Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    A mafarki ko ido biyu, Alhaji bai taɓa tunanin zuwan wannan rana ba sai da ta zo ɗin. Yau dai zahiri ba zance ba shi ne yake zaune a cikin falonsa babu kowa sai masu gadi da direbansa dake bakin gate su na hira da daddare. Gabaɗaya gidan ana idar da sallar magariba su ka daɗe. Duk an tafi wajen dinner ɗin Taj da Hamdi. Hatta masu aikin gidan babu wanda aka bari. Kasa zaman falon nasa ya yi ya shiga ɓangaren matan gidan. Nan kam sai da zuciyarsa ta motsa da tausayin kansa. Shiru ne mai ratsa ɓargo. Sai kayayyyakin ƴaƴansa da jikoki da ba a gama tattarewa ba. Wasu ma a ƙasa su ka bar nasu.

    “Ganɗoki” ya yi murmushi yana mai duƙawa ya ɗauke kwalbar turaren da aka bari a ƙasa.

    Samun kansa ya yi da tsince duk wani abu dake ƙasa wanda bai kamata ba. Yana yi ransa na tunatar dashi cewa duka mutanen da su ka shirya a wajen nan da ɗakunan matansa fa nasa ne. Zuri’arsa ce. Shi kaɗai a shekarunsa sittin da takwas ya tara jikoki sama da arba’in. Ga ƴaƴa ga tarin dukiyar da ko yau ya ajiye kasuwanci ba za su buƙaci komai ba a shekara goma masu zuwa.

    Ya auro mata masu mabambantan tushe amma waɗanda su ka yi tarayya wajen taya shi gina gida irin wannan. Tabbas shi ma ya sani cewa arziƙinsa ba a naira da kwabo yake ba. Iyalinsa sune arziƙinsa. Banda dai abubuwan yau da gobe da ba a rasawa amma ya tabbatar cikin ƴaƴansa babu fasiƙi. Allah Ya yi masa gamdakatar Ya shirya masa zuri’a. Kuma komai ya ce ya zauna daram kenan a gidan. Duka ya ɗauka ƙarfin ikonsa da tsare gida ne wanda cikakken namiji kaɗai ke iyawa.

    Sai gashi an wayi gari sun haɗa kai suna neman juya masa baya. Jiya sun tafi wajen kamu ƙwai da kwarkwata. Bayan saboda girman gidansa ƴaƴan dangi ma suna cin arziƙin ayi bikinsu a nan. Shi su ka tafi gidan Alh. Lurwanu don su nunawa duniya gazawarsa. Yau kuma Hajiya ta ce masa event centre za su je kuma sai an gansu. Abin tambaya a wajensa yanzu shi ne wai me yasa su duka su ke ganin aibun hukuncinnda ya yankewa Taj? Anya sun san yadda illar dake tattare da daudanci? Habibunsa fa daga son girki ya fara kamar wasa. Idan a baya Taj bai yi ɗabi’un mata ba yanzu zai iya. Surukuta ta shiga tsakaninsu da ɗan daudu kuma ga aiki suna yi tare. Ya numfasa a yayinda ya zauna ya kula cewa gyara sosai ya yiwa falon. Dole ne ya raba Taj da Hamdi. Barazanar da ya yi a Bauchi bata nufin ya karɓi wannan aure. Salwa ce ba zai taɓa bari ta kusanci danginsa ba. Duk lalacewar ɗan daudu yafi mushriki a wurinsa.

    ***

    Ƙememe Yaya taƙi shiryawa,wai ba za ta je wajen bikin ba. Duk ga ƴan uwa za su wakilceta. Za ta zauna a gida da Innarta Luba da ta zo jiya. Aka kaɗa aka raya taƙi chanja shawara. Gashi ƴan matan nata duka ukun basa nan. Yanayin gidansu bai basu damar yin ƙawaye ba. Shi yasa duk wani abu da za ayi da ƙawa tare su ke yi.

    Tun azahar Safwan ya kwashesu zuwa event centre ɗin inda a saman wurin ne za a rangaɗa musu kwalliya. Kowacce mijinta ne ya biya mata. Ita Hamdi lalle aka fara yi mata. Ɗaya daga cikin yayyen Taj tana da saloon da wurin lallen amare da na matan ƙwalisa. Wadda tafi iyawa ta tura ta yiwa Hamdi baƙi da ja. Tun kafin a gama ake santin kyawun da yayi. Ana gamawa aka koma kwalliya bayan tayi sallar la’asar. An fito da ita fita ta girma. Sai wanda ya sani ne kawai zai iya gane ita ɗin Hamdiyya ce ɗiyar Habibu Simagade. A haka kuwa za ka yi zaton ƴar wani ƙusa ce. Ana kammala kwalliyar tayi sallar magariba sannan ta saka kaya.

    Anti Labiba ce ta kira Sajida ta faɗa mata rigimar da ake yi da Yaya akan ta shirya. Sajida tana ji ta san babu wani kunya ko kawaici da yasa mahaifiyar tasu son zaman gida. A nata tunanin rashin zuwan zai taimaka ya ɗago darajar ƴaƴanta a idon mutane. Bata son yin abin da zai janyo mata ido harma ayi ta ambaton ita ce maman amarya, daga nan wanda bai sani ba a bashi labarin cewa babansu ma tsohon ɗan daudu ne.

    “Don Allah ba ta wayar Anti.”

    Harara kala kala Yaya ta gama yiwa Anti Labiba kafin ta karɓa.

    “Yaya me yasa ba za ki je ba?”

    Caraf a kunnen Hamdi. Ta karɓi wayar ana yi mata ɗauri da wani yadi haɗe da net mai santsi.

    “Yaya ba za ki ba?”

    Shiru tayi saboda taji yadda muryar Hamdin ta canja.

    “Yaya?”

    “Ina jin ki. Ga iyayenku nan. Kowa zai je. Me zan je yi ni kuma?”

    Zee da Sajida kusa da Hamdi su ka dawo su ka kara kunnuwansu. Kowacce tana iya gane zancen na Yaya akwai damuwa a ciki. Hamdi sai cewa tayi,

    “Wallahi Yaya idan baki je ba nima daga nan gida zan taho.” Su Zee jinjina mata su ka yi da thumbs up da ta faɗi haka.

    “Ke ba na son rashin kunya.”

    “Allah Yaya. Zan zauna a saman nan har sai kin zo.”

    Sajida ta miƙawa wayarta ta koma aka cigaba da ɗauri. Sai dai ana yi ƙwalla na sauko mata. Mai kwalliya tabi ta tada hankali. Idan kwalliyar ta caɓe ko amarya bata sauka da wuri ba za a sami matsala.

    “Za fa ta zo tunda taji kin yi rantsuwar nan.” Cewar Sajida.

    “Ke ma ai bata je naki ba.” Zee ta tunatar da ita.

    Ita dai me kwalliya haƙuri ta soma bawa Hamdi ganin wankin hula yana neman kai su dare. Sai da ya rage pins kawai za a saka a jikin mayafi da head ɗin sannan kukan nata ya ƙaru. Daga can ƙasan zuciyarta take yinsa. Ta ƙara jinjinawa uwa a duk inda take. Babu yadda za ayi ace Yaya bata son ganin ƴaƴanta a wajen bikinsu suna walwala kamar kowacce uwa. Amma kawai don kada a aibata mata su saboda yanayin tafiyarta shi ne ta zaɓi zaman gida.

    Da bikin Sajida duk sun ɗauka kawaicin uwa ne. Musamman da basu ga mahaifiyar Safwan a wajen event ɗin nasu ba (baban Safwan ya hanata zuwa). Yanzu kuwa jiya komai da iyayen Taj aka yi. Yau ma su ne ƙirjin biki. Sai ace babu mahaifiyarta? Saboda miskiniya ce.

    “Ya Hamdi meye haka ne? Ji idonki har ya soma caɓewa fa.” Cewar Zee ta ƙara miƙawa mai kwalliyar tissue domin a gyara idon.

    Sajida wayarta ta shiga dannawa tana cewa “bar ni da ita.”

    Sai ji su ka yi tana gaishe da Taj. Ta kuma faɗa masa kukan da Hamdi take yi da dalilinsa.

    “Saka mata wayar a kunne.”

    Da canjin numfashin da yaji ya gane ta saka mata ɗin. Da rarrashi ya yi mata magana.

    “Zan kawo miki Yaya in sha Allahu. Ki daina kuka idan ba haka ba kuma yau sai mun yi kuch kuch hota hai a gaban mutane. Mu yi ta rangwaɗa kai kamar ƙadangaru.”

    Dariya ce ta kama Hamdi. Sajida, Zee da maikwalliya su ka saki baki suna kallon ikon Allah.

    “Waƙar bata da hayaniya sai na taya ka.”

    “Haka ki ka ce?” Ya tambayeta yana murmushi “Wayarki na kusa?”

    “Eh”

    “To ki dubo waƙar I am a disco dancer a youtube. Ni kuma idan baki daina wannan kukan shagwaɓar ba in baki mamaki a gaban mutane. Ita zan yi. Kin kuma san zan iya. 80s aka yi ta ba ta zamaninku bace.”

    “To Baba Happy. Na ma share hawayen” ta goge idonta da kanta don barazanar Taj ba abin da za ta share bane.

    “Wannan ladabin ba na gaske bane. Sai na tambayi Sajida naji ko kin ƙara yin kuka.”

    “Allah na daina.”

    “Hamdiyya” ya kirata a tausashe.

    Kasa buɗe baki ta amsa tayi saboda kiran nasa na daban ne.
    “Uhmm”

    “I’ll see you later.”

    “Bye” ta miƙawa Sajida wayar.

    “Iiiiiikon Allah” Sajida ta faɗi baki buɗe “me zan gani ni Sajida ƴar Habibu? Hamdi? Dama rashin jin muryar mijinki ne yasa ki kuka? Shi ne ki ka ɗorawa baiwar Allah Yaya. Ai kuwa bari nace mata tayi zamanta.”

    Da sauri Hamdi ta miƙe tana kici kicin karɓe wayar “ɗaukota fa zai je ya yi. Shi yasa ki ka ga nayi dariya.”

    Zee tayi dariya “anya kuwa? Naji fa kina zancen wata waƙa wai bata da hayaniya.”

    “Ke, kira Ya Baballe ku gaisa kema ki ji daɗi.”

    “Baballen lafiya? Sunansa Sadiq” ta faɗa tana kallon yayyen nata.

    A tare su ka bushe da dariya sannan Hamdi ta koma ta zauna aka gyare fuskarta kamar bata yi kuka ba. Ana gamawa ta koma gefe ta buɗe youtube. Hannunta yana ƙaiƙayin ganin waƙar da Taj yake cewa zai yi. Da ta kunna ɗaya tayi kama da ta 80s ɗin daga ɗaukan ma. Ɗayar kuwa ɗaukan zamani ne. Bata ma ɓata lokacin kallon ta zamanin ba wadda ta kasance remake ɗin tsohuwar. Danna tsohuwar tayi inda kunya ta kusa sumar da ita da rawar da Mithun yake yi. Saboda raye raye nan taƙi jinin waƙe-waƙe. Idan Taj ya yi wannan girgizar da karya jikin tabbas a wurin dinar za ta tafi ta barshi.

    Su Zee dai kallonta kawai suke yi. Tana duban waya da ido ɗaya tana kawar da kai.

    “Ta fa ci kai wannan.” Sajida ta faɗi su ka yi dariya ko kula su bata yi ba duk da taji.

    *

    Da Taj ya gama wayar, ji ya yi an ture shi. Sai lokacin ya ankara ashe a jikin Kamal ya jingina da shauƙi na ɗibarsa. Ya rasa me yasa shi da Hamdi basa iya yiwa juna baƙunta. Kamar ba jiya jiyan nan da sauran ƴar rigimarsu ba. Yau kam komai ya wuce!

    Ɗaure fuska Kamal ya yi “Na ma rasa abin da zan ce maka Happy? Wato haka ake soyayyar ni ka barni ina fama da instagram da daddare?”

    Taj ya kama dariya “ba dai ka tsaya wasa ba? So kake sai Dr. Mubina ta kawo maka katin aurenta ka zo ka ce min zuciyarka za ta fashe ko?”

    “Allah ma Ya kiyaye. In sha Allah ba zan ga aurenta ba.” Cewar Kamal yana mantawa da wa yake magana.

    Wata irin juyowa Taj ya yi yana kallonsa “saboda kai za ka aureta ko kuwa ƙasar za ka bari idan ta tashi auren wani a dalilin nauyin bakinka?”

    Wayancewa Kamal ya yi “likitoci na auren ƴan kasuwa ne? Idan rabon wani ce sai in tafi China odar kaya kafin a gama bikin.”

    Tsaki Taj ya yi “ta nan kuma ka ɓullo? Hmmm, kai ka san yanayin aurena da matsalar Alhaji ne su ka shige min gaba. Ba don haka ba da yanzu kai ma kana kwanciya kamar gasara a ruwa idan kuna waya.”

    “Wannan karin magana ne ko me?” Kamal yana dariya ya tambaye shi.

    “A bakin Ƴar Ficikar nan naji.”

    Dariya su ka yi sannan Kamal ya ce zai fita waje ya tada mota kafin Taj ya fito sai su ɗauko Yaya. Ɓata lokacinsu faɗan iyaye zai jawo musu.

    Yana fita Taj ya bishi da ido. Jikinsa yana bashi tabbas akwai abin da ɗan uwan nasa yake ɓoyewa. Kwana biyu ma tunda ya dawo ya gan shi a rame. Yanzu ne ma ya ɗan ciko. Zuciyarsa ta bashi ko ma mene ne ya shafi Dr. Mubina. Kuma yafi tunanin ƙila soyayyar Happiness ce bata karɓa ba. Da an gama bikin nan zai je ya sameta har asibiti ko ya nemi gidansu. Indai ba wani aka bawa ita ba zai nuna mata cewa rashin karɓar Kamal asararta ce. Happiness is a rare gem. Ko shi da ya same shi a matsayin ɗan uwa ba ƙaramin dace ya yi ba.

    Ƙarasa shirinsa ya yi su ka fice daga gidan. A daidai bakin layin su ka ga motar Ahmad wanda dawowarsa kenan daga Bauchi. Horn su ka yiwa juna. Basu kula da Salwa a gaban motar da kuma Mami dake kwance a baya ba.

    Kiran wayarsa Kamal ya yi yana sanar dashi kayansa wanda duka ƴan mazan gidan zasu saka banda ango suna ɗakinsa. Sun bawa Anti Zahra ta ajiye masa kafin ta tafi.

    “Zan ɗan makara amma. A gajiye nake.”

    “Wai ina ka je ne? Ance tun safe ka fita.”

    Ahmad ya kalli bayan motarsa ya sauke numfashi.

    “Sai mun haɗu dai.”

    Da taimakon Salwa su ka shigar da Mami cikin gidan. Gabaɗaya ta rikirkice saboda ƙamshin turaren Taj da hancinta yake iya bambancewa duk inda ta ji shi. Ɗakin da take zama Ahmad ya ce su shiga da Mami.

    “Bari nayi wanka naje wajen dinner ɗinnan. Ba zan jima ba in sha Allah. Gobe da safe sai mu tafi asibitin.”

    Da azama ta miƙe ita ma bayan ta kwantar da Mami “Nima bari na shirya kafin ka fito.”

    Haɗe fuska Ahmad ya yi “Salwa.”

    “Na’am.” Sai kuma tayi murmushi “wallahi sauri zan yi Yaya.”

    “Ba ki da hankali ashe.” Ya nuna kansa yana juya ɗan manunin yatsansa cikin ɓacin rai “wa za ki barwa Mamin da kike zancen zuwa dinner?”

    Murmushi tayi “lahh, Ya Ahmad ai kai ma ka san ba zan tafi haka kawai ba. Tun a hanya nayi magana da Anti Zabba’u (ƙanwar Mami). Tana hanya ma don na faɗa mata mun shigo gari.”

    “Yaushe ku ka yi maganar ban sani ba?” Ahmad ya tuhume ta.

    “Tun jiya ne bayan mun yi waya da kai.”

    Zama ya yi a gefen gadon yana matse gaban goshinsa kafin ya ɗaga kai ya kalleta da takaici.

    “Dama shirinki kenan shi yasa ki ka yi min ƙaryar Alhajinku ba ya kula da lafiyarta?”

    “Wallahi Yaya…”

    A harzuƙe ya tashi kamar zai kifa mata mari “Shut up Salwa. You are very stupid.”

    “Don na ce zan je bikin ƙaninka kake zagina Ya Ahmad?”

    “Ba za ki ba! Ko ƙalau Mami take babu inda zaki. Haba! Yarinya kin bi kin haukace kuma kina neman haukata kowa. Taj baya son ki, kuma ko yana so ina cikin masu hana shi aurenki saboda baki san bambancin so da obcession ba.”

    Kuka ta fashe masa dashi. Tana jin saukar maganganunsa tamkar sukar mashi. Sai ta mallaki Taj a matsayin miji kuma akan idonsa ta ƙudurta a ranta.

    Mami tana daga kwance tana ɗaga lafiyayyen hannunta akan su yi shiru. Kallonta Ahmad ya yi ya fice kawai domin dai ba a canjawa tuwo suna. Alh. Mukhtar ya faɗa masa komai da yaje ɗaukarta. Ya kuma sanar dashi cewa ya saketa sannan idan sun tafi to ta tafi kenan daga rayuwarsa. Har abada baya son sake ganinta. Ƙannen Salwa mazan suna wajensa. Ita kuma ya ce idan sun gama zaman asibiti ya dawo masa da ita domin aurar da ita zai yi. Sun gama magana da wanda zai aureta ma.

    Wannan ne dalilin da yasa ya taho da ita. Ba wai ƙaryar da tayi masa ba. Don tabbas komai na buƙata Ahmad yaje ya samu suna dashi. Kawai mijin nata ne dai ya fita harkarta.

    “Zan jira Anti Zabba’u ta iso kafin na tafi.” Ta ce da Mami.

    “Uhmm uhmm Salwa” Mami ta ce da ƙyar.

    “Mami zani fa. Na san da lafiyarki ƙalau za ki bani goyon baya.”

    Banɗaki ta shiga ta sillo wanka. Ta fito tana cikin shiri Anti Zabba’u tayi mata waya cewa tana bakin gate. Garin saurin ta buɗe mata abu ya faɗo daga jikinta bata sani ba. Yunƙurawa Mami tayi ta leƙa abin. Sai da jikinta ya kama rawa. Sabuwar laya ce don zaren fari ne tas irin wadda take taunawa idan za ta yiwa Alh. Mukhtar magana. Zarginta akan Salwa ya tabbata. A asibiti Salwan tayi zaton bacci take ta ɗauki wayarta ta kwafi lamba. Kuma taji buƙatar da ta faɗa…tana son mallake wani. Sai yanzu ta gane malamin tsibbunta ne Salwan ta ɗauki lambarsa. Kenan duk abin da take yi ƴar na lura? Bata son inda tabi har rayuwa tayi mata wannan atishawar ƴan tsakin ita ma Salwa ta bi. Da ƙalau take duk inda ake takawa zata je domin farincikin ƴarta, amma bata so ƴaƴan su yi wannan rayuwar.

    Bakin Salwa kasa rufuwa ya yi da ta buɗe ƙaramar ƙofar gate su Anti Zabba’u su ka shigo. Don ma babu motar Ahmad ta san ya tafi. Gayya guda har su shida. Ita da ƴan matan ƴaƴanta guda uku. Sai babbar bazawara da goyo. Kowacce ta bawa shabiyar baya. Ita ma Anti Zabba’un ta gaji da aure aure ta haƙura. Dama kuma ta jima tana roƙon Mami ta tilasta Ahmad auren guda cikin ƴaƴan nata amma taƙi yarda saboda kar ta san kar ne. Sai gashi Salwa ta faɗa mata halin da Mamin take ciki. Da murna ta kwaso jiki. Ko Ahmad yana so ko baya so sai ya auri ɗaya kuma ya saki wannan mai dara daran idanuwan.

    Ita dai Salwa bata san Mami taga layarta ba. Ɗaukewa tayi ta tura a jaka. Ta gama shirinta tsaf ta haɗa da turaren wajen su Ummi ta fita. A rashin sani turaren aikin Alh. Usaini ta ɗauka tunda shi ne aka ce mata zai kawo soyayya tsakaninsu.
    A daidaita sahu ta samu har event centre ɗin. Motoci ko ta ina. Ta zo bakin gate tayi turus don babu kati!

    ***

    Shafawa ido toka Taj ya yi da ya shiga ciki ya ce da Abba ya roƙi da Yaya ta fito su tafi saboda abin da Hamdi ta ce. Yayan da Inna Luba suna zaune a wajen.

    “Ayi haka Taj? Muna da gefe bai fi ba?”

    “To nima dai idan bata fito ba tabbas babu inda zani tunda amaryar tayi rantsuwar ba za ta fito ba.”

    “Barni da ita. Yanzu zan kira in yi mata faɗa.” Cewar Abba yana ƙara kaurara murya don ya ƙara mata kwarjini.

    Taj ya ce “Abba me ɓoyon zai ƙara ko ya rage? Waye bai san ƴarka nake aure ba? Wa kuma kuke son ɓoyewa kanku? Kuna jin gata ne kuke yi musu? Mushirikai da fasiƙan iyaye ake gudun nunawa. Amma idan kuna yin haka nan gaba sai sun fi ku jin kunyar a ganku tare. Kunga sai ayi ta rubuta musu zunubin rashin kyautatawa iyaye.”

    “Kai Tajo, me yayi zafi?” Inna Luba ta ce a tsorace “ke tashi ki shirya ku tafi.”

    “Ke fa Inna?” Taj ya ɗaga mata gira “nawa kakannin babu. Ki zo ki wakilci kowa.”

    “Ja’iri, to bari nasa kaya. Dama wannan ƴar ce ta hana ni zuwa amma na so bin su wallahi” ta miƙe da murnarta.

    Murmushi Abba ya yi. Yaya da Inna Luba su ka shiga ɗaki. Basu daɗe ba kowacce ta fito cikin shiga mai kyau. Yaya lace ɗin da Mama ta aiko ta ce mata ankon manya ne ta saka. Kai kana ganinta banda lalurar ƙafa da ba ƙaramar mace za ayi ba. Fuska dai kam Masha Allah. Akwai kyau irin na Katsinawa wanda ƴaƴanta su ka haɗa da na Simagade su ka fito gwanin ban sha’awa.

    ***

    Ƙarfe bakwai da minti arba’in da biyar daidai Amma ta kira Taj ya ce mata suna wajen parking.

    “Bari a sauko da amaryar sai ku shigo.”

    “Amma tare muke da Yaya.”

    “Tun ɗazu nake lalubenta cikin baƙi. Gani nan fitowa.”

    Da kanta taje wajen motar ta riƙo Yaya su ka shigo. Mama na hangota daga wajen zaman iyaye ta tada Umma su ka ƙarasa. Hajiya ma ta ce da Inna lallai ta tashi. Tunda aka ce Taj ne ya kawota ta san tana tattare da jin nauyin shiga jama’a ne. Mutane sun fara kallon Yaya ana ƙusƙus da faɗin uwar amarya ce sai aka ga matan Alh. Hayatu Sule masu aji sun je inda take suna yi mata maraba. Kayansu ita da matan da Amma iri ɗaya. Sannan su duka har ƙasa su ka gaishe da Inna Luba. Wannan abu yasa duk mai abin faɗa ta haɗiye kayanta. Dukkan alamu sun nuna su ɗin suna cikin farinciki da son juna. Gutsiri tsomar ƴan gayya bata da tasiri.

    A ɓangaren amarya kuma ƴaƴan Amma wato Ihsan da Amira da kuma Anisa sun haɗu da masu ƙananun shekaru cikin ƴan gidansu Taj da Anti Zahra sai kuma Sajida da Zee wajen rako amarya. Gabaɗaya matan doguwar riga su ka saka ta wani yadi sky blue da ɗigon fari da pale yellow wadda aka yiwa wani irin ɗinkin bubu mai kyau. Umarnin Hajiya Gambo kenan. Duk wata jininsu da tayi ɗinki mai fitar da shape a gida zata ci bikinta. Babu head sai rolling da su ka yi da pale yellow ɗin yadi mai santsi. Babu yadda za ayi ka gansu basu burgeka ba. Modesty and elegance at its peak!

    Amarya Hamdiyya kuwa gown ɗinta fara mai dogon hannu kuma wadatacciya. Bata bi jikinta ta tona sirrin wanda ya bada sadaki a gaban kowa da kowa ba. A kanta anyi mata ɗauri da net silver wanda aka ɗorawa wani abin ado mai duwatsu sky blue na gashi ya kwanta ta ɓari ɗaya. Daga tsakiyar ɗaurin inda gashinta yake a suturce aka ɗora farin net dogo har ƙasa. Wuyanta sarƙar farin gwal ce. Sai clutch bag ɗinta da takalmi mai tsini sky blue. Tayi kyau har ta gaji.

    Ƙasa suka sauko sannan aka zo bakin ƙofa aka jera yadda za a shigo. Kallo ɗaya Anisa ta yiwa Hamdi tunda sai yau su ka iso ta ganeta.

    “Mai kukan uber?” Ta faɗa ba tare da wani tunani ba.

    Hamdi ta ɗago su ka haɗa ido. Ta saki murmushi mai ban sha’awa. Haka kawai sai Anisa taji ƙuncin zuciyarta ya kau. Ta matsa kusa da ita tayi musu selfie sannan aka ce su tsaya kamar yadda aka tsara musu.

    Matan layi layi suka yi hagu da dama har layi shida. Sai Hamdi a tsaye. A bayanta kuma Bishir da Abba. Sai kuma Kamal da Ahmad a bayansu. Sanye su ke da yadi pale yellow da aka yiwa ɗinki ma hannu da ya wuce gwiwar hannu da kaɗan. Daga hula har zuwa takalmi komai nasu iri ɗaya in banda agogo. Hamdi tayi zaton tafiya za su fara yi don hankalinta a tashe yake tun a nan ga hasken flash ana ta ɗaukar hoto. Ƙofar hall ɗin aka buɗe ta soma jin sanyi da ƙamshin wajen na buso ta sai ji tayi hannuwa sun kama nata da gentle riƙo. Tsigar jikinta tashi tayi da tsoro da kuma gane hannun waye. Tsayuwarsa kaɗai a kusa da ita ta sanya sanyin nan ya ragu don kansa. Ta ɗaga kai su ka haɗa ido.

    Kayan jikinsa sky blue ne harda babbar riga irin wadda ake yi ta zamani ba burum-burum ɗinnan ba. Shi ma hannun rigarsa ta ciki ƙarami ne kamar na ƴan uwansa. Ya sanya hula da takalmi cover shoe navy blue mai duhu sosai. Gashin baki da gemunsa da basu cika yawa ba sun sha gyara.

    “Ya Rabbi, har na fara tsoron ko ni kaɗai zan shiga” Hamdi ta faɗi a hankali tana kawar da kai don kallon nasa babu rissina a ciki.

    “Ina tare dake kowanne taku. Ki daina jin tsoro.” Ya bata amsa a kunnenta.

    Hannunta zai saki yaji ta kuma damƙe nasa.

    “Don Allah ka riƙeni har mu zauna. Zan iya faɗuwa da takalmin nan.” Ta marairaice masa idanu har lokacin tana magana a hankali don kada na gabansu ko baya su ji.

    “Awwwnnnn, zuciyata” Taj ya dafe ƙirji kuma da gaske yadda tayi ɗin ya shige shi ne sosai.

    Fari tayi da ido tana harararsa “A nan ɗin ma sai kayi?”

    “Kin gama dani ne Mrs Ha…”

    Wani abu su ka ji kamar harbin bindiga da ya katse masa magana. Sai kuma muryar MC yana sanar da shigowar ango da amarya da umarnin kada kowa ya bar wurin zamansa da sunan ɗaukar hoto. Wani irin kiɗan taushi ne yake tashi babu waƙa a yayinda suke shigowa wajen cikin nutsuwa. Matan dake gaba basu mai rawa sai ɗan kwanon hannunsu mai fulawoyi masu kyau da su ke ta watsawa sama.

    Da su ka iso gaba Yaya ta ƙyallara idanu ta hango ƴan matanta, bata san lokacin da idanunta su ka tara ƙwalla ba. Ta dinga hamdala a zuciyarta. Ashe Inna Luba ma hakan take a wajenta. Sai dai ita bata iya ɓoye nata hawayen ba. Jikokin kenan sai Halifa cikon na huɗu. Sai kuwa na yayarta abar alfaharinta har kullum. Amma dai jininta da take da cikakken iko dasu waɗannan ne. Da kanta ta dinga bin ƴan uwan Yaya wato ƴqƴan abokiyar zamanta mazansu da matansu a samu mai zuwa bikin nan amma yadda su ka ƙi zuwa na Sajida wannan ma ƙi su ka yi. Ta roƙi maigidanta ko sau ɗaya ne ya yi musu magana ko ya zo ƴarsa taji daɗi ya ce ba zai taɓa murna don ƴaƴan ɗan daudu sun yi aure ba. Su je can su ƙarata. Godiya kawai take ga Allah domin bai haɗa mata zuri’a da lalatattun mutane ba. Dukiyar bata tsole mata ido ba. Girmamawar daga surukan ƴaƴan shi ne komai a wajenta.

    A teburin gefensu Iyaa ce da su Ummi, sai kuma surukar Sajida da ƙannen Safwan. Shi da Baballe suna can ɓangaren maza.

    Amarya da ango sun sami waje sun zauna sannan ƴan rakiyar su ka koma nasu waje. Aka shiga cikin taro ka’in da na’in.

    An fara da addu’a daga bakin babbar baƙuwa Malama Maimuna. Bayan ta gama aka ce ta faɗi kalmomi biyu zuwa uku na shawara ga ango da amarya.

    “Tajuddin da Hamdiyya. Abu ɗaya zan faɗa muku. Duk abin da za ku yi ku tuna cewa kowa cikinku mai kiwo ne kuma abin tambaya akan kiwon da Allah Ya bashi. Duk wanda ya tozarta amanar Allah sai Ya tanadi amsar bayarwa.”

    MC ya karɓi mike ya ce “wannan fa damu duka take. In kin san satar fita kika yi ki ka zo nan babu ruwanmu. Kai kuma mai shirin samun sabuwar budurwa a nan domin ka ci zarafin ta gida ta hanyar kwaye mata baya kana tona mata asiri to kai ma dai ahir ɗinka.”

    Dariya aka yi sannan ya ce ina Hajiya Amina aminiyar Inna. Tasowa tayi ita ma ya buƙaci kalmar shawararta.

    “Kada ku yarda soyayya ta sanyaku saɓawa Mahalicci. A komai na rayuwa ba a yiwa umarnin da ya saɓawa Allah biyayya ga kowa.”

    Godiya aka yi musu sannan MC ya ɗora. Agendarsu ta gaba ita ce gasar da aka shiryawa team ɗin ango da amarya. Tambayoyi ne da za su amsa game da juna. Aka sanya kujeru biyu suna kallon juna su ka zauna. A team ɗin ango akwai Sajida, Zee da Halifa.

    Team ɗin amarya kuma Yaya Hajiyayye da ta ce ta fi kowa sanin duka ƙannenta, Kamal da Ihsan ɗin Amma.

    “Ba zan tambayeku birthday ɗin juna ba.”

    Ya raba musu takardu guda goma. Kowa a takardarsa zai rubuta amsa da taimakon team members ɗinsa. Wanda ya yi na ɗaya zai sa wanda ya faɗi yin duk abin da yake so.

    Ƴan biki aka kasa zaune aka kasa tsaye da ganin wannan sabon salon. Kowa ya zata rawa za a sha yadda aka saba ana liƙi a gaban DJ.

    MC ya ce “a rubuta min cikakken kwanan watan ranar da ku ka fara haɗuwa a cikin sakan talatin.”

    (12/08/2021)

    Kusan tare su ka ɗaga takardunsu kafin lokaci ya cika.

    Kemara ta ɗauka aka haska a manya manyan talabijin dake manne a jikin bangon hall ɗin ta kowacce kusurwa.

    Daga nan ya dinga yi musu tambayoyi akan juna. Kamal, Yaya Hajiyayye da Ihsan da ta rayu da Taj kafin tayi aure a US sun taimakawa Hamdi sosai. Kazalika su Sajida. Aka gama tambayoyi suna kunnen doki.

    “Dole a sami na ɗaya da na biyu fa. Team members ku koma ku zauna a barsu su kara su kaɗai.”

    “Banda ke Hamdiyya, wa Taj yafi so? Kai ma banda kai wa tafi so?”

    Suna gama rubutun su ka ɗago kai.

    “Happy Taj wa ka fi so?”

    “Alh. Hayatu Sule Maitakalmi” ya faɗi da murya mai ban tausayi. Inna sunkuyar da kai tayi ta bar su Amma dasu Mama su da share ƙwalla.

    “Amarya wa ki ka rubuta?”

    Takardar ta ɗaga masa (Alhaji) ta rubuta.

    Ƴan uwan Taj su ka dinga tafa mata suna murna.

    “Wa ki ka fi so amaryar Happy Taj?” MC ya tambayeta.

    Da murmushi ta ce “Mamana, Yaya” tana mai kallon inda Yaya take a zaune. Baiwar Allah ita ma ƙwallar ta kama yi.

    “Taj wa ka rubuta?”

    (Duka iyayenta)

    MC ya nuna Hamdi ya ce “a tafawa amarya Hamdiyya.”

    Wurin ya kaure da hayaniya da murnar mutane. Wurin amsa tambayoyin nan ba ƙaramin kiɗima jama’a suka yi ba tun ma suna tare da masu taimaka musu.

    Taj ya fitittike ya ce bai yarda ba.
    “Ni fa da gangan na faɗi saboda nayi zaton ba za ta iya amsa nawa ba tunda ban taɓa faɗa mata ba.”

    MC ya ce “Kaga rigimammen ango” aka bushe da dariya “abin da za ta saka ka kake gudu?”

    “Eh wallahi. Na san me wahala za ta saka ni.” Ya sha kunu da wasa.

    “Wai haka?”

    “A’a” ta amsa mischieviously. Kai kana ganin farincikinta ka san amsar bata kai zuci ba.

    “To ke mu ke sauraro”

    Hamdi ta zaro ido “wai a nan zan faɗa?”

    “Eh mana” cewar MC

    “Iyayenmu fa duk suna nan” ta kalli saitin teburin iyayen nasu a kunyace.

    “Ga takarda ki rubuta masa ba sai mun ji ba.”

    (Don Allah ka daina yi min waƙar India)

    Tana bashi ya saka loudspeaker a bakinsa ya karantawa kowa. Aka fara dariya da ya ce a bashi fili.

    “Waƙar ƙarshe zan yi irin wadda ake mirginawa a ƙasa ana kuka a gidan boss.”

    Hamdi duka hannuwa tasa ta rufe fuskarta.

    “Na fasa kada tayi mana kuka.” Taj ya faɗi yana murmushi.

    Mutane suna ta dariya. MC ya ce Taj ya faɗi wani abu kafin su koma mazauninsu.

    “Nagode Allah da Ya bani Hamdiyya Habib Umar. Allah Ya bamu zaman lafiya.”

    MC ya turawa Hamdi speaker saitinta “ke kuma me za ki ce?”

    Ta kalli Taj ta rufe fuska da gefen mayafi “Amin….au mungode zan ce.”

    “Awwnnnnnnn” ɗin mutane kamar ta fasa dodon kunne. Aka dinga tafa musu har su ka zauna.

    Mutane sun nishaɗantu matuƙa. Daga nan aka fara rabon abinci wanda a yau ma’aikatan Happy Taj su ka baje kolin basira wajen yin wanda yafi na kullum daɗi. Nau’in girki na gaske kala kala aka yi. Luciousbites da kanta ba saƙo ba kuma ita tayi snacks da kuma daddaɗan youghurt da furarta wanda ake sha ana santi. Juice kuwa sai wanda mutum ya zaɓa.
    Babu mutum ɗaya da zai ce ya tafi gida da yunwa. Kowa yaci ya ƙoshi.

    Bayan an gama ne DJ ya soma nasa aikin. Anti Zahra tana bawa Hayat ruwa ta hango Ahmad yana yi mata signal. Wayarta yace ta duba. Tana ɗauka call ɗin Salwa na shigowa. Kira yafi arba’in. A zatonta abin da zai ce ta duba kenan shi yasa ta ɗauka.

    Salwa ta saki wata wawiyar ajiyar zuciya “Anti ina ta kira…”

    “Banji ba ne Salwa. Ya gida?”

    A gadarance ta ce “ina waje tun ɗazu. Kin taho da katina?”

    Anti Zahra ta kalli Ahmad da har yanzu alamar duba waya yake yi mata da hannu tace “wane katin?”

    “Ba a aiko min ba?”

    “Ke da kike Bauchi ai ban san za ki zo ba.”

    Tashi tayi ta bar yaran a wajen ƴan uwanta da suke seat guda ta ƙarasa wajen Ahmad. Waje su ka fita saboda hayaniya.

    “Ya zance ki duba waya ki tsaya amsa kira kuma?”

    “Sorry, na zata kiran Salwa kake nufin na duba.” Ta nuna masa missed calls.

    “Ƙyaleta. Nayi miki text nace na taho da Mami bata da lafiya. Gobe zan kai ta asibiti in sha Allah.”

    “Subhanallah. Shi ne muke nan? Bari na ɗauko su Aisha mu tafi.”

    “Kada ki damu. Salwa na gidan. Bana so mu koma ne kiga baƙi. A can ma ya dace na sanar dake to kuma ban sami nutsuwa ba.”

    Murmushi tayi masa “babu komai. Amma Salwa fa ta ce min tana waje.”

    “Waje kuma?”

    “Eh, kati take so in…”

    “Koma ciki.”

    Yayi maganar yana sauko matattakalar da za ta sada shi da hanyar fita. A waje ya ganta tsaye can gefe ta rakuɓe kamar wata almajira. Duk sauron wajen nan ya tabbata ya gama cinyeta. Ta ɗan bashi tausayi amma bai nuna mata ba.

    “Taho mu je.”

    Masu gadin suna ganin shi su ka bata hanya ta wuce. Magana ta so yi masa amma babu fuska. Da sauri sauri ya ding tafiya sai da su ka shiga hall ɗin sannan ya nuna mata inda ango da amarya suke.

    Taj da Hamdi ke tsaye a filin rawa taƙi motsi. Ya riƙe hannayenta yana magana tana dariya. Ce mata yake ko dai ta saki jikinta ko ya kama break dance yanzun nan.

    “Kin gani Salwa? Ke ya fara sani kafin Hamdiyya. Da yana sonki da kece a tsaye a can. Don Allah ki samawa kanki lafiya ki jira naki mijin.”

    “Na haƙura Yaya. Tafiya ma zan yi.” Ta ce kamar gaske.

    “Jirani a nan in faɗawa Zahra. Nan da kamar 15 minutes sai mu tafi.”

    Yana barin wajen tayi gaba. Ido rufe ta nufi inda su Taj su ke. Sun bar rawar sai hotuna da ake ta ɗauka. Tun kafin ta ƙarasa inda suke Hamdi ta hangota. Gabanta ya kama faɗuwa sai ta soma karanta Ayatul kursiyyu. Salwa na zuwa ta shige tsakaninsu ko sallama babu.

    “Ya Taj ayi mana hoto.”

    Yadda kafaɗarta take gugar tasa ko Hamdi da suke tsaye tun dazu bata yi wannan tsayuwar dashi ba. Matsawa yayi da sauri yana a’ziyya a zuci sai ji yayi ta riƙe masa hannu. Wani maiƙo maiƙo da danshin da ya yi zaton na gumi ne daga hannun nata duk ta shafa masa.

    Idanun Hamdi a take su ka rikiɗe sai dai ganin idon mutane sai ta daure zuciyarta. Taj na jan hannunsa ya fara jin ciwon kai Salwa sai ta sake ƙarfin riƙon.

    Basu san daga ina ba kawai sai wani hannun su ka ji ya kama hannayensu dake haɗe ya raba.

    “Zan ci mutumcinki Salwa akan yarona kin ji ko.”

    A matuƙar tsorace Salwa ta dubi Inna. Hanjin cikinta su ka kaɗa. Layar da take shirin sakawa a baki ta tauna sannan ta umarce shi da ya biyota ta saɓule ba tare da ta sani ba. Barin wurin tayi da wani irin sauri. Tana tafiya Inna ta duƙa da sunan Allah a bakinta ta ɗauki layar. Sunan ɗanta ta gani ɓaro ɓaro a jiki. Ta haɗa ido da Hamdi da taga komai ta matsa kusa da ita.

    “Kama shi ku zauna. Zan faɗawa Amma a rufe taron haka.”

    Kai Hamdi ta gyaɗa. Ta riƙo Taj da idanunsa su ka birkice. Bayan sun zauna tana ta tofa masa addu’a a fakaice ya dawo daidai. Ya ce ta tashi ya kaita gida.

    “Su Yaya fa?”

    “Bishir zai kai su. I need alone time with you.”

    “Na’am?”

    “Nace muje na kama mana hotel.”

    “Wallahi ba haka ka ce ba.” Ta faɗa a tsorace.

    Dariya ya yi mata “Ki ka ce baki ji ba.”

    “Da wasa nake.”

    “Matsoraciya.”

    Addu’ar rufe taro aka yi. Kowa ya tashi cikin murna da jindaɗin wannan biki mai ban sha’awa. Baballe ya ɗauki Zee, Safwan ya ɗauki Sajida sannan Taj ya tafi da Hamdi.

    Ahmad da Anti Zahra kuwa mamakin duniya ne ya kama su da su ka shiga gida su ka tarar ana bushashar cin shinkafa dafaduka da farfesun kifi wanda ɗaya daga cikin ƴaƴan Anti Zabba’u ta dafa.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!