Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    Ɗazu da azahar mahaifin Alh. Usaini ya je hotel ɗin da su ke shi da Salwa. He got the shock of his life lokacin da ƙanin Usaini ya ƙwanƙwasa ƙofar su ka ji muryarsa yana cewa.

    “Ƙar ki taɓa ƙofar nan. Kada ki buɗe.”

    Ransa kuwa ya sosu fiye da tunani. Dama can barazana yayi a reception har aka rako su ɗakin. Saboda haka sai ya yi wa ma’aikacin hotel ɗin inkiya da hannu ya yi magana.

    “Yallaɓai baƙo ne da kai a ƙasa.”

    Da sauri Alh. Usaini ya ce “kada ka bari ya hawo gani nan saukowa. Ƙanina ne. Dama mun yi waya na faɗa masa ya same ni a nan ɗin.”

    Ya ɗaga yatsa ya gargaɗi Salwa “zan fita kuma na rantse da Allah idan ki ka min halin jakancin nan naki ki ka fito sai na ɓaɓɓalla ki. Wawiya kawai. Dalla can gafara in wuce.”

    Ta murguɗa baki tana yatsine fuska “jaka tana can gidan jaki mai furfura.”

    ‘Yau kuma jakuna mu ka koma’ Baban Alh. Usaini ya jinjina kai yana zancen zuci.

    Ran Alh. Usaini ya ƙara ɓaci sosai ya ɗaga hannu ya zabga mata mari.

    “Iyayena ki ke zagi Salwa? Iyayena?”

    Kumatu ta fara riƙewa ta ce “Ni ka mara?” Sai kuma ta cakumu wuyansa “wallahi ba ka doki banza ba. Yadda kake jin kana da gata nima ina da shi.”

    “To gatan naki ya zo yanzu don uban mutum.”

    Daga nan sai sautin duka da kukan Salwa da kuma maganganun Alh. Usaini. Baban ya nuna wa ma’aikacin hotel ɗin lallai ya buɗe kafin ayi kisan kai. Da yake tsoron afkuwar ɓarnar tafi yawa akan privacy ɗin costumer, dolensa ya buɗe. Su ka yi mummunan gamo. Tsananin fushi da ɓacin rai ya sa Alh. Usaini yiwa Salwa dukan biredi. Ita ma kuma ta samu nasarar jifansa da abubuwa don har goshi ta kumbura masa.

    Sandarewa ya yi a lokacin da idanun sa su ka sauka cikin na mahaifinsa da aka buɗe ƙofar ɗakin. Ya saki Salwa a gigice kamar wanda ya ɗauki garwashi ya kama rantse-rantse.

    “Wallahi biyo ni tayi Baba. Duk abin da ka ke zato ba haka bane. Sam ni ba na harkar mata.” Ya sassauta murya sosai “Salwa faɗa masa gaskiya. Ai babu komai tsakanin mu ko?”

    Maimakon ta faɗi gaskiya sai ta zaɓi amfani da wannan damar. Zubewa tayi a ƙasa ta kama kuka.

    “Mene ne tsakanin ku?” Baban ya fara tambayarta sai ya fasa ya dubi wanda ya rako su “kwanan su nawa a nan?”

    “Kwana uku ne.”

    “Shike nan. Kana iya tafiya.”

    Bayan ya fita Baban Alh. Usaini ya buƙaci Salwa ta bashi numbar wani nata su yi magana. Tana jin haka idanunta su ka raina fata, ta kasa motsawa. Sai ya kalli ɗansa. Yana iya ganin tsananin tashin hankali a tare da shi.

    “Ka karɓar min numbar wanda zai zo ya karɓeta ta koma gida.”

    Jikinsa na rawa ya tashi ya buɗe handbag ɗinta ya ciro wayarta. Wayar ma a kashe sai da ya kunna sannan ya bata don ta buɗe wayar.

    Jikinta ya yi la’asar don ta kula tsoron babansa yake yi shi ne ta ce “Ka bani abin da nake buƙata in tafi da kaina.”

    “Ai baki isa ba. Wallahi gara a zo a ɗauke ki in san na rabu da ƙaya.”

    Tsawa taji daga sama kafin ma ta sake yin gardama daga babansa
    “Ke! Bani number na ce yanzun nan. Ki tabbatar wadda za ki bani mai shiga ce.”

    Da ka ta karanto masa numbar Babanta saboda Ahmad dai baya nan sannan bata ga alamun za su wanye lafiya ba idan tayi ƙarya. Waje ya fita da ya yi dialing numbar. Salwa ta matsa kusa da Alh. Usaini kafin ya dawo.

    “Kaga ka bani abin da nake nema na tafi tun kafin ya dawo. Ban san me yake shirin yi ba kuma ba na burin sani.”

    “Hummm…kin makaro. Ƙaryar da ki ka yi masa da alama ke za ki kwana a ciki don na san dole ya kira baban ki a zo a ɗauke ki.”

    Wajen rabin awa ya share yana wayar kafin ya dawo. Umarni ɗaya ya basu kafin ya fita.

    “Zan dawo gobe in sha Allah. Ina fata idan na zo na same ku tare. Idan ka bari ta tafi Usaini to ka tabbatar babu ni, babu kai wallahi.”

    Yana gama magana su ka fice. Alh. Usaini ya ƙulle ƙofar ya dinga naushin bango kamar mahaukaci. Salwa jiki na ta tsuma ta ɗora hannuwanta akan kunnuwanta tana hawaye. Gabaɗaya a tsorace take kuma tayi imani motsin kirki idan tayi sai ya sake jibgarta.

    *
    Ko awa guda ƙwaƙƙwara Abban Salwa bai iya sake yi ba ya biyo hanyar Kano tare da ƙannenta. Saboda munin labarin da ya samu sai ya kasance ko murnar ganinta da aka yi bai yi ba. Mutumin da ya kira shi ya faɗa masa cewa ya same su da ɗansa su na rigima harda doke-doke. Shin yaushe lalacewarta ta kai haka ba tare da ya sani ba? Yanzu ya ƙara yarda duk wanda ya sayi rariya dole ya ga zubar ruwa. Cikin dalilai huɗu da Manzon Allah SAW ya hori musulmi da aure, guda ɗaya tal ya duba lokacin auren Mami wato kyau. Ƙwarai ta haifa masa kyawawan yara abin nunawa ta wannan fannin. Amma a halin yanzu hatta mazan ba wai ya sami yadda yake so bane daga gare su. Kawai dai ana cikin yanayin da babu gara ba daɗi.

    Takwas da arbain na dare a Kano tayi musu. Ko masauki bai nema ba ya kira Baban Alh. Usaini. Nan ya faɗa masa sunan hotel ɗin ya ce ya jira shi zai taho shi ma yanzu. Da su ka haɗu sun jima su na tattaunawa game da halin ɗan yau da abin da son zuciya ke kawowa. Baban Alh. Usaini shi ne ya kawo shawarar lallai a ɗaura musu aure. Wannan ne zai sa har ƴan baya ma su shiga taitayinsu.

    Matsanancin tsoron da ya kama Salwa da Alh. Usaini a yayinda iyayensu da ƴan uwan su su ka shigo ɗakin da su ke ba zai faɗu ba. Banda ƙannen Salwa biyu akwai wasu biyun na Alh. Usaini da Babansa ya taho tare da su.

    *

    “Aure???”

    Salwa da Alh. Usaini su ka yi tambayar da sun riga sun san amsarta ga iyayensu a lokaci guda. Kamar ba da mutane su ke ba. Babu wanda ya tanka musu. Sai ma Limamin Masallacin Khamsa Salawatin kusa da hotel ɗin da aka yi wa iso ya shigo ya zauna. Kafin wani lokaci ɗakin ya kasance babu masaka tsinke a dalilin mutanen da su ka shigo ganin ƙwaf. Labari ya bazu tun daga reception za a ɗaura aure. Sai ga mutane su na buɗe ɗakunan su suna tahowa kallo. Video kuwa harda masu yin live a social media handles ɗin su. Salwa sai wani ɗakin aka shigar da ita. Abu kamar almara. Aka ɗaura aure bisa sadaki naira dubu hamsin lakadan tsakanin Salwa hauka mai son ma so wani ƙoshin wahala da Alh. Usaini shugaban ƴan hassada da baƙinciki.

    Aure ne wanda iyaye su ka yi alƙawarin yin baki ga ƴaƴan nasu idan su ka kuskura su ka rabu.

    Bayan an watse ne Abban Salwa ya miƙa mata sadakinta a hannu. Shi ne take ta roƙo da magiyar ya yi haƙuri ya sa a sauwaƙe mata.

    “Aure an yi kenan in sha Allah. Daga nan in kun fita ku yanki daji ku fara bokanci ko bori tunda silar haɗuwar ku kenan.”

    Kalaman sa sun yi mata zafi. Yanzu kuma bokanci yake kira mata kamar ba ƴar cikinsa ba?

    “Daddy ni ce kuma zan yi bokanci?^”

    “Meye a ciki? Boka mushiriki, mai zuwa wajen boka ma mushiriki abu na Ɗanjuma da Ɗanjummai.”

    Su na ji su na gani iyayen su ka tattara su ka watse abin su bayan dogon gargaɗi akan dole su zauna tare. Su ka tafi tare inda Baban Alh. Usaini ya ce yau a gidansa za su kwana. Sannan gobe zai kira duk wanda ya dace ya san da auren domin su gabatar da junansu a gaban shaidu.

    Salwa kuka kamar ranta zai fita, Alh Usaini ko kallonta bai tsaya yi ba. Ya riga ya yi wa kansa alƙawarin zama da ita amma fa sai ta ɗanɗana kuɗarta. Son da yake yiwa kuɗin babansa bai kama ƙafar tsanar da ya yi mata ba. Ita ta ja masa komai. Ta saurari hukunci.

    ***

    Gaba na faɗuwa Taj ya kama ƙofar ɗakin Kamal. Hannun nasa har wani sanyi ya yi kamar ba a jikinsa ba saboda tararrabi.

    Bayan asuba su ka taho asibitin saboda kira da su ka samu akan tashinsa babu sauran magagin allura. Kowa ya kama shiri sai Alhaji ya ce su yi haƙuri a dinga tafiya in batches.

    “Kun gan mu unguwa guda idan mu ka cika musu wuri irin na jiya ba za su ji daɗi ba. Idan wasu su ka dawo sai wasu su tafi.”

    Ba dai haka su ka so ba amma sun san tsarin nasa shi ne daidai. Nan ba a jinya ba kamar tamu ƙasar ba. Sannan babu damar zama idan ba layin ganin likita ba. Maimakon su yi ta zama a mota ana jiran juna gara kowa ya kintsa a cikin nutsuwa.

    Taj da Hamdi da iyayensu mata ne su ka fara tafiya tare da Alhaji. Idan sun gama sai Ahmad ya taho da wasu. A hanya aka dinga mayar da zancen yadda ƴan uwa da abokan arziƙi su ka ƙarbi zancen abin da ya faru da aka kikkira su a waya. Don tausayi, sosai an tausaya kuma an jajanta. Amma fa hatta waɗanda su ke matsayin ƙanne a garesu babu wanda bai nuna ɓacin rai akan shirun da aka yi ba. Alhaji Babba ma cewa yayi zai zo amma ba don su ba sai don Kamal da kuma Yaya da tayi musu halacci.

    “Duk wannan bai isa ba Taj sai da ka san yadda kayi ka juya magana a wajen Jamila (Amma) ka sa ta kira ni tana yi min rashin kunya. Ƴaƴan arziƙi da rufin asiri aka san su.”

    Taj ya kyaɓe fuska har sai da Hamdi tayi murmushi. Kunya ta kama ta da ta kula ashe Mama na kallonta lokacin da take kallonsa ita ma.

    “Yanzu Alhaji ni ba ɗan arziƙi bane? Kuma dai maganar gaskiya ku ne fa ku ka hana mu yin ƙarya.”

    Alhaji ya bashi amsa da cewa
    “Eh, amma kuma duk mai hankali ya san akwai lokutan da ake yi wa gaskiya kwaskwarima don a sami zaman lafiya.”

    “Mix ɗin ƙarya da gaskiya fa kenan Alhaji.”

    “Dama duk tsayin shekarun nan bakin ka bai mutu ba Tajuddeen?”

    Me za su yi kuwa banda dariya. Tun farkon sanin ciwon Kamal sai yau ne aka samu sukunin yin farinciki daga zuci ba iya fatar baki ba kaɗai.

    Sai da su Alhaji su ka fito daga wajen Kamal sannan Taj ya taho zai shiga. Hamdi dama tun shigowarsu ta tafi wajen Yaya. Idan ƴan uwan sun sami nutsuwa za ta je su gaisa.

    “Rufe ƙofar” Kamal ya umarci Taj bayan ya amsa masa sallama.

    Wani babbasarwa Taj ɗin ya kama yi kamar bai ji shi ba. Kamal ya yi murmushi.

    “Da dai ka rufe kada kukan garada ya cika wa mutane kunne.”

    “Kuka za mu yi kenan? Abin babba ne”

    Taj ya rufe yana juyowa don duk a zatonsa Kamal wasa yake yi sai kawai yaga ya fashe da kuka. Kuka ba na wasa ba. It was coming from the dept of his heart. Kukan tsoro, ciwo da farinciki. Taj ya ja kujera ya zauna a gabansa. Bai ce masa komai ba sai da ya kula cewa ya fara jin sauƙin damuwarsa.

    “Was it that hard?” Ya tambaye shi a yayinda yake miƙa masa tissue.

    Nannauyan numfashi Kamal ya sauke sannan ya ce “it was. Taj I was so scared. Na zata zuwa yanzu na zama tarihi. Kai kuma ka shigo kana wani ɓata rai. Ni da cuta kai da shan kunu.”

    Abin da yake ransa ya amayar duk da ya yi matuƙar ƙoƙarin danne ɓacin rai a fuskarsa
    “Kamal kayi min adalci? Ni ne fa. Haba!”

    “Don Allah kada ka tuhume ni akan shirun da nayi. It was extremely difficult for me. Bana son ganin kuna yi min kallon tausayi ko a dinga koke-koke.”

    “Ka ga sharrin kallon movies ko? Wannan wane irin banzan tunani ne? Da kuma ka tafi fa? Happiness da ace ba ka sami kidney ba fa? Sai dai na zo na tarar da mummunan labari? So kayi ka tafi ka barni da tunanin irin halin da ka shiga yana haunting ɗina?”

    A raunane Kamal ya ce “ba haka bane.”

    “To yaya ne?” Bai san ya fara hawaye ba “I was happy Kamal. Ina dariya ina nishaɗi saboda na auri wadda nake so kuma na samu Alhaji ya yafe min. How could I be happy. I shouldn’t…”

    Kamal ya marairaice masa “Da ka zauna mun yi kukan nan kawai mun share. Wannan mitar bata da amfani. Laifi ne na riga nayi kuma na karɓa. Haba Happy na Happiness.” Ya kama murmushin ganin ya soma samun kansa “nace kai ma ka na kallon finafinai kenan ko? Na ga sai wani blaming kanka kake yi irin abin nan na masu ɗan uwa.”

    Cije leɓe Taj yayi yana harararsa. Daga ƙarshe ya yi kwafa gami da jinjina kai.
    “Za mu haɗu.”

    Daga nan hirar ta koma kan tambayar jikin Kamal da yadda yake ji a yanzu. Motsi kaɗan zai yi Taj ya dinga tambayarsa me yake so. Shi kuwa tambayar da su Alhaji su ka yi ta kakkaucewa amsa masa ya samu ya yi.

    “Happy wa ya bani ƙoda?”

    Alamun alhini Kamal ya fara gani a tattare da Taj shi yasa ko da ya wayance da cewa
    “Ban fahimce ka ba? Masu alhakin faɗa maka ɗin shiru su ka yi don su jiƙa min aiki?” Ya tashi zai fita “bari na kirawo maka Alhaji.”

    “Ka ajiye maganar wasa don Allah. I need…I must know.”

    Allah Ya sani bai so haka ba amma kuma rashin amsawar ba komai zai janyo ba sai tashin hankali ga mara lafiya, wanda kuma ko kusa ba a son haka.

    “Kamal, Yaya ce tayi donating. Yaya mahaifiyar Hamdi.”

    Da wani irin yanayi Kamal ya zabura sai da Taj ya danne masa kafaɗa.

    “Yaya fa ka ce. Let me go.” Ya doke hannun Taj “ka sake ni mana. Taj ba fa wasa nake ba. Ka ƙyaleni na tashi.”

    “Ina za ka idan ka tashi? Wai ma so kake aikin ya buɗe ka mayar da hannun agogo baya?”

    Kawai sai Kamal ya sanya tafukan hannunsa ya rufe fuska ya fashe da kuka. This time around fassara kukan nasa ma abin wahala ne.

    “She is fine fa Happiness. Wallahi jikinta da sauƙi sosai.”

    “Me ya faru? Na kasa fahimtar komai.”

    Taj took his time ya labarta masa abin da Mubina ta sanar da shi da Hamdi jiyan bayan komawarsu masauki. Guilt ke damunta har lokacin shi ne ta zaɓi sanar dasu yadda aka yi Yaya ta fara tunanin binta daga hirarsu a jirgi. Hatta recording ɗin saƙon da ta bari ya fayyace masa.

    “Na kasa murna Happy. I feel…Subhanallah” idanun Kamal cike fal da hawaye ya rirriƙe Taj “ka kai ni wajenta don Allah ko na tafi da kaina.”

    ***

    Ɗakin yayi shiru sai sautin kuka da yake fitowa daga wayar Ahmad ta speaker. Whatsapp call ya kira ta wayar Sajida. Ita da Zee da Halifa babu wanda ba ya kuka. Hamdi ma kukan take taya su. Yayinda Abba Habibu da Yaya murmushi su ke yi kawai wanda babu komai cikinsa illa dauriya. An ɗaga mata gadon ta yadda bayanta yana jingine da filo.

    Muryar Halifa ce ta fito daga wayar yana shessheƙa “don Allah a mayar da kiran nan bidiyo mu ganta.”

    “Yanzun nan kuwa” Ahmad ya saita wayar akan Yaya bayan ya juya call ɗin.

    Yaya tayi saurin gyara yanayin fuskarta gami da faɗaɗa murmushinta.

    “Kun ganni fa. Wallahi naji sauƙi sosai. Ku kwantar da hankalinku.”

    Hamdi ta ƙara musu da cewa
    “Da a ce da matsala kun san ba zan ɓoye muku ba.”

    “Wai me ya kai ki gidan mutane da sassafe Sajida? Nan yanzu ba na jin bakwai ta yi.” Abba Habibu ya yi maganar yana duban agogon wayarsa. Awa biyu ne tsakaninsu da Nigeria. Tara saura ƴan mintuna yana nufin a can bakwai ne saura.

    Sai lokacin Anti Zinatu da take ta aikin matsar ƙwalla tayi magana. Tun dare da Abba Habibu ya sanar da ita halin da ake ciki ta karɓi lambar Safwan da dabara a wajen Zee. Ta sanar da shi komai sannan ta buƙaci ya kawo Sajidan wajenta a lokacin da za a sanar da su. To ashe shi ɗin ma mutum ne mai saurin ruɗewa. Daga wayar nan bai sake yin wani abin kirki ba, ko bacci ɓarawo da ƙyar ya sace shi. Ai kuwa ana sallame asuba ya ce ta shirya su taho.

    “Ni dai yanzu alfarmar da zan roƙe ku don Allah kada wanda ya tayarwa Innata hankali. Ku bar zancen nan har sai na dawo in sha Allahu. In lafiya ta samu yadda ake so ma ba sai ta sani ba.”

    Shawarar Yaya rabi ce ta sami karɓuwa a wajen Alhaji. Batun a rufe maganar kuma ya ce ba zai yiwu ba.

    “Sadaukar da ƙoda babban abu ne wanda a halin da muke ciki yanzu da wuya maganar ta ɓuya. Idan wani bai fađa ba, wani zai iya faɗa. Saboda haka za mu jira ki sami sauƙi sai mu auna mu gani shirun da faɗar gaskiyar wanne ne yafi ko kuwa Habibu?”

    Tattaunawa su ka cigaba da yi cikin lumana da girmamawa na ɗan lokaci. Hamdi ta ji duk ta takura. Zantukan nasu sun shafe su amma bai kamata ta tsaya musu a wajen ba. Tunanin dabarar ficewa ta fara yi sai ga kiran Bishir ta wayar Hajiya. Ya faɗa mata yana ƙasa tare da Mubina. Wai tana son tafiya Madina ne yau shi ne ta zo tayi musu sallama.

    “Amma don ragon azanci ta kasa faɗa mana mu taho tare?”

    Dariya taji ya soma yi yayi magana da zolaya “Hajiyarmu ta gargajiya kenan. Yanzu duk ɓarin hawayen da ta gama yi a asibitin nan baki gane komai ba?”

    “Me aka yi?” Kafin ya bata amsa ta soma murmushi “kai Bishir ka tabbata?”

    “Kin gano kenan” ya kama dariya sosai. Mubina dake gefensa ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin ɓoye murmushin dake neman kufce mata. Ta ji abin da yake cewa ta kuma gane me hakan yake nufi.

    Hajiya cewa tayi su hawo da sauri sannan ta zaga bayan Mama ta faɗa mata yadda su ka yi da Bishir. Baki ya kasa rufuwa da Mama ta fesawa kowa zancen. Yaya ma daga kwance ta taya su murna. Sannan ko kusa bata yi mamaki ba. A ganinta dama soyayya ce kaɗai za ta sanya Mubina biyo bayan patient har wata ƙasar.

    Alhaji da Abba Habibu ma sun nuna farinciki ƙwarai. Hamdi sai ta sake amfani da wannan damar za ta sulale ta gudu kafin su farga. Kamar haɗin baki ta na buɗewa Taj ya turo Kamal akan wheelchair.

    Hirar iyayen a take ta yanke sai tambayar me yake faruwa.

    “Wajen Yaya na zo.” Kamal ya ba su amsa da kansa.

    Murmushi Yaya ta yi masa da su ka haɗa ido “ai bai kamata ka fito a wannan yanayin ba. Taj da ba ka kawo shi ba.”

    “Nayi ƙoƙarin hana shi Yaya amma wallahi ya ƙi. Dole na kira wani Nurse shi ne ya ɗora shi a nan” ya nuna wheelchair ɗin.

    A daidai lokacin kuma Bishir da Mubina su ka shigo ɗakin. Hankalin Kamal ya yi gaba bai kula da su ba da farko. Ya ce Taj ya matsar da shi daf da gadon Yaya. Ya tura shi kuwa jikin gadon sosai. Kamal ya miƙa hannunsa na dama dake ɗauke da canula saboda ƙarin ruwa da ake yi masa ya riƙe nata hannun sannan ya kalli Abba Habibu.

    “Abba na riga na zama ɗan Yaya shi ya sa ban nemi izinin taɓa hannunta ba.”

    Abba Habibu ya gyaɗa kai yana murmushin nan nasa. Ragowar kuwa duka aka yi shiru ana sauraron Kamal.

    “Duk wahalar dake tattare da ɗaukar ciki da haihuwa a wurin mata a ƙarshe tana da riba Yaya. Za a kalli mace a kira ta UWA ko da ɗan ba a gabanta yake rayuwa ba. Su kan su mata abinda ya sa su ke jurar wannan wahalar komai tsananinta bai wuce domin samun wannan matsayin ba. Mace za ta zama mai cikakken iko akan wani bawan Allah da yake rayuwa da jinin jikinta.” Ya ja numfashi “Allah Yana biyan wahalhalun da ta sha akan ƴaƴanta da mafi ƙololuwar daraja. Ya bata martabar da babu mai kamo ta a wajen wannan bawa har ƙarshen rayuwarsu su biyun.” Ya yi murmushi idanunsa fal hawaye. Ko da ya ɗaga kai ya kalli Yaya sai hawayen ya zubo. Nata ma ya zubo…idan ka cire Alhaji, Abba Habibu, Ahmad da Taj, duka waɗanda su ke ɗakin sai da su ka zubar da ƙwalla.

    “Yaya wace daraja ki ke tunanin Allah Ya tanadarwa matar da ta bawa ɗan da bata da alaƙa da shi ta jini wani ɓangare na jikinta don ya rayu? Bayan kin san cewa wahala, azabar ciwo da fargabar me zai je ya dawo a dalilin sadaukar da ƙodarki ba zai mayar dani ɗan ki ba. Taki juriyar naƙasu ce a jikinki da lafiyarki. Babu wata riba ta kurkusa ko ta nesa don ban ga abin da za a biya ki da zai maye gurbin ɓangaren jikin ki da ki ka bani ba Yaya.”

    “Kamal ka yi shiru don Allah. Jikin ka babu ƙwari.” Yaya ta faɗi cikin kuka.

    “Yadda ɗa baya yin godiya ga iyayensa akan haihuwarsa da su ka yi, haka ni ma ba zan yi miki godiya akan kyautar da ki ka yi min ba. Alfarma kawai na zo sake roƙa domin Allah.”

    “Ina jin ka Kamal. Don Allah ka daina kukan nan.”

    “Yaya idan kina lissafin ƴaƴanki ki dinga farawa daga Kamaluddeen Hayatu don Allah.” Kuka sosai yake yi a wannan gaɓar.
    “Idan kina da sirri irin na uwa da ɗa don Allah ki yi dani.” Yaya ta gyaɗa kai.
    “Damuwa ko wacce iri ce irin ta uwa da ɗa kada ki tsallake ni.” Nan ma ta sake nuna amincewarta.
    “Buƙata ko wacce iri ce ta uwa da ɗa ki fara faɗa min tunda kin ga Halifa ƙarami ne. Su Hamdi kuma mata ne ma su rauni.”

    “To Kamal” Yaya ta amsa cikin kuka.

    “Idan su Sajida sun yi miki laifi don Allah kada ki ɓoye min. Ki rufa musu asiri a wajen Abba amma ki sanar dani. Zan yi mu su faɗa tamkar cikin mu ɗaya.”

    “Na sani Kamal, ko babu wannan abu ai kai me tsaya mu su ne.”

    Kamal ya girgiza kai “a da sai dai nayi kara, yanzu kuwa duk abin da ya shafe ki Yaya ya zama dolena.”
    Ku san sai a lokacin ya lura da tsayuwar Mubina a ɗakin. Sai ya yafito ta da hannu. Ta so cogewa amma Mama da kanta ta kaita kusa da Kamal ɗin.

    “Kin amince da zaɓina Yaya? Idan na auri Mubina ƴar mu ta farko in sha Allahu sunan ku ɗaya. Sunan ta…” ya kalli Hamdi yana jiran ta ba shi amsa.

    “Khadija.”

    “In sha Allahu sunanta Khadija.”

    Yaya ta rasa abin cewa. Tana gudun zaƙalƙalewa a gaban iyayensa. Gashi kuma ya tsare ta da idanu yana kallonta with so much adoration.

    Alhaji ne ya yi stepping in da ya ga ta kasa magana.

    “Ba ki ce komai ba game da zaɓin ɗan naki Yaya?”

    Yaya ta ɗaga kai a rikice ta kalli Abba Habibu tana neman agajin sa. Ita fa komai bambarakwai take jin sa tun shigowar Alhaji ɗakin nata. Ba ta son yin abin da zai sake janyo wa mijinta abin magana.

    Cikin nutsuwa Hajiya ta matso ta kama ɗayan hannun Yaya a yayinda ɗayan har lokacin ya na cikin na Kamal.

    “Ko ba ki karɓi tayin da Kamal ya yi miki bane na zama uwa a gare shi?” Ta haɗa hannuwanta biyu tana magiya “Don Allah ka da ki kasa yi masa wannan alfarmar. Kamar yadda ya faɗa babu zancen biya ta kowacce fuska tsakanin mu. Hakan raini ne ma akan girman abin da ki ka yi mana. Ƙara shi cikin zuri’arki ne kaɗai abin da za mu iya duk da cewa mu ne dai da sake samun riba.”

    “Don Allah ku daina magana irin haka. Domin Allah nayi.” Ta zame hannunta dake cikin na Kamal ta nuna ƙirjinta “Karamcin Ubangina a gare ni mai girma ne. Shi Ya nufe ni da zuwa a lokacin da Kamal yake tsananin buƙatar hakan ba tare da sani ko shirin wanin mu ba. Kuma Ya azurta ni da dakewar zuciya na cika umarnin ƙaddara. Ni da har yau nake tsoron allura sai gashi na kawo kaina inda za a yanka min ciki. Na fi ku riba wallahi. Allah Ya bani ikon ceton rai sannan Ya ƙara faɗaɗa ƴaƴana.” Ta sanya hannu ta shafa kumatun Kamal. Shi kuwa ya ɗora hannunsa akan nata ya lumshe idanunsa cikin farinciki.

    Maimakon kuka kuma sai farinciki ya mamaye ɗakin. Mubina ta kasa daurewa ta bawa Yaya haƙuri domin tana ganin cewa ita ce ta jawo mata zuwa nan ɗin.

    “Kada ki sake magana irin wannan Dokta. Mu duka mu na yin komai ne cikin tsarin Ubangijinmu. Ba ki yi min laifi ba amaryar ɗana.”

    Kunya ta kama Mubina. Ta koma kusa da Hamdi ta sunkuyar da kanta.

    Da jindaɗi Alhaji ya ce “Tunda abin ya zo da haka ku ba ni dama na yi mu ku karambani akan Baban Khadija da Maman Khadija mana.”

    “Innalillahi…” Mubina ta faɗi a kiɗime da jin furucin Alhaji tana mai ƙanƙame hannun Hamdi. Ita ma dai babu halin zolaya kunyar ce ta kama ta.

    “Abban Kamal ka yi shiru.”

    “To Alhaji mun ba ka dama.” Abba Habibu shi ma dai yana cikin jin nauyin wannan sabon lamari.

    Shi kuwa Alhaji dama da gayya ya yi. Yana so ne ya canja takun mu’amala a tsakanin su tun wuri saboda a sake sabon lale tun kafin su koma gida. Waya ya ɗaga a gaban su ya kira kawun Dr. Mubina, yayan mahaifinta. Ita kanta ba ta san inda ya samo numbar ba tunda bai tambayeta ba. Maganar su ta ƙarshe ita da shi sosai dai tun kwanciyar Kamal a asibiti ne inda su ka fara haɗuwa har ya ce ya san Marigayi mahaifinta.

    Ya fara da gabatar da kansa wanda da alamu hakan bai yi wa kawun nata wahalar ganewa ba. Daga nan ga mamakin dukkanin su ya ɗauko maganar su da Kamal. Ya soma yi masa bayanin rashin lafiyar sa sai kawun ya ce ya gane shi. Bai dai san cewa ɗan Alhajin ne patient ɗin da ta dinga roƙonsa har ya barta tahowa duba shi da yin Umra ba.

    “Tunda dai har an dace ya sami ƙodar, ina ganin kawai ta zauna ta ƙarasa ladanta. Ina fata ka fahimce ni.”

    A take Alhaji ya danna speaker yana murmushi sosai. Komai ya zo masa da sauƙi fiye da yadda ya yi tsammani. “Ƙwarai kuwa. Na saka ka a speaker a gaban iyalina, Kamal da ita Mubina. Zan so ka maimaita abin da ka ce domin nima dalilin kiran kenan. Ina son a san da zaman mu zuwa lokacin da Allah zai sa ya sami lafiya ya dawo gida.”

    Kawu ya maimaita “Ka fi ƙarfin haka Alh. Hayatu. Me yiwu wa ba za ka iya tunawa ba amma ni abin yana raina sosai. Mun taɓa zuwa wajen ka nema wa yaran wasu ƙauyuka kuɗin jarabawar SSCE har su ɗari da sittin da bakwai. Bayan ka biya ka ɗauki ukun farko ka biya musu kuɗin jami’a in full sannan ka sa mu ka yi alƙawarin ba za su taɓa sanin kai ne ba. Shi ya sa wasu lokutan taimako yake zuwa ga bayin Allah ta inda ba sa zato. Sadaka babban jari ce.”

    Alhaji ya yi ɗan murmushi kawai. Ɗan Adam ba ma’asomi ba. Kullum mu na cikin iyo tsakanin dai-dai da kura-kurai. Yawan tuba, ƙoƙarin fifita aikata ayyukan alkhairi da uwa uwa kyautatawa Allah SWT zato shi ne babbar maslahar rayuwa. Zai iya cewa a tsukin lokacin nan ya ƙara fahimtar rayuwa ta fuskoki mabambanta. Da fari ya yi karo da tsohon kuskurensa sannan yanzu ya gamu da tsohon alkhairi. FABI AYYI AALA’I RABBIKUMA TUKAZZIBAN

    Kawu kuma ya ɗora maganar sa.
    “Mubina ki zauna ki ƙarasa ladan ki har a sallame shi .”

    Mamaki tayi sosai “Kawu aikina fa? Kuma …” ta saci kallon su Ahmad “ba ya buƙatar zama na.”

    “Ai kuwa ki shirya domin kowa zai tafi ya bar ki da shi. Haɗa ni da Alh. Hayatun.”

    Jikin Mubina ya yi sanyi ƙalau har ta kasa motsin kirki. Zuciyarta kawai ke harbawa da daidai da fitar kalmomin godiya daga bakin Alhaji domin ya cire wayar daga handsfree. Bayan ɗan lokaci ya miƙa mata wayar.

    “Je ki waje ki amsa”

    Da sauri ta fita har lokacin tana riƙe da hannun Hamdi. Ita kuma ganin haka sai ta nemi zare hannunta. Mubina ta dube ta da raunin murya.
    “Raka ni don Allah.”

    *

    Shiru Mubina tayi tana sauraron Kawunta.

    “Alh. Hayatu ya ce zai sake kira na anjima kaɗan mu ƙarƙare magana. Idan komai ya tafi daidai in sha Allahu yau zan sauke amanar ɗan uwana, zan aurar dake ga mutumin da na tabbatar ki na so sannan ga dangin da nake fatan ba za su taɓa wulaƙanta ki ba.”

    “Amma Kawu…”

    “Na san ban shiga haƙƙin ki ba da na yanke wannan shawarar. Soyayya ta Fisabilillahi ce kaɗai ta saka ki kusan zaucewa akan yaron nan kafin ki tafi. Yanayin ki ya bani tsoro shi ya sa ban hana ki tafiya ba da ki ka buƙaci zuwa Umra ke kaɗai saɓanin yadda mu ka yi shirin tafiyar gida cikin ƴan uwa.”

    Kuka ta fashe da shi.

    “Ki bar kuka Mubina. Ina son amincewar ki ne domin yanzu zan tafi wajen Umman ki. Ki amince?”

    Da ka ta fara amsawa sai ta tuna ba ya ganin ta shi ne ta ce “Uhm” a hankali.

    “Allah Ya yi miki albarka.”

    Rungume Hamdi tayi bayan ta gama wayar. Hamdi ta dinga bubbuga mata baya saboda kuka ne take yi sosai. Bata taɓa zato ko da wasa akwai ranar da burinta zai cika akan Kamal ba. Ta fi karkata da tunanin cewa zuwa yanzu ya ma bar duniyar.

    “Ki daina kukan nan haka Matar Yaya. Ni ce ke sujjada zan yi domin wannan babbar falala ce daga Allah SWT.” Hamdi ta rarrasheta.

    “Nagode Hamdi. Abin ne duk wani iri. Kin ga ana shirin aurar dani babu kowa nawa.”

    “Gani.” Ta sakar mata murmushi “Don Allah ko da wasa kada ki taɓa yi min kallon matar ƙanin miji. Ƴan gidansu sun yi min tarbar ƴa kuma ƴar uwa ba suruka ba. Ina ganin rashin adalci ne zai sa mu kuma mu ɗauki kan mu da wani matsayi daban da na ƴan uwan taka.”

    *
    A cikin ɗakin kuma bayan fitar su Mubina, Kamal ya ce Taj ya mayar da shi ɗaki. A hankali ya juya wheelchair ɗin yana mai kulawa da dukkan motsin da zai iya janyo wa Kamal jin zafi.

    Sallama Kamal ya yi wa kowa. Da ya zo kan Alhaji sai cewa ya yi da Taj ya tsaya.

    “Na ji kana ta magana a hankali ga Alhajin ka tambaye shi da kan ka?”

    Taj ya yi turus domin gabaɗaya bai gane me Kamal yake nufi ba. Ya kuma san cewa tunda ya yi haka to akwai abin da yake ransa. Lokacin wana shi ya samu. Sai ya rama ɓoye-ɓoyen da aka yi masa.

    “Me ka ke son tambaya?” Alhaji ya zuba mu su ido don ya gano wayon Kamal.

    “A bar maganar Alhaji. Zan dawo idan na kai shi ɗaki.” Taj ya ɗan tura Kamal sai yaji kujerar ta turje. Kamal ya saki burkin tayar don kada su tafi. Ya yi kalar tausayi.

    “Ai gara ka tambaya yanzu saboda ni bana so ka tafi ka barni ni kaɗai.”

    Abba Habibu murmushi ya yi. It is obvious Kamal a matse yake da son jin manufar maganganun Alhaji a waya. Ahmad kam dariya yake yi sosai.

    Alhaji ya yi ƴar dariya shi ma
    “Kamal ina jin ka. Me Taj ya ke son sani?”

    “Cewa ya yi wai ya ji kamar ana maganar aure na.”

    Taj bai san lokacin da ya ce “Ni? Kamal yaushe?” Don bai yi tunanin tambayar da Kamal ɗin zai yi kenan ba.

    Inna ta shigar wa Kamal “Ai tunda ya ce ka yi kawai ka yarda cewa ka yi ɗin don a zauna lafiya.”

    Da gangan Taj ya ce “Shikenan to.”
    Ya kalli Alhaji “na ji kamar ka na maganar aure na.”

    Ya yi nasarar tunzura Kamal kuwa don bai san lokacin da ya gyara masa ba.
    “Aurenka kuma? Yaushe ka yi aure da har ka ke tunanin ƙari?”

    “Ƙarin aure kuma Allah na tuba ai ba abu bane mai wahala.”

    “To wai nufin ka Hamdi za ka yi wa kishiya? Happy akan su fa ni babu ruwana da dangantaka. Hamdi comes first yanzu. Da kai da mazajen su Sajida duk ɗaya ne a wajena. Kai suruki ne, ni kuwa ɗa ne ko Yaya?” Shi ma ya rama zolayar da Taj ya yi masa.

    Sai ga Taj da riƙe haɓa. Aiki ya biyo ta kan ma su gida.
    “Lallai ma! Happiness kada mu ɓata daga farfaɗowarka fa. Har za ka faɗa min kusanci da Yaya?”

    “Wannan ko shakka babu.” Kamal ya ce kai tsaye “kai ƴa kawai ta baka. Ni kuwa ƙoda ta bani. Akwai jinin jikinta a tare da ni. Tsakanin mu ma babu haɗi.

    Mayar da rigimar tasu aka yi abin dariya a ɗakin. Taj ya nemi taimakon Abba Habibu da Yaya ta gyaɗa kai tana supporting ɗin Kamal.

    “Abba ka na jin sa fa.”

    “Ƙyale su Taj kai fa ɗan maigida ne. Shi kuwa Kamal agolan gida ne, ka san su akwai rawar kai. Gida na hannunka. Duk yadda ka dama dole a sha ko ba a so.”

    Dariya aka sake yi inda Kamal da Yaya su ka ce basu yarda da wannan muƙami da Abba Habibu ya bawa Taj ba. A wannan halin Hamdi da Mubina su ka dawo. Taj ya ja Kamal su ka koma nasa ɗakin. Ahmad kuma ya mayar da Mubina da Hamdi hotel. Yayinda Alh. Hayatu ya cigaba da nasa shirin daga nan. Ƴan uwansa maza ya kira ya sanar da su shawarar da ya yanke. Su ka yi na’am da farinciki. Yaya Babba ya shiga gaba su ka haɗu da ƴan uwan Hajiya, wani abokin Alh. Hayatu da ƴan uwa shaƙiƙan sauran matan mutum ɗaiɗai sai gidan Kawun Mubina. Shi ma kafin zuwan nasu ya riga ya faɗawa duk wanda ya kamata. Ana idar da sallar la’asar wanda ya yi daidai da magrib a birnin Jeddah aka ɗaura auren a masallacin unguwa.

    Asibitin gabaɗaya ya kaure da murna. Ma’aikatansu waɗanda su ka san Kamal da Yaya su ma duka sun taya su murna sosai.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!