Rayuwa Da Gibi – Chapter Thirty
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Wata doguwar allura Mubina ta zare daga tsakiyar cikin Kamal ta ajiyeta akan kwanon tasa daidai girmanta. Ta koma gefe ta haɗa yatsunta na hagu da dama ta sarƙesu, sannan cikin dabara ta cire gloves ɗinta. Duk abin da take yi kwata-kwata taƙi yarda ta haɗa ido dashi. Umarni kawai take bawa Nos ɗin da ya taya ta aikin akan abin da zai yi. Shi kuwa yana ta kallonta har ta gama bai ce uffan ba. Canjawar yanayinta ya sanya zuciyarsa tsirgawa don ya san bashi da nasaba da kasancewarsa babu riga a wajen.
Baya ta bashi yana daga kwance ta harɗe hannuwanta a ƙirji.
“Sauƙin da za ka samu yanzu ba mai ɗorewa bane. Daga shi sai dialysis wanda shi ma tasirinsa ba ya wuce lokacin da za a sami ƙodar da za a dasa.”
Numfashi kawai yaja da ƙarfi yana mai rufe idanuwansa. Zuciya da jikin nasa duka sun gaji. A ƙoƙarinsa na ganin bai ɗagawa kowa hankali ba yayi exhausting ɗin kansa. Duk wata lakar jikinsa mutuwa tayi sakamakon jin abin da tace. Tashi ma sai ya gagare shi. Ji yake kamar lokaci zai cimmasa yanzu yanzu. He badly needed a shoulder to cry on. A ɗan rarrashe shi a bashi baki. Sai yanzu yake nadamar ƙauron bakinsa. Sunan Happy yake kira a zuci domin shi ne zai iya bashi shawarar yadda za su fasa ƙwan a gida.
Shirun da ya yi ya sanya Mubina yin gyaran murya.
“Bari na baka wuri ka shirya.”
Da sanyin jiki ya yi mata magana kafin ta fita.
“Kada ki tafi Mubina. Bana son zama ni ɗaya don Allah. Not when you just told me I don’t have much time left.”
Tsayuwa tayi amma bata ce komai ba har ya mayar da rigarsa ya sanar da ita. Ta juya a hankali ta dube shi. Idanunsa sun kaɗa sun yi ja sosai. Sai wata ƙwalla da take barazanar wanke masa fuska. Koma mata ɗan yaro ya yi mai jiran rarrashin uwa. Komai nata da ya danganci juriya a take ya ƙwace. Jikinta ya kama rawa a yayinda ta fashe da wani irin kuka mai tsuma rai.
“Yaya za ka yi da haƙƙina da ka ɗauka Kamal?”
Idanunsa ko buɗewa da kyau basa yi ya ɗaga kai ya kalleta.
“Me nayi miki kuma?”
“Ka san baka da burin rayuwar duniya me yasa ka bari na kamu da son ka? Me yasa kake azabtar dani ta hanyar nuna min kanka a yanayin ciwo amma ka ƙi bani haɗin kan nema maka magani?”
“Ashe kina sona…” Kamal ya tattaro ƙarfin hali yayi murmushi gami da komawa ya kwanta “kinga har naji ƙarfi a jikina. Bari na huta sai na tafi.”
Wani irin kallo Mubina tayi masa “ka san ƙarfe nawa kuwa? Ko ka manta za a sake allurar ƙarfe shida na asuba?”
“Kada ki damu zan dawo in sha Allahu.”
Mamaki ya bata. Ta zata gaskiyar da ta faɗa masa mai ban tsoro za ta sa ya soma tunani da yin abin da ya dace. Rai a ɓace ta ce
“You are simply unbelievable! Me za ka je yi a gidan bayan dare ya raba? Kai da ka zo a sume ne kake zancen zuwa gida.”
Ya za ayi ya manta? Dama dauriya ya dinga yi a wajen dinner ɗin. Taj na fita da Hamdi ya kirata. Lokacin ta kusa gida ma tunda ita ma taje dinar. A asibiti su ka haɗu sai dai kafin ta iso ya suma a mota. Wurin parking ta dinga dubawa har ta gano motarsa tasa aka ɗauko shi.
“Zan fa dawo da gaske. So nake in sanar da Alhaji lalurata. Ko ba haka kike so ba?”
“Kada ma ka faɗa mana. Ni ina ruwana? Na daina damuwa.”
Kamal ya yi murmushi “to wallahi ki canja taku don soyayya babu nunawa juna damuwa bata da armashi. It won’t even last.”
Ƙwalla ta goge da ƙasan mayafinta ta harare shi “kai ɗin lasting zaka yi balle soyayyarka?”
“Ahhhh, abu na Allah…ki ka san ta inda sauƙi zai zo min? In warke muyi aure. Duk shekara na raka ki labour room ɗin can naku na sama.”
Ba lokacin wasa bane amma sai da Happiness ya sanyata murmushi sannan su ka fito daga ɗakin.
*
Alhaji bai yi mamaki ba da bincike ya nuna banda jinin Taj da ya hau babu wani abu da likitan ya iya gani da zai zama silar ciwon kai mai tsanani irin wanda yake fama dashi. Ya duba ido da kunne har ma haƙoransa domin ciwonsu kan jawo ciwon kai amma duk ƙalau suke. Kuma ya ce yana bacci.
“To ko stress ɗin biki ne?” Likitan ya tambaya da damuwa.
Miƙewa tsaye Alhaji yayi “kada ka damu doctor. Kawai ka rubuta masa pain reliever mu tafi.” Idan sihiri ne ba a asibiti za a gani ba.
Rubutawar ya yi su ka fito. Taj yana mai ƙara jin mamakin mahaifin nasa. Yadda yake abubuwa kai ka ce babu abin da ya taɓa faruwa a tsakaninsu.
Kowa tasowa yayi da ganinsu banda Hamdi. Da farko tana ganin ƙofar ta buɗe ta tashi da sauri. Tana haɗa ido da Alhaji sai ta koma ta zauna ta kama kallon gefe. Kama kanta tayi don kada ya faɗi abin da zai sake damunta.
Taj ɗin ma ƙin kallonsa tayi wanda Alhaji ya karanci yadda hakan ya dame shi. Da alama kasancewarsa a wajen ce kawai ta hana shi ƙarasawa gareta. Ita ma kuma dauriya ce da taimakon fushin da tayi tun a hanya ya hanata ko da satar kallonsa.
Murmushi Alhaji ya yi ba tare da ya sani ba. Wannan yarinya anyi rigimammiya. Wato ita nan maganarsa ce har yanzu ba ta haƙura ba. ‘To ai shikenan. Na san maganinku daga ke har Taj ɗin.’
“Abba zo ka kaisu gida sai ka taho da motar Taj ɗin.”
Zumbur ta miƙe tayi gaba. Taj ya auna yaga idan ya bari ta fita fa akwai matsala a gaba. Kai ya ɗan sunkuyar yaƙi kallon Alhaji da Abba ya ce,
“Ina zuwa Alhaji.”
“Ina za ka je?”
Hamdi da ta kusa ƙofa kuma taji maganganun da suke yi sai ta tsaya cak. Kuka kawai take son yi. Wato umarnin kada ya bita aka bashi yanzu kuma. Bata juya ba ta sake ɗaga ƙafa ita ma Alhajin ya tsayar da ita.
“Kema ina za ki je a daren nan kike ƙoƙarin fita ke kaɗai?”
“Tafiya za mu yi Alhaji. Dare ya raba sosai.” Abba Habibu ne ya bashi amsa.
“Ai na san daren ya yi shi yasa nace Abba ya kai ku gida kai da wanda ya tuƙo motar.”
Ba shiri Hamdi ta juyo. Taj ma dai Alhajin yake kallo.
“Ku kuma ku wuce mu tafi gida.”
“Mu su wa?” Taj ya yi tambayar a gaggauce.
“Kai da matarka mana. Ko kana tunanin a daren nan zan bari ka tafi gidan Ahmad ka tashe su?” A zahiri kuwa baya son yaje ne ya sake haɗuwa da Salwa ta ƙulla wani abin. Bai ga abin da zai sa ya bar Taj ya kwana nesa da gida ba yau ɗinnan.
Furucinsa Halliru mai tuƙo mota ne kaɗai bai bawa mamaki ba tunda bai san komai ba. Fuskokinsu su duka abin dariya don dai ma Alhajin yana gudun raini a gaba da ya dara. Idanun Hamdi ƙara girma suka yi. Na Abbanta kuwa da Taj sun yi micimici kamar ya ce zai yanka wani.
Taj baya son saka rai a banza sai cewa ya yi “ban taho da muƙullan gidan ba.”
“Naku gidan ba da gayyar mata ku ke shigarsa ba?” Alhaji ya ce yana tafiya har ya wuce Hamdi ya fita.
Bata iya tafiya ba sai da Taj ya ƙarasa inda take ya riƙo hannunta. Suna zuwa bakin ƙofa ta ƙwace hannun ta fito. Abba Habibu dai ya shiga duhu dole ya nemi ƙarin haske.
“Alhaji ina za su je ne?”
“Gidana.” Ya amsa kai tsaye.
Hankalin Hamdi sai yanzu ya yi asalin tashi. Ta dubi Abbanta tana girgiza kai kamar zata cire shi.
“Bishir muƙullin motar yana wajenka ko?”
Nuna masa muƙullin ya yi shi kuma kai tsaye ya yi gaba ko jiran wani ya yi magana bai tsaya yi ba. Ya sakar musu bomb ya barsu da hayaƙi.
“Abba don Allah ba za ni ba” cewar Hamdi harda hawaye.
Taj kuwa kai ya girgiza masa cike da murna “Abba ku tafi sai da safe.”
“A yi haka?”
“Abba kana ji fa Alhaji da kansa ya ce in zo gida na kwana ba roƙa nayi ba.” Ya kalli Hamdi, kallo na girmamawa “albarkacinki naci. Wallahi albarkacin aurenki ne. Nagode Hamdi.”
Shi ma Abba sai lokacin ya fahimta sosai. Ya riƙe hannuwan Taj su ka yiwa juna murmushi na farinciki.
“In sha Allah daga yau waccan magana sai dai a tarihi kuma. Allah Ya cigaba da toshe dukkan ɓaraka.”
“Amin Abba. Nagode. Nagode” Ya amsa da murmushi.
“Ni fa ba zan…”
“Bi mijinki ku tafi Hamdi. Sai da safe.” Abba ya katseta da sauri.
Yana gama magana yabi bayan su Halliru. Aka barta da Taj. Hannunta ya kamo kada su yiwa Alhaji laifin barinsa jira. Suna zuwa su ka samu ya shiga gaba. Su biyun su ka zauna a baya. Motar tayi tsit. Alhaji ne kaɗai yake jin wani irin farinciki na kasancewa tare da Taj a wannan yanayin.
Ribas Bishir ya yi idanun Alhaji su ka sake sauka akan motar Kamal. Da sauri ya ce da Bishir ya tsaya. Bai yi musu magana ba ya fita ya koma cikin asibitin. Shaf ya manta yaga motar lokacin shigarsu. To me yake yi a ciki basu gan shi a reception ba sannan bai neme su ba? Mota kuma tasa ce babu tantama.
Yana shiga ciki ya nufi wajen Receptionist ɗin sai ga Kamal da Mubina suna fitowa daga koridon inda Emergency room yake.
“Kamal?”
Hantar cikin Kamal sai da ta kaɗa da ya tabbatar Alhaji yake gani. Ya yiwa Mubina kallon tuhuma sai tayi saurin girgiza kai.
“Baka da lafiya ne?” Alhaji ya tambaye shi.
“A’a. Dawo da ita nayi daga wajen dinner.”
A tsanake Alhaji ya kallesu sannan ya ce “Me ka zauna yi to? Naga motarka tun zuwanmu kusan awa guda da ta wuce.”
Kamal ya rasa ƙaryar da zai gilla sai Mubina ce ta ƙwato shi saboda yadda taga ya gama ruɗewa.
“Emergency case na samu Baba. Sai yanzu na fito.”
“Allah Ya bada lafiya. Amma duk da haka da shi sai ya tafi gida tunda dare ya yi.”
Haƙuri Kamal ya bashi. Yana shirin tambayar waye babu lafiya Alhaji ya sake yi masa tambaya.
“Me ma ya zaunar da kai? Ko akwai alaƙa a tsakaninku da ban sani ba?”
Kaɗan daga aikin Alhaji kenan. Faɗin magana kai tsaye ba tare da ɓoye ɓoye ba. Mubina ji tayi kamar ƙasa ta buɗeta shige ciki. Kamal kuma da yake neman mafaka tuni ya cafke wannan damar ya nuna hakan ne.
Tsaf Alhaji ya haɗe rai kuwa.
“To ni bana son irin haka? Idan kana neman mace sanar dani ya kamata ka fara yi saboda nayi magana da manyan ta. Amma haka kawai ka ɗauko ƴar mutane ka zauna a wajen aikinta da talatainin dare irin wannan ai bai yi ba.”
“Ayi haƙuri Alhaji.”
“Kema da ki ka biyo shi baki kyautawa kanki ba. Na yarda da tarbiyar Kamal a matsayin uba amma ku ƴaƴan zamani ba a ci muki laya. Allah dai ya kiyaye kawai.”
Ita ma haƙurin ta shiga bayarwa ba ji ba gani.
Da dai Kamal yaga tarkonsa ya kama sai ya cigaba a haka. Ya karɓi laifin da bai yi ba ya cigaba da bada haƙuri. Sai da komai ya lafa ya tambayi waye babu lafiya. Da yaji Taj ne ai sai ya ture nasa ciwon ya fita. Mubina ma sallama tayi masa ta koma ciki.
“Alhaji mu je mana” ya dawo da ya ankara shi kaɗai ya fita.
“Jeka. Likitan da ya duba shi zan tambaya game da wani bayani da ya yi min.”
Da sauri Kamal ya wuce. Alhaji ya bi shi da kallo har ya fita sannan ya koma reception jiki babu ƙwari. Gabaɗaya Kamal ɗin ya sauya sosai. Tun rashin lafiyar kwanaki da aka ce allergy ne ya lura yaron nasa ba yadda ya saba yake ba. Ya dai haƙura da yawan tambayarsa ya jiki ne da yaga yana harkokinsa na yau da gobe babu fashi.
“Doctor ɗinnan da muka gama magana gobe ƙarfe nawa za ta tashi? Akwai patient da nake son ta duba min na manta ban faɗa mata ba.”
Wani ɗan littafi mutumin ya duba ya ce “yau bata da night (call), sai 3 na yamma kuma za ta shigo goben. Yanzu ma na san alfarma kawai ta yi masa tunda ya saba zuwa amma she is off.”
“Shi wa kenan?” Alhaji ya ɓoye matsanancin tashin hankalin da ya kama shi.
“Wanda ka gansu tare.”
“To nagode”
Wani irin sanyi mai farawa daga cikin ƙashi ne ya dirarwa Alh. Hayatu. Kamal bashi da lafiya kuma yana ɓoye masa.
Fargabar da ya dawo mota da ita ce ta hana shi sakar musu fuska yadda ya yi niyya.
“Alhaji ko su dawo motata?” Kamal ya tambaye shi bayan ya zauna mazauninsa.
Ba tare da ya kalli inda Kamal ɗin yake tsaye da Taj ba ya ce “Tunda cinyesu zanyi ko?”
“Tuba nake.” Kamal ya faɗi yana dariya “Happy mu haɗu a gidal”
Motarsu Alhajin ya koma shi kuma Kamal ya ja tasa shi kaɗai. Yana murna da Alhaji ya hana su biyo shi domin da sun ƙara lokaci a tsaye Taj zai cigaba da yi masa tambayar ƙure.
A motar ma duk da ba hira suke ba amma Alhaji sai da ya tambayi Taj ko Kamal ya faɗa masa me yake yi a asibiti cikin dare. Amsar bata sauya daga irin wadda ya bashi ba da kansa ba.
Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Kowa ya yi shiru har aka isa gidan. Da su ka isa tsayuwa su ka yi a bakin motar don basu san ina za su nufa ba kuma. Alhaji da ya san jiransa suke yi sai lokacin ya ɗan saki fuska bayan isowar Kamal. Wayar Inna ya kira kuma bai yi mamakin da bata yi bacci ba ta ɗauka. Ya ce mata ta fito akwai baƙuwa.
Inna ta taso da hijabinta don dama sallah kawai take yi tana addu’o’i. Da ta buɗe ƙofar sakin baki tayi kafin kuma ta fito waje sosai inda suke ta rungumo Hamdi.
“Alhaji lafiya dai ko?”
“Lafiya ƙalau. Kawai dai naga bai dace ta koma gida a daren nan ba tunda matar aure ce.”
“Haka ne” Inna ta gyaɗa kawai cike da mamakin da yaƙi ƙarewa “shi kuma wannan gidan Ahmad za a kai shi ko?”
“A’a” Alhaji ya amsa mata da wani irin murmushi a fuskarsa. Haka kawai yake jin son kyautata mata ko don yadda hankalinta ya tashi ɗazu “a gidan nan zai kwana.”
Wani irin farinciki mara misali ya sake mamaye Taj. Kamal kam rungume shi ya yi yana faɗin “mun gode Alhaji. Allah Ya ƙara girma. Ya ja kwana. Mun gode”
Ya dafa kafaɗar Taj ɗin “Happy zo mu je ka kwanta.”
Sake basu mamaki ya yi da cewa “Kada ku takura, ya kwana a ɗakin ƙasa na ɓangare na.”
Wai kuma sai ya juya zai shige ciki. Inna har lokacin tana riƙe da hannun Hamdi ta juya ita ma da sauri tana mai danne kukan da take shirin yi. Taj kawai ta kalla taga yadda furucin mahaifinsa na ƙarshe ya kawo wani irin hasken annuri ya shifiɗe masa a fuska. Sai hamdala da take ta karanta daga laɓɓansa. Abin da ake jira kuma ake ganin kamar ba zai yiwu ba ne ya faru a lokacin da ba a zato.
“Allah Ya faranta maka fiye da yadda kayi min. Ina roƙon Allah Ya kawo maka ɗauki ta inda ba ka zato akan duk masifa ko rashin kwanciyar hankalin da zai tunkaroka. Na gode Yaya Hayatu.”
Yau ake kira farar rana. Rabon da Zainabu Abu ta kira Alhaji da sunan da ta saba kiransa a matsayinsa na ɗan uwanta ya manta. Yana son ya juyo ya bata amsa daidai da addu’ar da tayi masa amma ga ƴaƴa da suruka a wajen. Don kada ya bada kansa sai ya gyaɗa kai kawai.
Hamdi ta ajiye fushinta a gefe domin wannan abu maƙiyi ne kaɗai ba zai taya Taj murna ba. Ita da bata cika son magana ba sai take jin ya kamata ta ƙara nunawa Alhaji cewa mahaifinta ya horar dasu da kyakkyawar tarbiyya. Da wannan tunanin a duƙa har ƙasa a gefen Inna. Muryarta a hankali cikin nutsuwa ta ce,
“Allah Ya saka da alkhairi Alhaji. Allah Ya bamu ikon faranta maka fiye da yadda kayi mana. Mun gode.”
Sai yanzu ya yi magana “babu komai. Ku shige ku kwanta.”
Inna dama jira take ta sami damar yin kukan farinciki. Da sauri ta wuce ciki. Tana riƙe da hannun Hamdi har ɗakinta. Ƴan kwanan kowa ya kwanta banda mutum biyu Badi’a da Sadiya da su ka san Taj babu lafiya. Basu tashi matan gidan ba su ka zauna jiran su Alhaji. Suna ganinta da Hamdi ta yi musu bayani kafin ma su tambaya.
“Aikin babanku ne ya taho da ita daga asibiti wai dare yayi.”
Badi’a ta ce “to ina Taj ɗin?”
Da wata irin murna ta wanda yake cikin zaƙuwar bada labari ta sake cewa “Alhaji ya dawo dashi gida”
Sai kuma ta faɗi cikin sujjada tana yiwa Allah kirari. Hanyar fita Sadiya tabi za ta fita ta fesawa ƴan uwanta Inna ta dakatar da ita. Ta nuna mata dare yayi ga gajiyar da aka kwaso. Da ƙyar Sadiya ta haɗiye zancen ta haƙura sai asuba.
“Hamdi akwai ruwa a heater. Ki ɗan watsa ruwa don jikinki yayi daɗi sai ki kwanta.”
Babu musu ta tashi za ta shiga banɗakin da Inna ta nuna mata. Jikinta tayi tsamin gajiya sosai. Innar ta bata wata doguwar riga da ƴar hula ta shige dasu. Kafin baɗakin akwai wani ɗan wuri da aka saka shoe rack da wani ɗan tabur inda aka ajiye mai da turaren jiki irin oils ɗinnan na Scentmania irin nata. Nan ne wurin shafa mai sannan mutum ya shiga ɗaki ya ƙarasa shafe shafensa. Wanka tayi ta ɗauro alwala. Tana fitowa ta samu su Sadiya sun kwanta. Sai Inna dake sallah. Dama tana kunyar yadda za ta kwanta ɗaki ɗaya da mahaifiyar Taj. Da taga tana sallah kawai sai ta zauna. Ita kuma Inna da ta idar ta tambayeta me ya hanata kwanciya.
“Nima sallar zan yi Inna.”
Wani murmushin farinciki da Inna tayi ya nuna tsantsar jindaɗinta. Ta bata hijab su ka yi raka’a shida sannan Hamdi ta soma hamma. Sai tayi kamar ta idar. Ai kuwa akan abin sallar Hamdi tayi bacci. Wannan qiyamul laili da tayi tare da Inna kuwa ta saya mata wajen da babu wata mace da za ta taɓa auren Taj ta mallaki wannan gurbi. Kaɗan daga sirrin Tahajjud!
A ɓangaren Alhaji kuma Kamal, Bishir da Abba da ya dawo daga baya duk ɗaki guda su ka kwana da Taj. Alhaji yana jiyo hayaniyar murnarsu kamar ba dare ba. Sai ya tuna ƙuruciyarsu da kuma samartakarsu da ya katse na tsayin shekaru. Rashin jindaɗin abin da yayi gami da tunanin wane ciwo ke damun Kamal sai su ka hana shi baccin kirki.
Wuraren huɗu da rabi yaji alamun an buɗe ƙofar ɓangaren nasa. Dama baccin babu nauyi. Da sauri ya leƙa domin ya gani ko jikin Taj ne ya tashi. Fitowarsa tayi daidai da fitar Kamal. Nan jikinsa ya sake mutuwa. Ya koma bakin gado ya zauna. Baccin da bai koma ba kenan sai kawai ya ta da nafila. Yana ji aka soma kiraye kirayen assalatu. A zuciyarsa ya ƙudurta sauka ya tashi su Taj nan da minti talatin sai su yi alwala su tafi masallaci.
Ko minti goma ba ayi ba yaji ana buɗe gate a hankali. Ya sake tashi ya leƙa sai ya hango motar Kamal ce ta fita. Bai yi wata wata ba ya sauka ƙasa da muƙullin wata sabuwar motarsa. Da kansa ya ja hankalinsa a matuƙar tashe. Rabonsa da tuƙi ya ma manta. Cikin sa’a da yabi hanyar asibitin sai ya hangi motar Kamal tunda titi fayau yake dai motoci jifa jifa.
Haka ya bishi har asibitin ba tare da ya sani ba. Yana parking bayan shigar Kamal ciki sai ga Mubina. Da sauri ta shiga asibitin tana magana a waya. Bayanta Alh. Hayatu yabi da sauri. Tana shiga cikin asibitin tayi hanyar emergency inda ya ga fitowarsu ɗazu ya kirata da kakkausar murya.
“Dr. Mubina”
Cikinta ya ba da wani mahaukacin sauti domin ta riga ta gane muryarsa. Ta juyo kamar mara laka a tsorace.
“Kai ni wajen yarona.”
Gaba tayi ya bita a baya har ɗakin. Ta buɗe da sallama. Nos ɗin da ya taya ta aiki da daddare yana tsaye akan Kamal dake kwance babu riga. Juyawar nan da Kamal ya yi da yaji motsinta sai idanuwansa su ka sauka a cikin na Alh. Hayatu Sule Maitakalmi.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
