Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-nine
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Addu’a kam babu irin wadda bakunan ƴaƴan Alh. Hayatu ba su yiwa Yaya ba ta samun lafiya cikin ibadarsu. Hamdi ta zauna ta dinga yi wa Allah SWT kirari tana faɗin buƙatarta. Da ƙyar ta iya baro masallacin saboda shauƙin kasancewa a waje mafi tsarki kuma inda take da tabbacin karɓuwar addu’arta. Sai bayan isha su ka koma Jedda. Ana yi musu tayin tafiya masauki amma kowa ya ce sai sun ga isowar Abba Habibu. Ahmad da yake tracking tafiyarsu ya sami bayanin tsaiko da aka samu da su ka tsaya transit a Egypt sakamakon hazo da ya lulluɓe garin. Haka su ka kasance jugum-jugum ana ta tasbihi a zuci da fatar baki.
A can Bauchi kuma mahaifin Salwa bai san me yake faruwa ba sai da Ahmad ya kira shi a waya. Keɓewa ya yi daga ƴan uwansa ya sami wuri ya kira shi. Abban nata bai ɓoye masa rashin jindaɗinsa ba kuwa.
“Haba Ahmad. Kai da nake yabon hankalinka, ta yaya za ka bari har a kwashi waɗannan kwanaki kafin ka sanar dani?”
Ahmad bai yi mamaki ba. Dole ko wane ne yaji babu daɗi. Shi yasa ya zauna yayi masa bayanin dukkan abin da yake faruwa da gidansu. Baban Salwa ya jajanta masa ya kuma yi masa uzuri. Musamman da yace ya dakata ne daman yana jiran ganin ko zata dawo, kada yayi saurin tayar masa da hankali.
“Babu komai. Zan nemeta a waya. Idan ban samu ba ma akwai wani ɗan ƙanwata da zai iya yi min tracing ɗin layinta.”
“Allah Yasa a dace. Nima zan cigaba da kiranta.”
Suna tsakar sallama Baban Salwa ya dakatar da Ahmad ya yi masa nasiha mai ratsa zuciya.
“Ana canja abokin zama amma kaga iyaye? Iyayen ma musamman uwa, sai dai haƙuri kawai. Na san kana ƙoƙari kuma kana haƙurin amma ka ƙara domin neman albarka ba don ita Mamin taku ba.”
Ɗacin abubuwan da Mami ta aikata waɗanda suka kawo su wannan lokaci ya dawo masa amma basu bari ya ƙi amsar shawarar ba.
“In sha Allahu. Nagode”
Da haka suka yi sallama. Ahmad ya koma cikin ƴan uwansa a inda suka taru suna jiran isowar Abba Habibu.
***
Daga lokacin da Abba Habibu ya sauka daga jirgi zuwa yanzu da yake fitowa da ƴar jakarsa a hannu, gabansa ya faɗi sau ba adadi. Tunani iya tunani yayi amma ya kasa samun abu guda da zai iya cewa shi ne yake jin ya sami Yaya. Haka ya fito da sassarfa yana jan addu’o’i daban daban. Yana sako ƙafarsa waje ya ɗaga kai yana waige-waige. Abokin Ahmad ya sanar da shi cewa Alh. Hayatu zai turo a ɗauke shi. Shi yasa yake baza idanu ko zai hango guda cikin yaran nasa. Sai dai abin mamaki maimakon ƴaƴan, Alh. Hayatu ya gani da kansa yana tunkaro shi.
Wani irin abu mai zafi yaji ya tsirga masa daga tsakiyar kai har tafin ƙafa. Ƙafar ta zaɓi wannan lokacin taƙi motsawa kwata-kwata ma. Yana gani Alh. Hayatu ya cigaba da nufo shi amma ya kasa ɗaga ko da ɗan yatsa har ya iso gaban shi ya tsaya.
Da rawar murya Abba Habibu ya ce “Tun a waya na ce da Ahmad ya faɗa min gaskiya yace min da ranta.”
Alh. Hayatu ya gyaɗa kai da sauri “da ranta Habibu. Iyalin ka tana nan da rai.”
“To me ya same ta? Ni na san gagarumar matsala ce kaɗai za ta sa ka zo tarba ta a nan.” Abba Habibu ya furta helplessly.
Alh. Hayatu kasa magana ya yi, sai wata uwar kunya da ta mamaye shi. Abba Habibu bai yi ƙarya ba. Haka nan me zai kawo shi tarbarsa? Mutumin da yake ƙyama yau a dalilin matarsa yana yi masa kallon mafi girman daraja a cikin mutanen da yake tare da su.
Kafaɗar Abba Habibu ya dafa ya nuno masa motar dake jiran su
“Zo mu tafi Habibu.”
“Kayya da dai ka faɗa min me zan tarar da nafi samun nutsuwa.”
Ya kalli Alh. Hayatu da yanayi da yasa dole ya ƙara jin tausayinsa.
“Ganin ka a nan da tausasa kalaman ka a gareni sun fi faɗar min da gaba fiye da wayar da Ahmad yayi min jiya. Don Allah ina zamu je? Ko dai da gaske ne an kama ta cikin masu nakasar dake taho wa bara?”
Ba a nan Alh. Hayatu ya so sanar da shi ba. A wannan yanayin na tsananin firgici da yake gani a wajen Abba Habibu bai dace ya tsorata shi ba. Gudun tarwatsa labarin a bakin yara shi ne musabbabin tahowarsa. Sai dai kuma har ƙasan zuciyarsa shi ya san babu wani lokaci da ya dace ayi breaking mummunan labari ga makusancin wanda abu ya shafa. Ana faɗa ne kawai idan dama ta samu tare da addu’ar haƙuri da tawakkali. Ba tare da jan rai ko kwaskwarima ba ya sanar da shi gaskiya.
“Ƙoda ta bawa Kamal. Tana kwance a asibiti yanzu haka muna jiran farfaɗowarta.”
Ko cikakken sakan Abba Habibu bai ɗauka ba wajen fahimtar kalaman Alh. Hayatu. Sun yi masa dirar aradu mai ƙarfi. Ga wasu irin tambayoyi suna tsaruwa a kansa cikin karo da juna wurin son fara fitowa. Amma duk da haka sai ya kasa furta ko ɗaya a dalilin tunawa da wayar da Yaya tayi masa tana neman izini.
“Yaya jikin Kamal ɗin?”
Mamakin wannan tambaya Alh. Hayatu ya yi kafin ya iya cewa da sauƙi a hankali.
“To mu je” Abba Habibu ya ɗaga ƙafa yana mai danne tsananin tsoron da ya taso masa.
Sai da suka shiga mota Alh. Hayatu ya kasa daurewa ya ce
“Ba ka tambaye ni lafiyarta ba?”
“Ka manta ka ce min ana jiran farfaɗowarta?”
“Haka ne.” Ya faɗi yana jinjina kai “to amma ba ka tambayeni komai ba?”
“Za ta bani amsa da kanta idan ta tashi in sha Allahu.” Abba Habibu ya jingina bayansa da kujera cikin yaƙini. A yayin da wani ɗaci ɗaci ya dinga taso masa na tsoro sai ya dinga faɗin “Hasbunallahu wa ni’imal Wakeel”.
Ba su ƙara magana ba har su ka isa asibitin. Abba Habibu yana tafiya ne tamkar a mafarki. Yadda aka yi ya iso ƙofar ICU ɗin abu ne da ko an saka masa wuƙa ba zai iya faɗa ba. Bai ma san lokacin da Hamdi ta iso ba sai ji ya yi ta faɗa jikinsa tana kuka.
Iyalin Alh. Hayatu kuwa gaishe shi su ke ta yi ya dinga amsawa da sakin fuska. Za ka rantse baya cikin mummunan tashin hankali mara misaltuwa. Sun yi mamakin hakan ƙwarai da gaske. Mafi ƙarancin abin da su ka yi zato shi ne yi
blaming ɗin Alhajinsu ya ce laifinsa ne matarsa take kwance a wannan yanayi.
Shi dai Abba Habibu bai ma yi la’akari da kallon kallo da su ke yi ba. A lokacin Dr. Hadifi ya iso, Alhaji ya matsa kusa da shi domin nemawa Abba Habibu izinin shiga wajen Yaya. Suna magana a gefe Abba Habibu ya ɗago Hamdi daga jikinsa ya kalleta a cikin ido ya girgiza kai. Bai yi mata magana ba a lokacin sai ya ja ta gefe ɗan nesa da sauran.
“A gabansu ki ke wannan kukan Hamdi? So ki ke su yi zaton kina baƙincikin sadaukarwar mahaifiyarki ga ɗan uwansu?”
“A’a” ta girgiza kai da sauri.
“Haka za su yi zato idan ba ki yi shiru ba mana.” Hannuwansa riƙe da nata ya rarrashe ta ” Don Allah kada ki sa su ji a ransu kamar sun yi wa kowa laifi. Wallahi da izini na ta bayar.”
“Abba da izinin ka?”
A gurguje ya faɗa mata wayar da su ka yi sannan ya cigaba da cewa “farinciki da nutsuwar zuciyar da zamu nuna musu shi ne zai yi nuni da cewa mun girmama wannan kyakkyawan aiki da tayi.”
Duk wannan bayanin da Abba Habibu yake yiwa Hamdi ashe a kunnuwan Alh. Hayatu, Hajiya da Taj yayi. Sun biyo bayan su ne a zaton su faɗa zai yiwa Hamdin.
Hamdi ta sanya ƙasan hijabinta ta goge idanunta. Cikin muryar kuka ta ce “Abba ina tausayinta ne kawai. Ga yanayinta ga ciwo. Gani nake kamar shi yasa ita bata tashi ba.”
A wannan halin ya ƙirƙiri ƴar raha domin kwantarwa ƴarsa da hankali.
“Kada ki raina min mata mana Hamdi. Ta haife ku ku huɗu rigis sannan ki dinga tunanin wannan zai bata wahala? Ko an faɗa miki kowa ma rago ne irin ku?”
“Kai Abba…” ta faɗi tayi murmushi akan kumburarriyar fuskarta dake jiƙe da hawaye.
Hajiya bata san lokacin da tsananin tausayi da girmansu yasa ta sake fashewa da kuka ba. Hakan ya bayyana musu cewa ba su kaɗai bane. Ta rungume Hamdi tana rarrashinta amma kuma ita ma ɗin kukan take yi sosai.
Alh. Hayatu ya kira Abba Habibu ya kai shi gaban Dr. Hadifi. Nan da nan aka shiga ciki da shi. Aka bashi riga da dukkanin kayan kariya ga mara lafiya domin kada a shiga da baƙuwar cuta. Sai da ya shirya tsaf aka bashi damar ƙarasawa gaban Yaya. Sannan Alh. Hayatu ya matsa gefe yana kallon what it truly means to be a great person. Kuɗi, mulki, lafiya, mazantaka da suna do not make a man. Habibu Umar Simagade ya nuna masa haka daga airport zuwa yanzu. Kuma duka abubuwan da yake taƙama dasu a yau ba su hana shi jin nauyi da kunyar wanda ya raina a baya ba. Zuciyarsa ta karaya matuƙa da ya tuna wani shuɗaɗɗen lokaci da Abba Habibu ya zo neman taimako wajen sa a kasuwa. Akan ce idan maye ya manta, uwar ɗa ba za ta manta ba. To shi dai da kansa mayen bai manta ba.
***
SHEKARUN BAYA
Abba Habibu ne yake tafiya a cikin kwanonin tsakiyar Kantin Kwari da gammo a kansa wanda ya ɗorawa madaidaiciyar cooler. Kayan jikinsa jamfa ce da wando kuma gwargwadon iyawarsa yana ta kamanta taku irin na maza, sai dai ko kusa baya iyawa. Tafiyar tasa tafi kama da rangwaɗa irin ta ƴan matan dake ji da kansu. Nauyin kayan da ya ɗauko ko kaɗan bai ɓoye yanayinsa na ɗan daudu ba.
Da kwatance saboda daɗewa da sababbin gine-gine a kasuwar ya gano jerin shagunan Alh. Hayatu. Cikin farinciki ya shiga da sallama daidai lokacin da yaran shagon su ke ganiyar ciniki da wasu kwastomomi. Alh. Hayatu kuma yana magana a gefe guda da ƴan mazan ƴaƴansa su uku. Dukkaninsu sanye su ke da shadda wagambari tana ɗaukar ido. Ahmad, Kamal da Taj. Kamar kowacce Juma’a, Alhaji ya tura an ɗauko masa su daga gida bayan sun dawo daga makaranta domin zuwa masallaci.
Alhaji na ganin Abba Habibu yaji tamkar an ɗauke masa wutar jikinsa. Sam baya son abin da zai haɗa su waje guda saboda yadda yake ƙyamarsa. Idan ya tuna Habibun da ya sani, ya kalli wannan sai yaji wani irin takaici.
Da ƙyar ya amsa sallamar da yayi. Kuma gabaɗaya ya tsargu da kallon su da mutanen cikin shagon su ka kama yi. Yana ji a jikinsa yau shi zai zama jigon gulmar cikin kasuwar.
Fuska cike da fara’a da jindaɗi Abba Habibu ya miƙa hannu zai dafa kan Ahmad yana cewa “girman ɗan mutum ba wuya. Yaya Hayatu haka Ahmad ya girma?” Ya kalli su Taj “waɗannan ƙannensa ne?”
Kafin hannunsa ya taɓa Ahmad tuni Alh. Hayatu ya janye ɗansa gefe ya kuma bi shi da kallon me-ya-kawo-ka?
Abba Habibu ya ɗan rissina gami da miƙa masa hannu sai dai haka ya koma da abinsa da bai mayar da musabahar ba. Still with a smiling face ya gaishe shi ya kuma tambaye shi lafiyar iyali.
“Ƙalau! Aiko ka aka yi ne?” Alh. Hayatu ya tambaya a ƙagauce.
“Dama magana na ke so mu yi”
Abba Habibu ya bashi amsa da sanyin jiki. Attitude ɗin da yake yi masa yasa shi shan jinin jikinsa. Shi ɗin ba baƙon da ake maraba da zuwansa bane.
Wata kusurwa a cikin shagon Alh. Hayatu ya ja shi maimakon su keɓe a office. Yadda mutane suke yanzun nan zai iya jin an yi masa muguwar fassara.
Cikin jin nauyi Abba Habibu ya keta billensa ya roƙe shi akan ya taimakawa rayuwarsa.
“Wallahi ban iya komai ba sai girki. Na fara koyon ɗinki amma saboda zama sai naji ba zan iya ba tunda na saba da kai komo. Ni kuma ba karatu na gama ba balle na nemi aiki.”
“Me ka ke so?”
“Ba na son zama cima zaune. Idan da hali ko yaron shago ka ɗauk…”
Ko direwa bai yi ba Alh. Hayatu ya hau shi da faɗa.
“A’a…kada ma ka yaudari kan ka. Ta yaya zan bari mutumcina ya zube a wajen sana’ata saboda kai? Ban gaya maka zaka yi nadamar wannan hanyar da ka ɗauka ba?”
“Ka faɗa Yaya Hayatu. Ba kai ba ma. Kowa ya faɗa kuma na gani.”
Idanuwansa su ka ciko da ƙwalla. Hakan ya sake ɓatawa Alh. Hayatu rai. Namiji har namiji amma mai saurin kuka. Tirrr da daudanci wallahi ya ayyana a ransa.
“Habibu ka san ban iya munafurci ba ko? To ba za ka zauna min a shago ba. Ana girmama ni a wajen nan.”
Abba Habibu ya yi murmushi “nima kaina ina ƙyamar yadda rayuwa ta kasance min amma wallahi girki kaɗai nayi a cikinta. Duk sauran shiriritar da kake tunani ban taɓa yi ba. Kuskurena biyu ne. Na farko da nayi tunanin dole sai na koma mace zan sami damar yin girkin da nake so. Na biyu kuma da na bari son girkin ya rinjayi zuciyata zuwa ga saɓon Allah.”
Ya haɗa hannuwansa biyu
“na tuba ga Ubangijina Yaya Hayatu. Ko zan mutu ina yawo a titi ba zan ƙara daudu ba. Tafiya, magana da wannan karya jikin ma don dai na rasa yadda zanyi na daina ne. Don Allah Ka taimaka min ko da jari ne.”
Zuciyar Alh. Hayatu ta fara karaya da zantukan Abba Habibu a wannan lokaci. Yanayin tamke fuskarsa ma ya sassauta. A lokaci guda yaji makamansa sun fara ƙarewa. Ya ja gwauron numfashi ya sauke.
“Ba zan iya zama da kai a kasuwa ba Habibu amma in sha Allahu zan taimaka maka.” Ya sami kujera ya zauna sannan ya dube shi “Yanzu idan na baka jari wace sana’a za ka yi?”
Murna, nutsuwar zuciya, ɗoki da girmamawa ga Alh. Hayatu su ka taru su ka mamaye zuciyar Abba Habibu. Bakinsa har yana rawa don tsabar farinciki.
“Girki!”
Alh. Hayatu yaji wani irin haushi da takaici sun lulluɓe shi. Girkin dai zai koma wa?
“Sana’ar abinci zan cigaba da yi domin a nan nake da ido. Kada na dulmiya kuɗin a inda zai salwata saboda rashin sabo. Ko yaya ka gani?”
Ɗaga murya ya yi “Baka shirya gyara rayuwarka ba Habibu. Ka zo ka fita. Fita na ce!!!” Ka nuna masa waje.
Abba Habibu ya waiga hagu da dama a rikice don bai san me ya sake tunzura Alh. Hayatu ba.
“Yaya Hayatu…” ya soma kiran shi da sigar magiya.
A yadda Alh. Hayatu yake ɗaga murya yanzu da yaran shagon nasa, kwastomomi da mutanen dake haraba kowa ya dawo da hankali garesu.
“Girkin ba shi ya kawo ka wannan mummunan matsayin na ɗan daudu ba? Shi ne za ka kalli tsabar idona ka ce min idan na baka jari shi za ka cigaba da yi. Anya Habibu kana da hankali kuwa?”
“Shi ne kaɗai nake ganin zan yi ba tare da mutane sun guji mu’amala dani ba. Yanzun nan fa kace min ba za ka iya zaman shago dani ba. Kana ganin akwai sana’ar da zan yi a saya a wannan zamanin namu da ake ƙyanƙyamin masu rayuwa irin tawa? Abincin mu ne kawai na san ba a gudu.”
“Habibu ka fita na ce. Kuma ko a hanya ka ganni kada ka kuskura kayi gangancin nuna ka taɓa sani na. Aikin banza.”
Jiki a sanyaye Abba Habibu ya ya juya zai fita. Idanuwan dake kallonsa sun fi ashirin. Nan take zuciyarsa ta sake raunana. Ƙwalla ta cika masa idanu taf sai dai bai bari ta sauko ba.
A wulaƙance Alh. Hayatu ya kalli cooler ɗin da ya shigo da ita. Ya sa ƙafa ya zungureta.
“Dawo ka yi mantuwa.”
Murmushin yaƙe Abba Habibu ya yi “dama kawo maka nayi a bawa yara.”
“A bawa yara? Me?” Ya sake tambaya yana taɓe fuska.
“Zabi ne aka soya”
Katse shi yayi da sauri
“Allah Ya kiyaye jini na su ci girkin ɗan daudu wallahi. Ba ma tare da yunwa Habibu. Ka kwashe kazantarka.”
Abba Habibu ya kalli kular ya koma ya kalli mutane suna ta ƙananun maganganu a gefensa. Jikinsa yaji duk ya mutu kamar anyi masa duka. Wannan kular ya tabbatar a yadda yake jin kansa ba iya ɗauka zai yi ba. Ƙwaƙƙwaran motsi idan yayi zai iya yin hawayen da Alh. Hayatu zai sake aibata shi a kansu. Rago zai kira shi.
“Don Allah ko a nan ne ka bayar.”
“Ai ba ni ba, wanda ya raɓe ni ma yafi ƙarfin cin abin hannunka.” Ya kalli biyu cikin yaransa “ku ɗauka a kaiwa karnuka tunda ba ya so.”
Jin haka Abba Hayatu ya koma ya ɗauki kular kafin su taɓa. Mahaifiyarsa ce ta dafa sai dai baya jin Alh. Hayatu yana buƙatar dogon bayani irin wannan. Da ya fita bai sake waigowa ba.
*
In ya tuna, shi da Abba Habibu basu sake haɗuwa ba sai da maganar auren Taj da Hamdi ta taso sai yaji a ransa tamkar Abba Habibu yayi nasara a kansa har sau biyu. Na farko izzarsa ta kife a ƙasa a yayinda ɗansa mafi soyuwa a gare shi ya zaɓi girkin da ya tsani gani a wajen ɗa namiji a matsayin sana’a. It was as if karma came knocking and laughing at him lokaci guda. Na biyu kuma shi ne yadda ƙaddara ta sake haɗa ɗan nasa da yar Habibu. Abu kamar almara. Idan ya ce bai yi tunanin ko asirice masa ɗa Abba Habibu yayi ba tabbas yayi ƙarya.
A karon farko zazzafar ƙwalla ta dinga kwaranya daga idanun Alh. Hayatu. After all these years, abar ikon Abba Habibu ce ta zama silar warakar gudan jininsa. Yau idan Kamal ya cigaba da rayuwa, Allah ne Ya yi ikonSa amma matar Habibu ce sila. Habibun da yake ganin bai cika mutum ba.
Wasu cikin kalamansa gare shi masu zafi su ka dinga dawo masa da wata irin amsa kuwwa. Shi ya faɗe su amma yau yafi Abba Habibu jin zafinsu. Nadama da tulin dana-sani su ka sarƙafi zuciyarsa. Tabbas tun a jiya zuciyarsa ta shiga alhini da jin nauyin abubuwan da ya yi a baya. Amma a wannan sa’ar, da Habibu ya zo gabansa amma ko kusa fuskarsa bata nuna alamun zuciyarsa na ɓoyon baƙincikin sadaukarwar matarsa ba. Hasalima tuhumar kukan ƴarsa yake yi har yana shawartar ta da kada tayi abin da su da aka yiwa alfarma za su ji babu daɗi. Sai ya ji komai ya kwance masa. Babu sauran jin kai da ƙafafa. Shi Hayatu ya yarda ƙaddara bata fi ƙarfin kowa ba. Zaɓin yadda ɗan Adam zai tafiyar da halin da ya tsinci kansa shi ne ma’aunin dacewa.
“Alhaji lafiya? Me ya faru kuma?”
Firgigit Alh. Hayatu ya dubi su Hajiya dake tsaye da wasu cikin ƴaƴansa suna kallon shi. Kawar da kansa ya yi gefe bai cewa kowa uffan ba.
Kallo guda Inna ta yiwa yaran nasu su ka fahimceta. Kafin wani lokaci dukkaninsu sun bar wajen. Masaukinsu Ahmad ya ce su zo su tafi saboda asibitin ba a jinya. Kamal kuma yana buƙatar hutu sosai tunda ko magana bai fara yi ba. Ya dai dawo hayyacinsa amma yana cikin magagin ciwo.
“Mubina tare za mu tafi ki samu ki ɗan yi bacci ko yaya ne.” Ya dubi Taj “ka zauna da Hamdi sai ku taho tare da su Alhaji.”
***
Tsaye a bakin gadon Yaya, Abba Habibu ne da wata nurse. Sharuɗɗan shiga ICU ɗin ta bashi wanda a ciki ta nanata masa banda ɗaga sauti cikin magana ko kuka. Ya tambayi ko zai iya taɓa ta tayi masa izini amma shi ma ba riƙo mai ƙarfi ba. Komawa tayi table ɗinta a can tsakiyar ɗakin ta barshi gefen da aka keɓewa Yaya.
Abba Habibu ya daure sosai ya hana kansa kuka ko da a zuci. Gani yake da zarar ya karaya wani abu zai iya samunta. Hannunsa ya ɗora akan nata ya riƙe kamar zasu yi musabaha.
“Ashe waliyya nake aure ban sani ba? Gaskiya ki tashi haka nan in kwashi tubarraki.”
Kamar daga sama yaji muryar Yaya tana magana a hankali sosai. Salati ne take yi da sauri-sauri cikin kiɗima. Abba
Habibu ya ranƙwafo kansa su ka haɗa ido. Ai da ya tabbatar ta tashi da saurinsa ya juya zai fita domin ya kira nurse. Ita kuwa Yaya ta sake damƙar hannun tana mai jin tsoron kada ya fita ya barta.
“Sannu. Nurse zan kira a zo a duba ki.”
A hankali ta rufe ido ta buɗe cikin nutsuwa. Sai a lokacin ta dawo hayyacinta.
“Yaushe ka zo?” Kafin ya amsa ta kaɗa kai “kai ne ɗin dai ba gizo idanuna suke ba ko?”
“Ni ne Jinjin. Yau na zo. Yaya kike ji a jikin naki? Ki bari na kira Nurse.”
Cikin ƙanƙanin lokaci likitoci biyu da nurse su ka tsaya akanta. Aka duba lafiyarta sosai su ka tabbatar cewa babu sauran matsala. In sha Allahu bata cikin haɗari. Sannan aka bata awa guda ta sake hutawa kafin a mayar da ita ɗaki.
Wannan abu ya farantawa Abba Habibu rai sosai. Bayan fitar likitocin waɗanda su ka jima suna yabonta kafin su tafi, Yaya ta dubi Abba Habibu. Bayani ta so yi masa yace sam bai yarda tayi magana ba.
“Ki bari sauƙi ya samu shine babban burina. Ina so dai ki saka a ranki cewa kin yi jihadi kuma ko kaɗan baki ɓata min rai ba.”
Lokaci na cika ko minti biyar ba a ƙara ba aka gangaro Yaya zuwa ɗakin da hukumar asibiti ta tanadar mata na musamman domin karramawa. VIP wing aka nufa da ita wanda sai an shiga lift an sake ƙara hawa uku akan inda su ke. Tun a ƙofar ICU ɗin Hamdi ta kama mata hannu tana biye dasu. Idanunta jazur duk ta fita hayyacinta amma a haka take ta murmushi saboda kada ta karyar mata da zuciya.
Taj tsayawa yayi tare da Alhaji. Yana kallo su Hajiya su ka bi su a baya.
“Ka bi su mana” cewar Alhaji gare shi.
“Abin da ya hana ka bin su nima shi ya hana ni Alhaji.” Ya kalli Alhajin da ɗan murmushi a fuskarsa “na san ba surukuta ce ta hana ka bin su ba.”
Alhaji ya numfasa yana bin hanyar da aka gangara gadon Yaya da kallo. Ya jinjina kai sannan ya zauna a kan kujerar. Taj ma kusa dashi ya zauna su ka kasance gefe da gefen juna sun jingina baya da bango.
“Ɗan Adam ba ya gane cewa ba a bakin komai yake ba sai ya ga ikon Allah a inda yake tunanin wayo ko dabararsa sun ishe shi.”
Kallonsa Taj yayi yana sauraronsa da kunnuwan basira amma bai ce komai ba. Alhaji ya cigaba da magana.
“Idan wani ya ce min ɗan cikina mace ma ba namiji ba zata ci abinci da sana’ar abinci wallahi zan ƙaryata Taj. I was so confident cewa Allah Ya lamunce min rayuwata akan tsarin da nake so. Ina da kuɗi kuma nayi muku tarbiyya daidai gwargwado. Fitintinun zamani da ake kuka dasu babu ko ɗaya a cikin gidana. Ƴaƴana duk inda su ka shiga ana alfahari dasu. Na zata…”
muryarsa ta kama rawa
“Taj na zata gobe na kamar yau zata cigaba da kasancewa muddin rai. Hmmm”
Ya sauke ajiyar zuciya da ƙarfi.
“Tajuddeen Hayatu sai ka zaɓi kitchen. Sana’ar da bayan ƙiyayyar da nake yi mata ban taɓa hango wani nawa cikinta ba. Kuma kamar da gayya sai ga ka da auren ƴar Habibu. Wato Taj da ace zan iya fito da zuciyata ka ga tsanar da na yiwa auren ku a dalilin Habibu, da ko da wasa ba za ka tunkare ni da maganar Hamdiyya ba.”
Taj ya yi kasaƙe yana jin furucin mahaifinsa dalla-dalla.
“Subhanallah! Komai yana tafiya cikin tsari da ƙudurin Al-Hakimu. Ba don auren ku ba da babu abin da zai kawo mahaifiyar Hamdi inda muke ko da a asibitin nan take aiki. It’s like everything happened for this day Taj. Allah Ya rubuta da ƙodar matar Habibu kuma surukarka Kamal zai cigaba da jan numfashi a duniya. Kuma duk tarin shekaruna sai a yanzu na gane wannan izinar.”
“Tsarki ya tabbata ga Sarkin da gyangyaɗi da bacci ba sa cikin siffofinSa.” Taj ya faɗi cikin shauƙin alawar imani wadda zaƙinta yakan tashi a lokutan da bawa ya yaba wa sarautar Ubangijinsa, gatansa, majiɓincin lamuransa.
Alhaji ya gyaɗa kai sai da raunin murya ya ce “Zuciyata ta cika da kokonton karɓuwar dukkan alkhairi na na baya.”
Wani irin kallo Taj ya yi masa ya ce “Alhaji me ya sa za ka yi wannan tunanin? Don Allah ka kyautatawa Allah zato.”
A gurguje Alhaji ya bawa Taj labarin abin da ya gama tunawa ɗazu akan zuwan Abba Habibu neman taimako wajensa a shekarun baya.
“Ka san Annabi SAW ya gargaɗe mu da gujewa girman kai da illarsa akan ayyukan ladan mu.”
“Haka ne.” Cewar Taj da sauri yana jiran yaji sauran abin da Alhaji zai ce.
“Dole na daina yaudarar kaina idan ina son ganin daidai. Tabbas tuntuni na jima da ji a raina cewa Habibu ya tuba. A zuciyata ina muradin janyo shi jikina in inganta masa rayuwa. Amma a gefe guda ina tunanin makomar mutumcina a idon duniya. Ina ƙyamar a ce ina mu’amala da mutum irinsa.” Muryarsa ta koma abin tausayi a yayinda yake cewa “kaga gabaɗaya fushin nawa ya zama ba don Allah ba. Girman kai ne kawai ya hana ni yin abin da ya dace ba wai don ban san ya dace ɗin ba. Tun girma da arziƙi ban nemi shiri da shi ba gashi yanzu dole in ƙanƙantar da kai a gaban sa tunda girman da arziƙin nasa ne. Kowa yaƙi sharar masallaci…”
“Yaya Hayatu dai ba zai yi ta kasuwa ba!”
Tare su ka juya da jin muryar Abba Habibu a gefen su. Abba Habibu ne tsaye shi da Hamdi. Ganin su ya sa su miƙewa su ma.
Tun shigar su ɗaki, Yaya ta ce Hamdi ta koma su dawo tare da Taj. Ta hango shi yana ja da baya. Mama ta ce musu tana tunanin yana jin nauyin fuskantarta ne bayan ta gamu da lalura a dalilin ɗan uwansa.
“Ai kuwa ba zan yarda da wannan tsirfar ba. Maza bi shi ki ce ina nemansa.”
Da ta fito sai ta manta a hawa na nawa su ka baro su. Ta koma tambaya shi ne Abba Habibu ya hana Umma da tayi yunƙurin rakota biyota. Ashe rabon za su ji maganganun su Alhaji ne.
“Habibu…” Alhaji ya fara cewa da wata ƙaramar murya kamar ba shi ba. Sai dai Abba Habibu bai jira ya gama magana ba ya girgiza masa kai.
“Ko me za ka ce don Allah ka bari indai ina da sauran mutumci ko yaya a idon ka. Ya wuce. Komai ya wuce in sha Allahu.”
“Ba za ka bari na baka haƙuri ba?” Lura yayi Taj ya yiwa Hamdi alama suna shirin barin wajen ya koma gare su “kada ku tafi.”
Abba Habibu ya tsaya tare da yaran nasu suna kallon Alhaji.
“Ƙaddarar auren ku ita ta kawo mu wannan ranar saboda haka ina so ku shaida kuma ku taya ni bawa Habibu haƙurin dukkan wani abu na rashi daɗi komai girma ko ƙanƙanta da na taɓa yi masa.”
Da rashin jindaɗi Abba Habibu ya ce “Amma na ce ya wuce. Ban riƙe ka ba wallahi.”
“Kayya dai Habibu. Zuciya tana son mai kyautata mata ne. Abubuwan da nayi ko bakin ka bai faɗa ba na san dole rai ya sosu.”
Murmushi kawai Abba Habibu ya yi ya ƙara maimaita cewa komai ya wuce. Su ka koma ɗakin Yaya tare. Alhaji gabaɗaya ya kasa sakewa duk yadda Abba Habibu da Yaya su ka yi ta ƙoƙarin nuna babu komai. Hakan yasa su Hajiya tsangwamar kansu su ma.
Tun abin yana burge Taj har dai ya ƙosa su bari haka nan. Alhaji yana ta maimaita ban haƙuri. Abba Habibu yana ƙoƙarin nuna komai ya wuce. Iyayen su mata kuma suna taya mazan su.
“Alhaji da dai kun bar abin nan haka kun fara tunanin gaba. Misali kaga kai sai kayi fama da su Daddy (Yaya Babba) kafin su karɓi uzurinka na ƙin faɗa musu ciwon Happiness da wuri. ” Ya juya ya kalli Abba Habibu “su Zee za su iya saurin fahimta idan ka kira su amma Inna Luba dai ban sani ba ko za ta yarda ba sayar da ƙodar Yaya kayi ba.” Ya mayar da duban sa ga su Hajiya yana sosa tsakiyar kai “yau dai ya kamata ku kikkira naku ƴan uwan ku ma ko kuwa?”
Ɗakin ya yi tsit. Taj ya harba bomb ya barsu da jiran tashin sa. Wayar da basu yi tunanin kira ba a tsukin kwanakin baya sai yanzu su ke tsoron abin da zai biyo baya. Tabbas ƴan uwan kowannen su za su ji babu daɗin ɓoye musu zancen nan ba.
Da ya kula attention ɗin su ya samu don irin su Inna har an ɗauko waya sai cewa ya yi “amma dai kada ku kira yau domin tunda magriba ta wuce a gida dare ya riga ya yi. Zancen zai iya hana wasu bacci. Ga masu BP da ƴan rikicin tsufa.”
Mama dai hannu ta ɗaga za ta kai masa duka ya zille da sauri yana dariya. Su ma ɗin su na son yin dariyar amma babu hali. Zungurin da ya yi musu akan wayoyi masu mahimmanci da ya kamata su yi duk ya ɗaga musu hankula.
“Zo mu tafi Hamdi. Its late and I am tired.”
“Haƙƙun! Sannu mai mata. Wato ta zo ku tafi ko? Kai babu ruwan ka tunda mu tayar mana da namu BP ɗin kuma za ka hana mu bacci ba.”
Umma ce tayi maganar tana harararsa sama da ƙasa. Dole kowa ya dara kuwa har Yaya akan gadon ta. Daga dai su ka yi sallama domin su ƙara raguwa. Abba Habibu kaɗai za a bari. Su Alhaji gabaɗayan su kuma su ka fito tare.
Agogo ya nuna ƙarfe uku da kwata na dare. A muhalli uku bayin Allah suna kan abin sallah cikin ganawa da Ubangiji SWT. Abba Habibu na zaune hannuwa a sama bayan ya idar da nafila yana mai ƙasƙantar da kai cikin neman yardar Allah. Fatansa Yaya da Kamal su koma gida da ƙafafun su. Sai kuma ya miƙa dukkan al’amuransa, na iyalinsa da na dukkan wanda mu’amala ta haɗa su komai ƙanƙanta ga Allah SWT.
A cikin ɗakin Alhaji ma shi kuka yake yi sosai yana roƙon gafarar Sarkin Sarakuna SWT.
Hakan kuma take tsakanin Taj da Hamdi. Gajiyar da su ka kwaso bata hana su raya daren da sallah ba domin kyakkyawan fata akan gobe.
A ɗakin Kamal, idanu ya buɗe tar cikin hayyacinsa. Tashin farko ya kai hannunsa ciki ya tabbatar akwai yanka alamun an yi masa aiki. Bai san lokacin da ya runtse idanunsa ba yana faɗin
“Allahu Akbar. Allahu Akbar. Allahu Akbar”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
