Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-seven
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
A dalilin ba lokaci ɗaya aka saya musu ticket ba, wurin zaman Yaya da na abokan tafiyarta daban daban ne. Ɗan saurayin cikinsu Yaya tayi niyar bawa boarding pass ɗinta domin ya duba mata wurin zamanta, haka Abba Habibu ya sanar da ita tayi. Ya ceba inda mutum yake so zai je ya zauna ba. Ta ɗaga hannu za ta bashi Mubina ta riga karɓa. Ta kaita har wurin kujerar ta taimaka mata da ɗora hand luggage a sama sannan ta ɗaura mata belt. Ko ba a faɗa ba ta riga ta gane Yaya bata raɓa shiga jirgi ba.
Yaya tayi ta godiya da sanya mata albarka. Ita kuwa Allah Ya sani da biyu take yi. Kafin jirgi ya tashi bayan kowa ya zauna ta zo ta roƙi wadda take kusa da Yaya da cewa mamanta ce su ka yi musanyen seat. Wannan abu yasa Yaya jindaɗi matuƙa. Ta saki jiki da Mubina suna ta hira. Da jirgin zai tashi duk wani tsoronta Mubina ce ta dinga kwantar mata da hankali. Har aman da ta dinga ji Mubina leda ta bata sannan ta dinga shafa mata baya tana cewa ta hura iskar bakinta a ledar. A haka har su ka daidaita a iska.
“Allah Ya yi miki albarka Ya raya miki zuri’a. Ya jiƙan mahaifa.”
“Amin Mama.”
“Yaya yaran su ke kirana. Kema in babu damuwa ki dinga kirana da hakan.”
Da murmushi Mubina ta ce “to Yaya.”
Lokacin da aka kawo abinci Yaya bacci take yi. Mubina ta tasheta ta ci sannan da dabara ta sako zancen da ta zauna dominsa.
“Takardar nan ta passport ɗin ki naga jininki O- ne ko?”
“Ban dai riƙe ba amma tun a gida yara ke cewa O. Wani abin ne?”
Da sauri Mubina ta girgiza kai tana mai son ɓoye zallar farincikinta sai dai Yaya ta fi ta wayo.
“Babu wata matsala. Jinin naki mai kyau ne domin babu wata lalurar da za a buƙaci wani abu na sassan jiki da ba za ki iya taimakawa ba.”
“Ikon Allah. Ki ce idan na koma in nemi ƙarin sadaki a wajen Abban su Hamdi.”
Dariya Mubina tayi kawai sannan ta kuma tambayarta ƴaƴanta nawa.
“Huɗu ne.”
“Kin taɓa yin ɓari?”
“Wai, sosai kuwa. Biyu nayi kafin babbar. A tsakaninsu kuma yaran na ƙara uku. Wani lokacin sai na sa rai da cikin sai ya zube.”
Mubina bayani gamsashshe tayi wa Yaya game da rhesus da irin rawar da yake takawa idan aka sami saɓaninsa a tsakanin mata da miji wurin haihuwa.
“Ilimi kogi. Dole ake cewa tafiya mabuɗin ilimi. Kinga zaman abin da bai kai wuni ba amma na ƙaru.” Da yake ita ɗin akwai zurfafa tunani sai ta tambayi Mubina me yaja hankalinta har take ganin farinciki a tattare da ita game da jinin.
Kunya ta kama Mubina.
“Allah ni likita ce. Yana ƙayatar da mu ganin masu abin da wasu su ke buƙata ido rufe.” Tayi dariya “kada ki ce yau kin gamu da mayya.”
Yaya ma dariya tayi. Sai dai kuma daga lokacin ta dinga karantar Mubina. Akwai abin da take ganin ta ɓoye mata. Kai gani ma take tana son faɗa mata amma kamar tana jin tsoro. A zuciyarta ta ce ‘Allah Yasa alkhairi ne’.
***
Yau sun tashi jikin na Kamal kwata kwata babu daɗi. Anyi alluran, an saka ruwa amma duk da haka ciwo yaƙi sauka. Su Umma ke kuka Hajiya na rarrashinsu. Tun zuwansu ko sau ɗaya bata zubar da hawaye ba. Halin da ta riski Kamal a kullum gani take ba zai shiga wata sa’ar ba. Sai dare take zuwa asibitin. Kullum tana hanya daga Jeddah inda asibitin yake zuwa Makka ta wuni a Harami tana ibada. Ta zabge sosai kamar ba ita ba. Masu rarrashin nata kuma sun fita nuna rauni. Suna tausayin Kamal suna tausayinta.
“Yanzu Alhaji ace Kamal yana cikin wannan yanayi amma Taj bai sani ba? Anya kun yi musu adalci kuwa? Ka yiwa sauran ƴan uwansa adalci? Yau ko addu’a su ke yi masa ai zai sami rangwamen ciwo.” Cewar Mama tana zubar da hawaye.
“Kin fi kowa sanin cewa dukkaninsu sai sun taho. Ina gudun su zo a yanzu su haɗu wajen kashe masa ƙarfin gwiwarsa da koke kokensu.”
“Ka yi haƙuri amma wannan magana fa ba hujja bace. Yaron da ya tashi a gidan gandu irin namu ace yana jinya da jama’ar da ko rabin gidan basu kai ba ai zai ji babu daɗi.”
“Hajiyayye bata faɗa muku za su taho ba?”
“Ta faɗa. Kayi haƙuri. Na rasa me ya dace ayi ne.” Ta cigaba da kukanta “ko sake auna jinin nasa za ayi a tabbatar? Ko kuma…”
“Mama ki yi haƙuri”
Kamal ne ya yi maganar yana mai runtse idanuwansa. Komai a jikinsa ciwo yake yi. Magana ma da ƙyar yake cijewa ya yi.
Muryarsa da su ka ji ce tasa su duka matsowa kusa da gadon nasa suna yi masa sannu. A lokacin Bishir ya shigo da waya a hannu yana kallon Alhaji.
“Ya Taj ne wai yake ta neman Ya Kamal. Ya tayar da hankalinsa wai tun jiya basu yi magana ba. Me zan …”
“Kira min shi.”
Inna ta hana “Kamal yanzu ba lokacin da za ka biye masa kuna hira bane.”
“Bai sani ba Inna. Ki ka sani ma ko bamu da rabon sake ga..”
Umma bata bari ya gama magana ba ta ce “Ya isa. Kira masa shi Bishir.”
Kiran yayi amma Kamal ba zai iya karɓa ba sai Bishir ne ya kara masa a kunne.
“In ka fara neman mutum kamar tsohuwar bazawara ta fito neman miji.” Kamal ya faɗi yana murmushi da ƙyar.
Taj ya yi murmushi “Ba zan ji haushi ba balle buƙata ta taƙi biya.”
“Me ka ke so?”
“Tambaya zan yi maka. Please ka matsa daga inda su Alhaji su ke.”
“Na matsa. Mene ne?”
“Me Alhaji yake ɓoye mana ne Happiness? Tun tafiyarku hankalina ya kasa kwanciya. Amarcin ma na kasa sakin jiki nayi abuna yadda ya dace.”
“In na yarda da kai in tafi a tsaye. Akwai damuwar da zata sa ka kasa amarci?” Yana maganar ne ido a rufe don baya son haɗa ido da iyayensa.
Ai kuwa hatta Alhaji sai da duka su ka yi dariya. Kamal ya nuna wa Taj lallai komai lafiya ƙalau. Ba yadda ya iya dole ya yarda.
“Mun haɗu da Mubina a airport da mu ka raka Yaya. Anya ibada ku ka je yi kuwa?”
Nan ma Kamal dariya yayi. Shi da Alhaji sun san da zuwanta. An kuma faɗawa su Hajiya. Ta ce duba shi za ta zo yi amma kowa ya san zuwan nata na sallama ne. Bakunan su ne dai ba za su iya faɗin abin da yake zuci ba. Sun cire hope.
“Happiness amana…”
“Me?” Kamal ya dawo daga tunani. Bai ji me Taj yace ba.
Taj ya sake maimaita cewa zai bashi amana. Ya sanar dashi lalurar da ta same shi da abin da su Salwa su ka yi. Shi ya so fara faɗawa amma ya gagara samunsa a waya. Hankalin Kamal ya tashi sosai.
“Ka yi min addua kafin na zo. Idan ban warke ba to ka shirya. Ni yara 12 za a haifa min kuma cin mu da sha duka wuyanka zai dawo.”
“Har wasa kake yi da abu mai mahimmanci irin wannan?”
“Ina da kai Happiness mene ne zai dame ni? Amma nayi tunanin za ku j8 zancen a wajen su Alhaji fa. Sai naga da kai da su Bishir shiru. Ya Ahmad kuma kunyar nemansa nake yi.”
“Da gaskiyarka. Amma na san ba zai riƙe ka a rai ba. Yana masallaci.”
Suna gama wayar, Hamdi dake zaune kusa da shi tana shirya akwatin tafiyarta ya fuskanta.
“Kin san Allah, akwai abin da yake faruwa mai girma da su Alhaji. Yau kwana nawa a ce babu wanda ya faɗawa su Happiness abin da ya faru?”
“Maybe don kada su tashi hankalinsu tunda ibada su ka je” ta faɗa domin kwantar masa da hankali.
“Allah Ya kai mu gobe. Idan ma akwai wani abu zan gani.”
“Me yasa ba za ka yi tunanin komai lafiya ba?” Hamdi ta sake faɗi.
“Saboda jikina yana bani cewa akwai problem. Kin tuna abin da ya faru daga ciwon kan da nayi a wurin dinner? Saboda damuwa gida Alhaji ya mayar dani. Sai yanzu da na faɗa musu hancina da harshe sun zama useless ne su ke nuna min rashin damuwar da nayi tsammanin gani.”
Zungure shi Hamdi tayi tana murmushi “wannan dai rigima ce kawai da shagwaɓa. To taho in jajanta maka. Ni ai ba na kira komai naka useless ba.”
Taj ya saki fuska yana murmushi. “Allah ko Mrs Happy?”
“Kana musu ne?” Ta kashe masa iso.
Aikin da take yi ya nemi rabata da shi taki yarda tana yi masa dariya. Yanayin damuwar da ya shiga ya kau. Ya koma tsakaninsu sai tsokanar juna.
“Wannan akwatin kin haɗa shi ya kai sau goma.”
“Ba fa zan damu ba idan ka tsoka ne ni akan wannan tafiyar. Kuma baka ga komai ba. Rawar kai sai na saka harami.” Ta tashi tana buɗa kafaɗa “kai dai Allah Ya kai mu.”
“Amin.”
***
Daga airport ya kamata su raba tafiya da Mubina. Su Yaya Madina za su fara tafiya ita kuma cikin Jeddah za ta ƙarasa asibitin da Kamal yake mai suna King Abdul Aziz Medical City. Yadda ta dinga bin Yaya tana taimaka mata da abubuwa duk da cewa abokan tafiyarta ma suna ƙoƙari duk sai ya dami Yaya. Jikinta ya bata akwai wata a ƙasa. Kafin tayi tambayar ne Mubina ta ce za ta shiga banɗaki. Yaya sai ta nemi su jira domin su yi sallama.
Zuciya cike da tunani da fargaba Mubina ta shiga banɗaki. Ta shige guda ta rufe kanta kawai ta fashe da kuka. Duk yadda take son Kamal ta sani cewa idan Yaya mahaifiyarta ce ba za ta yi na’am kai tsaye ta bada ƙodarta ba. Uwa fa aka ce. Ina adalci da sanin ya kamata idanta ingiza wadda bata sani ba tayi abu saboda nata son zuciyar?
“Allah Ka yafe ni” ta faɗa tana sake goge hawaye.
Tana buɗe ƙofar tayi ido huɗu da Yaya.
“Lafiya dai ko Mubina? Na ji ki shiru.”
Murmushi ta kama yi na dole “abu ne ya shigar min ido. Kin gan shi yayi ja ko? Mu je na ɗauki kayana kada na sa ku yi dare a hanya.”
“To” Yaya ta ce ba don ta yarda ba.
Da su ka fito taxi Mubina ta shiga. Yaya na kallo motar kawai taji wani abu ya tsungule ta. Jakarta ta hannu ce kawai a jikinta ta dubi matan tawagar tasu ta ce musu tana zuwa.
“Maman Sajida ina za ki?”
“Ku wuce Madinan don Allah. Zan same ku da yardar Allah.”
Suna ta tsayar da ita amma ina. Da irin nata saurin ta shiga tasin gabanta ta nuna masa wadda Mubina ke ciki tana shirin barin harabar airport ɗin.
“Haza sayyara” ta nuna motar, shi kuwa ya gane ya gyaɗa kai “to yalla-yalla, ta’al-ta’al. Kuḍi, uhmmm, riyalai haqibatun” ta jijjiga masa jakarta.
Bawan Allah damuwar da ya gani a tare da ita ta ishe shi. Kuma duk daƙiƙancin mutum dole ya gane me ta faɗa. Zama ya ce tayi ya kwashi mota su ka bi su Mubina.
Tafiya kamar ba za ta ƙare ba. Wajen minti talatin sannan motar ta tsaya a bakin asibitin. Yaya ta bari sai da Mubina ta shige ta wajen wata ƙofar gilas da wani yaro mai fuskar Taj yake tsaye yana jiranta sannan ta bi bayansu. Haka kawai ta dinga jin faɗuwar gaba. Tana tafiya basu ganta ba har su ka shiga lift. Nan fa ake yinta. Na farko bata taɓa shiga ba kuma bata san inda za su je ba. Ita a tunaninta ma ƙofar ɗaki ce. Ta tsaya a jiki ta fara ƙwanƙwasawa sai ga wani mutum. Ya tsayar da lift ɗin taga ƙofa ta buɗe amma basa ciki.
“Ya Hayyu Ya Qayyumu. Ina su ka ɓace kuma?”
Kamar daga sama sai taji kuka a bayanta. Juyawar nan da za ta yi taga Hajiya ce a birkice. Babu ɓata lokaci sai ta shiga tunda Hajiyar ma ya shiga kuma san bata lura da ita ba. Addu’a take yi tana wani irin kuka. Alhaji da kansa ya yi kiranta ya ce ta dawo jikin Kamal babu daɗi.
“Allah na gatan bawa. Ya Rabbi ga Kamal. Ubangijina ka ƙara rufa min asiri akan ƙaddarar rayuwa. Allah kada in yi saɓo. Ka taimakeni Ya Rabbi. Wayyo Allah. Allah Ka dubi Kamal.”
Yaya ta gama sarewa da lamarin nan. Me ya sami Kamal wanda su Taj basu sani ba? Tayi imanin babu abin da zai zaunar da Taj yana raha a gida bayan lalurar da same shi da ya san ɗan uwansa yana wani hali.
Da sassarfa Hajiya ta fita daga lift ita ma Yaya tabi bayanta. Don ma tana ɗan jiri saboda rashin sabo. Ƙofar ɗakin a buɗe take. Tana hango Kamal a kwance da likitoci a kansa. Fuskarsa ɓoye cikin abin shaƙar iska. Don dai taji Hajiya ta ambace shi ne ta gane shi. A ƙofar ɗakin Yaya Kubra ce ta rungume Alhaji tana kuka. Inna, Umma da Mama kowacce fuska jiƙe da hawaye. Mubina kuwa gefen bango ta samu tana wani irin kuka a hankali. Bata yi tunanin ƙarasawa garesu ba. Ta tuna kalaman Mubina ne kawai. Wani likita na fitowa daga ɗakin Yaya ta bishi da sauri. Hankalinsa a tashe kamar ba zai tsaya ba sai kuma ya tausaya mata. Saurin da take yi da ƙafarta a haka ya san akwai wahala.
Yaya ta nuna ɗakin ta sake haɗo larabcinta na islamiyya a karo na biyu.
“Haka gurfa…” ya gyaɗa kai “to ma haza Kamal?”
Likitan ya kalleta yana son yi mata bayani amma sauri yake yi. Juyawa yayi sai ta kuma kiransa. Da ya juyo zai nuna mata inda za ta je reception idan taimako take nema sai ta miƙa masa takardar nan da aka rubuta jininta.
“O netif (negative)” ta nuna ƙirjinta “Kamal ahali (ɗan uwanta ne).”
“Alhamdulillah” ya fara cewa zai koma ɗakin ta girgiza kai.
“Hausa…a nemo mai yi min Hausa.”
“Hausa? Nigeria? Kano?”
“Nace maka ahali ai su ɗin” ta kuma nuno ɗakin.
Ya gyaɗa kai kuwa ya ce ta biyo shi. Suna tafe yana buge bugen waya. Bata san cigiyar mai jin hausa yake yi ba. Ba a wahala ba ya samu. Mai shara ne amma ya tadi gida. Ba shi da nisa dai. Wuri mai kyau aka bata ta zauna har mutumin ya zo. Ɗan Katsina ne yake aiki a nan. Shi likitan ya faɗawa ya tambayeta alaƙarsu. Sun yi mamakin wai wan mijin ƴarta ne Nan da nan ta faɗa. Sai ya sanar da shi ciwon Kamal da abin da yake buƙata. Yaya ta dafe ƙirji da fari. Sai kuma kawai ta fashe da kuka tana faɗin,
“Allah Hakimu. Allah Hakimu.” Daga ƙarshe ta ɗauko wayarta ta nuna nambar Abba Habibu ta ce a kira shi. Likitan da kansa ya kira.
Yana ganin baƙuwar namba ta Saudiyya ya ɗauka. A kiɗime yake sosai. Abokan tafiyar sun kira gida sun ce a faɗa masa abin da ya faru. Bai riga ya sanar da su Sajida ba amma ya gama gigicewa.
“Ina kika je? Kin jefa ni a wani irin tashin hankali.”
“Allah Ya huci zuciyarka Yayana Habibu. Tuba nake Abban Sajida.”
Murmushi ya yi “yanzu kina ina?”
“Asibiti.”
“Baki da lafiya ne?” Ya sake tashin hankalinsa
“A’a, alfarma nake nema domin babu lokaci.”
“Kin fara tsorata ni. Me ya faru?”
“Yaya Habibu mijin Jinjin miskiniyar Allah. Da uwata da ubana Allah Ya gatance rayuta da iyayenka. Kirari nake maka mijina a duniya da ƙiyama. Ƙanin Zeenatu uban Zeenatu ɗawisun zuciyata. Domin isa da alfarmar Mai Duka kayi min lamuni in share hawayen wata uwa kamar yadda Allah Ya share mana ranar auren yaran nan”
“Me kike so?” Ya ce da tsinkakkiyar zuciya.
“Ceton rai zan yi!”
“Kiyi min magana yadda zan gane.”
“Wallahi ba zan iya ba. Amma ina so ka sani cewa ikon Allah ne ya kawoni ba tanadinmu ba. Komai da yake faruwa damu daga tsarin Mai Kowa da Komai ne.”
“Jikina rawa yake yi. Idan na hanaki za ki haƙura?”
“Sosai kuwa. Amma ina da yaƙinin cewa kai ɗin kafi kowa kyawun zuciya a duka mutanen da na sani. Duk abin da za kayi domin ka taimaki wani kana yi. Shi yasa Allah ba Ya barin kowa yaga bayan ka.”
“Khadija.” Ya kirata da sunanta na gaskiya.
“Yayana.” Ta amsa da dakakkiyar murya don bata son komai ya karyar mata da zuciya.
“Ki kira ni idan kin gama. Tsoro mai girma ya shiga zuciyata. Amma naji ba zan iya hanaki ko mene ne ba. Allah Ya baki ikon yin taimakon ba tare da kin wahala ba.”
“Amin.”
Sallama su ka yi ta ce ta shirya. Likitan ya kira hukumar asibiti ya sanar. Komai cikin gaggawa ake yi saboda Kamal ya kai wata gaɓa mai sammatsi. Aka gama cike ciken takardu sannan aka bata form ta cike da taimakon mai sharar nan da yake karanta mata ya fassara.
Daga nan lab aka je aka yiwa Yaya dukkan wani gwaji na dacewa. Sakamakon da aka samu sai shukura. Likitan ya ce su je wajen su Alhaji ta ce a’a. Kawai a zo ayi. Ɗaki VIP aka bata ta zauna kafin a shiryo Kamal. Tana zama ta dubi mai sharar nan. Ɗan dattijo ne kamar Abba Habibu.
“Yaya sunan ka ne Malam?”
“Salisu.”
“To Mal. Salisu recoder nake so ka kunno min a waya zan yi magana. Idan an fito daga aikin ka kunnawa su Alh. Hayatu.”
A wayarsa ya kunna ya bata. Ta kara a bakinta ta soma magana. Kalaman da take yi sun shige shi fiye da tunani har ta kai yana zubar da ƙwalla.
*
A ƙofar ɗakin su ka dinga zubewa suna sujjadar godiya ga Allah. Likita ya ce an sami donor amma ba a bari sun san waye ba. Mubina sai da ta tuno Yaya. Sai tayi murmushi tana godiya ga Allah da bata yi mata magana ba.
Kamal bai san a inda yake ba har aka gama komai aka shiga tiyata. Kamar wasa sai da su ka kwashi awa huɗu ana abu ɗaya sannan aka kammala. Addu’a kam da shi da Yaya duk sun sha ta sosai.
*
ICU aka gangara su su biyun domin kulawa ta musamman sannan wanda ya jagoranci aikin ya zo ya sami su Alhaji. Fuskokinsu duka babu nutsuwa. Yana tsayuwa su ka taso gabansa.
“Alhamdulillah, it was a success.”
Kowa sai hamdala da ajiyar zuciya suna rungume junansu.
“What about the donor?” Alhaji ya yi tambayar dake gabansa.
“He” likitan ya nuna Mal. Salisu yana murmushi “will explain.”
Kallon rashin sani su ka yi masa. Ya murmusa ya ce dama basu san shi ba. Shi kuma bashi da wata alaƙa da donor ɗin. Amma ga saƙon da ta ce a kunna musu idan an fito. Daga gyaran muryar Mubina ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba da ta gane Yaya ce.
(Assalamu alaikum wa rahmatullah. Suna na Khadija Yusuf wadda aka fi sani da Jinjin matar Habibu.)
“Wannan ba muryar Yayan Hamdiyya bace?” Umma ta soma magana da wata irin kaɗuwa.
“Ku saurara” Alhaji ya karɓi wayar don ji yayi duk wani gashi na jikinsa ya miƙe tsaye.
(Na bawa Kamal ƙoda ba bisa tilastawa ko cinikayya ba. Cikin Hikimar Allah maigidana ya biya min kuɗin Umara da tanadin shekaru. Sai gashi ina zuwa Allah Ya yi sanadin da naga Kamal a yanayin da nayi imanin ƴan uwansa na gida basu sani ba. Kuma ni kaɗai ce Allah Ya ni’imta da damar taimaka masa a kusa. Lallai Girman Ubangijina ba abin wasa bane. Ya tsara komai daki daki ni wace ce da zan fahimci hakan kuma na juya baya? Na aminta saboda Kamal na zo a wannan rana. Allah Yasa lafiyar ta samu. Ina fata mahaifinka ba zai ƙyamaci rayuwarka da ƙodar miskiniya ba. Abu na biyu kuma idan ban tashi ba don Allah ku faɗawa Abban su Sajida ba a bina bashi kuma ni ma bana bi. Na sallami kowa kafin na taho. Akwai banki a ƙasan gadona. Na tanadin auren Halifana ne. Sajida, Hamdi da Zeenatu don Allah ku haɗa kai ku zama sirrin juna da ƙaninku. Ina yi muku fatan Allah Ya albarka ce ku a duk inda kuke. Allah Ya tsayar da ku duka akan ƙafafuwanku ta yadda babu wanda zai zamewa wani nauyi a gaba balle har ya ƙosa a sami tawayar zumunci. Ku bawa Abbanku goyon baya ya sake aure. Yaya Habibu Allah Ya gatance maka kamar yadda kayi min. -Cikin kuka ta cigaba da magana- bakina ba zai taɓa daina yabonka ba har numfashin ƙarshe. A wajen wasu ka gaza, a wajena kuwa a wannan zamani babu mai martaba da daraja kamar ka. Allah Yasa Habibu ne mijina a lokacin da Allah Ya sabunta min halitta da miƙaƙen jiki a aljanna. A ƙarshe don Allah ku roƙa min gafarar iyayena. Ku cewa Baba ina gaishe shi. Ku bawa Innata haƙuri.) Sai ta ɗan ja hanci (umara na zo ashe bani da rabon ganin ɗakin Allah da ziyarar masoyina. Amma Alhamdulillah. Kamal da zuciya ɗaya zan taimaka maka. Allah Ya bamu alkhairi. Nagode.)
Audio ɗin a nan ya ƙare. Mal. Salisu ya faɗa musu yadda ta sanar dashi zuwanta asibitin. Mubina ta biyo ba tare da ta sani ba.
“Wallahi ban sani ba. Kuma ni bamu yi zancen da ita ba.” Mubina ta faɗi a ruɗe.
“Hikimar Allah aka ce Dr. Mubina. Magana ta ƙare.” Inna ta faɗi tana ɗan bubbuga mata baya.
Alh. Hayatu kuwa juyawa yayi zai bar wajen. Ahmad ya bi shi da sauri. Su Hajiya ma tambayarsa au ke yi ina zai je a wannan yanayin.
“Ashe duk baku ji lokacin da ta ce Umra ta zo ba?”
“Mun sani dama. Taj ya so mu jinkirta tahowarmu tunda ita kaɗai ce mu ka ƙi. Ashe saurin da muke yi ita ce maganin komai.”
“Ahmad samo min mota na koma hotel na sako harami na.”
“Alhaji…” Inna ta soma magana.
“Idan bata tashi ba fa? Umrar zan yi mata. Ai ya halatta ka yiwa wanda bashi da dama ko?” Yayi tambayar ga Mal. Salisu.
“Ana yi.”
“Nima zan yi mata” Hajiya ta share hawaye ta miƙe tsaye.
“Nima”
“Nima”
“Nima”
Sai da ya rage Bishir kaɗai sannan Alhaji ya ce ya haƙura kada a bar asibitin babu kowa. Ahmad ma zama ya yi saboda Alhaji ya bashi aikin neman visa da ticket ko nawa za a kashe domin kawo Abba Habibu.
Da su ka fita a mota abin mamaki ga iyalinsa dake baya bai wuce yadda yake ta goge idanunsa da bayan hannu ba. Yau Alh. Hayatu ne yake kuka akan wani ba jininsa ba. Tun yana yi a zuci har ta kasance suna jin shessheƙarsa. Wannan yasa babu wadda bata bayyana nata kukan ba. Direban tasi ɗin yana son tambayarsu amma kasa. Sai haƙuri kawai yake basu.
Jiransu su ka buƙaci yayi su ka shiga hotel ɗin su ka yi haramar Umra kamar yadda yake a tsare cewa mai shiga Makka daga Jeddah nan ne Miqatinsa. Mutum biyar su ka fito a tare. Alh. Hayatu, Haj. Gambo, Mama A’i, Umma Jamila, Inna Abu da Sulaiman Hayatu Sule (Abba) da niyyar yiwa Jinjin ɗin Abba Habibu Umra a ƙasa Mai Tsarki.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
