambayan Duniyan nan,ammh Saleem yacemai babu komai,domin yayi alqawarin babu wanda zaisan Abunda ke ransa sai ya aiwatar da Abunda ya kudirta Shekara da Shekaru,Saleem yana da zuciya sosai da kuma tsantsane ya tsani mutum wanda baisan darajan manya ba balle kuma wanda baisan darajan mutane ba,Yana da tsanani a kan ra”ayinsa in yakafe kan Abu mawuyaci ne kikaga ya dawo ga Abun nan,Kallon daya zakamai ka Fahimci ko yana cikin kunci ne,saboda baya gayyatoma kanshi Fuskar dariya ko Rahama akallon farko,sai ka zauna dashi ,yana da Kawaici da hakuri,ammh baya kaunar mutum mai cin zarafi mutum dan”uwansa,Lokaci daya Malika tasamu girbin tsana mafi girma aransa,wanda ko barci yake yana mafarkinta sai kaga ya farka yana Fadin *MALIKA MALIK..*Sai na rama..”Sai daga baya sai ya Fahimci tsabar yadda yasa ka Abun ranshi ne,kuma ya fahimci Abun bazai taba gushewa ba,sai ya nunama malika iyakarta,bai gama jin ya tsani rayuwar kudi da wayewa ba,sai da yaji duka Tarihin rayuwar malika yaji yakara tsanarta da kuma kyamatanta,da duk wasu hallayanta,kana yayi tir da Mahaifinta domin bai bi Turba mai kyau b wajen samar da ita kanta Malikn ba,,kwata kwata ba macen aure bane,ba macen mutumci bane,Aranar dayasamu lbrinta yakwana yana Tunanin mafita

    Ada yaso ya Ci ubanta batare da alakar aure ta Shiga tsakaninsu ba sai ya duba da ita malika bazata damu ba,domin dama bata daraja kanta ba, balle tadamu don wani ya banzarta da darajanta,babban Abun damuwar mutumcinsa da kuma mutumcin Family dinsa,tare da tarbiyan da Abbi da Ummi suka basa,mezai ce musu in har ya aikata wani barna,wanda bai kamata ba tabbas wajen Ramuwa,shi zai kashe kansa bayan yabarma zuru”rsu abun fada na har abada,shikuma yayi watsi da mutumcinsa,don duk Duniya babu Abunda Saleem yafi darajawa kamar LOKACI DA kataba MUTUMCINSA.

    shine dalilin da Yasa yayanke shawarar aurenta duk da shikanshi in ya tuna hakan sai ya tsani kansa,ammh bashi da mafita ne sai ta hanyar aure,yadda zai ci ubanta dakyau bayan ya nunamata cewa duk wanda yataba kakinsa ko yaci zarafin wani ko yataba mutumcinsa wlh tallahi bazai taba kyalesa ba.

    Baya da ra”ayi zama agidajen gwannati wanda take ba ma”aikatan ta, gidanshi ya siya wani Dan daidai mai dauke da Flat biyu sai haraban farfajiya wajen adana motoci,nan bayan Headquater su ne,a anguwn Birnin ruwa.

    Wannan Shine.

    ________________________

    *WACCE MALIKA MALIK..*

    “””*ALHAJI ABDULMALIK DAN KASUWA* Shine asalin sunan mahaifinta wanda ya kasance bakatsine wanda ya Fito daga jahar katsina A karamar hukumar * MALUMFASHI*.

    Alhaji Abdulmalik,yataso ahannun kakarsa ne ta bangaren uwa,sakamakon maraya ne,duka iyayansa sun rasu Tun yana karami,ya taso ahannun kakarsa mai suna INNARO,wacce ita silam sangarta da kuma rashin kwaba da Alhaji Abdulmalik yataso dashi tun yana yaro,sakamakon gidansu irin gidan gandun nan,kowa Abunda yaga dama Shiyakeyi,gabadaya gidan yayi suna arashin tarbiya da Sanin mutumcin manya kawunanshi ma haka sukeyi shiyasa shima yataso awannan Turban,inda Allah ya taimakeshi innaro batayi wasa da karatunsa ba,dayake kafin mutuwar mahaifinsa dan kasuwa ne sosai yana da Abun hannunsa,to tun da aka raba gadonshi innaro take juyamai dayake itama irin yar Duniyan nan ne babu Ruwanta duk wata kasuwa dake ci ranaku duk tasansu,to dashi take mai hidima har ya kammallah sakandiri sch dinshi ya wuce jami”ar Usman DanFodiyo University inda yake karantar Business Admistration,domin tun yana karaminsa yana da burin zama gawurtattacen dan kasuwa,wanda zai tara kamfonino ya dinga harka Da turawa duniya tasanshi.

    Zuwanshi mkranat ne,suka hadu da IGP KABIR KUMO,Har sukayi abota na tsawon lokacin da suka dauka suna mkarantar dayake kuma dukkansu kowa kwaro ne adepartment dinshi,shiyasa sukayi zarra,amakarantan kowa yasansu,ko alokacin Kabir yana yawan yimai Fada in yaga sun Fita ammh lokacin sallah yayi kowa yatashi yana barin jikin zuwa masallaci,ammh banda shi,toh ganin kabir nayimai Fada ne yasa yafara kokarin gyarawa ammh na ganin ido ne,indai basa tare,Abdulmalik bai damu da yin sallah akan lokaci ba,wani lokacin sai yazo barci zai hada su duka gabadaya,ga shi bashi da ilimin addini,ko kadan ko sallar ma nashi akwai gyara,shidai kawai Babu Abunda yasani sai yayi karatu yazama yawani mai kudi ,duniya tasanshi yayi gina gida mai kyau da tsari,ya kuma auri mace kyakyawa kullum burin Abdulmalik kenan

    gama karatunsu shi yaraba zumuncin dake tsakaninsu,domin tun suna gabda gamawa Kabir ya lura sam Abdulmalik yarage sakamarmai Fuska kuma yarage shigemai kamar da,saboda yana mai Fada da nasihan yabi Duniya ahankali,shiyasa da suka gama mkranta bayan Kabir yatafi police staff jos sau biyu sukayi waya da Abdulmalik inda yake sanar dashi yasamu schoolarship daga gwannatinsu,zai tafi kasar England achan zai yi master dinshi,fatan alheri Kabir yayimai,toh Tundaga lokaci babu wanda ya sake neman kowa domin Abdulmalik na zuwa kasar England ya chanza layi kuma baida contact din kabir din Shiyasanya basu kara jin juna ba.

    Zuwanshi kasar England itace mafarin komai ba,domin Tunda Abdulmalik ya Shiga cikin Turawa shikenan Burinshi yakaru,yayi budewar ido sosai mussaman da mata,sai dai Abu dayane Allah ya tsareshi baya neman mata,sai dai iyakarsa ya tsaya iya Romance da Abun da ba”a rasa ba,ammh bai yarda ya zama mazinaci ba,yayi kokarin maida hankalinsa kan Abunda ya kaishi har ya kammallah master dinshi,akuma shekaran ya dora da phd dinsa duk akan harkan kasuwanci,akuma alokacin ne yafara aiki da wani kamfanin Turawa na sarrafa takalma,ko shekara baiyi ba akamfanin suka samu lambo yabo,saboda yadda ya jawo musu kasuwa da suna sosai aduniya Tuni Abdulmalik yaji kanshi yayi sama balle da kamfanin ta shiryamai taron godiya tare da wasu kyautan kudade,da kuma dorashi amtayin Md na kamfanin alokacin.

    Juliyat tana daya daga cikin ma”aikatan wannan kamfanin,wanda Tunda tasaka idonta akan Abdulmalik taji duk Duniya babu wanda takeso sama dashi,ganin yaki bata fuska sai tayi ta amfani da kissa da kissina irin na mata har yafara kulata da sunan aiki,sunyi tsawon wata Shida suna Abota kafin ta rikide takoma soyayyah mai zafi,basu Rufe Shekara ba sukayi aure,wanda dalilin haka sai da yayi alqawari da iyayan Juliyat cewa bazata taba chanza addini ba,kuma ya yarda saboda shikanshi ilimin Addinin bai gameshi ba balle yagane illah dayayima rayuwarsa.

    Sunyi aure tatare a gidanshi wanda kamfani ta mallakamai,watan su goma da Aure Juliyat ta haifi yarta mace,wacce tasha wahala sosai wajen haihuwarta,wanda sai da akayi mata C.S cikin ikon Allah juliyat batayi tsawon rai ba don ko Abunda ta haifa bata gani ba,Allah yayimata rasuwa,mutuwa data girgiza Abdulmalik sosai,kwanaki akayi ana shagali kafin abunne gawan Juliyat,itakuma Jaririyar data haifa sai ya mikata ga mahaifiyar Juliyat wato MADAM DORA,ta riketa kafin yadawo daga Seminar da zashi wanda kamfaninsu taturashi har kasashe uku,zai dawo nan da wani lokaci,ta karba tana kuka domin yarinyar babu inda tabaro uwarta Juliyat,ranar da zai tafi ya sakamata Suna *MALIKA*

    _Ammh ta hanyar nuna min kauna da soyayyarku wajen Siyan *MALIKA MALIK* Akan Naira 200 kachal👌,ta wannan account Nombar, *0552179550 JAMILA UMAR GTB,sai ki Turo Shaidan biya ta wannan nombar *09069067488* ko kuma katin waya na MTN,shima sai ki Dauki hoton katin aturo kai tsaye ta wannan Nombar *09069067488* Sai kun zo ina maraba daku masoyana.._

    *Karku manta da garabasanmu mai son Siyan Biyu KISHIN MATA,na HAFNAN,300 ne kachal👌shima zai iya Turo ta nombar bankin dana bada ko katin waya na MTN ta nombar saman dana bada, ko kuma kai tsaye ku Tuntubemu ta wadannan Nombobin domin karin bayani*…

    _plz and plz zan Roki wata alfarma masu yiman VTU,Ko Tranafer don Allah su bari gamai bukatar Siyan Littafin malika malik,kai tsaye ya Turomin ta account Nombata 0552179550 JAMILA UMAR Gtb,ko kuma kai tsaye Amin mgana ta Wannan Nombar 09069067488,Aturo creadit kai tsaye bayan andauki Hoton katin,ina maraba daku masoyana na gaskiya_

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!