Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Salati a jere a jere Amma ta dinga yi a yayinda Alh Babba yake sanar da ita abin da yake faruwa. Tana yi muryarta na rawa bata ma san cewa ta fara kuka ba sai da taji yana rarrashinta.

    “Yaya Babba dashen ƙoda fa ka ce…” muryarta ta sarƙe a tsakiyar zancen.

    “Godiya ya kamata mu yi wa Allah ba kuka ba. Banda haka da yanzu wani zancen ake ba wannan ba.”

    Da ta tuna hakan sai taji wani irin tsoron Allah Ya sske shigarta. Barin ma da ya ɗan labarta mata yadda aka yi Yaya ta je asibitin.

    Bayan hankali ya ɗan kwanta tayi masa zancen yaushe za su tafi.

    “Mu bari zuwa nan da kwana biyu tukunna. Sannan don Allah ki kama bakin ki kiyi shiru. Su Taj basu san komai ba. Haka ma shi Habibu da yaransa. Ke kaɗai da sauran ƴan uwa na faɗa wa domin Hayatu yana cikin ruɗani. Lallai yana buƙatar tausasawa daga wajen ƴan uwansa.”

    ***
    Tashin hankali mara misali ne ya kama Abba Habibu bayan sun gama waya da Yaya. Awanni shida sun wuce amma ya rasa inda zai tsoma ransa. Ya sake kiran layin da ta bada numbarsa su ka yi magana yafi a ƙirga ba a ɗauka. Lokacin likitan yana cikin tiyata ana transplant surgery ɗin. Da ya fito kuma wasu abubuwan su ka ɗauke masa hankali.

    Can bayan isha ya dawo daga masallaci sai ga wayar Ahmad. Shi dai tunda yaga baƙuwar lambar Saudiyya kawai ya ɗauka da sauri. Sallama ya yi yana jiran ta amsa sai yaji muryar namiji. Zuciyarsa bata ƙara tsinkewa ba sai da Ahmad ɗin ya gabatar da kansa.

    “Ahmad ne, yayan Taj.”

    “Ahmad kana da labarin halin da iyalina take ciki ne?” Ya tambaya da sanyin jiki. Zuciyarsa ta bashi dalilin kiran kenan.

    “Alhamdulillah.” Ahmad ya kasa ɗorawa daga nan.

    “Hamdala ai wajibin musulmi ce ko a bakin kura yake. Ina nufin labarin da zan iya bawa ƴaƴanta. Kuma tana da uwa da uba a raye. Su ma ina neman abin faɗa musu.” Ya ce da wani irin yanayi mai raunana zuciyar mai sauraro.

    “Haka ne” Ahmad ya yi jim kaɗan sannan ya cigaba da magana “akwai abokina da zai zo nan gidan ka yanzu. Na faɗa masa sunan unguwar. Idan ya zo zai kira ka.”

    Allah kaɗai Yake riƙe da Abba Habibu. Maganganun Ahmad sun sake dulmiya shi cikin fargaba.
    “Abokin ka? A gida na? Me zai kawo shi?”

    A gurguje Ahmad ya ce ticket za a saya masa inji Alh. Hayatu. Idan anyi sa’a yana da visa to a gobe zai sami damar tahowa sai dai ba jirgin su Hamdi ba.

    “Ni ɗin Musulmi ne Ahmad. Kullum ina adduar kada Allah Ya ɗora min ƙaddarar da tafi ƙarfin imani na. In sha Allah idan ka faɗa min gaskiya ba zan kasa ɗauka ba.”

    Cike da jin nauyi Ahmad ya ce “Don Allah kada ka tambayeni. Ba zan iya faɗa maka ba. Na dai san tana nan lafiya.”

    “Hakan ma amsa ce. Da ranta kenan.”
    Sai ya ƙara da cewa “ina Alhajin?”

    “Nauyin ka ba zai bari ya iya yi maka magana a waya ba. Ya tafi yiwa Maman Hamdiyya Umra amma ka kwantar da hankalinka da ranta. Wannan shi kaɗai ne abin zan iya faɗa maka.”

    “Nagode.”

    Da ya ajiye wayar sai hawaye ya sauko masa. Ya sharce su da sauri. Yawan kuka yana daga cikin abubuwan da yake gudu saboda kada a danganta shi da mata.

    “Me kika yi Jinjin? Wane irin taimako ne?”

    Abokin Ahmad ya kira shi. Ya bada passport ya koma cikin gida. Zee da Halifa basu san wainar da ake toyawa ba. A wannan yanayin na zulumi ya kwana bai runtsa ba. Ƙarfe tara da rabi na safe abokin Ahmad ya kira shi ya ce su haɗu a airport nan da uku na rana. Jirgin da zai bi takwas zai tashi na dare.

    Kaɗuwa iya kaɗuwa Abba Habibu ya gama yi. A haka ya dinga ɓoyewa Zee da Halifa saboda rashin sanin amsar da ta dace idan sun nemi ƙarin bayani. Kaya kala uku ya iya haɗawa a wata ƙaramar jaka. Suma ɗin don ya san dole ne dai ya canja ba don haka ba da a haka zai tafi. Agogon bangon ɗakin ya kalla. Goma ma bata yi ba. Gani yake kamar ya jawo lokaci ya ganshi tare da Yaya ko a wane hali take kuwa.

    “Abba in yi tuwon shinkafa da rana?”

    Muryar Zee a ƙofar ɗakin yaji. Sannan ya tuna ai bashi da damar tafiya ya barsu su kaɗai a gida. Dole wani ya san me yake faruwa. Shiru ba zai kai shi ko’ina ba.

    “Abba?” Zee ta sake yin magana a hankali don ta fara tunanin ko bacci ya koma.

    Tasowa yayi ya buɗe ƙofar ta matsa masa ya fito.

    “Kada ki ɗora komai yanzu sai iya wanda za ku ci. Shi ma ɗin kaɗan. Zan ɗan fita unguwa na dawo.”

    Yanayinsa ya bawa Zee tsoro. Ta kalle shi a tsanake.
    “Abba baka da lafiya ne?”

    “Me ki ka gani?” Ya ƙirƙiro murmushi.

    “Wallahi duk kayi wani iri.” Ta faɗi da sanyin jiki. A zuciyarta kuwa tunani take ba zai wuce kewar Yaya yake yi ba.

    “Bacci ne bai isheni ba. Matata ta tafi ta barni.”

    Zee ƙumshe baki tayi tana dariyar shaƙiyanci. Da haka Abba Habibu ya samu ya fita ba tare da ta tsananta bincike ba.

    *

    Anti Zinatu da sauran yan uwan Abba Habibu sun shiga mummunan tashin hankali bayan ya gama faɗa musu halin da ake ciki. A gidan Anti Zinatun suka haɗu domin ya kikkira su kafin ya iso gidan. Cikin sa’a kuma duka babu mai uzurin da ya hana shi fitowa akan lokaci.

    “Wai ba da dangin mijin Labiba ta tafi ba? Ya aka yi cikinsu babu wanda ya bi bayanta?”

    Wadda tayi tambayar tana rufe baki Abdulƙadir ya yi musu alama da hannayensa akan yana so su saurare shi. Sai da yaga sun dawo da hankali gareshi ya dubi Abba Habibu cikin yanayi na jin nauyi.

    “Gaskiya ina tsammanin abin da nake ji yana faruwa a Iyafot ɗin ƙasa mai Tsarki fa gaske ne.”

    “Me kaji?” Suka haɗa baki wajen tambayarsa.

    Sai da ya ɗan jajantawa kansa girman maganar kafin ya fitar da ita.
    “Yaya Habibu kayi haƙuri da furucina amma magana ta gaskiya ita ce yanzu an tsananta kame da binciken masu nakasa.”

    Da sauri Abba Habibu ya canja zama “me? Me ka ke nufi?”

    “Naga ya faru a unguwarmu. A’ilo Gurguwa ko ƙasar bata shiga ba aka aunota gida. Kuma kusan kowa ya sani cewa bara ta tafi yi.”

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Ya Salam. Subhanallahi…” Abba Habibu yake ta faɗi shi kaɗai. Sauran ƴan uwansu kuwa sai sallallami.

    Abdulƙadir ya dubi Abba Habibu “bani da tabbas amma ina zargin haka ɗin ne. Idan ba haka ba me zai sa a kama ta?”

    “Ni fa ban ce an kama ta ba” Abba Habibu yaci gyaransa da wuri “iyalin Yaya Hayatu sun san halin da take ciki. Faɗa ne ba za su yi ba a waya.”

    “Ba da nufin tozarci nake yi maka zancen nan ba. Na faɗi abin da na sani ne saboda ka tafi da shirinka wajen kareta.”

    “Maganganunka tsorata ni suke yi Abdulƙadir. A bar zancen nan kawai.”

    Anti Zinatu tana zubar hawaye ta ce “Habibu ko mun ƙi ko mun so fa da ƙamshin gaskiya cikin zancen nan. Kamar yadda yace ne ka tafi da shiri a zuciyarka kada gaskiya ta baka mamaki. Zuciyata sam bata son wannan tunanin to amma shi kaɗai ne muke iya hasashe.”

    Abba Habibu gani yayi bashi da wata hanyar kashe maganar. Sun riga sun ƙarfafa zarginsu. Shi kuwa tunanin kaɗai ma ya ishe shi fargaba. A Saudiyya, Sijin (prison) suke kai kusan duk mai laifi irin wannan su ajiye. Idan na korowa gida ne daga can ake kai su airport. Masu hukuncin kisa….inaaa. Zumbur ya miƙe ya zura takalmansa.

    “Bari na ƙarasa gidan na sanar dasu su shirya su taho. Wannan magana kuma don Allah ayi shiru sai naje na ganewa idanuna.”

    Zaman bai ƙara masa komai ba sai tashin hankali. Ya yi imanin basu faɗi komai domin cusguna masa ba. Iya gaskiyar da suke iya hangowa ce aka faɗa masa.

    A hanya yayi ta tufka da warwara akan abin da zai faɗawa su Zee. Da fari tunanin ya ce musu Inna Luba ce babu lafiya. Da sauri ya girgiza kai da ya hango saurin gano shi da za ayi. Idan basu bishi ba tabbas zasu kirata a waya domin jin yanayin jikin nata. Daga nan ita kuma nata hankalin ya tashi. Ƙarshe dai gaskiyar da yake gudu dole ya faɗeta domin duk inda yace musu zai tafi dole za su kira waya.

    *

    Abba Habibu ya kasa hakuri ganin ya gama bayani amma Halifa da Zee ko motsi basu yi ba. Zuciyarsa tana cike da fargabar kada su matsanta masa da tambaya akan kwaskwarimar da ya yiwa zancen. Nuna musu yayi cewa Alh. Hayatu da kansa ya kira shi yace bai dace Yaya ta tafi ita kadai ba. Shine yasa aka yi masa komai cikin gaggawa don ya tafi da wuri.

    Kamar ba za su yi magana ba sai kuma Zee ta fashe da kuka. Tana jan hanci tana magana.

    “Wallahi Abba tun zancen tafiyar tunanin da nake ta yi kenan nima. Kasan ko taimako take nema ba lallai ta sanar da abokan tafiyarta ba. Gashi Allah Ya kawo mata sauƙi da wurwuri.”

    Murmushi Abba Habibu yayi da jin zancenta.

    “Hamdala ya kamata kiyi ba kuka ba.”

    Halifa kuwa cewa yayi
    “To yanzu dai gidan wa zamu je mu zauna don wallahi tsoron gidan nan zan ji idan mu biyu ne kacal”

    Zee ta ce “Abba mu tafi gidan Anti Zinatu ko?”

    Da tsokana Halifa ya ce “Malaminmu dai ya ce mata masu aure su dinga yin komai da izinin miji.”

    A fusace Zee ta tashi. Halifa ya fita da gudu ta bishi. Abba Habibu kuwa ya jinjina taimakon Allah mara yankewa. Ya gama tayar da hankalinsa sai gashi cikin sauki ya sami mafita.

    *

    Da ɗokin tafiyar nan Hamdi ta wuni jiya. Amma zuwa dare gabaɗaya jikinta ya mutu. Zee da Sajida da su ka yi waya ma babu ƴar zolayar nan da suke yi mata na ba saban ba za ta shiga jirgi. Hirar tafiyar Abban nasu ma sama-sama ta saka musu baki. Halifa kuwa dama list ya ce zai tura mata kamar yadda ya bawa Yaya. Harda cewa kada ta damu tunda Abba zai tafi zai rage wasu kayan.

    Yanayinta ya dami Taj sosai amma kuma bashi da kuzarin yawaita magana. Ya rasa mene ne yake ci masa rai ya hana shi walwala. Haka su ka kwana a gidan kowa da abin da yake kai komo a ƙirjinsa. Da safe su ka haɗu ƙarfe tara a harabar gidan Alh. Hayatu. Wata luxury bus ɗin gidan mai ɗaukan mutum talatin suka shiga direba ya kai su airport. Jirgin Abba Habibu sai uku. Su zasu shiga Qatar Airways, shi kuma zai shiga Ethiopia.

    *
    Saɓanin abin da ƴan uwan Taj suka yi zato na cewa zai dage sai Hamdi ta zauna kusa dashi kamar yadda tsarin boarding pass ɗinsu ya nuna, sai suka ga akasi. Daga zolaya a ka ce ta zauna seat ɗaya da ƙannensa sai suka ga ta tafi ko a jikinta. Zama tayi ta rufe idanunta tun kafin jirgin ya fara motsi. Taj kuma bai yi cigiyarta ba. Da Yaya Hajiyayye ta kula ne ta zo da kanta ta kamo hannunta.

    “Ina yi miki kallon wayayyiya za ki wani bari ƴan uwan miji su shigar miki hanci? Zaman me zaki yi a cikinsu bayan ga mijinki?”

    “Nan ɗin ma duk ɗaya ne.” Hamdi ta amsa da sanyin murya.

    “Duk biyu dai.” Cewar Yaya Hajiyayye. Ta kaita inda Taj yake. Ƙanwarsu dake zaune a wajen ta harara ba shiri ta tashi tana dariya.

    “Mu fa rigima muka so haɗawa. Muce sai ya biya zata dawo nan. Amma sun manna mana hauka ko magana babu wanda yayi.” Ta faɗi tana dariya.

    “Sun san me suka taka ne. Gashi nan babbar yaya ta shigar musu. To mu dai duk da haka sai an biya mu. Abaya za ka saya mana dukkanin mu.”

    Sai a lokacin Taj ya magantu bayan Hamdi ta zauna.
    “Dama ku biyun nan akan ku Alhaji ya fitar da zakka. Ƴan 419 kawai. Yahoo girls.”

    Ai kuwa me zasu yi banda dariya. Har Hamdi sai da tayi. Da aka yi sanarwar kowa ya zauna Taj ya saka mata seat belt sannan ya kama hannunta ya sarƙe da nasa. A lokacin taji komai ya kwance mata. Raunin zuciyarta ya ninku sosai. Ƙwalla ta taru ta cika idanun fal.

    “Happy” ta kira Taj da murya a shaƙe.

    Ya gyara zama “Uhmm.”

    “Me yasa na daina ɗokin tafiyar nan?”
    Bata jira yayi magana ba ta fashe da kuka mai tsuma zuciya.

    “Shhhh. Please….” ya ɗago haɓarta.

    Abin da ya gani bai yi masa daɗi ba. She looked so confused. Ya buɗe hannuwansa ya yi mata kyakkyawar runguma. Tayi kukan mai isarta amma bata ji sauƙi ba. Suna wannan yanayin har jirgin ya gama taxi ya tashi. Riƙon da tayi masa ne kawai ya ƙara ƙarfi amma bata yarda da ɗago kanta ba. Jim kaɗan bayan jirgin ya daidaita a iska Taj yaji riƙon yayi sako-sako. Ya ɗan girgizata bata motsa ba, sai ma kwanciya da ta gyara a jikinsa tana bacci.

    Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasul ya karanta ya tofa mata sannan ya ranƙwafa ya kwantar mata da kujerarta. Baccin mai nauyi ne ya kama ta. Yaji daɗi domin jiya shi da ita marathon ɗin juye juye kawai suka dinga yi. Ba ita ta farka ba sai da ya rage bai fi minti talatin su sauka a Doha ba. Za su yi transit na awa biyu sannan su kama hanyar Saudiyya.

    Kowa watsewa yayi an tafi window shopping. Masu ra’ayi kuma idan sun ga abin da suke sha’awa za su saya. Hamdi da Taj kaɗai aka bari. Suna zaune gadin kaya sannan ba hira suke yi ba.

    Yaya Hajiyayye tana ankare dasu. Bata jima ba ta dawo ta sanya su a gaba.

    “Wai har kun fara faɗa ne daga aure?”

    “Tuf, tuf, tufff” Taj ya kama tofi da baki.

    Kama ƙugu tayi ta harare shi
    “Ni kake tofewa Tajo?”

    “Kece ana zaman lafiya zaki kawo abin da babu.”

    “Ai naga sai wani basarwa kuke yi. Ko laulayi kika fara ne Hamdiyya?”

    Yadda ta sako maganar kai tsaye sai da Hamdi ta zabura ta hau rantse-rantsen ita bata da komai.

    Shi kuma Taj sai cewa yayi “ki ka sani ko akwai?”

    Wata uwar harara Hamdi ta watsa masa ba shiri.
    “Ni wallahi ƙalau nake.”

    Yaya Hajiyayye ta kallesu tayi dariya. Kunya duk ta kama Hamdi. Taj ya tashi yace ta taso su zaga su ma.

    “Indai da matsala Hamdi ki faɗa min. Ko baki yi karatu da Firdaus ba kinsan dai na haifeki. Taj ɗin ma…”

    Da sauri Taj ya katse Yaya Hajiyayye kafin ta gama bayar dashi a gaban matarsa.
    “Haba, haba Yaya Hajiyayye. A lissafin waɗanda kika haifa ai kinsan dai babu ni. Sai da na zama mutum fa aka yi miki aure.”

    “Wai ka zama mutum. Taj kaji tsoron Allah. Lokacin da kuke zuwa gidana fa ko tsar…”

    Da wani irin sauri Taj ya tashi yana dan dukan laɓɓansa a gabanta don tayi shiru. Tuni ta gano ashe ta ɗauko hanyar bada maza. Ita da Hamdi suka ƙyalƙyale da dariya.

    Ya harari Hamdi “Ke kuma meye abin dariya?”

    “Ba dariya nake ba ciwon kumatu ne ya kamani.” Ta bashi amsa tana gimtse wata dariyar.

    A haka Yaya Hajiyayye tayi amfani da hikimar manya ta mantar dasu damuwarsu. Su ka rankaya da ita wajen ƴan uwansu ana ta raha har lokacin boarding ɗinsu yayi.

    A gefe guda ta tsaya tana kallon ƙannenta lokacin da suke ta hayaniya ta saki murmushin da ya tsaya a fatar bakinta kaɗai. Jikinta a mace yake da nauyin tunani kala-kala. Zuwa yanzu ta riga ta tabbatar ko me zasu tarar idan sun haɗu da ƴan uwansu ba mai daɗi bane. Fatanta kawai Allah Yasa yazo da sauƙi.

    ***

    JEDDAH

    A cikin ƴaƴan Alh. Hayatu ashirin da takwas, mutum biyar ne basu sami damar zuwa Umrar da aka fake musu da ita ba. Daga mai haihuwa ko yau ko gobe sai uku a ƙasashen ƙetare, ɗayar kuma an saka mata ranar defence na Masters a Sokoto.

    Da suka sauka daga jirgi sun yi zaton Umra zasu fara yi. Dama Abba ya yiwa Taj kwatancen inda zasu same shi idan sun fito. Basu wahala ba kuwa suka hango shi a jikin wata farar bus mai girma. Direbanta yana ciki a zaune. Da murnarsu suka nufi motar sai dai Abba sam babu wani kuzarin kirki a tare dashi sai yaƙe.

    Tambayar da Taj ya fara yi masa da ya miƙa masa hannu ita ce

    “Ina Happiness?”

    “Suna hotel. Motar zata yi kaɗan idan dukkanmu muka taho.”

    “Ka san kuwa ni bana ƙaunar takura.”

    Kowa ya yiwa kanwarsu da tayi maganar dariya saboda ƙibarta sannan suka fara tafiya.

    Taj da Hamdi wuri ɗaya suka zauna. Tana jikin taga shi kuma yana gefenta. Duk motsinsa tana karanta yadda walwalarsa ta sake ɗaukewa.

    “Kamar kana cikin damuwa.”

    Ɗan guntun tsaki ya fara yi na frustration.
    “Kin san irin abin nan da mutum yake gane akwai matsala amma ya kasa pin pointing ɗinta?”

    Hamdi ta gyaɗa kai.

    “To haka nake ji.”

    “In sha Allahu ma babu komai.”

    Suka sarƙe hannuwansu waje guda har zuwa lokacin da motar ta fara slow. Nan fa hankalin kowa yayi mugun tashi. Sunan asibiti suke gani ɓaro-ɓaro. Daga jerin kujerun baya mafi kusa da direba Yaya Hajiyayye ta zura hannu ta kaiwa Abba duka a kafaɗa. Jikinta yana wata irin rawa.

    “Abba waye a asibiti? WAYE?” Da muryar kuka ta ƙara da cewa “Dama jikina ya bani wallahi”

    “Yaya ki bari mu shiga don Allah.”
    Abba ya bata amsa da sanyin jiki.

    Motar kuwa ta ruɗe da hayaniyar fargabar ƴan uwan. Direban na tsayawa suka dinga fita da sauri. Taj ne kaɗai bai fita ba kuma ya hana Hamdi tashi sai da kowa ya fita.

    “Ka tashi mu fita don Allah.”
    Ita kanta a gigice take.

    “Happiness ne fa bashi da lafiya. Ina jin ma babu shi gabaɗaya.”

    Tafin hannu Hamdi tasa ta rufe masa baki. Sai ga hawaye ya sauko daga idanunsa. Hamdi ta rungume shi ita ma ta soma nata kukan. Tayar da ita yayi suka fita gaba na faɗuwa. Suna sauka daga motar suka ga Ahmad da Mubina.

    “Hamdi ban so maganata ta tabbata ba. Kinga Dr. Mubina” ya nuno mata su “dalilin Kamal ta zo na tabbata.”

    Jikinta ya sake yin sanyi ƙalau har suka isa inda suke. Ahmad ya ɗan bugawa Taj kafaɗa. Mubina kuma ta rungumo Hamdi jikinta suka shiga lift kamar tana so ta rarrasheta. Mamakin hakan ya kama Hamdi. Ba wai bata damu da Kamal ba, amma a ganinta akwai waɗanda suka fita buƙatar rarrashi akan sa ko me ya same shi.

    Tamkar wanda bashi da laka Taj ya dinga tafiya da ƙofar lift ɗin ta buɗe. Suna yin kwanar farko ya hango zugar gidansu harda iyayen a corridor ana ta koke-koke. Taj ya kalli sama inda aka rubuta ‘Room 7’ sai yaji hankalinsa ya sake tashi. Wani zafi ya mamaye jikinsa. Bai san yadda aka yi ya isa gaban Alh. Hayatu ya tsaya ba.

    “Alhaji me ya same shi?”

    “Kidney transplant aka yi masa.”
    Ya bashi amsa amma hankalinsa yana kan Hamdi. Wani irin nauyinta yake ji.

    Taj yayi gaba da sauri zai shiga ɗakin idanunsa sun yi wani irin ja mara misali. Bishir ya riƙe shi da ƙarfi ya janye shi daga wajen. Umarnin likitocin Kamal ne suka ce kada a shiga ɗakin duk da ya farfaɗo. Yana buƙatar hutu sosai. Ita Hamdi bata kula da abin da ya faru ba. Hankalinta yana kan su Inna. Ta rasa me zata yi saboda kowa hankalinsa a tashe yake. Kawai sai ta duƙa da nufin gaishesu. Umma tayi saurin tareta a jikinta.

    “Tashi Hamdi. Zo mu ƙarasa can ki zauna.”

    Ta girgiza kai.
    “A’a zan zauna a nan nima.”

    Ga mamakinta da na sauran Alhaji da kansa yace ta bi Umma.

    “Ku je Hamdi.”

    Bata da zaɓi sama da bin Umman. Kallo duka sai ya dawo kanta. Haka ta bisu cike da tsarguwa. Me yasa za a ce ita kaɗai ta tafi? Ko sirri zasu yi? Ko dai Kamal ɗin ya…

    “Hamdiyya”

    Muryar Hajiya ce ta fito da yanayi mai ban tausayi. Hamdi ta juya ta ganta a tsaye. Hajiyan ta da ta sani da wannan dake gabanta da bambanci. Ramar da alamun rashin kwanciyar hankali sun yi yawa sosai.

    “Hajiya yaya mai jikin?”

    Hannuwanta Hajiya ta kama ta rufe da nata yatsun. Hamdi ta ɗaga kai taga Inna, Mama da Umma duka suna kallonta da wani irin yanayi na tausayi. Idanuwansu sun nuna alamun an sha kuka. A take jikinta ya soma rawa. A take taji gwiwoyinta sun saki ba za su iya ɗaukar nauyinta ba. Bata san jikinta ƙasa yake yi yana neman wajen zubewa ba sai da Hajiya ta rungumeta a jikinta.

    Da kuka Hajiya tayi mata magana suna wannan yanayin.
    “Hamdiyya na rasa me zan fara ce miki. Godiya zanyi ko haƙuri zan baki?”

    “Hajiya ku faɗa min abin da yake faruwa. Wallahi ji nake kamar zuciyata za ta buga don fargaba.”

    Jin haka sai Hajiya ta ja hannunta har gaban Inna ta haɗa hannuwansu.

    “Kai ta.”

    Gaba na matsananciyar faɗuwa Inna ta riƙe Hamdi har ICU ɗin mata. Ta jikin gilas ɗin ƙofa Inna ta nuna mata gadon da Yaya take kwance.

    “Wwwwaaaa..yyyyeee?”

    Ta matse hannuwan Inna ba tare da ta sani ba tana kuka. Jikinta kuwa tamkar mazari yana ta rawa.

    “Rage sautin muryarki kada ace mu bar wajen.”

    “Na rage. Nayi shiru….”

    Hamdi ta soma faɗi sai ta kasa ƙarasawa. Wani abu ta lura dashi daga yanayin kwanciyar mara lafiyan duk da bata ganin fuskar. Ta saki hannun Inna ta sanya duka hannuwanta ta dafa gilas ɗin ta sake kara fuskarta da kyau. Realization hit her kamar an jefeta da dutse.

    “Yaya?” Ta juya da sauri “Inna, Yaya ce a kwance?” Sai hawaye kamar famfo.

    Inna ta gyaɗa kai, itama wani sabon hawayen yana zubo mata.

    Kokawa Hamdi ta fara yi da ƙofar ɗakin sai dai ko gezau taƙi motsi. Inna tayi saurin riƙe mata hannuwa tana turjewa.

    “Yaya ce Inna. Ku barni na shiga.”

    “Ba za su bari ba Hamdi. Zo mu je nayi miki bayani.”

    Hamdi taƙi tashi sai kuka kawai da take yi tana roƙonsu da su faɗa mata gaskiyar halin da Yaya take ciki. Mubina ce ta tafi da niyyar kiran Taj suka haɗu a hanya. Muryar Hamdi ya jiyo shi ne ya taho da sauri.

    “Me ya same ta? Me aka yi mata take wannan kukan?”

    Mubina ta haɗiyi yawu. Ganin bata da niyyar faɗa masa sai ya ƙara sauri ya zagaya ta inda suke.

    Inna na ganinsa ta fara cewa “Taj kama min ita mu bar wurin nan kafin…”

    Riƙe hannunta yayi zai janyeta duk da cewa hankalinsa yayi masifar tashi sai yaji ta turje. Maimakon ta bishi sai ta janyo shi jikin ƙofar ta nuna masa Yaya ta gilas ɗin da ake hangota. Da sanyin murya mai tsinka zuciya Hamdi tayi masa magana.

    “Yaya ce. ICU aka rubuta kuma Yaya tana ciki. Ji nake duniyar ta tsaya min. Ka taimakeni…” ta juya tana kallon su Inna “ku taimaka min. Ku taimaka mata.”

    Ta sulale a ƙasa a hankali tana ajiyar zuciya. Kukan ma ya ɗauke mata. Taj kasa taɓata yayi saboda maganganunta tamkar almara yaji su. A kiɗime ya koma jikin gilas ɗin ya sake kallon wadda take kwance. Ya dawo ya riƙo hannayen Inna jikinsa yana tsuma

    “Inna da gaske Yaya ce?”

    Hannunsa da na Hamdi ta kama ta nufi hanyar lift. Su biyun a take suka nuna ba zasu fita ba.

    “Zaman ku babu abin da zai ƙara musu. Addu’a suke buƙata. Ku zo muje mu samu wuri nayi muku bayani.”

    Tana rufe bakinta Mal. Salisu mai shara ya iso wajen. Idanuwansa akan Hamdi suka tsaya. Inna ta lura da haka. Sai ta ce,

    “Ƴarta ce.”

    Mal. Salisu ya jinjina kai “wannan ne mijin nata ɗan uwan Kamal?”

    Inna ta gyaɗa kai.

    “To ku zo muje. Alhaji yayi magana da Dr. Hadifi ya sama muku inda zaku keɓe ku yi magana.”

    A baya su ka bi Mal. Salisu har zuwa bakin wata ƙofa ta wani ƙaramin ɗakin taro. A nan suka tarar da Alhaji, su Hajiya da Yaya Hajiyayye, Yaya Kubra da Dr. Mubina. Hamdi bata san da yaya ta ƙarasa shiga ciki ba. Ta dai ganta zaune a kusa da kujerar Alhaji. Kwantar da kai da murya yayi sosai babu isa da ɗagawa wajen yi mata bayani.

    “Dashen ƙoda aka yiwa Kamal. Ciwo yayi masa tsanani…”

    Hamdi bata tuna da wata surukuta ba ta katse masa hanzari a firgice tana kallonsa da dara-daran idanunta.
    “Ta Yaya aka dasa masa?”

    “Ki yi haƙuri Hamdi.” Mama ta ce cikin kuka.

    Tashin hankalin da ya sake bayyana a fuskar Hamdi har yafi na farko. Tana so tayi ihu, kuka ko ƙorafi amma duka ta kasa. Zuciyarta ce kawai take harbawa fiye da ƙa’ida. Taj duƙar da kai yayi ƙasa don bai ma san me yake ji ba a lokacin.

    Sai shiru ya mamaye wajen na ƴan daƙiƙu sannan Hamdi ta iya samun damar yin magana da dashashiyar murya.

    “Da izininta aka ɗauka?”

    Umma tayi gaggawar amsawa
    “Sosai. Mu bamu ma san ita ce donor ɗin ba sai da aka yi.”

    A hankali Hamdi ta ɗaga kai ta kalli Alhaji. Yayi mata kwarjini amma dole tayi masa tambayar dake ranta.

    “Alhaji don Allah ba tursasata aka yi ba?”

    Raunin muryar Hamdi a yayin da take kwaɗayin samun amsar da zata sassauta raɗaɗin zuciyarta ya shiga jikin kowa. Taj kam gabansa faɗuwa yayi. Idan amsar bata yi daɗi ba me zai ce da Hamdi?

    “Baiwar Allah ni nafi cancanta ki yiwa wannan tambayar.”

    Kowa ya kalli Mal. Salisu. Cikin tausasan kalamai ya sanar dasu yadda komai ya kasance har aka yi aikin. Abu na ƙarshe kuwa shi ne kunna musu audio ɗin Yaya. Kuka kuwa har su Inna da ba yanzu su ka fara ji ba. Ita dai Hamdi zuciyarta kusan tsayuwa tayi ma. Kukan kuma ya ƙi zuwa balle ta sami salama.

    “Idan kuna son sake tabbatarwa zan iya kai ku a nuna muku CCTV. Jiya sai da muka kalla tare da Dr. Hadifi wanda ya jagoranci aikin.” Ya ƙarƙare da cewa ” Malama Khadija ita ta kawo kanta asibitin nan da ikon Allah.”

    “Ya Allah. Ya Allah Ka basu lafiya. Allah Yasa anyi aikin a sa’a.” Hamdi ta shiga furtawa.

    Mamaki ya turnuƙe Alhaji da sauran mutanen. Ji wani irin tawakkali a tattare da ƙaramar yarinya. Domin ta ɗan sami sauƙi ya sanar da ita tahowar Abba Habibu wanda bata da masaniya. Ko a lokacin da ya faɗawa su Zee hanasu sanar da ita yayi. Ya san halinta. Bagarar da ita akan kada ta tsawaita tambaya zai fi wahalar da shi fiye da ƴan uwanta.

    Abin da kawai ta ce shi ne “Allah Ya kawo shi lafiya. Mungode.”

    Daga nan bata ƙara magana ba kuma bata yarda ta haɗa ido da kowa ba. Bata so ainihin damuwarta ta bayyana. Cike take da fargabar me zai faru da Yaya. Me ya hanata farfaɗowa? Idan gudan ƙodar ta sami matsala yaya zata yi?

    Hanyar banɗaki ta tambayi Yaya Kubra ta nuna mata. Taj yayi saurin tashi zai bita sai Ahmad ya sha gabansa har ta fara nisa.

    “Kuka zata je ta kuma yi” ya faɗi yana ƙoƙarin kaucewa Ahmad ɗin dake tare duk hanyar da ya bi.

    Tausayi Taj ya bashi sai dai a ganinsa Hamdi tana buƙatar ɗan lokaci ita kaɗai a wannan yanayin tunda babu kowa daga gidansu a kusa. A tausashe ya yi masa magana.

    “Allow her Taj. Let her cry.”

    Taj ya girgiza kai “she needs me. Don Allah ka bari na bita.”

    “Ɗan uwanka aka sakawa ƙodar mahaifiyarta fa Taj. Kamal ya farfaɗo amma ita tunda aka fito bata buɗe ido ba. So kake tayi ta murmushin ɗan uwanka zai tashi ko kuwa tayi kukan mamanta a gabanka? Give her that space ko na minti goma ne to sort her feelings please.”

    “Amma..” ya soma cewa cikin damuwa.

    Alhaji ya ɗora hannu a kafaɗarsa sai yayi shiru ya juya yana kallonsa
    “ka bi umarnin yayanka.”

    Haƙura yayi ba don ya so ba.

    ***

    A cikin banɗakin, Hamdi ƙulle kanta tayi ta fashe da kuka mai matuƙar ban tausayi. Tana yi jikinta yana rawa. Idan Yaya bata tashi ba ina zata saka kanta? Me ta taɓa yiwa iyayenta na kyautatawa da zata iya dogara dashi taji salama a bayan su? Wai ma wace magana suka yi ƙarshe? Wane hali Abbansu zai shiga? Tambayoyi birjik a ƙoƙon kanta. Tayi kuka sosai har sai da taji kamar hawayen ya daina fitowa sannan ta buɗe ƙofar ta fito.

    A inda take tsaye daga bayanta ƙofofi ne na toilet guda takwas. Gabanta kuwa dogon sink ne da kawonan famfo da madubi. A gaban madubin ne taga wata mata wadda da alamu balarabiya ce sai dai bata iya ganin komai illa idanunta. Sanye ta da abaya da niqab harda safar hannu. Hamdi ta kasa ƙarasawa gaban sink ɗin saboda kunya da taji tunda ta san dole matar ta gama jin kukan da tayi. Ga mamakinta matar sai ta ɗage niqab ɗinta. Ba yarinya bace. A ƙalla tayi hamsin a ƙiyasinta. Matar kawai buɗe hannuwanta tayi ta matso ta rungume Hamdi. Kamar tana jira ta ƙanƙame wannan complete stranger ɗin ta sabunta kukanta. Tana yi matar tana bubbuga mata baya har tayi mai isarta ta ɗago kai a kunyace.

    “Am sorry”

    Da turancinta irin na larabawa matar ta tambayeta “You lost someone?” (Rashi kika yi?)

    “No, my mother is in the ICU” (Mamana tana icu)

    Matar ta ce mata ta duba Husnul Muslim akwai addu’a sahihiya daga Manzon Allah SAW da ya ce musulmi su dinga karantawa a yayinda su ke cikin damuwa ko tashin hankali.

    (La’ilaha illallahul Azimul Halim
    La’ilaha illallahu Rabbul arshil Azim
    La’ilaha illallahu Rabbus samawati wa Rabbul ardi wa Rabbul Arshil Karim.)

    Da murmushi matar ta ƙara da cewa “Na rasa kalmomin da zan nuna miki alkhairi da albarkar dake cikin yi wa Allah kirari da wannan addu’ar. Ki yita da yarda, aminci da imani. In sha Allah za ki faɗawa wani a gaba. Allah Ya yaye miki damuwa.”

    Ba tare da musayar suna ko wani information game da juna ba suka rabu. Hamdi taji wani irin ƙwarin gwiwa tamkar Yaya ta tashi ta gama. Ta yabi Allah, tayi Masa godiyar haɗata da wannan mata sannan ta buɗe wayarta ta duba Husnul Muslim ta buɗe addu’ar ta fara yi. Da yake kuma ta ssnyawa zuciyarta cikakken yaƙini, nan da nan taji salama a ranta. In an cire jajaye kuma kumburarrun idanunta, za a iya cewa tafi kowa dauriya da ta koma cikin su Yaya Hajiyayye.

    Ko zama bata samu tayi ba Ahmad yace su tashi domin shirin tafiya Umra. Wasu cikin ƙannensa suka so kawo turjiya wai sai Kamal ya tashi zasu tafi.

    A fusace Umma ta daka musu tsawa ganin an kiransu ɗaya bayan ɗaya suna noƙewa kamar ƙananan yara.

    “Kai dalla can ku tashi. Na zata kuna da hankalin sanin cewa nacewa ibada ake yi idan ana da buƙata a wajen Allah SWT.”

    Babu shiri suka fara tashi. Ta harare su “in kuma zaman ku ka fi so sai a bada himma amma ba a nan ba. Yanzu ma alfarma suka yi mana aka bamu wajen zama.”

    Shi dai Alhaji yana kallonsu har suka fice bai ce uffan ba. Zuciyarsa gabaɗaya ta shiga tunanin da fuskar da zai kalli Abba Habibu idan ya iso. Ya ɓoyewa iyalinsa yadda suka yi da likitoci akan rashin farkawar Yaya da wuri. Amsar guda ce. Ta zubar da jini sosai a lokacin aikin. Duk da an saka mata wani, amma jikinta bai daidaita ba har yanzu.

    “Ya Allah, Ya Allah Ka rufa min asiri Ka bawa wannan baiwa taka lafiya” ya faɗi a hankali iya laɓɓansa.

    ***

    “Kin san Allah Yaya Zahra yau zan tafi gida. Na gaji! Ba zan iya ba.”

    Zahra ta kalli ƙanwarta Ilham dake tsaye ta sanya hannu ta riƙe ƙugu tana faman yin ƙwafa da motsa kai hagu da dama cikin ɓacin rai.

    “Ki gaishe da su Mama”

    Zahra kawai ta iya cewa da sanyin murya ta sami waje ta zauna akan kujera a falo. Alamun gajiya ta kowacce fuska sun bayyana a tare da ita. Da gani bata cikin nutsuwa.

    Ilham sai taji kunyar abin da tayi. Cikin jin nauyi ta zauna a kusa da yayarta ta ɗan dafa ta.

    “Ki yi haƙuri. Kawai gani nayi kina ta wahala da matar da ba wani mutumci ne da ita ba.”

    Da sauri Zahra ta kalli hanyar ɗakin Salwa inda Mami take kwance yanzu. Ilham ta gane tana tsoron kada Mamin taji ne. Sai dai ita ko a jikinta. Mami ta sirewa kowa a gidansu saboda ire-iren rashin mutumcin da ta dinga yiwa Zahra. A haka ma don ba gari ɗaya suke ba.

    “Na rasa me yasa Mama tace ki cigaba da kula da matar nan bayan ƴar cikinta ma ta gudu. Shima kuma Daddyn Hayat yayi tafiyarsa ya barki.” Ta taɓe baki “kada ki ji haushina amma Allah na tuba wace Umra zai tafi alhalin ya bar mahaifiyarsa a wannan halin?”

    Zahra ta girgiza kai “Ilham indai kin gaji ki tafi kawai.”

    Ilham ta sami waje ta zauna a kusa da yayarta. Jikinta yana bata akwai wata gagarumar matsalar a gefe wadda tasa dole Ahmad yayi nisa da gida a yanayin da ake ciki.

    “Yaya Zahra me yake faruwa ne don Allah? Ban kai matsayin da za ki faɗa min damuwarki ba?”

    Sai da Ilham ta zubar da hawaye kamar yadda Zahra take yi bayan ta sami amsar tambayarta. Cikin kuka ta sanar da ita abin da yake faruwa a gidan surukinta.

    Tayi mata bayanin tsaka mai wuya da Ahmad yake ciki wanda indai bata tausaya masa ba, bai kamata ta ƙara masa damuwa ba. Ga Maminsa a wannan yanayi. Ta sami labarin an saki su Salwa a wajen Ahmad amma har yau bata dawo ba. A gefe guda kuma ga Kamal a kwance, sun samu da ƙyar jiya anyi masa transplant amma daga nan ba za ta ɗorar da komai ba.

    “Amma Yaya Zahra su da suke da yawa don dai shi kaɗai ya dawo saboda mahaifiyarsa ai bai kamata ya zama laifi ba.”

    “Alhaji ko sunan Mami baya son ji. Kuma kinga abubuwan da Salwa ta janyo musu. I know he feels responsible shiyasa na tabbata nauyin faɗa masa yake ji. Sannan komai na gidansu shi yake sakawa a matsayinsa na babban ɗansa namiji. Wannan ma zai iya contributing.” Cewar Zahra a sanyaye.

    Ilham ta jinjina kai a hankali sai kuma ta kama dariya tana cewa “lallai aure ibada ne. Duk takurar da kike ciki amma kina auna komai ta fuska daban daban da yadda zai yi affecting mijinki.” Ta murmusa “na ɗauki wani gagarumin darasi. Na san dole yana alfahari dake”

    Zahra tayi murmushi “za ki cigaba da tayani zama?”

    Ilham ta zumɓura baki ta koma ta kwanta akan kujera alamun dai ta fasa tafiyar. Zahra kuwa ta daddage ta kai mata duka a ƙafa sai da tayi ihu.

    “Me nayi miki kuma?” Ta tambaya tana murza ƙafar.

    “Tayar min da hankali mana. Wai ni kike yiwa barazanar komawa gida ƴar rainin hankali.”

    Ilham ta tuntsire da dariya “sai ga Yaya Zahra an kwantar da kai ana marairaice murya.” Wani dukan Zahra ta kai mata ta miƙe babu shiri ta gudu.

    A cikin ɗaki, Mami ke kukan zuci ita kaɗai. Ga ƴan uwa, ga ƴaƴa amma babu kowa a kusa da ita!

    ***

    A wulaƙance Alh. Usaini yake duban Salwa. Tana durƙushe a gabansa ta fita kamaninta saboda tsabar naci. Shi ko ganinta baya son yi saboda yadda yake jin haushinta. Makauniyar soyayyarta ta janyo tonuwar asirinsa da lalacewar aikinsu gami da korar da mahaifinsa yayi masa. Da azal ta hau shi kuma ranar da aka sako su a titi ya ganta tana tafe tana jan ƙafa. Ya tsaya rage mata hanya da manufa guda…ci mata mutumci akan asarar da ta janyo masa. Sai aka yi rashin sa’a ashe ƙarfen ƙafa ya kwaso. Wani hotel ya tafi da ita yana ayyana azabar da zai gana mata. Ashe ita za ta gana masa.

    Salwa ta nace lallai sai ya kaita wajen malaminsa. Tana da tabbacin za ta sami kan Taj tunda ta shaida da idanunta yadda wancan maganin ya birkita masa lissafi. Ba don iyaye sun shigo ciki ba da yanzu ƙarshenta an fara shirye shiryen rufe Happy Taj.

    “Zan yi maka biyayya Alh. Usaini. Duk abin da kake so zan baka banda mutumcina.” Murmushi ƙayatacce ta saki sannan ta ɗora da cewa “Taj nake tanadarwa kaina.”

    Wani kallon banza yayi mata yana ɗage hanci kamar tsohuwa zata tsallake lambatu
    “Wai ke wawiyar ina ce? Ana so dole ne? Banda masifa irin taki waye ma yake ta soyayya yanzu? Life is all about money, money and more money.”

    “Ba za ka gane ba. Wallahi ni Taj ne rayuwata. Idan ban aure shi ba zan iya rasa raina.”

    “Ƙaryar banza. Me ya hana ki mutuwa tuntuni?” Ya ɗan sassauta murya “kinga ki zo ki tafi gidanku don Allah. Hotel ɗinnan sun hana ni fita saboda ke. Naje checking out ance sai mun fito tare don kada na bar musu liability.”

    “Ka taimaka ka haɗamu. Nayi maka alƙawarin ba za ka ƙara jin ko da suna na ba.”

    Wani baƙinciki ya tokare masa wuya. Ya tashi kamar zai kai mata duka sai ya fasa. Baya son janyowa kansa wata sabuwar rigimar.
    “Wayyo Allah na. Salwa ki tafi kada na illata lafiyarki.”

    “Zan jure. Wallahi ko me zaka yi min zan jure. Ka taimaka min.”

    A hasale ya zauna. Magana da mahaukaci ɓata lokaci ne. Ba don Allah Yasa mata basa gabansa ba da tuni sunan Salwa sorry. Ita ko tsoro bata ji ba take zaune da shi a hotel a ɗaki guda. Safe, rana da dare duka zancen ɗaya ne. Idan yana so tayi shiru sai dai in yana waya. To gashi ta ƙare masa. Duk wani wanda zai roƙar masa mahaifinsa ya yafe masa ya zare hannu a kansa. A halin yanzu bashi da tudun dafawa. Wannan ma yana daga cikin abubuwan da suka kashe masa gwiwar yi mata wani abu. Tunani da damuwarsa sun shallake ƙaramar lalurar Salwa ta son maso wani.

    Abin da bai sani ba shi ne akwai wata ƙanwar kakarsa ta wajen uwa da ta saka baki akan maganarsa. Ga tsufa ga lalurar ƙafa amma a haka tasa aka kaita gaban mahaifinsa har gida ta bashi haƙuri a madadinsa. Ganin girmanta yasa shi yafe masa. Bayan ta tafi ya saka aka binciko masa inda ɗan nasa yake. Bayan nan aka tabbatar masa da cewa tunda ya shiga hotel ɗin bai fita ba. Abin ka da ɗa da mahaifi. Sai ya tashi da kansa yace ƙanin Usainin ya kai shi.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!