Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-six
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Taurin zuciya ya hana Hamdi kukan da sauti. Sai hawaye kawai da ajiyar zuciya. Ji take kamar ta buɗe ido ta ganta a gaban Yaya. Auren za ta ce ta fasa da gaske. Gashi dai zuciyarta tana ƙaunarsa. Ƙauna da son da har yanzu bata taɓa faɗa masa ba saboda kunya da jan aji na mata. Sai dai tayi abin da zai gane shi ɗin mai matsayi ne babba. Tana tanadin kalmominta masu tsada zuwa lokacin da za su kasance a muhalli guda. Abin da ya gagareta fahimta bai wuce yadda ta rufe ido ta iya kiran shi munafuki ba. Haƙiƙa duk wanda ya santa zai yi mata shaidar tsiwa. Amma rashin kunya irin wannan kuma ga mijin aure, abu ne da ita kanta bata taɓa kawowa zata yi ba. Kuma har yanzu yadda take jin son nasa haka kuma wani irin haushinsa yake cin zuciyarta. So take kawai ya sake yin wani abin ita kuma ta cigaba da faɗa masa abin da zai ji haushi.
Shi kuwa Taj ya ma rasa me yake yi masa daɗi a duniya. Juya mata baya ya yi ya runtse idanunsa. Sai ya yi yunƙurin juyawa yaga halin da take ciki, sai yaji zuciyarsa tana tuna masa kalamanta a gare shi. Ransa ya ƙara ɓaci har wani tafasa zuciyarsa take yi. Muddin za ta cigaba da yi masa rashin kunya yana kyautata zaton zai iya yi mata dukan da sai an ɗagata….Duka??? Ai ko ƙannensa mata ba za su yi masa wannan shaidar ba yayi saurin kwaɓar kansa. Me ya kai shi marinta?
A hankali ya juya su ka fuskanci juna. Kumatunta ya yi shatin yatsunsa raɗau. Gabansa ya faɗi da ganin aika aikar da ya yi a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci. Wayarsa ya ɗauko ya kira Sajida don tabbas ba zai iya kai Hamdi gidan a haka ba.
Hamdi na cikin yanayin ɓacin ran nan taji yana cewa ba zai sami damar kaita ba. Da haka ta gane da wa yake wayar. Bata san me Sajidan ta ce ba ya bata wannan amsar.
“Lafiyarta ƙalau, kawai dai tana cikin yanayin da bai kamata taje ko ina ba. So please ki min alfarma kada ki faɗa a gida cewa bata zo ba.”
Kallon mamaki Hamdi ta fara yi masa. Kafin kuma cikin fushi ta fara neman karɓe wayar. Za ta soma ɗaga murya ya danne wayar da kafaɗarsa ita kuma ya sanya hannu guda ya rufe mata baki. Ɗayan kuma matseta ya yi a jikinsa da shi. Ya yi ɗan murmushi da Sajidan ta soma cewa ta gane duk da muryarta ta bada ita.
“Ba fa abin da kike tunani bane wallahi. Fitowar ce dai kawai ba zan iya ba.”
“Ko dai bata da lafiya ne?”
“She is fine. Bari tayi miki magana.”
Kallon gargaɗi ya yi mata kafin ya cire hannunsa daga bakinta a hankali ya kara mata wayar a kunne. Ta ɗaga jajayen idanuwanta ta dube shi. Kalmar ‘please’ ta karanta a laɓɓansa. Ranta sosai yake ƙuna.
“Ya Sajida.”
“Alhamdulillah” hankali kwance tunda taji muryarta ta ƙara da cewa “asha soyayya lafiya.”
Da sauri Hamdi ta yanke shawarar fađa mata me ya faru.
“Mar…”
Bai bari ta ƙarasa ba ya cire wayar. Ta buɗe baki za ta yi magana da ƙarfi yadda zata ji ya zauna tare da ita a jikinsa ya turata ƙuryar kujera yana girgiza kai. Dolenta tayi shiru kawai sai harare harare bayan ta tattare ƙafafunta ta cure jiki waje guda.
Sam ba zai yarda a ganta da shatin nan har a fara tambayoyi ba. Muryarsa ya gyara ya ce
“Don Allah Sajida. I realy need this favour from you. Kin san dai ba zan cutar da ita ba. Duk da tana ta rigimar sai na kawota.”
“Subhanallahi. Ya Taj me ya kawo wannan maganar? In sha Allah babu mai ji. Ita kuma kada ma ka biye mata.”
“To nagode.”
Akan centre table ɗin wurin cushion chairs ɗin mai kyau na gilas ya ajiye wayar ya fuskanceta. Zuciyarsa tana ta kai komo wurin faɗa masa ƙarya da gaskiya. Ya rasa tudun dafawa guda ɗaya. Hannunsa ya kai kumatunta zai taɓa tayi saurin karewa da nata,tana mai sadda kai ƙasa. Bai kulata ba ya riƙe hannun nata ya kai ya taɓa inda ya yi marin. Baya jin za ta kai shi jin ciwon wannan abu.
“Am sorry” ya ce muryarsa a shaƙe.
Ai kamar ya kunna famfo. Sabbin hawaye su ka sauko mata. Muryarta har ta soma dashewa ta ce,
“Mari na fa kayi.”
“You hurt me with your words Hamdi. Munafuki, kuma ki ce ban haifu ba?”
Cikin kuka tana ajiyar zuciya ta bashi amsa “Allah maganar da kanta ta fito. Ban yi niyya ba.”
Muryarta ta sake karyar masa da zuciya.
“Duka ba halina bane. Ki yi haƙuri.”
Da ka ta amsa. Ya sanya hannayensa duka ya rungumota. A lokaci guda kuma zuƙatansu su ka dinga harbawa da faɗuwar gaba. Kamar hakan laifi ne gagarumi. Kusan a tare su ka saki juna.
“Mu yi sallah sai na samo miki abinci. Me za ki ci?”
Zumɓura masa baki tayi “ni bana cin girkin maza.”
Ya ɗage gira yana ɗan murmushi “da gaske?”
Ta san manufarsa shi yasa ta ce “sai na Abbana kaɗai.”
“Za ki ci nawa nima.” Ya ɗauko copy ɗin menu ɗinsu daga kan table ɗinsa ya bata.
Ko buɗewa bata yi ba ta ce ” abin da babu a nan zan ci.”
“No problem.”
Sallar azahar su ka yi. Ya ce ta jira shi zai iya kaiwa awa ɗaya kafin ya dawo. Tana ji ya rufeta da muƙulli ta waje. Ta koma kan kujerar da ta taɓa yin bacci ta kwanta ta rufe ido. Ƙamshin turaren Salwa da ya kama office ɗin yana cigaba da shigarta a hankali. Shi ma kuma da ya shiga kitchen ɗin, ƙamshin da ya rage a wuyansa tunda ya wanke hannayen a wajen alwala ne ya dinga bugarsa. Yaransa suna son zuwa ganin sabon girkin da babu a menu ɗinsu amma a karon farko ubangidan nasu bai bada wannan fuskar ba. Ya gama dafa Afghani pulao ɗinsa yana kaucewa haɗuwa da Abba. Saboda gani yake suna ganin juna zau gane me ya yiwa ƴarsa.
***
Ummi da Salwa rungume juna su ka yi cikin farinciki bayan ta koma. Alh. Usaini yana daga cikin mota yana kallonsu. Murmushi ya saki na samun nasara. Malamin tsibbun da ya bashi turarukan ya tabbatar masa da cewa babu abin da zai hana shi samun biyan ɓukata. Duk abin da zasu yi basu isa su kara dashi ba. Turaren farko na raba Taj da matarsa wanda shi ba abu bane dake gabansa, ya dai karɓa ne saboda Ummi da Salwa da za ta yi musu aikin. Sanin halin mata na barbaɗa da surutu, idan Ummi taji shiru tunda ta san inda yake za ta iya tona masa asiri. Ba dai tsoronta yake ji ba. Wani ƙuduri ya ɗora akanta wanda baya son a sami tangarɗa a gaba. Babban aikin yana ga turare na biyu wanda Taj da Hamdi basu ma ji ƙamshinsa ba. Shi ne mai muguwar tsadar wanda a sannu zai kassara Happy Taj sai dai a dinga faɗinsa kawai a labari.
“Baki ga idonta ba da ta ganni a jikinsa.” Cewar Salwa tana ƴar dariya. Magana ta gaskiya ita ce yau tayi abin da bata taɓa ba. Shigarta da rungumar Taj babu guda da ta saba dashi bisa tarbiyar mahaifinta da Ahmad. Son zuciya da rashin haƙuri yasa ta tsallaka titin da Mami taso tayi amfani da kyanta taje gareshi tuntuni.
Ummi ta bata hannu su ka tafa
“Muna nan dake za ki ji anyi saki nan da ƴan kwanaki”
“Banda rashin kamun kai ma ba ayi bikinsu ba amma take binsa har office? Me kike tunanin zai faru da ban je ba? Kuma fa babanta a wajen yake.”
“Ɗan daudu har wani uba ne? Ƙila ma shi zai kitsa mata ya ce ta dinga zuwa. Kin san fa su sana’arsu tambaɗewa tayi yawa. Da ba ƴarsa ya aura ba ma zai iya kawo masa wata.”
Salwa ta jinjina kai “ai kuwa dole ma su rabu. Ba zan ma yi zaman kishi da ƙazamai irinsu ba.”
“Turaren nan ƙarshe ne. Kuma ko asiri tayi ta same shi to wanda ya bani wannan ya ce min babu wanda ya kaishi iya sihiri.”
“Idan anyi aurenmu za ki kaini wajen Ummi. Ko don gudun matsala a gaba. A bani shi a hannu in dinga juyawa.”
Wata uwar shewa su ka sake yi. Ummi tana ta son Salwa tayi ta tafi amma taƙi motsi. Ita kuwa ba don ta matsu ayi aikin ba da ba za ta fito ba. Ɗan jarabar gidansu Baballe yana hanya. Idan Iyaa ta faɗa masa yawonta da ya ƙaru a kwanakin nan bata san me zai yi mata ba. Wata zuciyar har tana raya mata ko su ma ƴan gidan ta samu a rufe musu baki. Kuma a kautar da idanunsu daga kanta.
***
Irin mutumci da karamcin da Yaya take gani a wajen bayin Allahn nan dake gabanta sai hamdala. Mata huɗu ne. Ɗaya ance mata ƙanwar Alhaji ce Amma. Sunan ba baƙonta bane a wurin Taj. Matar ta haɗu iya haɗuwa amma she is so down to earth in ji bature. Girman kai da nuna isa duka babu su a tare da ita. Mata ukun kuma Hajiya ce da Mama da Umma. Su kam ko cikinsu ɗaya iyakar abin da ido zai gani kenan. Allah Yasa ita ma bata yi ƙasa a gwiwa ba. Ta kira Iyaa da kuma su Anti Zinatu saboda bata san me za su tattauna ba. An dai ce mata akan maganar biki ne.
“Ranar Asabar in Allah Ya yarda maza za su kawo lefe. Sati mai zuwa muke son ayi biki ta tare.” Hajiya ce take wannan bayani.
Amma kuma ta ce “ayi mana haƙuri mun zo da maganar a taƙaitaccen lokaci. Mun ga babu amfanin ayi aure kuma duka ba wani uzuri ne a gabansu ba ace tana gida har yanzu”
Anti Zinatu ta nuna musu hakan ba zai yiwu ba
“Wannan gaskiya ne. To amma Hajiya kun san shiri irin namu yana buƙatar lokaci. Ina laifin wata guda ko biyu? Mai ƴaƴa mata baya rasa ɗan tanadinsa. To amma ba zai isa ace mun rufeta mun kai ɗakin miji ba gaskiya.”
Jin haka Amma ta ce mata “Hajiya Zinatu mu ba baƙin juna bane. Wuri guda muka tashi. Babu zancen ɓoye ɓoye. Na tabbata kun san akan girki Yaya Hayatu ya kori ɗansa daga gida. Haka nan ba za mu manta yadda ya juyawa kyakkyawar zumuntarsa da Yaya Habibu baya akan ƙaddarar da ta same shi ba.”
“Haka ne.”
“Babu wanda ya taɓa kawowa zai amince da auren nan amma gashi anyi. Mu duka nan muna tsoron kada jinkiri yasa ya ɓullo da wani abin. Tunda ko me Taj ya yi baya burge shi. Don Allah ku barmu mu bawa duk maraɗa da mahassada kunya.”
Ita dai Yaya jikinta ya soma sanyi. Anya ba wani abin su ka ji ba wanda yasa su ke so a gaggauta bikin nan? Kada fa azo a mayar mata da ƴa ƙaramar bazawara idan Alhaji ya canja ra’ayi.
Bata yi nauyin baki ba kuwa ta faɗa musu.
“Ni dai idan kun san da matsala don Allah ku faɗa mana sai a yiwa tufkar hanci tun wuri.”
“Ko ɗaya. In sha Allahu alkhairi zamu ƙulla. Mu dai fatanmu ku bamu haɗin kai. Zancen shiri kuma wallahi Innar Taj da ƴan uwanta sun ce ko tsinke kada ku damu da saye. Komai na biki su za su yi.” Cewar Umma don ta kwantar musu da hankali.
“Ayi haka?”
Amma ta ce “An ma yi. Ba don abubuwan da su ka gabata ba ina da yaƙinin da Yaya Hayatu ne zai aurar da ƴaƴan gidan nan. Haka nan Allah Ya haɗa jininsu wanda a yanzu idan ina kallon Taj da Kamal su suke tuna min. Bambancin shekaru bai hana su ƙulla kyakkyawar mu’amala ba.”
Yaya da Anti Zinatu sun yi ta ja amma babu yadda su ka iya da waɗannan gogaggun matan. Ƙarshe Yaya ta ce bari ta sansanar da Abba. Ɗaki ta koma ta kira shi a waya. Ya tuna yadda su ka yi da Taj yace ta amince. Zai san yadda ya yi tunda anyi aure Hamdi ba ikonsu bace. Idan su ka cigaba da ja’inja ba zai amfanesu ba. Yau ko ƙofa Taj ya ƙwanƙwasa yace a bashi matarsa basu da hurumin hanawa a shari’a. Balle kuma bidi’o’in biki da ko babu su aure ya ɗauro.
Sun nuna jindaɗinsu da amsar da ta kawo. Cikin farinciki Mama ta zayyane musu yadda su ka yi nasu tsarin bikin. Idan akwai abin da su Yaya su ke so sai su faɗa. Alhamis mai kamawa za ayi kamu. Ranar Juma’a kuma dinner. Asabar ana la’asar za su zo su ɗauki amarya. A kaita gidan Alh. Hayatu. Daga nan Taj zai ɗauketa (wannan shirin Amma ne. Tayi rantsuwar Taj ba zai fara rayuwar aure ba sai ya taka gidan mahaifinsa. Kuma da izinin uban.)
Iyaa ta ce hakan ya yi musu. Ranar asabar za su yi yininsu a gida. Kuma tana roƙon a barsu su ɗauki nauyin abinsu. Dariya ta bawa su Hajiya. Kowa ya yi na’am da yadda zaman ya kasance. Aka rabu cikin mutumci. Bayan an cika musu ciki da daddaɗan abinci.
***
“Ba za ka ci ba?”
Hamdi ta tambayi Taj bayan ya ajiye mata wani faffaɗan plate mai kyau da haɗaɗɗiyar shinkafar da sabo yasa bai jima ba ya gama dafawa. Asalinta girkin mutanen Afghanistan ne amma ya ta sami karɓuwa a wasu sassa na ƙasashen Asia. Afghani Pulao dafaffiyar shinkafar basmati ce wadda cikin kayan ƙamshin dafata harda sinadarin cumin da cardamom. Sai kuma naman ƙaramar dabba wanda ake marinating ɗinsa da kayan ƙamshi kafin a dafa shi ya yi laushi luguf. Ita kuma shinkafar ana haɗata da caras da aka yayyanka sirara kuma ƙanana. A haɗa shi da raisin (bushasshen inibi) wanda ake soyawa sama sama da sugar sannan a haɗa da nuts.
Kansa da ya soma juyawa tun baysn ya sake arba da ita yake matsawa da hannu ɗaya.
“Ki ci kawai. Bana jin yunwa.”
Ba shiri ta ture plate ɗin.
“Meye haka?” Ya ɓata rai. Zuciyar tana kuma ciwo shi.
Ita ma baki ba linzami yau ta turo shi “na san me ka zuba tunda na shiga tsakaninka da Salawaitu.”
Dariyar dole ta sa Taj “Salwa ce ta koma Salawaitu?”
“Gaskiya dai na faɗa. Gashi nan ranka ya ɓaci don na canja mata suna.”
“Ke za ki ji daɗi a ɓata naki?” Ya tambaya yana ƙarewa yadda take murguɗe murguɗen baki kallo.
“Mutum ya daɗe bai ɓata ba. Kuma na faɗa ɗin. Salawaitu, Salwanatu, Sal…”
Hannunsa da yake jin kamar ƙwaƙwalwar kansa gareshi, yana marmarin sake dukanta ya damƙe a da ɗan uwansa ta baya. Dukanta yake so ya ƙara yi. Rashin kunyarta da a mizanin masu tunani ma wani ko kallonta ba zai yi ba idan tana yi shi ne yake jin kamar ya kama ta da duka.
“Ki ci abincin nan kafin na dawo.”
Ya kama ƙofa zai fita yana ji tayi siririn tsaki. Innalillahi…har tafin ƙafarsa yake jin ɓacin rai. Garam haka ya buga ƙofa ya sake rufeta a ciki.
Ta zauna tana ta faman girgiza ƙafa. Bata so ya fita ba tare da rigimar ta girmi haka ba. Ya saketa kawai ta huta. Ta kalli abincin ta janyo plate ɗin a fusace.
“Idan ban ci ba ma waccan Salonin zai bawa.” Ta faɗawa kanta domin ta sami nutsuwar ci.
*
Mota Taj ya koma. Idanunsa jawur kawai don yaƙi biyewa zuciyarsa. Shi ya tabbatar da zai taɓa lafiyarta tabbas zai ji dama a ransa. Kamal ya kira ta whtsapp.
Bawan Allah sauƙi ya samu tunda aka fara sabon treatment. Kusan babu sauran kumburi. Sai duhu da yayi wanda a da ya ɗara Taj haske. Fari ne sosai kamar duka ƴaƴan Hajiya.
“Happiness”
Ya kira shi da wata irin murya mai rauni. Abin da yake faruwa tsakaninsa da Hamdi a ƙasa da awa biyu is not normal. Ta yaya zai dinga jin son dukanta kamar ba matar aurensa ba? Yarinyar da ɗazun nan yake jin zai iya keta bille ya aikata kowacce irin rashin kunya yau ɗinnan akanta.
Da tsokana ya ce “Happy nawa na gargajiya. Ka kai Mrs Happy gidan Sajidan ko kuwa naka gidan?”
Taj ya ɗan yi murmushi “I’m in trouble Happiness. Yaushe za ka dawo?”
Salati Kamal ya yi kafin ya hau shi da faɗa “wane irin rashin haƙuri ne da kai ne Happy? Kwana nawa ya rage ta tare? Yanzu tana ina? Allah Yasa ba hotel ka kai musu ƴa ba.”
“Ba shi bane. Kai ma ka san ɗazu wasa nake maka..wata matsalar ce daban.”
Hankalin Kamal kwanciya ya yi. Da safe da su ka yi waya ne Taj yace masa zai je kai Hamdi gidan Sajida. Amma fa har gidan da za su zauna sai sun je. Kamal ya dinga yi masa magiyar kada ya kunyata su amma ya dage sai sun je saboda kawai jindaɗin tsokanar ɗan uwan nasa.
“Ina jin ka to. Me ya faru? Ba dai sakin ta kayi ba?”
Kamar zai yi kuka ya ce “Marinta nayi Kamal. I slapped Hamdi har hannuna ya fito a kumatunta.”
Tashi tsaye Kamal ya yi. Ya koma ya zauna sannan ya kuma tashi.
“Mari? Hamdin? Me tayi?”
Yadda ta kasance daga shigowar Salwa har fitarta Taj ya faɗa masa.
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil.”
“Sai rashin kunya take min. Ni kuma ina jin kamar na shaƙeta na huta.”
“Daina faɗa Happy. In sha Allah zan yi booking next flight na taho.”
“Ana haka dama? Kana son mutum kuma kaji kana son inflicting pain a jikinsa? Happiness indai haka ake aure wallahi kada kayi. It hurts…so much.”
“Kuka kake yi? Happy?” Shiru bai amsa ba “Tajuddin?”
Katse wayar Taj yayi. Ya shafa idonsa yaji shi a jiƙe.
“What is wrong with me?”
Ɗazu ma sun kallon juna da Hamdi ya yi hawayen nan. Shi yasa ya juya mata baya kafin ta gani.
Bai yarda ya sake komawa saman ba sai da su ka yi jam’in la’asar yaga fitar Abba. Ya koma ya sameta tayi sallah ita ma. Kanta a ƙasa tana ta avoiding kallonsa. Hakan ya fiye masa komai.
“Zo mu tafi.”
Kamar jira take ta miƙe. Ta hanyar da su ka zo su ka koma.
Salwa baƙin naci sai da taga fitar motarsa sannan ta tashi ta tafi gida. Yau yadda zuciyarta take wasai har girkin dare ta yiwa Gwaggonta.
***
Abu ya ƙara taɓarɓarewa tsakanin Hamdi da Taj amma babu wanda ya sani. Yanzu ko a waya su ke magana sai anyi faɗa. A kwana na uku wanda ranar ne Kamal ya dawo ya sanya Taj a gaba ya kira Hamdi. Irin faɗan da suke yi ya tayar masa da hankali sosai.
“Ni wannan abu ya ishe ni. Kaje ka auri Salwa. Ka cinyeta. Ka haɗiyeta ma duka. Amma don Allah ka rabu dani. Bana sonka. Bana son auren.”
Guntun tsaki ya yi “matsalata dake bakinki baya shiru. Just keep quite for once. Maybe zamu iya komawa daidai idan kina kama bakinki.”
“Anƙi ɗin.”
“Kin san zan iya zuwa har gidan in hukunta ki ko?” Ya gargaɗeta. Kafin ya kira kuma kamar ana azalzalar zuciyarsa. Kewarta kawai ke damunsa.
“Kuma aka ce maka iyayena za su zuba ido kayi yadda kake so?” Tana wani irin cije baki ta ce ” Bar ganin Abbana yana yi maka aiki. Wallahi kana kuma taɓani idan na sanar dashi zai rama min.”
“Me ya kawo zancen iyaye kuma?”
“Naga ƴaƴan masu kuɗi sun raina iyayen irinmu ne.”
“Allah ki kiyayeni.”
Ya soma magana Kamal ya karɓe wayar. Sallama ya yi wadda Hamdi tana ji nutsuwarta ta dawo harda gaishe shi.
“Me yake faruwa Hamdiyya?”
Kuka ta saka masa. Duk tambayar duniya ta kasa bashi amsa sai “shi ne” kawai da take ta faɗi. Da ƙyar ya rarrasheta sannan ya yi mata tambaya.
“Kina son sa?”
“Shi ma ba sona yake ba.” Ta amsa da kuka.
Kamal ya kwantar da murya “wa yake ta tashi? Ƙanwata nake tambaya. Kina son Taj?”
Hamdi ta kalli ɗakinsu da babu kowa ta ƙara tabbatarwa ita kaɗai ce sannan tayi magana.
“A da ba.”
“Yanzu fa?”
“Nima ban sani ba. Salawaitu yake so. Ni kuma sai in yi ta son shi? Haka ake yi?”
Murmushi ya yi. Ya sami amsarsa koda ba kai tsaye bane.
“A’a gaskiya. Abin da nake so dake dai don Allah ki bar abubuwan nan tsakaninmu. In ki ka bari wani yaji har aka raba auren ina mai tabbatar miki Salawaitun zai aura.”
Wawan duka Taj ya kai masa a baya. Baya ƙaunar zancen Salwa tuntuni balle yanzu da yake cikin damuwa shi da amaryarsa.
Ajiyar zuciya tayi “Ba zan faɗa ba”
A ransa yake auno yadda zai tsokanesu duk su biyun idan komai ya daidaita. Yana gama wayar ya koma kan Taj.
“Happy ina ganin wannan maganar fa ba tamu bace mu biyu.”
“Me kake nufi? In faɗawa wani? In aka ce na sake ta fa?” Ya soma magana cikin tashin hankali.
Nutsuwa Kamal ya yi wanda yasa Taj ya gyara zama.
“Me ka ke tunani?”
“Ka faɗawa Inna.”
“Inna kuma? Me za tayi?”
“Duk matsalar duniya Happy uwa ce ƙarshenta. Ko bata magance ba in sha Allahu za ta faɗa maka yadda za ka yi. Sannan ga addu’arta da bata da shamaki. Abin naku kamar asiri.”
Kallonsa Taj ya yi “kai duka matsalolinka kake faɗawa Hajiya?”
“Wanda ya dace lallai ta sani ba.”
Kallon tuhuma Taj ya yi masa
“Me yasa ka ɓoye mata ciwonka bayan ka san idan tayi addu’a za ta karɓu?”
Gaban Kamal faɗuwa yayi. Cikin sarƙewar harshe ya ce “ai…dama. hhhh. Saboda gudun tashin hankalinsu ne.”
“I see” kawai Taj ya ce.
Kamal duk ya ruɗe “Kayi haƙuri don Allah. Ban ɓoye da wata manufa ba.”
A nutse Taj ya karance shi. Inda ya dosa daban da inda yake tunanin Kamal ya dosa. Kenan akwai abin da Happiness yake ɓoyewa wanda bai sani ba? Shi ne mai dogon bakin faɗa masa komai wato.
“Akwai abin da ka ke ɓoye mana ne banda allergy da asirinka ya tonu?”
Wani gwauron numfashi da Kamal yaja sai da Taj yaji hantar cikinsa ta kaɗa. Babu shakka akwai sirrin da bai sani ba. Zai kuma sani ne don Kamal bai isa ya ninke shi baibai ba tunda ya gano da matsala.
“Shi ne. Allergy ɗin ne. A China ma ya tashi. Ba ka ga har wani duhu nayi ba?”
“Na gani. Yanzu nake shirin cewa ko man bleaching ɗin naka ne ya ƙare a can?”
Kamal ya taso ya yi kansa. Su ka gama zolayar juna sannan Taj ya koma cikin Happy Taj.
***
Shiru shiru Salwa tana jiran wayar Taj amma ko flashing babu. Hankalinta ya soma tashi. Kwanakin da aka ɗiba domin aurensu sun kusa. Ta kira Mami tana ta kuka. Mamin ta ce mata ta taho gida.
“Idan na ƙara nesa dashi ai babu lallai ya tuna dani ma.”
“Ki taho nace miki. Zan sake shiri.”
Ta samu Salwan ta amince za ta dawo. Sai dai bata san ta ina za ta fara ba. Alh. Mukhtar ya sake kiran Alhaji akan maganar ranar da za su je wajen kawunsa amma ƙememe yaƙi ɗauka. Baya son yi masa ƙarya sannan kuma baya son faɗa masa gaskiya. Idan ya faɗi gaskiyar girmansa da kullum yake tattali ne zai zube. Daga baya ne ya tausaya masa da yawan wayar ya ɗauka ya ce ya ƙara wata guda. Saboda wasu uzurirrika da su ka taso masa. Alh. Mukhtar dai tunda ya sami amsar bawa Mami hankalinsa ya kwanta.
“Nufinsa sai waccan yarinyar ta tare sannan zai auri Salwa?”
“Ina laifi?”
“Ai kuwa akwai shi tunda nima ban zauna da kishiya ba. Ƴata ma daga ita sai miji.”
***
Girki ya faɗo kan Inna ranar Juma’a. Da ta haɗa abincin Alhaji Bishir na shigowa ta ce ya kai masa. Kuma bata leƙa ɓangaren ba kamar yadda su ka saba. Mai girki za ta je ta zuba masa abinci su yi hira. Idan ya gama ta aikawa sauran matan cewa ya dawo. Duk za su zo a ɗan taɓa hira sannan su tashi.
Abinci ya yi kusan awa guda Alhaji yana kallonsa. Ga yunwa ga gajiya amma yaƙi zubawa. So yake yaga iya gudun ruwan Zainabu Abu. To dai tun bayan masallaci har la’asar bata shigo ba. Da ya dawo daga masallaci cikin gidan ya shiga ya wuce ɗakinta. Jallabiya ce a jikinsa yana danna counter mai fasalin carbi ta sama.
Babu kowa a falo. Ya shige uwar ɗakin. Yana sanya ƙafa ita kuma tana ɗora waya a kunne. Don ya san da wa take magana ta kira Taj da sabon suna.
“Angon Hamdi”
A tunanin Alhaji ko da gangan ta ɗauki wayar. Hannu yasa ya karɓe. Ganin sunan Taj da gaske sai ya miƙa mata. Ita kuwa ta saka speaker yadda ta saba idan ita kaɗai ce a ɗakin saboda wayarsu bata ƙarewa da wuri.
“Inna kina ji na kuwa?”
“Me ka ce?”
Bai san yadda za ta ɗauki maganar ba amma dole ya đauki shawarar Kamal yau. Faɗan da su ka yi da Hamdi a motarsa Allah ne kawai ya bashi ikon mallakar kansa ya buɗe mata ƙofa ya ce ta fita. Daga zuwa kai mata kati cibi ya zama ƙari. Saboda yau ta iya bakinta bata ce komai ba shi ne ya ce ba a yi mata tarbiyar godiya ba. Ai kamar jira take. Tunda ta buɗe baki ta fara surfa rashin kunya sai da yaji inama bai je gidan ba.
Gyaran murya ya yi “na ce ko za a fasa bikin?”
Alhaji da ya kama hanyar fita sai gashi ya dawo. Inna tayi sauri za ta mayar da wayar iya kunnenta ya harɗe fuska. Taɓe baki tayi a ranta ta ce ana so ana kaiwa kasuwa. Dama taji yadda ya rikice da yaji bashi da lafiya.
“Kai da ka san baka son biki ne yasa ka bari mu ka zazzage asusunmu? Haƙuri za ka yi kawai.”
“Uhmmm, Inna ba bikin ba. Auren nake nufi.”
Bata san lokacin da ta gyara zama ba.
“Ka fara shaye shaye ne? Auren? Saki fa kenan.”
Baya son yawan tada maganar don ransa ƙara ɓaci yake. Amma dolensa ya faɗa mata gaskiya.
“Matsaloli muke ta samu. Kullum sai mun yi faɗa.”
“Wannan shaiɗan ne kawai. Ku dage da addu’a.” Ta ce, hankalinta ya soma kwanciya.
“Inna har marinta nayi.”
Shiru ya yi yana jiran yaji me za ta ce. Ta kalli Alhaji shi ma ya kalleta.
“Taj ka sameni a gidan Yaya Malam (yayanta na biyu.)”
Ta miƙe ta dubi Alhaji da ya yi tsaye kamar an dasa shi.
“Ka yi min izinin fita?”
“Jeki.”
Hijabi kawai ta ɗauka ta fita ta shiga ɗakunan su Hajiya ta ce musu ga inda za ta je. Duk su ka bata saƙon gaisuwa ga iyalin gidan. Direba ta kira su ka tafi. Aka bar Alhaji da tunani. Yadda hankalinsa ya tashi sai da yaji kamar ya ce Taj din yazo gida. Abin da mamaki ace wai shi ne da marin mace. Wace irin tarbiyya Habibu ya yiwa ƴaƴansa?
*
Ƙasa da awa guda uwa da ɗa su ka keɓe a falon maigidan. Taj ya zayyane mata abubuwan da su ka faru. Bata ko tambaye shi me ya kai shi tafiya da Hamdi wurin sana’arsa ba.
“Idan na fahimta da kyau tun daga zuwan Salwa ku ka fara faɗan?”
“Haka ne. Na so yi mata bayanin babu komai a tsakaninmu amma ta rufe ido tana gaya min maganganu.”
Inna tayi salati sannan ta ce “ya maganar azkar? Kana yi?”
Kai ya sunkuyar “ina yi.”
“Ni da kai ne Taj. Ka faɗa min gaskiya.”
“Allah ina ƙoƙartawa Inna.” Ya kuma faɗa don ta yarda da shi.
Aikin gama ya riga ya gama. Ko yana yi dama ba zai hana ƙaddara da ikon Allah faruwa ba. Sai dai ya sauƙaƙa.
Gargaɗinsa tayi akan kada ya yarda su sake haɗuwa. Wayar ma ko ita ta kira kada ya ɗauka. Sannan mafi mahimmanci ya tabbatar kalmar saki bata shiga tsakaninsu ba.
“Ka tashi ka tafi. Za ka ji ni in sha Allah idan mun gama magana da Yaya Malam. In ma sihiri ne to in sha Allah zai koma ya ci mai shi. Addu’a, sadaka, qiyamul laili da hanyoyin neman kusanci da Allah nake so ka runguma kaji ko?”
Ya gyaɗa mata kai kamar yaro.
“Ki yi haƙuri na tayar miki da hankali. Alhaji ya kamata na nema…”
Wani irin tausayinsa ne ya kama ta. Ta dafa kansa tayi masa addu’o’in neman tsari wanda Ayatul Kursiyyu ke kan gaba. Sai da ya tafi ta fashe da kuka. Duk ya wani rame. Kana ganinsa ka san hankalinsa ne ba a kwance ba. A gidan ta zauna har yayan nata ya dawo ta faɗa masa. Ya kwantar mata da hankali.
“Kada ki ƙulla sharri akan wanda ki ke zargi. Shi zargi dama bashi da kyau a addini. Zan kira shi ya zo gobe in sha Allah.”
“Yaya har zasu yi lafiya kafin bikin?” Ta tambaye shi da damuwa.
“Ke ta biki ma kike wato?”
“A’a, tsorona kada ta tare yadda yake cewa yana jin kamar yayi ta dukanta yaje ya lahanta ƴar mutane.”
Kwantar mata da hankali ya yi.
“Allah zamu roƙa ba mutum ba. Shi kuma ba ayi maSa gaggawa. Tunda ya ce idan mun roƙa zai bamu to ki saka ranki a inuwa. Ko daga ina matsalar take bata wuce Qulhuwallahu, Falaqi da Nasi ba.”
Da ƙwarin gwiwarta ta fita daga gidan. A ranar yadda ta hana idonta bacci haka ta tada Taj. Shi kuma ya sami kansa da turawa Hamdi saƙo.
(Idan Allah Yasa kin gani kafin safiya ki tashi ki yi sallah da addu’a. Idan akwai alkhairi cikin aurenmu Allah Ya warware mana matsala.)
Sai uku da rabi ta gani da ta tashi fitsari. Ta ɗauro alwala ta zauna tana ta kuka. Zee na jinta amma ta ƙyale. Yaya ce ta bata aikin sanya mata ido saboda kwanakin nan kowa ya san ta canja.
A ɓangaren Alh. Hayatu kuwa, yana ganin shigowar Inna ya kira Yaya Malam.
“Ka biyo sahun ɗanka ne?” Malam ya faɗi kai tsaye domin duka gidansu dai haushinsa su ke ji.
Murje ido ya yi tunda in ba a nan ba babu wanda zai tambaya kuma
“A gabana ta fara wayar shi yasa. Da gaske ya mari matarsa?”
“Ƙwarai kuwa.”
“Kaga abin da nake faɗa ai. Namiji mai irin sana’arsa fa ji yake kamar shi ma mace ne. Shi yasa yake daidaita tunaninsa da nata. Cikakken namiji ba zai fara kai hannu daga aure ko wata ba ayi ba.”
Yaya Malam dai dariya kawai ya yi. Ya shaida duk wata rigima da yake yi bata yi tasirin hana shi son ɗansa ba. Abin da yaji ya faɗa masa. Ya yi godiya su ka yi sallama.
Washegari ya san da zancen kai lefe da maza za su yi. An kira shi ya gani bayan an kammala komai. Harda akwatuna huɗun da Amma ta taho dasu waɗanda kayan ciki su ka amsa sunan kayan ƴar gata. Tunda ba dashi za a yi ba babu wanda ya sa masa ido da ya yi sammakon fita. Ko matansa bai faɗa musu inda za shi ba. Ya dai yi musu sallama ya fice. Yana zama a mota ya ce da direbansa Bauchi za su je.
“Bauchi Alhaji?”
“Ba ka san hanya bane?”
Da sauri ya hau bada haƙuri “na sani. Allah Ya kai mu lafiya.”
“Amin”
Zuciyarsa a baka take da ɓacin rai. Bai runtsa ba jiya tunda ya yi waya da Yaya Malam. Arziƙin rabon Ahmad dake tsakaninsa da Mami yasa ba zai haɗata da hukuma ba. Amma tabbas sai tayi nadamar kai ɗansa gaban ƴan iskan bokayenta. Bai san bata da masaniyar abin da Salwa tayi ba.
***
Tun dare Ƴar Ficika da yaransa su ke aikin kayan kwalamar da za a tarbi masu kawo lefe dasu. Shi ya ce da Abba lallai ko ruwa kada ya siya. Za su kawo komai.
“Abin zai yi yawa. Don Allah kada ka wahalar da kan ka. Kada ka manta girma fa ya cimmana.”
Yar Ficika ya karya kai yana riƙe da ƙasan jallabiyarsa.
“Haba Simagade, ina aikin yake a nan? Ai idan daɗin miya bai karya ludayi ba, wahala ba za ta karya guga ba. Ka ganni nan…” ya bubbuga ƙafa a ƙasa “digirgir nake a tsaye. Abin da zan yi in daɗaɗa maka ba zai taɓa zame min wahala ba.”
Abba ya yi masa godiya. Ƴar Ficika ya koma cikin kitchen ɗinsu inda ake ta yanka naman kaza. Guda cikin yaran ya samu yana gyara wutar gashi.
“Tasalluwa me za ayi da wannan uban garwashi?”
“Ba gasa naman za ayi ba?”
Duka Ƴar Ficika ya kai masa a ƙeya “sai shegen rawar kai yawa akwalan keke. Abin da ya kamata ba shi kake yi ba. A zafin nan za a gasa nama tun yanzu a ajiye? Ba sai ya buga ba?”
Tasalluwa ya ɓata rai “daga abin arziƙi?”
“Idan aka basu naman yana hamami ai raini za ka jawowa ɗiyar tamu. Ko baka san ɗan Alh. Hayatu Maitakalmi take aure ba?”
Tasalluwa ya tafa hannuwa “eyyee, ashe abin babba ne, wai an kashe kwarkwata da taɓarya. Aikin na bajinta zamu yi.”
Wani dake kusa yana jin hirar tasu ya ce “ai ke dai Allah Ya kawo kuɗi talauci yaji kunya. Nan da lokacin da za ta haihu kaji hamsin za mu babbake ba ashirin ba.”
“Ahayyeeee”
Su ka dinga tafawa ana tsara irin girkin da za ayi idan Hamdi ta haihu. A cewarsu aikin yau ba ayi yadda ya kamata ba saboda tsadar rayuwar da ake fama. A haka kuma ba ƙaramin ƙaƙari Ƴar Ficika ya yi ba. Kaji ashirin za su yiwa gashin tukuba, meatpie, donut da cake duka guda ɗari ɗari yaran da su ka ƙware a nan fannin su ke yi. Sai abincin gargajiya. Tuwon shinkafa da miyar gyaɗa da kabewa wadda taji naman rago da alayyahu, waina, funkaso da alkubus kuma da farfesun kai da ƙafar rago. Sai lemon ginger da zoɓo da su ka ƙware wajen yi ana zubawa a sababbin robobi masu tambarin sunan gidan abincin nasu. Shi dai ya haƙura ya san ya makara, da wuya ya haifa. To amma fa wanda Simagade ya haifo musu sai inda ƙarfi ya ƙare.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
