Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty-two
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
“Salwa kuma Alhaji? Wani abu tayi?”
Ahmad ya yi tambayar ne saboda a tunaninsa ciwon Kamal kaɗai ya isa ya gigita Alhaji. Me zai sa ya tuna da Salwa har ya nemi a taho da ita a lokaci mai mahimmanci irin wannan?
Gwiwa a sage ya tambaye shi “Laifi tayi ko?”
“Kai dai ka taho min da ita.”
Yana bashi wannan amsar ya gane ko ma mene ne ba abin wasa bane tunda lalura mai girma kamar ciwon ƙodar Kamal bai hana shi nemanta ba. A kitchen ya same ta da himilin kwanuka kamar a gidan ake taron biki. Ko tausayi bata bashi ba don taurin kai da kafiya gami da son zuciyarta ne ya jawo mata. Abu guda ne dai. Ya sanyawa ransa sai ya bi kadin dukan da aka yi mata a cikin gidansa. Su Habitti ba a ci bulus ba. Muƙullin mota ya ɗauka ya ce da Zahra kiransa ake yi a gida game da bikin Taj ya fice.
Da ya kira Salwa su tafi ba ƙaramin rawar jiki ta dinga yi ba. Bata san ina za su je ba amma hankalinta duk ya tashi. Tayi zaton ya canja shawara ne zai kai ta tasha ta koma gida. Ta dinga bashi haƙuri da magiya. Bata san damuwarsa ta ninka duk wani abu da ya shafeta ba. Ciwon Kamal ya ɗaga masa hankali sosai.
Haƙurin da take bayarwa kamar ba shigarsa yake ba. Shi ne ta koma barazana
“Yaya Ahmad kada ka ɓata kuɗinka. Ba zan tafi ba domin na tabbata Taj zai zo gareni da ƙafafunsa. Ko mun je Bauchi zan shigo wata motar na dawo.”
Ko ci kanki bai ce mata ba. Bashi da wannan lokacin. Ita kuwa bata sam ta shiga one chance ba sai da ta gane hanyar ina su ke bi. Ta zaro idanu da su ka ƙanƙance cikin kumburarriyar fuskarta. Ta kama ƙofa a tsorace tana kokawar buɗewa a titi.
“Me za ka kaini ayi min? Yaya Ahmad buɗe min na fita.”
A haukace take dukan gilas tana neman yi masa ɓarna. Ya juyo ransa yana suya ya daka matsa tsawar da ta gigita ta. Saboda tsorata da tayi a lokacin da za a tambayeta sunanta da wuya ta faɗa farat ɗaya.
“Salwa!!!”
Laƙwas tayi a kan kujera har su ka isa. Su ka shiga falon tare ya sami gidan a cike fam. Zuciyarsa a take ta faɗo ƙasa daga ƙirjinsa saboda mummunan tunanin da ya zo masa. Allah Ya taimake shi su na ganinsa aka soma bashi labarin abin farincikin da aka wayi gari dashi a gidan. Idanunsa su ka sauka akan Kamal zaune a tsakiya. Wata irin ajiyar zuciya yayi mai ƙarfi sannan ya sami damar sakin ransa ya shiga cikinsu. Ko gaisawa basu gama yi ba Alhaji ya buɗe ƙofar ɓangarensa ya kira shi.
“Ahmad kai fa nake jira.”
Da saurinsa ya tashi har yana tuntuɓe. Kamal ya sha jinin jikinsa. Ƴar hira da dauriyar da yake yi ya kasa jurewa. Ɗakinsa zai koma kawai kafin Alhaji ya neme shi. A hanyar fita ya yi kiciɓus da Salwa. Da yake bashi da masaniyar me yake faruwa sai bai canja mata ba.
“Salwa? Ashe tare kuke ki ka tsaya a nan?” Ya kalli fuskarta “me ya same ki haka a fuska?”
Yuuuu idanu su ka dawo kanta. Jiki a mace kamar magen da aka tsamo daga lamba two ta ƙarasa ciki tana raɓe raɓe. Ƴaƴan gidan dai babu sauyin fuska amma iyayensu ko kallonta basu yi.
“Zamewa nayi.”
“Allah Ya sauwake” ya ce ya fita.
Ita kuma ta ƙaraso aka gama yi mata sannu sannan ta matsa gaishe da su Inna.
“Hajiya ina kwana?” Ta durƙusa a gabanta.
“Lafiya” ita ce taƙaitaciyar amsar da ta samu ba tare da sakin fuska ba.
A ranta tayi tsaki. Ai dai ba ita ce ta haifi Taj ba take wani sha mata kunu. Ko ita Innar bata fi ƙarfin a kai sunanta gaban malam ya ƙulle mata baki ba. Nan gaba ma wajen malamin Ummi za ta je domin da alama zai fi na Mami iya aiki. Muskutawa tayi ta ƙara matsowa ciki.
“Mama…”
Mama bata jira ta gama gaisuwar ba ta tashi abinta tana duban Amma.
“Uhmmm, Jamila duba ki ga me Taj da Hamdiyya suke yi a ɗakin nan har yanzu shiru.”
Jin furucinta yasa gaban Salwa ya faɗi, ya sake faɗuwa. Baki ya kama rawa kamar mazari ya ji kiɗa. Dama ga fuska a kumbure. Sai tayi wani irin yanayi mara kyau duk suna gani.
Umma tayi dariya “kema dai Mama da rigima kike. Ba kya ko tsoron me za a buɗe a tarar? Sabon aure basa son sa ido fa. In ba haka ba kuwa sai aji kunya.”
Inna tashi tayi zumbur ta bar musu wajen. Su ka dinga dariya banda Amma da bata gane manufarsu ba.
“Takwara me ki ka mayar min da ɗa ne? Ki ka sani ko bacci ya samu tana yi?”
“Sai ya zauna korar mata sauro ko?” In ji Hajiya.
Umma da Mama sai shewa harda tafawa. Ƴaƴan na gani amma su ma basu san me ake yi ba.
Ita dai Amma tashi tayi ta barsu suna kallon suman zaunen Salwa a fakaice. Ta zubawa ƙofar ɗakin Inna da Amma ta nufa ido tana jiran ganin da gaske Hamdi za ta fito daga ciki ko yaya? In tana ciki me ya kawota gidan da sassafe? Ko dai ita ma murnar ta zo taya shi? Ai kuwa da an kira iyayenta marasa kamun kai. Me zai hana su jira ido na ganin ido? Don baƙin naci an biyo shi har gida a lokaci irin wannan da yake buƙatar ahalinsa.
*
Duk da ba komai Amma ta ji ba amma iya maganganun da su ka shiga kunnuwanta sun fahimtar da ita me yake faruwa. Akwai wani abu da Alhaji ya yiwa mahaifin Hamdi. Jikinta kuwa ya yi sanyi sai dai wayewa da sanin yau da gobe yasa ta je musu da fuskar rashin sani. Bayan ta gama ɗorawa Taj laifin hana Hamdi zuwa cin abinci, sai ta shiga ta riƙo hannunta.
“Sai da na shigo nake jin ashe jiya rigimar babanku ta haɗa dake.” Hamdi ta sunkuyar da kai kawai tana murmushi “Zo ki ci abinci in kai ki gida in kuma bada haƙuri kada ace ba za a bamu ke anjima ba.”
Sake yin ƙasa Hamdi tayi da kanta cike da kunya. Balle da Taj ya ce shi zai kai ta.
Ya ce da Amma “Akwai maganar da za mu yi da ita.”
“Fita idona Taj.” Ta harare shi.
“Please mana Ammata.”
“Don ƙaniyarka ka san irin bikin da ake ta yiwa Hamdi a falo?”
“Ni kuma?” Hamdi ta fito da idanu.
Amma kuwa sai dariya ta sami damar tsokanarta domin a yanayin fuskokinsu ba za ta so su fita ba. Gidan akwai manya da masu experience da yawa. Yanzun nan za a harbo jirginsu a gane da matsala.
“Harda masu cewa ko a biyo ku da abincin nan idan ya so sai muje mu karɓo miki kayanki a gida.”
“Ya Rabbi, to ya zan yi? Ko kada na fita?”
Kai da ganin idanunta da jin muryarta ka san hankalinta ya nausa da nisa. Kunya, tsoro da jin nauyi sun cika mata ciki. Da Taj ya dubeta sai da yaji kamar ya kamota a gaban Amma ya ɓoyeta cikin jikinsa. She looked so cute and innocent kamar ba bakinta bane ya gama zaro masa zantuka ɗazu.
“Wasa take yi miki. Ko Amma?” Ya rage murya shi ma ɗin ba son jin wata magana babba yake yi a bakin ƴan gidan nasu ba.
Dariya Amma tayi musu. Tana yi musu fatan alkhairi a zamansu. Sun dace sosai da juna. Sweet young Hamdiyya and Charming Happy Taj. Za ta cigaba da sanya musu ido a fakaice ta gani ko za su shirya ba tare da tsoma bakin manya ba tunda ta kula basa so a sani. Idan basu daidaita ba sai ta shiga tsakani kafin ƙaramar magana ta zama babba.
Hamdi ce ƙarshen fitowa daga ɗakin bayan Amma da Taj. Salwa ta kasa ɓoye baƙinciki da kishinta a fili. Wata irin zabura ma tayi daga zaune. Numfashinta ya nemi yankewa. A zatonta turaren jiya sake janyo ɓaraka zai yi tsakaninsu. Me Hamdi take a gidan?
Wata zuciyar ta kwaɓeta da sauri. Ko dai har an sami matsalar? Maybe shi ne aka turo su gida sulhu. Munafukar dariya tayi a zuci. Ta miƙe tsaye domin ta nunawa kowa matsayinta a wajen Taj. Kashe murya tayi tana kwarkwasa.
“Ya Taj”
Ai fa ta zo gidan yawa. Idanu sun fi goma a kanta. Hamdi wani malolon abu taji ya mata karan tsaye a wuya. Faɗi take tana nanatawa In sha Allahu ba za ta sake kiransa da Ya Taj ba. Sunan ko daɗi babu ashe, bata sani ba sai yau.
Taj kuwa Hamdi kawai ya kalla tayi kamar bata jinsu. Murmushi ma take yi abinta da ƴan uwansa suke ta nuna mamakinsu akan kwanan da tayi basu sani ba. Aka dinga yiwa ƴan kwanan ɗakin Inna surutu. Su ka ce ita ta sanya su yin shiru saboda kada su tashi Hamdin da hayaniyarsu. Shi da ya san akan tsini yake ba zai yi kuskuren sake ɓata mata rai ba. Kawar da kansa ya yi kamar bai ji ba. Yana gudun me zai faru idan ya amsa. Ta sake shaƙa har wuya. Abinci ƴan uwansa su ka kawo wa Hamsi shi ne ya samu ya fita wajen Kamal.
Amma ta karanci duk motsinsu. Me yake faruwa ne wanda bata sani ba? Zama bai ganta ba. Ɗakin Mama ta shige inda Inna ta shiga ta zauna jin abubuwan da bata san da su ba. Mamaki mabayyani ta nuna akan wannan sabon al’amari.
“Ashe yarinyar nan bata da wayo ban sani ba? Ana soyayya dole ne?”
“Gabaɗaya ta ɓata rawarta da tsalle. Halin da uwarta ta so nuna mana a gidan nan shi ne ita ma take son gwadawa.”
Umma kallon Mama tayi da mamaki “kada ki ce min asiri ne ya koreta, don na tabbata ko ita ce autar mata akan ƴan biye biye tsaf Alhaji zai nuna mata ƙofar gida.”
Hajiya ta murmusa “ai har yau bai san mun san ainihin me ya dinga faruwa ba. Bayan wani asirin ma a gabanmu take yi kawai don ta san ta ɗaure mana baki. Ai ke dai anyi abu fa a gidan nan. Allah kada Ya maimaita mana kawai.”
“Amin. Don dai kam ko Taj ya rasa mace in sha Allahu babu shi babu wannan yarinyar.” Cewar Mama.
Hirar shekarun baya su ka koma yi. Inna ta sake kaɗuwa da jin wace ce Mami. Ashe zama bai ganta ba kuwa. Dole ta dage ta nesanta Taj da Hamdi daga Salwa.
*
“Yaya haka Ahmad? Ni da na kira ka mu san abin yi sai ka kama kuka?”
Ahmad bai san cewa duk bayanin da yaji a waya bai kama ƙafar wanda ya ji yanzu ba. Ƙodar duka biyu Kamal ya rasa kuma wai cikin su ashirin da bakwai babu wanda tasa za ta yi. Idan babu mai taimakon Kamal a cikinsu daidai yake da babu Kamal ɗin.
“Alhaji bayaninka fa yana nufin duk yawanmu ba za mu amfane shi ba tunda babu jinin wanda ya dace dashi.”
“Haka su ka yi min bayani da likitan.”
“Anya ba ya faɗa bane kawai saboda baya son takura kowa?” Ahmad ya yi tambayar da basu san amsarta ba.
Alhaji sai ya shiga tunani. Tabbas kowa a gidansa ya yi fice akan wata halayya. Indai ana batun sadaukarwa to Kamaluddin ɗinsa shi ne na farko. Wuyarta ka nema zai baka ko shi ne abu na ƙarshe a tare dashi. Ba abin mamaki bane in ya zamo yaƙi yarda a cire ƙodar kowa a dasa masa.
Wannan tunanin kaɗai ya haskaka zuciyar Alhaji. Zai nemi Kubra ta haɗa shi da likitan da ya dace a Aminu Kano Teaching Hospital. All hope is not yet lost.
Sun tattauna yadda za su yi idan aka yi rashin sa’a da gaske babu wanda jinin nasa ya yi daidai. Alhaji ya sanyawa ransa daga yau zuwa sati in ba a dace ba za su bar ƙasar. Ɗan lokacin ma ya bari ne saboda su sami damar yin booking ɗin asibitoci a ƙasashen waje. Duk wanda aka sami appointment da wuri, shi za su je. Baya son su fara tafiya a can ma ace ƙodar ake buƙata dole kuma babu mai bayarwa.
Da su ka gama ne Ahmad ya ce “maganar Salwa…”
“Yauwa…” ya tashi “mu je ƙasan. Wani rami nake son toshewa kafin ya zama ƙofa.”
Gaban Ahmad faɗuwa ya yi “Alhaji ka sami labarin tana son Taj ne? Nayi mata faɗa. Ko a hanyarmu…”
“Bana fatan abin da zai sa na ci zarafin jininka Ahmad. Amma tabbas idan Salwa ta cigaba a turbar da ta ɗauka to lallai za ta fuskanci fushina.”
Hankalinsa ƙara tashi ya yi. Me kuma tayi?
Bai sami amsarsa ba sai da su ka shiga mota ya matsa mata da tambaya saboda abin da Alhajin ya yi ya bawa kowa mamaki. Hamdi ya nema suna saukowa. Amma ta ce masa ya yi sa’a kuwa domin yanzun nan suke shirin fita ita da Hajiya da Na’ima wadda ke bin Hajiyayye za su kai ta gida.
“Da kun koma kun ɗaukota kuwa” cewar Alhaji yana shafa kan ƙananun jikokinsa “ni na kawota. Idan ba a jira na mayar da ita ba sai a nemi izini na kafin a kaita gida.”
“Mun kusa yin laifi ashe. To Allah Ya bada haƙuri” in ji Umma.
Gabansa Amma ta kawo Hamdi. Ta durƙusa ta gaishe shi kai a sunkuye. Yadda ya amsa mata da sakin fuska har Inna sai da ta jinjina lamarin.
“Ni dai ba zan bar magana a cikina ba.” Amma tayi maganar da ta janyo hankalin kowa gareta “da mun san aurenki ne zai dawo da Taj gidan nan Hamdiyya ai da ranar da ya fita zai dawo. Sannunki Hamdiyya tauraruwar Tajuddin.”
Dariya aka kama yi. Ita kuwa ta cigaba da cewa “Allah kuwa da gaske nake. Ji fa irin fara’ar da kake yi mata Yaya Hayatu. Irin ka yi na’am ɗinnan da auren hands down.”
Hararar ƙanwar tasa ya yi ya ce “A’a hands up.”
Yaran kuwa me zasu yi banda dariya. Da kowa ya nutsu ne Alhaji ya ce ina Salwa. Tana daga gefe ta kawo wuya da abubuwan da ake yi a falon. Tasowa tayi kamar ƙwai ya fashe mata a ciki. Tayi zaton magana zai yi mata a gabansu sai ya ƙara gaba ta bishi. Kowa na gani amma ba a san me yake cewa ba.
“Kin ga matar Taj ko?”
Shiru tayi da farko. Ya nanata tambayar da wata irin murya mai cikar kwarjini.
“Kin ga Hamdiyya matar Taj ko?”
“Eh” ta gyaɗa kai da sauri.
“Kin kuma fahimci me yasa na nuna miki ita ko?”
Nan ma eh ta ce ba tare da jiran ya kuma tambaya ba.
“To kada na ji, kada na gani Salwa.” Ya juya mata baya “ki je Ahmad ya mayar dake gida.”
*
“Yarinyar nan ya nuna min” ita ce amsar Salwa ga Ahmad da ya kusan kai mata duka akan ƙin amsa masa tambayar me Alhaji ya ce mata da farko.
“Wace yarinya?”
Ciki-ciki ta ce “matar Ya Taj.”
“You are the least of my problems Salwa so ko ki buɗe baki ki bani amsa ko ki riƙe abinki duk ke ta shafa.” Ahmad ya faɗi da faɗa-faɗa.
Yadda su ka yi ta faɗa masa. Ya kalleta yana mai taɓe baki.
“Kina gab da yin nadama mara amfani idan baki dawo daga rakiyar zuciya ba. Duk wanda ya bari tasa ta mulki tunaninsa da wuya yake cin riba. Dubi yadda gabaɗaya ki ka sauya akan wannan obsession ɗin naki. Kin zubar da mutumcinki ana ta takawa a banza.”
Ci kanka bata ce masa ba. Yana magana ma Ummi take turawa text tana neman inda za su haɗu yau. Ta riga tayi nisa bata jin kira. Burinta kawai Taj ya so ta ko iyayensa basa so kuwa sai sun yi aure.
***
GIDAN TAJ DA HAMDI
(Sponsored by annurifoods, nafsbedding and meensincense)
Jeren gidan amarya ba mai yawa bane ta ɓangaren gidan Abba Habibu. Inna tayi rawar gani da nunawa fiye da tunaninsu. Ta cika gidan da komai na buƙatar amarya da ango. Sai dai kuma duk da haka Abba da Yaya basu fasa yin nasu ba. Makusantansu ma sun nuna bajinta ba kaɗan ba. Kayan zaƙi na gara irinsu dubulan, alkaki, nakiya, gireba, bakilawa da cincin Ƴar Ficika da muƙarrabansa ne su ka yi. Abin ka da tsofaffin takari, nasu ya sha bamban sosai da wanda aka saba.
Iyaa kuwa gidan ƙanwarta taje a hotoro aka rakata wajen wata ƙwararriya a harkar kayan kaɗi da abubuwan abincin gargajiya. Samira Muhammad kenan, mai Annurfoods. Mace mai faram faram da iya mu’amala. Tun abin da ya haɗa Ummi da Hamdi a makaranta Iyaa take neman hanyoyin daɗa wanke iyalinta duk da su Yaya basu canja musu fuska ba. Bayan gudunmawar kuɗi da su ka bayar shi ne ta haɗo wannan. Da ta kawo kayan Yaya kasa rufe baki tayi. Wanda ta haɗawa amarya dole ta ajiye domin babu yadda za a kai Hamdi ba tare da kayan annurfoods ba. Garin kuka da kuɓewa masu kyau a madaidaitan bokiti. Sai daddawa wadda ana haɗa kayan Anti Labiba ta ce ita dai ayi haƙuri sai ta ɗiba saboda daɗin ƙamshinta. Babu warin nan mai hawa kai mutum ya rasa inda zai yi da ransa. Sai nau’in yaji daban daban. Jan yaji mai tafarnuwa da wanda babu, na daddawa da kuma na ƙuliƙuli. Niƙaƙƙiya da kuma markaɗaɗɗiyar gyaɗa (gari da paste), garin ɗanwake, garin kunu wanda yaji duka kayan haɗi da kuma soyayyen man shanu mai daɗin ƙamshi. (Samira Muhammad 08039183880, instagram @annurfoods.ng)
“Altine wannan kaya basu yi yawa ba?” Faɗin Yaya tana jin kamar tayi kuka saboda karamcin da ake ta nuna musu.
“Ina abin yake Jinjin?”
“Haba dai, wannan yafi ƙarfin a bi shi da kalmar ina abin yake. Ke dai Allah Ya biyaki da mafificin alkhairi.”
Iyaa ta ce “amin Ya Allah.”
Sajida aka damƙawa kayan a hannunta da umarnin idan sun je gidan tunda da wuri za su fita kafin a kai amarya ta saka komai a inda ya dace.
Ana haka su Amma su ka yi sallama. Allah Yasa sauran safiya ce. Babu baƙin fuska a gidan. Aka sauke su a falo. Hajiya ta fara da bawa Yaya haƙurin tafiya da Hamdi da Alhaji ya yi. Don ta rufa masa asiri ma ta ƙara da cewa yayi haka ne kawai don ya kula suna cikin damuwar ciwon Taj.
Yaya tayi murmushi. Gashi dai an shigo gidan amma hannun Hamdi yana cikin na Amma a gefen Hajiya tayi mata riƙo na ƴar da ake ji da ita.
“Wallahi babu komai. Da nan da can duk ɗaya ne.”
“Kin sami labarin Alhaji ya yiwa Taj izinin komawa gida?” Amma ta yi tambayar saboda ita fa a yanzu wannan yafi bikin ma a wajenta.
“Ƙwarai kuwa…” sannan Yaya ta taya su murna.
Cikin mutumci aka gama komai. Za su fita Amma da bata iya shiru ta ce da Yaya don Allah wane irin turare ne aka saka a ɗakin yake fitar da ƙamshin da su ke ji tun shigowarsu? Hajiya girgiza kai ta kama tana murmushi. Amma bata iya baƙunta ba. Sai dai idan bata ga fuska ba. Ta gode mata dai saboda ita ɗin ma surukuta ce ta hanata tambaya tun shigowarsu. Daɗin ƙamshin ba daga nan ba. Bayan kujera Yaya ta nuna musu. Inda aka ajiye turarukan wuta a cikin bokitai an rurrufe bakunansu da salatif.
“Ko kunnawa ba’ayi ba. Na gidan ƴarku ne.”
Tashi Hamdi tayi ta bar falon. Yaya ta ƙwalawa Zee kira. Tana shigowa ta ce ta ɗauko a buɗe musu su gani.
“Haba Maman Hamdi? Don Allah kada a buɗe. Ƙamshin ne ya yi min daɗi na kasa barwa cikina” Amma ta faɗi da sauri.
“Ni dai ban ga komai a ciki ba. Nan kuke ta cewa an zama ɗaya” cewar Yaya tana kama guda ɗaya “in sun je gidan yanzu ma buɗewa zasu yi su zuzzuba a rufe sauran.”
Da ƙyar su Hajiya su ka hanata buɗe musu. Bayan tafiyarsu ta sanya a ranta lallai za ta sayi wani ta aika musu. Zuciyarta kuwa fari ƙal don daɗi. Duk da ana ta yaba ƙamshin a gidan tayi zaton na ganin ido ne kawai. Sai yanzu da waɗanda basu san dashi ba su ka yi magana ta kuma gaskatawa.
Matar Halliru maƙobcinsu Hairat ce ta dinga zuzuta kyau da ingancin turarukan wata ƴar garinsu Bauchi. Da farko Yaya har cewa tayi duk turarukan Kano ace sai ta nemi na wani gari? Matar Halliru taƙi haƙura domin ta san me za su rasa idan ba a saya ba kamar na lokacin bikin Sajida. Na wajenta da basu da yawa ta kawo. Zee ta kunna da yamma. Sai da kowa ya fito tsakar gida ranar. Washe gari Yaya ta karɓi numbar Amina (08036387204, instagram @meens_incense). Ta kira su ka yi ciniki akan farashin da idan ka karɓi turaren ma sai ka ce sadaka kawai aka baka.
Da turarukan su ka iso kasa rufe baki tayi don murna. Ta dai ɓoyesu kafin Hamdi ta dawo gida ranar saboda ko za ayi mata faɗa sai ta kunna. Soyayyarta da ƙamshi ta daban ce. Ga dai turaruka kala kala, kwalaccam ɗinta kuwa abar duƙan ƙirji ce (I mean it, the scent simply calms the heart), sai kuma humra irin wađanda sai hancin da yaci karo dasu ne kawai zai gane.
Haka aka tattara komai aka zuba a mota domin kammala gyare gyare kafin zuwan amarya.
***
Banɗaki Ummi ta shiga da waya ta turawa Alh. Usaini saƙo cewa jiya ma Salwa ta sake shafawa Taj turaren nan. Kuma da alama anyi nasara domin ta sami labari a daren aka kai shi asibiti. Daga maganar da taji Baba Maje da Iyaa suna yi bayan wayarsa da Abba Habibu da safen ta fahimci ba rashin lafiya bace kawai ta kama shi. Salwa kuma ta tabbatar mata a text. Ita Iyaa da wuri ta tafi gidan bikin. Ta barsu in sun gama girki da gyaran gida sai su biyota kafin dai a fita da amarya. Yana karantawa ya kirata.
Da ta ɗauka tsoro ya bata da taji ya fashe da wata irin dariya mara daɗin ji.
Da jindaɗi ya ce “Ƙarshen wannan ɗan daudun ya zo.”
“A’a fa, ba ɗan daudu bane” Ummi taji ba za ta iya shiru ba. Ko makaho ya shafa Taj ba zai kira shi ɗan daudu ba, balle mai ido. Idon ma irin nata mai son abu mai kyau.
“Ummi kenan. Wai me ya hanaki cewa ayi aikin da za ki sami soyayyarsa maimakon wannan sakaryar Salwan?”
“Bana ra’ayin namijin da kowa ke rububi.” Tana ji Alh. Usaini ya yi dariyar rashin yarda.
Tunanin Taj ya so ta bai zo kanta ba saboda tayi nata binciken akan waye shi. Labarin mahaifinsa kaɗai ya isheta dalilin mayar da kwaɗayinta. Sannan ta san cewa ko ana muzuru ana shaho a yadda Baba Maje yake ganin darajar Abban Hamdi, da wuya ta gaske a barta ta aure shi. Ita kuwa abin da take ji a kansa ba na irin mu’amalarta da banzayen samarinta bane. Ya girmi hakan. Shi yasa kawai taga babu mafita sama da rusa shi. Ita da Hamdi kowa zero. Mafi munin hassada kenan.
“Ki tabbatar kin je kai amarya kuma kin bibiyi me suke ciki na ƴan kwanakin nan. Kin san na faɗa miki aikinsa a hankali yake ci.”
“Bana son yin abin da zai sa a zargeni. Ba wani shiri muke da Hamdi ba kuma kowa ya sani.”
“Sai ki san yadda za ki yi.” Ya ɗaga mata murya kamar wata ƴarsa.
Bai san bashi da wani kwarjini a idonta ba. Yana shiru ta ce “Ban gane ba? Wannan abu fa duk kai ne da riba. Idan ka damu ka sa malamin da ya yi maka aiki akan Taj ɗin ya tura aljanu su binciko maka mana. Mtseww”
Wayarta ta kashe ta sake buga tsaki.
“Aikin banza. Ni za ka ɗagawa mur…”
Haɗiye maganar tayi cikin tashin hankali saboda haɗa ido da tayi da Siyama. Ita kuma cikin sauri da ta karanci fuskar Ummin sai ta kama ɗaɗɗaga ƙafa.
“Fitsari, fito don Allah.”
Fitowar Ummi tayi tana wasiwasin Siyama taji wayar da tayi ko kuwa.
Gaba na faɗuwa Siyama ta dakata a bakin ƙofa ta nemi mafita don kaɗan daga aikin Ummi tayi mata wani abu idan ta san ta ji.
“Naji kina ta gunaguni da tsaki, ba dai flushing ki ka yi yaƙi tafiya ba? Kada na shiga nayi gamo.”
Ba kunya Ummi ta saki fuska harda ƴar dariya “shiga ki ganewa kanki” ta turata ciki. Siyama na nuna kamar bata son shiga ta bari Ummin tafi ƙarfinta. Fitsarin da ya kawota da gaske ta daina ji. Tabbas akwai manaƙisar da Ummi take shiryawa Hamdi da Taj tunda taji sunayensu. Hankalinta ya tashi. Har su ka tafi gidan bikin tana faman satar kallon Ummi.
Da zuwansu babu daɗewa ta nemi keɓewa da Iyaa. Ummi kamar an tsikareta ta tashi tayi musu laɓe. Da taimakon Allah ta sami basirar lauya zancen. Wata maganar daban ta ɗauko har Iyaa za ta fara yi mata faɗan me yasa ta janyota akan shirme, sai ta ƙifta mata ido. Ganin haka sai ta kalli bakin Siyama da ta faɗi sunan Ummi iya leɓe. Wannan yasa ta fahimta.
“Iyaa za ki barni zuwa kai amarya har ango yazo? Ni fa ban taɓa zuwa ba.”
“To naji sai ki biyo yayanku don na san zai je ko don ɗauko Zee.”
Murna ta kama yi harda rungume Iyaa. Da wannan ta samu Ummi ta daina saka mata ido har ta sami damar sanar da Iyaa wayar da taji.
“Ban ji ance komai ba amma ko da wani abu zai biyo baya to da hannunta wallahi.”
Sallamarta Iyaa tayi ta jingina da bango domin gabaɗaya jikinta ya mutu. Nauyi taji jikin yayi mata ta sulale a wajen kawai ta zauna. Babu abin da take yi sai kiran sunan Allah da neman agajinSa. Haƙiƙa kowane ɗa da halinsa yake zuwa. Tarbiya bakin gwargwado sun bawa ƴaƴansu. Amma tun ƙananun shekaru tanƙwara Ummi ke wahalar dasu. Bata da bakin ɗorawa ƙawaye alhakin ɓata mata ƴa domin kuwa duk inda Ummi ta zauna ita ke shugabantar waɗanda take mu’amala dasu. Ita ce boss mai sawa da hanawa. Ko dai kawo ƙara da wasu iyayen ke buri da alfaharin gara a kawo musu ƙarar ƴaƴansu akan su kai na wasu da tayi ke bibiyarta? Duk inda Ummi ta zauna sai tayi faɗa kuma ana bincike ita ce mara gaskiya. Kuskurenta a lokacin da suke cikin yaran yarbawa a tsakiyar Agege shi ne na jindaɗi da Ummi bata taɓuwa. Babu mai yi mata kwarjini ko ya bata tsoro. Kana cewa kule take ce maka asss. Wata maƙociyarta bahaushiya a lokacin ta kan ce
“Iyaan Baballe ki daina murna. Duk da cewa ba ma son a zalinci yaranmu to amma fa idan sun fita ya dace ki dinga addu’ar kada su taɓa ɗan kowa. Babban abin alfaharin rayuwa shi ne kayi dace kai ko wani naka bai zama silar ƙunci ko zubar hawaye ko jinin wani ba. Sannan kaima kada ɗan kowa ya yiwa naka. Ko babu komai akwai baki da ido kuma su ɗin gaskiya ne. Allah Ya kyauta.”
Amsarta a lokacin ita ce tunda suna zaune a waje irin wannan ba za ta so yaranta su zama lusarai ba. Wannan mata kuwa ta nuna mata cewa duk runtsi ai gara idan an je gaban Allah ka zama mai kai ƙara da a kai ƙararka. Za ta koyawa yaranta su ƙwaci kansu amma kada su zama silar rigima kuma banda zalunci da wuce gona da iri. Manzon Tsira SAW cewa yayi kada mu cutar kuma kada mu bari a cucemu.
Hawaye ya zubowa Iyaa. Ta ɗauki laifin ta ɗorawa kanta. Cin zalin da Ummin da dinga yiwa Siyama ne yasa ta canja tsarin tarbiyar lokacin. To amma ɗan wannan guntun sakacin da kuma halayyar fiɗrar da aka haifeta sun riga sun yi tasiri.
“Allah na tuba. Allah Ka duba min.”
Wata walwala da jindaɗinta duk sai su ka kau a lokacin. Ciwon kai ta ɗorawa laifin hakan da Yaya ta tambayeta game da sauyin da ta gani a tare da ita.
*
“Kai Happiness me ya same ka haka ka kumbura?”
A madadin sallama abin da Taj ya fara cewa kenan da ya shiga ɗakin Kamal.
Son faɗawa Happy gaskiya yayi sai dai kuma a ganinsa faɗa a yau ba ƙaramin rashin adalci bane. Babu yadda za ayi Taj ya san gaskiya kuma ya tare a gidansa a yau. In ya yi haka kuwa ya cutar da Hamdi.
“Wai ashe kifi ne jikina baya so yanzu ni ban sani ba? Jiya da ka kula tun a wajen dinner bani da kuzari. Kifi na ci last kafin mu tafi.”
“Subhanallahi. Kuma Alhamdulillah tunda an gano. We’ll just avoid it don a zauna lafiya.”
“We? Kai kuma me zai sa ka daina ci?” Kamal ya tambaye shi.
“Ai ka sanni da kirki. Ba zan so na dinga ci a gabanka ba.”
Da dabara Kamal ya sauya zancen da dai yaga Taj ya yarda.
“Wai ni ya na ganka haka kamar ba wanda ya kwana gida ɗaya da Hamdi ba?”
“Akwai ƙura fa Happiness. Alhaji ya ɓallo min ruwa jiya.” Ya faɗa masa abin da ya faru.
“Tabɗijam ake cewa ko cabɗijan…yanzu kana nufin ni da kai yau duk pillow za mu runguma?”
Bugu Taj ya kai masa ya goce “ta Allah ba taka ba. In sha Allahu gadona da naka yau sai an sami bambanci.”
“Salman Khan na Hamdiyya wato ana yi maka kallon salihi ashe ashe ba haka bane.” Kamal ya faɗi yana yi masa dariya.
“Aure dai nayi…idan mutum yaji haushi wata asabar ɗin mu kai shi ɗakin doctor”
“Maimakon ka zo mu zanta yadda za ayi a shawo kanta tun kafin ƴan kai amarya su watse ka zauna tsokana.”
“On a serious note kana ganin abin da take so zai samu yanzu? Alhaji fa take so ya canja yadda yake yiwa Abba. Bata san na fita son hakan ba ta ɗauki fushi dani.”
Shawarwari Kamal ya soma bashi sai dai a yau ko kusa zancen ba shigarsa yake ba. Ya riga ya san da me zai kama Hamdi a hannu. Damuwarsa yanzu canjin da ya gani tattare da Kamal mai yawa tsakanin jiya da yau. Happiness is hiding something. Yana ji har cikin ɓargonsa. Ko maganganun da suke yanzu yana hango pain ɗin da ɗan uwansa yake ƙoƙarin ɓoye masa. Dole zai yi wani abu a kai. Kamal bai fi shi wayo ba.
*
Wannan asabar ta kafa tarihi mai girma a gidan Alh. Hayatu. Yinin bikin Taj da aka shirya yi a gidan wan Inna sai ya dawo gidan mahaifinsa. Ƴan uwa na kurkusa da su ka san me ya wakana tsakanin uba da ɗa sun taho harda maza irinsu dattijon arziƙi Yaya Babba su ka yi fatan alkhairi su ka tafi tare da Alhaji. Aka dinga kiran ƴan biki cewa venue ya canja last minute. Ƴaƴa, surukai da jokokin Marigayi Alh. Sule Maitakalmi sun gwangwaje cikin farinciki. Inna da ƴan uwanta su Hajiya anko su ka yi da Amma uwar goyon Taj. Ango ya fito tsakiyar dangi babu shayi ko tararrabi gwanin ban sha’awa.
Wai aka ce taɓa kiɗi taɓa karatu. Da yake a gida suke matashin ɗan Yaya Kubra ne yayi musu DJ. Ba kunya ita da kanta ta ce masa ya kunna musu waƙar da ta faɗa masa tun a gida. Ta sanya autar Alhaji Surayya tayi coordinating komai. Layi aka yi a jere tun daga Yaya Hajiyayye har ita Surayyan. Dukkaninsu sanye da anko iri ɗaya na shadda light brown. Ɗinkin mata irin ɗaya, haka ma na mazan. Daga kan Yaya Hajiyayye kuma ta jere Inna, Umma, Mama da Hajiya a gefe da gefen juna.
DJ ya saki waƙa su ka dinga bi.
Hurry hurry come carry your baby go
Come and see my mother ahh….
Kowa sai ya bar abin da yake yi ana kallon zugar gidan Alh. Hayatu. Babu wanda bai yi rawa ba idan an zo kansa, har Ahmad da tun safe yake cikin ƙunci. Sai yanzu da yaga Kamal yana walwala har yafi Taj rawar ma ya sake. Bayan sun gama matsawa su suka koma gefe suna nuna uwayensu ana ta dariya.
Wani abin burgewa shi ne da Taj ya taka har gaban Amma yana nunata da hannuwansa biyu yana faɗin come and see my mother. Bata san lokacin da ƙwala ta zubo mata ba. Ya rungumeta a wurin yana ɗan dukan bayanta.
A wurin kowa har angon wannan wunin is the best event. Kowa yaji daɗi. Ana la’asar Mama ta ce ayi haramar ɗauko amarya a kaita gidanta.
*
Ƙarfe biyar da rabi motocin kai amarya su ka cika layin gidan Abba Habibu. Motoci na alfarma da kece raini. Taj bashi da wasu abokai na a zo a gani sai cikin ƴan uwansa. Su ne kuma su ka cika wurin ƙwai da kwarkwata. Kowa ya zo ɗaukar amaryar Taj.
Su ma biki suka yi sosai. Gidan Abba Habibu babu masaka tsinke. Abinci da abin sha sai mutum ya ture.
Ƙarfe uku aka shige ciki da amarya. Kayan gyaran jikin da Amina Meens_insense take yi Hairat matar Halliru ta saya domin yau. Ba don nisa ba da ita da kanta za ta sake yiwa Hamdi gyaran nan kafin a kaita. Sake scrubbing jikin tayi ta turarata sosai. Bayan an gama ta sanyata ta tashe jikinta da kwalacca ɗin meens ɗin. Sannan tabi gaɓoɓi da oil ɗin scentmania. Ita kanta Hamdi duk kukan rabuwa da gida da ta fara sai da ta dakata ta shaƙi ƙamshin sosai.
“Hamdi kada ki yi wasa da ƙamshi. A jikinki da gidanki. Rahama ne shi babba kuma abokin yaƙi da nasarar kamo zuciyar maigida. Mace mai wayo bata bari mijinta yaji wari a jikinta.”
“Ba za ki amsa ba uwar miskilanci? Ana baki darasi kin wani haɗe rai.” Cewar Sajida tana harararta da gefen ido.
“Idan na amsa ace bani da kunya. Nayi shirun kuma ban tsira ba. Me ya hanaki yi min kara ki ce to?” Hamdi ta rama hararar.
“Ba laifinki bane. Gidan miji za ki kwana yau, dole ki min rashin kunya.”
Sajida ta faɗa da rawar murya.
“Kinga kin saka ta kuka ko?” Zee ta matsa jikin Sajida ganin har ta soma zubar da hawaye.
Jiki a sanyaye Hamdi ta matsa kusa dasu “ni me na ce don Allah. In ranki ya ɓaci ki faɗa min mana. Meye na kuka?” Ita ma sai ƙwalla.
“To ni wa zan rarrasa cikin ku?” Zee ma ta kama kuka.
Rungume juna su ka yi suka kama kuka haiƙan. Ta tabbata yau su uku kowa makwancinta daban. Aure abin so kuma abin alkhairi ya rabasu.
Hairat fita tayi ta basu wuri. Ana ganinta a waje aka fara tambayar ko Hamdi ta gama shiri.
“Yaya leƙa ɗakin.” Ta ce da Yaya.
“Ga iyayensu nan…” Yaya ta faɗi cikin kunya.
Hairat kuwa ta ce ita ya dace taje. Ƴan uwan nasu ma su ka goyi baya. Tana shiga ta samesu su uku suna sharɓar hawaye. Da su ka ganta wajenta su ka ƙarasa kowacce kukanta ya ƙaru. Ta fara yi musu nasiha sai gashi tabi sahu. Sai da aka ji shiru aka biyo bayansu. Inna Luba da kanta da sanya Hamdi a gaba ta saka kaya. Riga da zani na leshi mai ɗan karen laushi. Fuskarta babu makeup sai hoda da kwalli da ɗan pink lipstick sama sama. A haka ma tayi kyau sosai.
“Har a fita ban yarda ki sake sanya min ƴa kuka ba. Ki daure ki riƙe hawayenki don Allah.”
“Haba Inna? Ba ma ta ni kike yi ba sai Yaya?” Hamdi ta kyaɓe fuska.
“So so ne Hamdiyya…” cewar Inna Luba tana dariyar tsokanar jikar tata.
“Amma son kai yafi ko? Naji da ana cewa wai mutane sun fi son jikokinsu akan ƴaƴa.”
Inna Luba ta kaɗa baki ta ce “Duk ƙarya ne.”
“Ai kuwa sai na faɗawa Yaya ta daina jin babu daɗi idan kina shareta.”
“Zo nan don ƙaniyarki” Inna Luba ta yafito ta ta gudu.
Matar Kawu Abduƙadir ƙanin Abba Habibu ce ta zauna da Hamdi bayan ta gama shirin ta bata kayan gyara ba mata da sati guda kenan ana bata ta shanye.
“Ki kula da abincin da kike ci da tsafta. Wannan sinadari ne. Kada ki dinga yi musu shan ƙoshi don Allah. Komai saisa-saisa yafi”
Sunkuyar da kai tayi har ta gama yi mata bayani ta tashi. Daga nan gida ya kaure da guɗar shigowar dangin Taj. Cikin Hamdi ya yamutsa da wata irin fargaba. Kukansu ita da su Zee ya dawo sabo fil. Aka fita da ita ko Abbanta da taci burin gani bata sanya a ido ba. Yadda ya bar gidan ranar kai Sajida ita ma haka yayi mata. Ba zai iya ganin fitarsu ba.
A motar Kamal aka sanya amarya. Mummy matar Yaya Babba da uwargidan Alh. Lurwanu wan Inna su ka saka ta a tsakiya. A gaba kuma wata Anti Zinatu ce.
Rantsuwa kala kala Kamal ya yiwa Yaya Kubra akan lafiyarsa kafin ta bari ya fito. Tana barazanar za ta tona masa asiri yayi dariya.
“Ni za ki lallaɓa kafin na tona naki asirin. Alhaji da Yaya Ahmad sun san da ciwon. Na rufa miki asiri ne dai kawai…”
“Alhaji ya sani? Kamal ka kyauta kenan? Idan ya san nima na ɓoye ka san me zai min?” Ta katse shi a tsorace.
“Shi yasa nace ki barni na fita kada na janyo miki” dariya ya yi mata ta bashi hanya da zai fita ya ce “ba maganarki ce bana ji ba, sai dai ina so ki min haƙuri don ban sani ba ko wannan ne abu na ƙarshe da zan yiwa Taj.”
Haka ya fita ya barta tana share hawaye. Ta gama ƙarar da duk basirarta da waɗanda za ta nema amma ba a dace ba.
***
Gidan amarya ko yaya yake sai kaji ana son barka. Balle kuma gidan Tajuddin da Hamdiyya. Duk wanda ya shiga da santin gidan yake fita. Kayan ƙawa da ƙyale ƙyale an saka amma masu aji wanda basu cika waje sannan basu fiye ƙyalƙyali ba. Harkar girma da girma kawai. Inna da masoyanta waɗanda su ka goya mata baya sun yi rawar gani sosai. Haka zalika Abba Habibu da Yaya. Basu kwanta anyi musu komai ko don gudun raini da wulaƙanci.
Da sunan Allah a baki da zuci iyaye su ka kai Hamdi ɗakin aurenta. Aka kuma umarci ƴan uwanta da su bar kuka haka nan saboda ta sami nutsuwa. A gidan aka yi sallar magariba sannan aka soma tafiya. Yan matan dangin amarya da ango kowa da irin salon nasiha da shaƙiyancin da yake yiwa amarya a kunne. Da aka watse ya rage Sajida da Zee sai Siyama da sa’aninsu daga ƴaƴan ƴan uwan Abba Habibu. Sun zage sun sake gyare komai kafin shigowar angwaye. Iyaa bata bari Ummi ta bi su ba.
*
Taj ya haɗuwa da Alhaji kafin su fita. So yayi su gana su kaɗai ya ƙara yi masa godiyar dawo dashi cikin ahalinsa da yayi. Sannan yana so ya faɗa masa yanayin Kamal da baya yi masa daɗi. A ƙarshe ya roƙe shi ya matsawa Kamal ɗin ya sanar dashi damuwarsa. Tunda ya san ba zai kalli idon Alhaji ya yi masa ƙarya ba.
Da Ahmad su ka shiga wajensu Hajiya. Kowanne ɗaki idan yaje sai anyi masa addu’a. Sisters ɗinsa su ka kama koke koke. Ahmad ya haɗasu manya da yara ya dinga faɗa.
“Auren ku ke yiwa kuka?”
“Kwanansa ɗaya a gida fa zai sake tafiya.”
“Sai ka koma basu gaji da ganinka ba” cewar Ahmad yana haɗe rai don baya son ɓata lokacin da ake yi.
Taj ya kanne ido ɗaya ya kawar da kai gefe “ni dai Hamdi”
“Lahhhh”
Suna tsokamarsa wai bashi da kunya da ya faɗi haka a gaban iyaye ya ce su ma basu da ita da su ka kawo zancen ya sake kwana. Aka gama wasa da dariya su ka fito. A hanya ya fara faɗawa Ahmad damuwarsa akan Kamal.
“Gabana har faɗuwa yake yi idan ya faɗo min a rai. Gani nake kamar ba wani ciwon allery.”
Ahmad yayi ta maza sosai da ya iya daurewa ya cije yadda Taj ba zai gane ba.
“Ka tambaye shi?”
“Ina ɗauko maganar yake neman hanyar canjata.”
“Kada ka sa komai a ranka. Zan binciko maka.”
Ajiyar zuciya Taj yayi “nagode Yaya.”
Shiru su ka ɗanyi kafin Ahmad ya ɗauko zancen Salwa.
“Naji duk abin da tayi. Kayi haƙuri. Yau na so ta koma Bauchi amma ban sami zama ba.”
Katse shi yayi “Yaya Ahmad don Allah mu bar zancen. Ƙanwarka ce. Nima kuma ƙaninka ne. Na san babu sani ko goyon bayanka saboda haka kada ka ja zancen nan ko ka bani haƙuri. Ita ce ma zan bawa saboda ƙin karɓar tayinta da nayi.”
Samun gidan yawa irin na Alh. Hayatu mai tattare da haɗin kan iyali ba abu ne mai wahala ba. Na farko mutum ya zaɓo mata nagari sannan ya tafiyar da mu’amalar gidansa a bisa tsarin shari’ar musulunci. Na ƙarshe kuma ya dage da addua. Saɓani a yau da kullum dole ne. Amma a ƙalla wasu abubuwan da dama sai dai kaji ana faɗi ba dai a gidanka ba.
A farfajiyar gidan su ka haɗu da sauran ƴan uwansu da tsiraran abokai. Sai Safwan da Baballe. Ahmad ya ce ba zai shiga ba a matsayinsa na wan ango. Su Kamal ne su ka raka shi ciki.
“Ya Taj ina ledar kazar amarya? Ko tana mota?”
Abba ne ya yi tambayar kafin su bar bakin motocin. Taj ya tsaya turus, wallahi ya manta ana wannan siyayyar. Bai taɓa raka ango ba amma Kamal ya faɗa masa.
“Subhanallahi…zo ka siyo min.” Ya zira hannu a aljihu.
“Gashi na siyo” Kamal ya ɗago ledoji biyu daga gaban motarsa.
Rungume shi Taj yaje ya yi.
“What will I ever do without you?”
“Sake ni dalla kada ka sani kuka” Kamal ya ture shi. Taj yaƙi saki. Bishir da wani cousin ɗinsu harda ƴar ƙwalla.
“Ya aka yi ka san ban saya ba?”
“Wallahi jiki na ne kawai ya bani.”
Murmushi suka yi sannan Taj ma ya karanto addu’a kafin ya shiga gidansa karo na farko a matsayin mijin aure.
A falo su ka sami ƴan matan amarya da amaryarsu a tsakiya an lulluɓeta da laffayar jikinta. Tana ji ana gaishe gaishe an barta da faɗuwar gaba. Ta kama hannun Sajida tayi masa kyakkyawan riƙo kamar za ta tsinke mata shi.
Addu’a da fatan alkhairi aka yi musu a mutumce. Babu wannan rashin kunyar rungume rungumen sabbin aure da ake a gaban mutane. Ko kuma maganganu na rashin ɗa’a tsakanin angwaye da amare. Da aka gama Safwan ya ce ya kamata su tashi haka nan. Waɗanda za a kai gida su fito a kai su.
“Ni dai ina da abin cewa guda ɗaya kacal. Happy…” Taj ya kalli Kamal.
“Mrs Happy…” Hamdi ma ta ɗaga kai a hankali amma bata buɗe fuska ba.
“Duk abin da za ku yi, ku ji tsoron Allah. Ku yiwa juna uzuri kuma ku kyautatawa juna zato.”
Yanzu dai bata yi kuka sosai ba da zasu tafi sai hawaye. Taj ya fita ya raka su sannan ya rufo ƙofa ya dawo.
Hamdi tana nan bata motsa ba. Ya yi murmushi ya ƙarasa kusa da ita ya zauna. Gabanta ya kama dukan tara tara. Yau da anyi an gama. Inda take yanzu gidansu ne ita da Taj. Magana take jira ya yi ko wani motsi duk taji shiru. Ba zato taji saukar abu a gefenta. Ta ɗaga kai da sauri, kafin ta buɗe fuskar Taj yasa hannu ya haɗe gaban laffar ta saitin fuskarta.
“Ni zan buɗe. Kada ki ɓata min tafiyar tarihin wannan daren.”
Komawa tayi jiki babu kuzari ta zauna da ta gane babbar rigarsa ce ya ajiye a kusa da ita.
Rage tsayi yayi a gabanta ya ce “Zan taɓaki Hamdi. Kin bani dama?”
“Na’am?” Hamdi taji wata baƙuwar murya ta fito daga bakinta ma’abociyar tsoro.
“Na fahimci a tsorace kike ne shi yasa na faɗa miki.”
Kafin ta sake yin magana taji hannuwansa a duka kafaɗunta ya tayar da ita. Sannan ya kama laffayar ya soma warwareta har ta ƙare. Ya kalleta daga sama har ƙasa ya godewa Allah a ransa.
Babu zato daga gareta kawai taji ya janyota jikinsa ya sanya hannuwanta a gefe da gefen cikinsa sannan ya rungumeta. Sun ɗauki lokaci a haka kowa yana fama da yanayin da ya shiga kafin ya ɗago haɓarta yana kallon idanunta.
“Mun shirya Hamdi? Kin daina fushin?”
“Ba fushi nake ba.”
“Har akan maganar ɗazu?”
“Ɗazu gaskiyata na faɗa maka ai” ta ɗan kawar da kai.
“Kina nufin yau ni da gwaurayen da su ka fita daga gidan nan bamu da bambanci?”
So tayi ta haɗe fuska don ya san mahimmancin abin da ta faɗa amma wannan maganar sai da tasa ta yin murmushi.
Sannan ta ce “Haka ne.”
Hannunta ya riƙe su ka zauna “su rungumi pillow nima na runguma kenan fa?”
“Uhmm” ta amsa kunya na kamata.
Taj ya kalleta da kyau ya ɓata rai “ke Allah kuwa da sake. Sadaki fa na biya.”
Da dabara ta ɗora hannu a kan bakinta don kada yaga dariyar da take neman yi.
“Aka biya maka dai.” maganar ta fito kamar ba daga bakinta ba.
Ƙayataccen murmushi ya yi “Lallai, kin ce wani abu. Zan tuna miki a lokacin da baki zato.” Ledojin da Kamal ya ajiye akan centre table ya buɗe “zo mu ci abinci. Kuma kada ki ce kin ƙoshi.”
“Ƙoshi kuma? Yunwa fa nake ji.”
Ƙasa ta zamo abinta ta zauna. Taj ya shagala da kallonta ta nuna masa ledojin da ido.
“Ba za ki taimaka min ba?”
“Amarya nake. Yau ɗaya ina zaune kayi min komai.”
“Burina ma kullum na taimaka miki.” Ya wuce kitchen ya samo tray da kofuna.
Tana zaune ya buɗe ledojin ya ajiye tray ɗin a tsakiyarsu. Akwai youghurt da juice, sai snacks irin su doughnut, croissant da pizza. Ga kwali madaidaici a ciki akwai cake da aka rubuta beautiful beginning Happy and Mrs Happy.
“Allah Sarki Happiness mai sona da gaskiya.” Taj ya yi magana yana kallon Hamdi a kaikaice.
Ta gane da biyu yayi magana shi yasa ta ce “Wallahi kuwa, Allah dai ya ƙaro aminci.”
Taj ya yi ƙwafa kawai ya buɗe ledar gasashshiyar kaza da gurasa.
“Wanne za ki ci?”
“Mene ne wannan?” Ta nuna croissant ɗin.
“Abincin maza ne.” Ya tsokaneta.
Yana rufe baki ta ɗauka ta gutsira harda lumshe ido ta ce da daɗi.
“Na ce miki na maza ne.”
“Nima ai ta mazan ce”
Hamdi is just too cute. Yadda take maganar kaɗai ya gama hargitsa masa tunani.
“Har mu nawa?”
“Ga Abbana, ga Halifa sannan…”
Ya zuba mata idanu. Dole taji kunya ta saki murmushi.
“Sannan kuma ga Happy nawa.”
“Happy naki.” Ya maimaita da murmushin jindaɗin. Ture tray ɗin ya yi ya dawo kusa da ita kamar zai mayar da ita jikinsa ya ce “saboda Allah da gaske kike to akan maganar nan?”
“Da gaske nake.”
“Amma in banda ke wa yake kama wani da laifin da ba nasa ba?” Ya marairaice mata.
Yadda komai tayi yake taɓa masa zuciya bai san ita ma haka yake a wajenta ba.
Haɓarta ta ɗora akan tafin hannunta ɗaya tana kallonsa ta ce “Yanzu ya kake so ayi?”
Kalmomi neman ɓace masa suka yi saboda har cikin zuciyarsa yake jinta.
“Stop acting all coy…”
“Meye coy?” Tambayar ma a yangance tayi ta.
Ba kuma wani abu bane yasa take yi masa haka sai don kada ya ɗauki zafi akan shawarar da ta yankewa zamansu. Soyayyarsa tana jinta kamar da ita ta rayu. Ɓata masa rai is the last thing on her mind. To amma me zai faru idan zama yayi zama sai kawai Alhaji ya yiwa Abbanta abin da zata ji haƙurinta ya ƙare? Idan wataran ta kasa riƙe bakinta ta rama fa? Da wane ido za su kalli juna ita da Taj?
“Acting all lovey dovey,.. and shy…and bold, and….”
“This?” Hamdi ta saƙala hannuwanta a wuyansa.
Gabaɗaya su ka tafi. Sai da ya kaita kan kafet ɗin. Fuskokinsu na kallon juna. Numfashinsu na gauraya sannan zuƙatansu na bugawa lokaci guda.
“Hamdiyya”
“Taaajjj” sunansa ya fito da wani irin shauƙi kwatankwacin yadda ya kirata.
“Duk abin da za ki yi, ki ji tsoron Allah kada ki ɗauki alhakina.”
Murmushi mai kama da dariya tayi “Ba zan ɗauka ba.”
Tausayi ya bata ta danno wuyansa ya ƙara yin ƙasa. Ta ɗago kanta a hankali su ka haɗu. Bata sani ba ko don yau a gidansu suke babu fargabar da yake barinta da ita ta tunanin wani zai gansu. Sakin jiki tayi ta bari yana kissing ɗinta kamar ranar ya fara. Sai da zancen ya fara fin ƙarfinta ta shiga neman ƙwatar kanta.
“Yunwa…yunwa nake ji Allah.”
Ƙarfin hali ya yi ya sake turo mata tray ɗin da su ka ture da ƙafa. Kallon duk motsinta yake yi ta rufe ido.
“Ni gaskiya kunyarka nake ji. Ka daina kallona.”
“Ji min gulma. Ki gama tumurmu…”
Hannu tasa ta toshe masa baki “ba ni bace.”
Taj ya kama dariya “haka ne. Mrs Happy ce.”
Ƙin kallonsa tayi. Saboda kunyar da ta rufar mata bata san ta loda abinci da yawa a gabanta ba.
“Ni fa ba ci zanyi ba.” Ya yi maganar yana bin gefen kunnenta da wuya da bakinsa.
“Nima na ƙoshi.” Ta matsar da tray ɗin. Abin da yake mata ya toshe duka senses ɗinta.
“Cikinki duk ya cushe ko? Tashi kawai muje mu kwanta.” Ya tayar da ita jikinsa.
Harararsa tayi tana magana da shagwaɓa “Amma dai a tarihin angwaye kai ne ka fara hana matarka cin abinci ranar da aka kawota. Duk labarin da nake ji tura musu abinci ake yi ko basa so.”
“Cewa za ki yi duk na fi sauran son matata. Ba zan takuraki ba but I promise you komai dare ki ka ji yunwa ki tada ni. Zan kawo miki abinci.”
Da gaske…ba a taɓa cinye Taj da magana. Hankali kwance ya lauya zancen ya fitar da kansa.
Abincin da ba a ci ba kenan. Ɗakinta ya rakata wanda yake da ƴar tazara da nashi ta shiga wanka shi kuma ya koma falo. Yana kwashe abincin nasu yana rausaya. A fridge ya ajiye komai inda ba za su lalace ba. Ya ɗauki robar youghurt ɗaya ya kai ɗakin Hamdi da kofi sannan ya tafi nasa ɗakin.
Youghurt ɗin ta fara sha tana mamakin yadda aka yi yunwar da take ji ta ɓace. Ta gama shirinta tsaf yadda aka yi mata huɗuba a gida. Sassanyan ƙamshi yana tashi koina a jikinta. Ta kawo hijabinta har ƙasa ta ɗora akan rigar baccin da ta saka mai santsi wadda ta tsaya mata a gwiwa.
Taj ma nutsuwa ya yi ya gama shirin bacci sannan ya taho ɗakinta. Wani abu ne ya bashi mamaki da yana shiryawar har ya kashe masa dukkan karsashi da ɗokinsa.
Da ya saka kaya ya fesa turaruka da body spray sosai amma sam bai ji ƙamshin ko guda ba. Ya ɗauki turaren ya kara a hancinsa amma har lokacin babu. Ya koma toilet ya đaga sabulunsa wanda yanzu da yana wanka yake sake yaba ƙamshinsa sai yaji yanzu baya jin komai.
Zuciyarsa wani irin harbawa tayi. Yaje ya buɗe fridge nan ma babu komai. Hankalinsa a tashe ya ɗauki kwalin juice ya kafa kai don yana son jin sanyi a zuciyarsa. Sai dai me??? Harshensa kwata-kwata babu ɗanɗano.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
