Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Ya yunƙura zai tashi ba shiri don ya san yau ɗin abin da zai fuskanta sai ya gwammace kiɗa da karatu. Alhaji ya yi masa alama da ya koma. Ya sake yunƙurawa dai sai Alhajin ya kalle shi yana mai buɗe masa idanu. Dolensa ya koma ya tada kai da filo.

    Mubina dake tsaye da tasar allura tayi wiƙi-wiƙi da idanu ya duba “Ƙarasa ki duba min shi mana.”

    Tayi sauri ta isa gaban gadon. Ido Kamal ya rufe don allurar akwai zafi. Alhaji yaji wani irin tausayinsa ya tsirga masa. Kujerar gaban gadon yaje ya zauna. Ya kama hannun Kamal na dama ya riƙe. Irin riƙon ƙarfafa gwiwa da rarrashi.

    Dama yaya lafiyar kura? Duk wani emotion na rauni da Kamal yake adanawa tun farkon rashin lafiyar a lokaci guda ya fashe. Ya ƙara ƙarfin riƙon hannun mahaifinsa yana kuka mara sauti. Tsananin tausayinsa yasa Mubina taya shi. Nos ɗin ma kawar da kai gefe yayi. Shi kuwa Alhaji dakewa ya yi duk irin yadda hankalinsa ya tashi.

    “Kuka a gaban mace Kamal kamar wani mace? Ni fa ka san ba shiri nake da rago ba.”

    Hawayen ƙaruwa su ka yi. Ya dawo da kansa saitin Alhaji kawai ya cigaba da abinsa.

    Alhaji yayi murmushi “matana basu taɓa ganin hawayena ba duk shekarun nan. Kai kuwa ka saka mace a gaba kana abin kunya. Ko batun alaƙar taku shi ma ƙarya ku ka yi min?”

    Girgiza kai Kamal ya yi. Alhaji ya dubi Mubina da allura a hannu tana kallon ƙasa. Allurar ya ce tayi tunda da alama akan lokaci ake buƙatarta. Ba don haka ba ya san Kamal ba zai fito da asuba ba. Bayan anyi allurar wadda yadda yaga an soka ta ciki ya ƙara kiɗima shi sai ya tambayi Nos ɗinnan abin sallah. Gari har ya soma haske basu yi asuba ba. Daga kan gadon Kamal ya bi shi sallar. Bayan sun idar suna zaune su biyu, Alhaji yana zaune akan abin sallah ya tambaye shi game da ciwon.

    “Lalurar dake damunka a hanyar fasiƙanci ka same ta ne?”

    “A’a Alhaji” ita ce amsarsa.

    Muryar Alhaji ta karye domin a tsorace yake Allah Ya sani. Kamar kada ya idar da sallah ya yi tambayar tun farko.

    “To me yasa? Mene ne dalilin ɓoyewar?”

    “Saboda maganin ba mai samuwa bane Alhaji. Ƙoda nake buƙata kuma …”

    Yana son yin faɗa amma ya san cewa abin da zai sa Kamal yi masa ɓoyon ciwo ba ƙaramin abu bane.

    “Gani, ga ƴan uwanka mutum ashirin da bakwai amma ka kasa faɗa? Bayan na san karamcin da Allah Ya yi min a gidana. Yau ko babu ni babu mahaifiyarka ina da yaƙinin cewa sauran uwayenka za su tsaya maka ka samu a jikin ƴan uwanka ko da kuwa ƴaƴan cikinsu ne.”

    Nan dai Kamal ya yi masa bayani akan matsalar da aka samu. Bai gamsu ba sai da Mubina tayi masa fashin baƙi. Amma duk da haka zuciyarsa fafur taƙi amincewa. Ana bayanin yana jin zufa a duka jikinsa. Gabansa kuwa faɗuwa kawai yake yi.
    Yayi salati yafi a ƙirga. Kamal ya yi mamaki domin faɗa yasa rai zai yi masa.

    “Alhaji baka yi min faɗa ba.”

    “Wane irin faɗa kuma Kamal? Ta yaya ma za ka yi tunanin zan maka faɗa? Halin da zuciyarka take ciki na firgicin ciwon ma da ina da iko wallahi zan raba ka dashi. Da ace akwai yadda zanyi cikin ku babu mai yin atishawar da zai ji a jikinsa. Baka ganin dalilin ciwo na dawo da ɗan uwanka? Ta yaya kai kuma zan yi fushi da kai?”

    “Kayi haƙuri.”

    Tare su ka fito bayan allurar ta saki Kamal. Alhaji ya dage sai dai ya bishi a motarsa. Zai turo a ɗaukar masa tasa.

    “Kawo muƙullin to..” ya miƙa hannu zai karɓa. Alhaji ya hana.

    “Da ƴaƴana da jikoki kake tunanin zan yarda kana rabin mutum ka ja ni?”

    Suka yi dariya sannan su ka shiga Alhaji ya ja su. Jifa jifa su kalli juna su yi murmushi don su kwantarwa juna hankali.

    “Alhaji don Allah maganar nan..” Kamal ya fara roƙonsa da su ka isa gida.

    “Shiga ciki Kamaluddeen” Alhaji ya katse magiyar da ya so yi masa akan ya yi shiru da maganar.

    Bayan Kamal ɗin yabi ya same shi yana yiwa su Taj ƙaryar abin da ya fitar da shi da asuba. Murmushi yayi musu bayan ya amsa gaisuwarsu. Su huɗu yau su ka kwana a ɗaki guda kamar wasu yara ƙanana.

    “Yaya kan naka?”

    Abba ya wani turo Taj gaba “taɓa shi kaji Alhaji. Jikin da sauƙi. Ai jiya bamu yi bacci ba saboda yi maka gadinsa.”

    “Nagode Sulaiman. Yau ni ne abin tsokana ko? Ko da yake girmanka ne baban Hayatu.”

    Aka saka dariya sannan ya haye sama ya kira Ahmad. Taj ne kawai ba ya sakin jiki ya yi dariyar saboda har yanzu zuciyarsa ta kasa gaskata wai shi ne a gida.

    ***

    Rabon da Abba Habibu yaga rigimar Yaya irin wadda ya gani tun bayan dawowarsa a daren jiya ya manta. Ta nuna masa rashin jindaɗinta sosai. Da mitar ta kwana ta tashi.

    “Amma dai kin san ba dawa taje ta kwana ba.”

    “To mene ne maraba? Gidan surukan da bata riga ta tare ba saboda Allah. Salon a sami abin goranta mata nan gaba.”

    Kwanciya Abba ya gyara don bacci sam bai ishe shi ba. Ya yi dare a waje sannan rikici ya hanasu bacci sosai.

    Yaya ta haɗe rai “kwanciya ma za ka yi?”

    “Da fa? So ki ke muyi ta ɗaga murya a sami abin goranta mata da yawa?”

    Saukowa tayi don kanta da taji me yace “amma ka san damuwata. Ina gudun kada ace bamu saya mata mutumci ba.”

    “Akwai mutumcin da ya wuce auren da aka ɗaura mata? Kuma na nanata miki cewa ba Taj bane ya ce ta zo su tafi. Yaya Hayatu ne ya ce ta bi mijinta.”

    “Zancen nawa dai ya fito. Ya ce ta bi shi saboda yana ganin ya isa. Ni bana son wani ya rainaka ne.” Ta faɗi da ƙanƙanuwar murya.

    “Nayi zaton kin yi min sanin hagu da dama ashe ba haka bane? Wallahi kuɗi ko muƙami ba zai sa na wulaƙanta ƴata ba. An riga an ɗaura aure. Bai kamata na nuna mata bijerewa umarnin mahaifin mijinta garesu daidai bane. Ko har kin manta matsayin da muka haɗu da Taj tsakaninsa da babansa?”

    Jikinta sai ya sake yin la’asar. Ta kama bakinta bayan ta bashi haƙuri. Bawan Allah dama ba riƙo gare shi ba. Nan da nan ya kashe wancan zancen ya sako maganar kai amarya tunda ya san dole za a dawo da Hamdi daga gidan Alh. Hayatu. Sai da su ka gama tsara komai ya koma ya kwanta ita kuma ta fito falo.

    A firgice ta sami Zee tana kai kawo. Zee ɗin na ganinta tayi maza ta rufe ƙofar falon kada kowa ya ji.

    “Yaya kada ki tada hankali idan ki ka ji me zan faɗa.”

    “Allah Yasa dai lafiya Zee.”

    “Jiya Hamdi bata dawo gidan nan ba.”

    Da gangan Yaya ta ce “kai haba?”

    Zee ta sake kwantar da murya “Wallahi kuwa. Nayi ta kiran wayarta bata ɗauka. Sai da asuba tayi min message wai tana gidan su Ya Taj.”

    “Indai haka ne ai babu damuwa.”

    Zee kasa ɓoye mamakinta tayi. Da tsammanin faɗa ta zo sai ta samu ba haka ba. Yaya ta gama tsokanarta sannan ta taimaka tayi mata bayanin me yake faruwa. Su ka gama dariya da tunanin me za su ce da mutanen da suka kwana idan aka fara cigiyar amarya.

    ***
    Hajiya, Umma da Mama sai da safe Inna ta sanar dasu duka abubuwan da su ka faru a gidan da daddare, har ma da baƙuwarsu. Murna a wurinsu ba a cewa komai. Dawowar Taj abin farinciki ne da shi kaɗai ya cancanci ayi ƙwarya ƙwaryar walima saboda farinciki.

    “Amma banda abin Alhaji me zai sa ya taho da Hamdiyya bayan tare da mahaifinta su ke?” Umma ta faɗi bayan sun ɗan nutsu da murnar.

    “Kema dai Jamila kamar baki san halin mijin naki ba. Ƙarshenta gani ya yi kamar Taj ya damu shi ne zai taho masa da ita don ya kwantar masa da hankali. Son ƴaƴa kuma a wajen mutumin nan ai ba a magana.” In ji Mama.

    Wata uwar guɗa su ka ji daga falo. Dama suna ɗakin Mama ne. Inna ta sallami kowa ta bar Hamdi saboda baccin da ya sake ɗauketa bayan tayi sallar asuba.

    Fitowa su ka yi iyaye, ƴaƴa da jikoki. Ashe Amma ce tayi fitowar sassafe ko wanka bata yi ba. Hijabi kawai ta ɗora akan rigar baccinta ta fito. Tana ganin matan gidan, musamman Inna sai ta kama kuka.

    “In da na san aure ne zai dawo da Taj gida ai da ko kwana guda ba zai yi a matsayin ɗan da uba ya kora ba. Kai, Allah mun gode maKa.”

    Waɗanda basu sani ba duk sun ji a lokacin. Murna da farinciki kamar me. A wajen Taj ta sami labari tun daren. Nan falon nasu su ka kira Kamal ya shigo da Taj. Sai abu ya koma kamar ranar kowa ya ƙara ganinsa tun tafiyarsa ta farko. Waɗanda basu kwana a gidan ba ma duk an kira su. Kafin bakwai sun cika gidan. Taj murmushi kawai yake yi. Yana cikin farinciki fiye da kowa. Ciwon kan ma ya tafi gabaɗaya ya tafi. Zuciyarsa kamar yau aka dasa masa ita. Babu damuwar komai a ciki. A gaban ƙafafun Amma ya zauna akan kafet tare da ƴan uwansa. Baka jin komai sai hamdala da ake yawaita yi.

    “Kai ku duba min Hamdiyya ko ta tashi.”

    Hajiya ce tayi maganar tana mai duban ƙofar ɗakin Inna. A take mutum uku ƴan mata da wasu biyar cikin jikoki su ka miƙe a guje kowacce tana cewa ita za ta duba.

    “Mijinta na zaune wa ya aike ku?” Mama tayi musu tsawa. Sai kuma ta kalli Taj “tashi kaje mana.”

    “Ina?” Ya tambaya don bai san kan gidan ba yanzu.

    “Tana ɗakin Inna” cewar Firdaus.

    Tashi ya yi kafin yana waige “wanne ne?”

    Yayinda wasu ke nuna masa, masu hankali wannan tambayar fami tayi musu. Inna mai yawan kawaici sai gata ta duƙar da kai tana share hawaye. Ace ɗan halak bai san ɗakin mahaifiyarsa ba a gidan ubansa! Tabbas wannan abu akwai ciwo.

    Yana ganin halin da su ka shiga ya yi saurin barin wajen domin baya son ayi ɗa kwance uwa kwance. Murnar kowa za ta koma kuka. Abin da ba zai so ba. Tafiyarsa kuwa tsokanar ƴan uwansa ta janyo masa. Aka yi ta masa dariyar shaƙiyanci. Hakan sai ya hana koke koken da iyayensu su ka fara.

    *
    Hamdi ta fi minti goma sha biyar tana son fitowa amma tana kunyar mutan gidan. Na farko bata san lokacin da kowa ya fita ba saboda bacci…..’bacci a đakin uwar miji don abin kunya’ shi ne abin da ta fara faɗawa kanta da ta farka. A saman kayanta na jiya kuma taga an ajiye sabuwar doguwar riga an cireta daga leda amma da tag. Da ta ɗaga wani irin ƙamshi ne mai daɗaɗa ruhi yake tashi a jikinta. Babu makawa turara ta aka yi. Ga wata ƙaramar ledar an saka sabon brush. Ta san ita aka ajiyewa. Banɗaki ta shiga tayi wanka a gurguje ta fito. Bata son kowa ya shigo ya ganta. Musamman Inna. Gaban dressing mirror ta zo ta tsaya ta shafa man da Innar ta nuna mata jiya. Daga nan bata sake taɓa komai ba ta saka rigarta mai kyau ta yafa ƙaramin mayafin ta fita falon ɗakin. Nan ma babu kowa shi ne ta dinga zuwa ƙofar fita tana dawowa.

    Buɗe ƙofar taji anyi tayi saurin gyara zama a zatonta Inna ce. Sallamar da ya yi ce ta sake tada mata hankali. Idan wani ya shigo ya gan su a ɗakin fa? Idan Inna….

    “Baki amsa min sallama ba kin tsaya kina yaba Salman Khan daga sama har ƙasa.” Taj ya faɗa yana zama a kan kujerar da take.

    Da sauri ta tashi tsaye tana kallon ƙofa ta ce “Ni ba kai nake kallo ba” da ƴar tsiwarta saboda ba wai ta manta abin da ya yi bane jiya.

    “As if…” sai kuma ya koma kallon falon yana inhaling ƙamshinsa kafin ya miƙe tsaye “Wanne ne ɗakin baccin Inna?”

    Da hannu Hamdi ta nuna masa. Yadda ya dinga tafiya ne ya taɓa mata zuciya. Ta bi bayansa har ciki. Nan kam har lumshe idanu ya dinga yi saboda yadda ƙamshin ɗakin yake nutsar masa da zuciya. Irin ƙamshin da ya dace da Innarsa. Mai sanyi, daɗi da kuma kama waje ya zauna a ran wanda ya shaƙe shi.

    Juyawa tayi za ta fita ta bashi wuri sai kawai taji ya janyota ya rungume ta baya. Duƙar da kansa ya yi daidai kunnenta. Wani nau’in ƙamshin ya shaƙa mai daɗi. A ransa ya ƙudurta neman sunan mai sayarwa a wajen Inna don ba za a bar matarsa da gidansa a baya ba.

    ” Yau ma arziƙinki na ci aka ce na shigo ɗakin Inna kamar yadda Alhaji ya barni na shigo gidan nan domin ki. I owe yoy big time Hamdi. Thank you.”

    Tausayinsa taji kamar daren jiya ta ce “Na taya ka murna Happy.”

    “Kin dai taya mu.” Ya juyo da ita suna fuskantar juna.

    “A’a fa. Ni dama tun farkon zuwana Alhaji bai koreni ba.”

    “Sai ni uban ƴan taurin kai ko?”

    “Ni dai ban faɗa ba” tayi murmushi.

    “Kin ayyana a ranki na sani.” Ya kama hannuwanta yana murmushi.

    “Ka dai tsargu kawai saboda baka da gaskiya”

    Janta ya yi wajen gadon “Zo mu ɗana gadon Inna.”

    “Ni kaza?” Hamdi ta ce a firgice “kada ka janyo min abin faɗa har jikoki mana.”

    Zillewa tayi ta fita daga ɗakin ya bita falo kafin ta fita.

    Haƙuri ya bata akan maganganum Alhaji ga Abba jiya.
    “Abin da nayi jiya har yasa ki fushi was for you Hamdi. Na san baki ji daɗi ba amma ina so muyi clearing issue ɗin kafin anjima.”

    Da ya san amsar da za ta fito daga bakinta da bai tayar da wannan maganar ba. Kallonsa tayi. Kallo mai tarin ma’anoni. A wajenta kuwa da manufa ɗaya tayi shi…(na san abin da nake yi).

    “Uba uba ne Ya Taj. Nagode da baka barni na yiwa Alhaji rashin kunya ba da yanzu ina nadama don ba tarbiyar gidanmu bace. Amma ina so ka sani cewa WALLAHI ba zan taɓa sakin jiki a gidanka ba sai Alhaji ya ɗauki Abbana da darajar da Allah Ya bashi.”

    “Me kike nufi?” Taj ya tambayeta da yaji komai nasa ya fara kwancewa.

    “Aurena kayi ba sadaka aka baka ba. Allah Ya sani ba zan iya ɗauke kai ina gani ana yiwa mutum mafi girman daraja a wurina irin haka ba. Sai in ga kamar nima na yarda bai kai a girmama shi ba.”

    “Amma ni wane irin girma ne bana bashi?”

    Abin da bata son farawa don kar ta kasa dainawa ne ya zubo. Hawaye. Hankalin Taj ya sake tashi. Ya matso ta matsa baya.

    “Ba da kai nake ba. Ba kuma faɗa nake da Alhaji ba. Amma kai ma ka san irin matsayin da ya bashi daga maganarsa ta jiya. Kana gani ko zuwana nan ba shawartarsa ya yi ba duk da dai an ɗaura aure. Ko don ya taɓa yin daudanci ne?”

    A lokacin ya gane Hamdi bata da labarin ainihin abin da yake tsakanin iyayensu maza. Bata san sanayyarsu ta wuce ta zaman unguwa ɗaya ba. Akwai sauran rina a kaba kenan. Amma da ta buɗe ƙofa ce ta kawo ƙarshen zancen.

    Sam bata nuna musu taji maganganunsu na baya bayan nan kuma ta fahimci inda suka dosa ba. Faɗan hana Hamdin fitowa tayi masa.

    “Abinci za ta ci a mayar da ita gida.”

    ***

    Wayar Alhaji ce ta tayar da Ahmad daga baccin da ya koma. Kamar yadda dalilai daban daban su ka hana yawancin mutan gidansu bacci, shi ma haka Salwa tayi sanadin wargaza nasa zaman lafiyar da ta gayyato Anti Zabba’u gidansa.

    Ana kiran assalatu da ya tafi masallaci su ka tattara za su bar gidan ko tsinke basu gyara ba daga ɓarna da almubazzarancin da su ka yi da daddare. Suka taɓa ƙofa su ka ji a garƙame. Ya sanya kwaɗo ta waje da zai fita. Anti Zabba’u ta dinga ruwan ashariya tana cewa tafi ƙarfin Ahmad ya wulaƙanta ta.

    “Mu gyara gidan nan kawai kafin ya dawo. Ni bana son rigima.” Wata a cikin ƴan matan ta ce.

    Rai a ɓace Anti Zabba’u ta ce “An faɗa miki saboda shara ya rufemu? Nuna isa ne kawai da cin mutumci irin na uwarsa.”

    “Duk da haka gara mu gyara. Zan fi son mu fita salin alin kafin ya fahimci halin da waccan mara kunyar take ciki.”

    Da wannan maganar su ka duƙufa. Gyaran dai sai a hankali amma dai yafi babu. Duk abin da su ke yi kuwa Anti Zahra tana jinsu tayi zamanta a ɗaki. Mami ma taji komai tana cike da takaicin ba za ta iya ɗaukar mataki ba.

    Da ya dawo don kansa ya ce su bar aikin saboda yadda su ka tasarma damalmala gidan. Ruwan mopping wannan klin aka zuba masa kuma ba a bari ya narke ba aka matse mop ɗin sama sama aka soma yaɓawa a ƙasa.

    “Ga gidanka nan za mu fita amma wallahi Ahmad bashi kaci. Wannan wulaƙancin sai kayi nadamarsa.”

    “Boka ne fa ki ke taƙama dashi. Ni kuma da wanda ya busawa bokayen rai na dogara. Ki ajiye makaman kawai ayi zumunci Fisabilillahi.”

    Ƙwafa tayi. Ranta yana tafarfasa. Mutumin da ta bawa kuɗinta kuma aiki bai ci sai ya yi nadama shi ma.

    Sun zo fita Ahmad ya ce “ina Salwa?”

    Kamar jira suke kuwa yana magana su ka fice gabaɗaya a gurguje. Bai tsaya tambayarsu ko lafiya ba ya shiga ɗakin ya ganta a zaune a kan kafet da kumburarriyar fuska tana kuka.

    “Tunda bugun fanke kaɗai su ka yi miki ki taso ki gyara gidan nan yanzu yanzu.”

    “Yaya baka ganin fuskata ne?” Ta sauke mayafinta yadda zai gani da kyau.

    “Allah Ya ƙara. Maza ki fito ki gyara gidan. Amma ki fara duba ko Mami tana buƙatar wani abu.”

    Kwanciyarsa kenan Alhaji ya kira. Dama ya tsorata saboda yayi wuri mutum ya amsa waya. Hankalinsa sai ya nemi barinsa bayan ya faɗa masa me Salwa tayi da kuma babban abin wato ciwon Kamal. Muryarsa kuma rawa take yi sosai.

    “Ban faɗawa kowa ba sai kai. Ina buƙatar ka zo mu yi shawara Ahmad. Zan iya rasa Kamal a kowacce daƙiƙa.”

    “Kayi haƙuri. In sha Allahu zamu sami mafita. Gani nan zuwa.”

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!