
Maleeka Malik
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
1
"""Da misalin karfe 11:20pm na daren Ranar jumma"a Akan Titin dake tsakanin Dutsenmah da katsina wacce take gabda shiga katsina.
Adaidai kan Titin akwai yan Sanda wadanda suke patrole awajen,Suna tsatsaye ne Gefe kuma ga motocinsu guda biyu akallah yan sanda zasu kai su Biyar kowannesu, sanye da uniform dinsu bakake,da ganin kayan jikinsu basai ka tambayesu ba,zaka gane dukansu inspector ne,domin basu da kowani Rank ajikin kakin nasu,dukkansu fuskarsu sanye da Hula p-cap,da bakaken safan hannu sai manya manyan Tociloli masu bala”in haske kamar ta yan fashi,wanda in aka dallareka dasu, sai ka dakata saboda bala”in haskenta,Duk motar da tazo wucewa sai sun tsaidata sunyi bincikenta saboda tsaro dakuma bincike, wanda daga sama suka sameshi saboda masu shiga da fita da mugayen makamai wanda ake Shigo dasu daga bodar katsinar aboye.
Motocine jere guda goma sha biyu dukkansu 11 din iri daya ne Corollahx sai babban ciki wacce tafita dabam itace Range cover baka ce gabadaya motar Tinted ne gaba da bayanta kowacce mota bayan motan an saka musu Nomba mai dauke da Tambarin MALIKA MALIK1 har zuwa na 12,gudu suke ta shararawa bisa Titin Dutsenma zuwa katsina,Tundaga nesa Yan sandan suke Dalle su da fitila Tunda sukaga yadda suke gudun ganganci bisa Titi.
Sai da suka kawo gab kana suka fara slow,motar Farko Tana tsayawa Suma na baya suka tsaya,Wani inspector ne ya karisa kusa da motar yana kwankwansa glass din motar,sai da aka bata lokaci kana aka zuke glass din motar.
Wani Inyamuri ne zaune a mazaunin Direba sanye da wasu kaya brown colour Riga da wando da alamu dai kamar Uniform ne,Kallonsa yayi daga sama har kasa kamar yadda Dan Sanda ke karemasa kallo,Cikin gadara ya furta”Lafiya mallam.?.”Dan Sandan yayi mamakin jin Hausa abakinshi don akallon Farko bai yi kama da wanda yakejin Hausa ba.
Gyara tsayuwa yayi yana fadin”Zamu bincika duka motocinku ne,daga ina kuke da tsohon daren nan? kuma kuke gudu ba bisa ka”ida ba..?.”Yafada yana leka motocin dake bayansa Dan ware ido Direban yayi yana fadin”kai kana ko da hankali kasan motocin waye ka tsare kuwa? dariya Dan Sandan yayi yana fadin”Wannan bashi ne Abun da na Tambayeka ba,tambayanka nake daga ina kuke,? bai mai mgana ba kawai sai ya kada kai yana fadin”Zaka shiga mtsala matukar MADAM Ta fahimci meke Faruwa..”Yafada kai tsaye.
Tana kishingide abayan motan Tana Karanta jaridar Dailytruth bata ma Fahimci meke Faruwa ba,sai zuwa chan Ta fahimci motar da suke ciki ta tsaya cak,cikin mamaki ta dago da kanta bayan Ta kauda jaridar lokaci daya take fadin”Joy Har mun iso gidane..?daga gaban motan ya amsa mata da fadin””A”a madam yan Sanda ne suka tsaidamu wai zasu binciki motocinmu…”Wani zabura tayi tana fadin”What…? wani banzan Dan sanda ne ya tsaidamin motoci,i swear sai na koya masa hankali sai ya gane ba”a yima MALIKA MALIK wargi..”
Tafada cikin Fushi kafin ta balle murfin motan ta fice,Doguwa ce sosai kirarta irin kirar Cocacola ce,Tana sanye da Riga da wando blank and white,tayi Stoking ta ciki ta Kama gashin kanta da band daga tsakiyar kanta bayan ta saki jelan Ta baya,Kafanta sanye da wani takalmi sawu ciki mai tsini sosai blak colur ne,shima Doguwar Fuska gareta wanda kusan Rabinta yake rufe dawani bakin glass,mai kyau da tsari,yadda ta fito cikin Fushi ya sanya duka bodygourd dinta suka Firfito,suna take mata baya cikin Fushi Tanufi wajen Dan Sandan da suke Rigima da Direnba Tun Farko.
Ganin yadda suka nufosu ne yasa yan sandan dasuke gefe suka kariso daidai lokacin data kariso Gabansu ta tsaya suma Bodygourd din nata,sukaci burki abayanta Gilashin idonta ta cire tana fadin”Waya sakaku ku tsare ma mutane motoci,?kuma don Rashin kunya harda motocina,cikin shashancin ku,Uban waya sakaku,waye shugabanku C.P ko IGP gayamin Shiyace ku tsare motocin MALIKA MALIK..? tafada cikin Tsawa Tana binsu da wani matsiyacin kallo.
Jin sunan da tafada ne yasasu mamaki dama sun dade suna jin lbrinta da irin Rashin mutumcinta gashi yau sun gamu da ita,saboda kwarjinta da haibanta dukkansu sun kasa maida mata da martani balle wani cikinsu yayi magana.
Yana cikin motar yan sand’an Ta patrole video call yake Shida YAYA MARWAN.. Hira suke sha suna dariya,ta madubin motan yake hango Abunda ke faruwa,saurin yima Marwan sallama yayi Shiko yana tsokanarshi da INSPECTOR.. Cikin hanzari ya katse wayar lokaci daya yana bude murfin motan ya fito,dogon Namiji ne,sanye da bakaken kaya Riga da wando harda wata rigar sanyi wacce takaimai har zuwa gwiwansa,ba”a iya ganin Fuskarsa saboda ya sanya p_cap ne kuma ya sauko da ita ta Rufemai rabin Fuska,cikin takun isa ya nufi wajensu ammh duka hannuwansa suna,coge a aljihun wandonsa ne.
Tana ganin ya Fito daga motan Ta nufeshi tana fadin”AU shine wannan yabaku umarnin ku Tsaremin motoci ko,toh yau zan koyamasa Hankali in yana neman na goro ne,ko na Sigari bazai kara yunkuri sawa Atsareni ba…”Tafada Tana karisawa garesa Tana zuwa batayi wata wata kawai ta kifesa da mari jikake Kau…!Saboda zafin marin saida ya fito da duka hannuwansa daga aljihu har wayarsa ta fito ta fadi bai sani ba,Hannu biyu ya sanya ya dafe Fuskarsa yana binta da kallon mamaki,miyau ta tsirtamai kafin tace”U Stupid kai ne kasa wadan nan kananun karnukan naka su tsaremin motoci ko,Dama ku yan sanda ba mutane bane,all of u,are Monkey and bakusan komai ba sai tsaida motoci kuna karban na goro dana Sigari Tunda daman ba Abunda kuka iya sai shaye shaye da yima mata Fyade ko,?Toh as From Today bazaku kara tare wata mota ba, joy bring d box Now…”
Tafada ciikin Tsawa Da hanzari wanda aka kira ya nufi mota ya dauko wata yar karamar akwati yazo gabanta wani abu kawai ya danna sai Ga kudi suka bayyana dollars ne Shimfide batai wata wata ba ta dumbuza ta watsamai Afuska tana fadin”Take d money ayi na goro dana Sigari banzaye Yan”iskan kan hanya kawai,wlh i hate aikin yan sanda hardama Uniform dinsu all of dem basu da wani amfani a akasarmu sai lalacewa,Next time ka sake sakawa Atsare motocin MALIKA MALIK..Kagani wlh sai na saka an batar dakai Rubbish…”Tafada tana juyawa kamar walkiya Sukuma suka take mata baya.
Tunda ta kifamai mari da wadandan mugayen maganganun datake fada suka daskaran dashi gabadaya Tunaninsa da zuciyarsa ta tsaya lokaci guda,wani bakin ciki da takaichi tare da wani Fushi suka lullubeshi,kowacce kalma in ta fada sai yaji kamar saukan aradu,tacima kakin yansanda mutumci tayi jam”i gabadaya ta hada kenan harda mahaifinsa mafi soyuwa garesa,wanda yabada komai nasa domin Taimakon kasarsa,yan sanda da basa barci domin kare dukiyan al”ummah da lafiyansu sune take kira basu iya komai ba sai shaye shaye dayima mata fyade,kakin dayake burin yaga ya sanya ajikinsa Shitake kira Rubbishi…Ina!Da sake Tuni wani Bakin ciki mai hade da wani Tarnakin hawaye suka kwaranyomishi tana gabda da Shiga mota ya daga murya cikin Fushi da amo mai Sauti yace”” MALIKA MALIK…!SAI NA RAMA… …”yafada cikin wani irin amo,waigowa tayi kafin tayi danyi dariya tace”Ok start d game young police man..”Tafada kan Tafada mota,dukkansu kowa yakoma motarshi Suka tadasu suka wuce da gudun bala”i kamar zasu bankesu.
Suna Wucewa ya nufi mota yana fadin” Inspector Saleh take me to home now…”Yafada muryansa ya fara rawa saboda bacin rai lokaci daya ya bude gaban motan ya shiga,da hanzari Inspector saleh yayi mgana da sauran yan Sandan kafin shi ya nufi motar ya shiga mazaunin direba yaja sukahau kan titin da Sauri,Suma din dai cikin katsinar suka nufa adaren.
Anguwan LAYOUT suka nufa daya daga cikin anguwannin masu hali dake cikin katsina ta dikko Dakin kara,kofar wani makeken gida motar patrole ta yan Sandan tayi parking Tunkafin motar tagama tsayawa ya bude murfin motan, ya Fita da Sauri yarda yake tafiya kadai zaka gane yana cikin Fushi ne da Fusata.
Inspector Sale ya kalleshi yana kada kai,bai Fito daga motar ba, yamata kwana ya juya lokacin agogon dake hannunsa yake nuna karfe 1:00am na dare,shiko yana zuwa jikin get dinsu yasaka hannu ya shiga bugawa da karfi kamar zai tashi sama,megadi dake zaune gefe gyangyadi yafara dibamshi kamar amafarki yaji bugun get,da hanzari ya mike sanye da yake da uniform irin na yan mopal,koda yaji bugun bai razana ba,Nufar get din yayi yana Fadin”Who iz dis..?
Tsaki yaja kafin yace AM SALEEM FREEKING KABIR KUMO.. Yafada ransa na kuna,da hanzari jikinsa na rawa da bari yabudemai karamar kofar yana Fadin”Am sorry sir did know….”Baigama Rufe baki ba ya wucesa Fuu kamar iska baki ya rike yana binsa da kallo,domin a iya saninsa Saleem baida dabi’ar shariya.
Maida kofar yayi ya Rufe yana Fatan Allah yasa koma miye ya Faru mai dadi yadda yake alfahari da wanda zai gaji Yallabai.
Babbar kofar da zata sadaka da babban falon gidan Abude take,sakamakon ansan komai dare zai dawo yana Shigowa Falon babu kowa yadda yake tafiyane zai ankarar da mai kallonsa kamar agauce yake.
- Maleeka Malik – Chapter One 1,873 Words
- Maleeka Malik – Chapter Two 3,015 Words
- Maleeka Malik – Chapter Three 3,113 Words
- Maleeka Malik – Chapter Four 3,042 Words
- Maleeka Malik – Chapter Five 3,203 Words
- Maleeka Malik – Chapter Six 3,533 Words
- Maleeka Malik – Chapter Seven 3,111 Words
- Maleeka Malik – Chapter Eight 3,499 Words
- Maleeka Malik – Chapter Nine 4,167 Words
- Maleeka Malik – Chapter Ten 3,582 Words
- Maleeka Malik – Chapter Eleven 2,828 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twelve 3,291 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirteen 2,928 Words
- Maleeka Malik – Chapter Fourteen 3,897 Words
- Maleeka Malik – Chapter Fifteen 2,669 Words
- Maleeka Malik – Chapter Sixteen 3,688 Words
- Maleeka Malik – Chapter Seventeen 3,831 Words
- Maleeka Malik – Chapter Eighteen 4,205 Words
- Maleeka Malik – Chapter Nineteen 4,470 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty 4,185 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-one 4,343 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-two 3,394 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-three 3,599 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-four 4,539 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-five 4,875 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-six 3,527 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-seven 4,169 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-eight 2,135 Words
- Maleeka Malik – Chapter Twenty-nine 1,927 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty 2,658 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-one 2,317 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-two 2,390 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-three 2,771 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-four 2,362 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-five 3,139 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-six 3,106 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-seven 2,449 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-eight 2,347 Words
- Maleeka Malik – Chapter Thirty-nine 5,212 Words
-
Zafin Kai Chapter 2: 2 Samirah ta rasu ne bayan da azabar tayi masu yawa ta girmi tinani da dauriyarsu harma da duk jarumtar da suke tinanin sunada ita, Cikin tsakiyar dare guraren…
-
Zafin Kai Chapter 1: BismillahirRahmanirRaheem Allah yabamu ikon gamawa lafiya 1 Gyara tsayuwarta tayi ahankali tana sauke idanuwanta daga kallon dattijuwa kuma tsohuwar matar dake…
-
Nihaad Chapter 3: ~ 3 8months earlier… Zaune yake saman farar kujera dake kusa da dakin mai gadi, ya fi awa daya xaune wajen, lkci lkci yake goge zufan fuskarsa da…
-
Nihaad Chapter 2: ~~ 2 Dumbin gaisuwa da fatan alkhairi xuwa ga iyayen gidan Khaleesat’s Palace, my die hard fans🥰😍 Su Hajjaju Chamo me gwala-gwalai duk da jarin ya…
-
Nihaad Chapter 1: ~ 1 All thanks to Allah SWT for giving me the ability and privilege to present to you this book. My mother Hajiya Hajarah Allah ya karo farin ciki da kwanciyar…
-
(Download) NiDa Ya Ahmad – Complete by AsmaLuv: ABUJA A hankali manya manya motoci ke tafiya saman titi jiniya ce ta kardaye saman layin da xai sadaki da gwarinfa acikin garin abuja daga ganin motocin xaka…
