Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-four
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Har su ka ƙarasa gida idan sun kalli juna sai sun yi murmushi. Abin da ya ɗaurewa Hamdi kai shi ne yadda Taj har wani kawar da kai gefe yake irin na masu jin kunya. To ai ita ma kunyar take ji. Kuma ita ya dace ta dinga yin haka. Sai gashi kafin tayi yake yi. Gajiya tayi lokacin sun iso layinsu ta kalle shi.
“Wai mene ne?”
Gefe ya kaɗa kai yana wani rufe ido “Awwnnnnn, ni ki daina tambayata. Kin fi ni sanin ko mene ne.”
Murmushin fuskar Hamdi ɗaukewa yayi. Ta soma harararsa.
“Banda waƙa kuma harda irin haka kake yi?”
“Irin yaya?” Ya tambaya kamar bai gane manufarta ba.
“Meye wani awwnnn don Allah?”
Hannu ya kai ya shafa kumatunta “Saboda ina son ganin wannan hararar da juya idanun naki. You always look cute.”
Murmushi ta soma yi ya kuwa sake cewa “awwnnnn” yana dafa saitin zuciyarsa.
Wannan karon dariya tayi. Irin dariyar da bai taɓa gani daga gareta ba. Zuciyarta tayi fari kamar auduga.
“Kin san wani abu? Zo mu shiga ciki kafin haƙurin Abba ya ƙare.”
Bakin ƙofar gidansu ta kalla. Ai kuwa Abbanta ne yake ɗan leƙowa. Bai yi zaton za su yi dare ba. Kuma sun iso ɗin ma taƙi fitowa. Shi ne ya kasa sukuni. Kada fa ta biyewa Taj al’amari ya kwaɓe a gaba.
“Zan kira ki idan naje gida. I hope ba da wuri ki ke bacci ba.”
Bata iya bashi amsa ba da ta hango inuwar Abban da gaske. Kamar an tsikareta ta fito da sauri. Tana hango shi ya koma cikin gida ta bi bayansa. Taj ya yi murmushi kawai. Ya juya baya zai yi ribas ya yi arba da ledojin da ƴan uwansa su ka ajiye mata. Parking ya gyara ya ɗebi yadda hannuwansa za su iya ɗauka ya je ƙofar gidan yana sallama.
Caraf yaji Abba yana yiwa Hamdi faɗan kada ta manta da maganarsu. Shi ba zai iya ja da Alh. Hayatu ba. Jin sallamarsa yasa shi yin shiru. Hamdi kuma ta ruga ciki da sauri.
“Taj baka tafi ba?” Ya fito waje.
“Saƙonta ne ta manta.” Ya nuna ledojin hannunsa.
“Harda wahala haka?”
“Ƙanwarsu su ka yiwa. Bari na shigar mata dasu.” Taj ya wuce ciki kafin Abban ya ce shi zai karɓa. Hakan zai zama raini ma.
A tsakar gidan ya sake sallama, Yaya ta amsa da yi masa izinin shiga falon. Akan kujera ya ajiye ledojin ya ce da saura. Ta saki baki har yaje ya dawo. Lokacin ita da Abba ne a falon. Waɗanda ya dawo dasu har sun fi na farkon yawa.
“Mene ne haka Taj? Daga zuwa gaishe su kuma sai ka haɗota da wannan kayan?”
“Babu ruwana Yaya. Ƴan uwanta ne su ka bata.”
Yaya dai bata jidaɗi ba. Ta san kwaɗayi ba halin Hamdi bane to amma za a iya fassara ta dashi ga wanda bai santa ba in yaga kayan. Da dai bata karɓa ba. Kiranta tayi ta dawo falon da sauri don kiran ta san na faɗa ne. Kaya dama ta tafi cirewa. Wata free doguwar riga ta saka da hula a kanta.
“Me yasa ki ka karɓo kayan nan Hamdi? Tarbiyyar gidan nan kenan?”
Durƙusawa Hamdi tayi a gaban kujerar da ya zube kayan tana ƙare musu kallo. Ita kanta bata san sun kai haka ba.
“Allah Yaya ba roƙa nayi ba. Ba ma a hannuna su ka bani ba.”
Kusa da ita Taj ya dawo ya zauna a ƙasa ya fara sauko da kayan gabansu.
“Yaya yanzu abin hannun ƴan uwana kike faɗa a kai? Kin san da roƙa tayi nima ba zan yarda mu taho dasu ba ko?”
Yaya ta ce “Kada ka kare mata. Ai ta san irin abin da ya dace da wanda bai dace ba.”
Hamdi ta sunkuyar da kai ta ce “Ki yi haƙuri.”
“Ni ya kamata na bata haƙuri. Na zata mun zama ɗaya ne ko ban aureki ba shi yasa ban ɗauki karɓar kayan a matsayin laifi ba.” Ya yi wani iri da fuska yadda za a tausaya masa “a zatona na kai matsayin da zan iya tambayar Halifa da yake ƙarami abu idan ina so. Na ɗauka hakan ne a wajenku ku ma. Kuskuren daga gareni ne. Ki yi haƙuri.”
Yaya dariya ta kama yi. Abba kuwa ya girgiza kai don dama ya san za a rina.
“Anya Taj ba ɓatan kai kayi na zaɓen aiki ba? Da lauya ka dace. Yanzu Fisabilillah wannan marairaicewar duk don nayi maganar karɓar kaya ne?”
Da rashin jindaɗi kamar gaske ya ce “To Yaya abin hannun ƴan gidanmu ai baya cikin wanda za a yi mata faɗa a kai ko?”
“Baya ciki. Magana ma dai ta wuce.”
Ya kalli Abba dake yi musu dariya da Hamdi da kana ganinta ka san taji daɗin ceton da ya yi mata a hannun Yaya.
“Gara dai na baki haƙuri kuma nan gaba duk mu kiyaye.”
“Nace magana ta wuce Taj.”
“Mungode. In sha Allah zan yi musu magana su ma kada su sake…”
“Ya Rabbi. Taj a bar maganar nan. Ni na fara kuma na janye.”
Yaya ta faɗi da ta rasa yadda za tayi dashi ya yi shiru. Tashi ma tayi tace musu sai da safe. In ta biyewa Taj sai ta koma basu haƙuri tana tumami a ƙasa. Ai kuwa su ka sanya dariya harda shi uban gayyar. Yaya da Abba na miƙewa ya ɗaga hannunsa yana kallon Hamdi. Bata kula da cewa basu gama fita ba ta tafa dashi a hankali. Yaya na gani ta ƙara sauri. Abba yabi bayanta yana dariya.
“Ai naga kayan amma ban ce komai ba saboda sanin halinsa. Da yanzu muna ƙofar gida yana kalallameni yadda ya yi miki.”
“Ka san Allah? Zuciyata fes nake jinta. Sajida da Zee duka mazansu su na son su. Hamdi kuwa nayi zaton Allah auren rufin asiri ne. Ashe da gaske yake da yace yana sonta.”
“Da kin tuna Yaya Hayatu sai in ce miki halinsu guda. Kaifi ɗaya ne. Kawai dai shi bashi da tsatstsauran ra’ayin uban ne.”
“Ita ma ja’ira anya bata son shi kuwa? Da tabi ta ƙulla masa kafin su haɗu. Ban zata za a sami kanta da wuri ba haka. Amma yanzu ko makaho ya san inda zuciyarta ta dosa.”
Abba jikinsa duk ya yi sanyi da irin murnar da take yi da kuma gaskata batun Hamdi na son Taj.
“Uwar zamani. Kina nan kina zancen soyayyar ƴaƴanki.”
Tayi dariya “a uwar ɗaka ba. Da mahaifinsu.”
Zee ce ta tayata kwashe kayan zuwa ɗakin Abba bayan tafiyar Taj. Tafiyar ma don dai kawai dare ya soma tunda an idar da Isha’i. Ba don haka ba yadda ya soma samun kan amaryar tasa da sai abin da aka gani.
*
Washegari kamar yadda su ka shirya zuwa gidan Sajida, Zee da Hamdi sun kammala ayyukansu na gida da wurwuri. Tsabar ɗokin son ganin ƴar uwar tasu da aka hana su yi da wuri ko ƴar cacar bakin da su ka saba ba ayi ba. Yaya zuba musu idanu kawai tayi. Sai gasu shaɗaya da rabi sun fito cikin shiri.
“Wadda ta san ta tambayi mijinta ta zo ta wuce. Wadda bata tam….”
Hamdi ce ta fara cewa “Innalillahi” hannunta na sauri ta buɗe jaka ta ɗauko waya za ta kira Taj, Yaya ta ce ba za ta lamunce titsiye ba.
“Tunda ku ka fara zancen nan ai saboda nauyin dake kanku yasa na hanaku wannan ziyarar ta rashin kan gado da ake yiwa amare da zarar sun tare. Amma ban faɗa muku izinin fita ya bar hannunmu ba?”
Idanun Zee harda ƙwalla ta soma roƙonta “don Allah ki bari mu tambaya yanzu. Allah ni mantawa ma nake yi.”
“Haƙƙun, ai kuwa sai a fara shirin tariyarku tunda zaman gida ya sa kun manta darajar da Allah ya yi muku. Ƙarshenta a waje ma idan wani ya yi muku magana sauraronsa za ku yi saboda kun manta.”
Zamanta tayi akan kujera tana kallon ƴaƴan nata. Babu wadda bata tunawa ta kira mijinta ta nemi izinin fitar ba aƙalla sau uku. Idan tayi magana sai su hau dariya suna tsokanar juna. Jiya da daddare har za ta sake yi musu tuni Abba ya ce ta ƙyalesu. Indai basu yi da wuri ba to kira cikin dare ko da safe duk ɗaya ne. Titse ne wanda maza da yawa basa so.
“Yaya don Allah.” Hamdi ta sake roƙonta kamar tayi kuka.
“Kun san babu abin da naƙi kamar mutum ya dinga kira min mantuwa. Maganar nan mun yi yafi sau nawa. Amma aka rasa mai aiwatarwa. Sai ku koma ɗaki ku kwanta. Hutun ma ai abin so ne.”
Waya Zee ta đauko ta duba. Ita dai jiya da yamma a text ta tambayi Baballe. Tunda ta tura text ɗin bata ƙara dubawa ba saboda ta san in ya gani kiranta zai yi. Wurin da ya tafi aiki a Kaduna ƙauye ne. Tana dubawa kuwa sai taga ya yi mata reply. Izinin fitar ya bata da bayanin raunin network da ya hana shi kiranta tun safiyar jiya. Ihun murna ta kama yi harda tsalle.
“Yaya ya barni. Allah ni an barni. Kin gani” ta miƙa mata wayar don ma kada ta ƙaryata ta.
“Sai ki zo ki tafi. Allah Ya tsare. Ana la’asar ki fito.”
“Don Allah ki barni in kira yanzu.” Hamdi ta soma yiwa Yaya magiya. Da ƙyar ta aminci. Ta kira shi ya fi sau biyar baya ɗauka. Hawaye kawai ta soma don wani irin abu ne ya sami wuri a maƙoshinta ya zauna.
Duk magiyarta kuma Yaya ta ce babu inda za ta. Duk da taji tausayinta amma ba za ta buɗe ƙofar irin haka tsakaninta da mijinta ba. Wannan kuskuren na miji bai sani ba ko ya ce kada ayi, uwa kuma ta ce sai anyi ba da ita ba. Bata buƙatar wani ya faɗa mata irin sa’ar da tayi da Allah Ya aurar mata da ƴaƴan lokaci guda.
Ganin halin da ta shiga yasa Zee cewa ta fasa fita. Yaya ta ce bata isa ba. Haƙuri ta bawa Hamdi ta tafi. Ita kuma ta shige ɗaki ta sha kukanta ta more. Tun Yaya na ɗan jiyota har taji ɗif. Ta leƙa ɗakin ta sameta ta duƙunƙune jikinta tana bacci. Ga shatin hawayen da ya bushe ya fito raɗau akan hodar da ta shafa. Murmushi tayi ta kirata shagwaɓaɓɓiya a zuci. Ta tabbata daga ita har Zee ɗin daga yanzu za su bawa abubuwan da su ka shafi aurensu mahimmanci. Dama wani darasin sai uwa ta daure zuciyarta take iya koyar dashi.
Shabiyu ta gota Taj ya farka daga baccin da ya ɗauke shi a dalilin ciwon kai da murar da su ka dirar masa bayan ya dawo jiya. Magani ya sha amma baccin ya gagara. Sai bayan ya yi sallar asuba sannan ya samu ya kwanta.
Missed calls ɗin Hamdi da ya gani ya yi tunanin ba lafiya ba. Sai kuma yaga message tana roƙon zuwa gidan Sajida. Ya kwatanta lokacin da ta kira da sanda ya gani. Yau akwai daru da alama. Yawan kiran ya san a matse take da tafiyar. Ko abinci bai nema ba bayan ya yi wanka ya fita saboda Salwa da ta kankane falon. Yau Happy Taj yana fin kullum cika. Idan ya shiga sai an gan shi kawai. Shi yasa ya yanke shawarar fara zuwa ganin Hamdi.
Zai kirata ya ce mata ya zo yayi sa’a Halifa ya dawo daga Tahfiz. Yaje ya gaishe shi sannan ya shiga ya faɗawa Yaya saboda Hamdi na banɗaki tana watsa ruwa. Yaya ta ce a faɗa masa ya shigo. Shi kuma gwanin sai da ya faɗa masa wanka take yi kafin ya faɗi saƙon Yayan. Ƙananan kaya ya saka shi yasa ya so zama a mota da farko. Tunda Yaya ta ce ya shigo babu yadda ya iya.
“Ya na ganka haka yau? Ko ba ka jindaɗi ne?” Yaya ta tambaye shi ganin fuskarsa ta ɗan faɗa akan ganin da tayi masa jiya.
“Mura ce ta saka min ciwon kai.”
“Ai kuwa gashi naji muryarka ta canja. Allah Ya ƙara sauƙi.”
Hamdi bata san yazo ba. Wata shirt mai gajeren hannu ta saka da zani ta fito ko ɗankwali babu. Fuskarta fayau sai idanu a kumbure saboda kukan da tayi. Babu abin da ke tashi a jikinta sai wani irin ni’imtaccen ƙamshin body oils ɗin Scentmania. Gwaji kawai tayi tunda dama tun kafin fitarsu ta so sakawa amma sanin rashin dacewar haka a addinance yasa ta fasa. Wurin ƙarfe goma na safe taga saƙon Yaya Kubra ta whatsapp. Ashe tun jiya ma ta turo. Bata yi mamakin ganin sunan ba saboda Firdaus ce ta zauna tayi ta kiranta da lambobin ƴan gidan tana mata saving.
Bayanin sirrin dake tattare da ƙamshi ga matar aure ta turo mata wanda ainihin mai turarukan Scentmania ta tura mata. A ciki ta gane ƙamshi ba ƙaramin tasiri gare shi ba idan ana amfani dashi ta hanyar da ya dace. Musamman idan mace tayi katarin sani da sayen body oils ɗin da ita dai Hamdi bata taɓa jin ƙamshi irin nasu ba. Har shawara take bayarwa cewa yana da kyau mace ta samu wani ƙamshi da za ta yawaita amfani dashi wanda miji zai ganeta dashi. To ko makamancinsa yaji a waje ita zai fara tunawa ya sami nutsuwa. Gashi wai har classes tana yi. Sannan packages ɗin ba dai arha ba. Dole ma ta faɗawa su Sajida idan ta huce daga fushin yau. Don tana ta hango su ana can ana raha banda ita. (07065525409 – Scentmania by Sana)
A ƙofar falon ta tsaya don kads Yaya tayi mata magana akan idonta.
“Yaya me za a dafa na dare?” Tayi magana muryar nan na nuni da har yanzu ranta ba a sake yake ba.
Daga ciki Yaya ta amsa mata.
“Abincin daren za ki ɗora tun yanzu? Ƙarfe biyu ma bata yi ba.”
“Gara na gama tun yanzu.”
“Ai fa yau tunda na hanaki fita sai abin da hali ya yi. To shigo ki gaishe da mijinki da jiki. Baya jindaɗi.”
Labule ta ɗaga tana cewa “waya ku ka yi?” Sai ta ganshi a zaune ya jinginar da kansa a jikin kujera. Ciwon kan ke neman dawowa harda zazzaɓi. Da baya ta fara tafiya za ta koma.
“Ina kuma za ki? Fita zan yi gidan Gwaggo Dela in duba ta.”
Ta gaban Hamdi ta zo ta wuce abinta. Tana fita tsakar gida ta ja kunnen Halifa akan kada ya shiga falo sai Taj ya tafi. Dariyar shaƙiyanci kawai ya yi. Tana jiyo shi ta ce
“Ɗan banza.” A ranta kuwa gani take in ba wajen matarsa ba yanzu ina zai je in bashi da lafiya. Uwa ce dai tafi cancanta yaje ya narke mata da shagwaɓa da rakin maza. To kuma babu dama.
Sai da Yaya ta fita daga gidan sannan Hamdi ta yarda ta ƙara kallon Taj. Yana daga zaunen ya nuna mata kusa dashi da hannu amma bai yi magana ba. Ta juya ta kalli bayanta sai ta girgiza kai.
“Please. Bani da lafiya fa.” Taj ya faɗi yana lumshe idanu.
Shahada tayi kawai ta biye masa duk da kafin yazo da ta gama fushin rashin amsa wayarta da ya yi. A hankali ta isa bakin kujerar amma taƙi zama. Ya miƙa hannu ya janyota gefensa.
“Bani da ƙarfin ɗaukanki saboda wani irin weakness da nake ji. Da tun daga bakin ƙofar zan taroki.”
Rumgumota yayi a gefensa. Ƙamshin jikinta mai sanyi ya buge shi. Bai san lokacin da ya sanya fuskarsa a tsakanin wuyanta ba. Ta fara noƙewa taga kamar ma angiza shi take sai ta haƙura.
“You smell…” ya kai hancinsa bayan kunnenta ya ja numfashi ya sauke a hankali “relaxing and sweet.”
Ɗumin da taji a fuskarsa dake bin wuyanta yasa ta daina mutsu-mutsu har ta tabbatar ba normal ɗumin jikin mutum bane.
“Zazzaɓi kake yi haka?” Ta faɗi tana janye jikinta don su fuskanci juna.
“Uhmm.” Ya amsa da rashin kuzari “harda kaina.”
Juyawa tayi ta taɓa goshinsa. Ya ɗora hannunsa akan nata. Cike da kasala ya ce,
“Ba don bana jindaɗi ba da na nuna miki yadda shigar nan taki tayi min kyau.”
Hannunsa dake tracing ƙaramin hannun rigarta ta riƙe tana mamakin yadda yake tunanin wani abu daban da zazzaɓin jikinsa. Sake janyota yayi ya mayar da kansa kafaɗarta yana ƙara rungumeta.
“Ina zuwa.”
Fita tayi ta barshi. Ya runtse ido don kan nasa ba da wasa yake ciwo ba. Duk yadda aka yi zirga zirga da rashin hutun kwanakin nan ke tambayarsa.
Abinci tayi niyyar kawo masa sai tayi tunanin babu lallai ya iya ci. Ta ɗauko gasara ta dama masa kunu da tsamiya kaɗan saboda yaji daɗin bakin. Da ta koma falon idonsa a rufe ta same shi. Ta zuba kunun a kofi ta zauna a gefensa.
“Ya Taj?”
A hankali ya buɗe idonsa. Ta nuna masa kofin. Ya buɗe bakinsa.
Ƙofa ta kalla “Yaya fa za ta iya dawowa.”
“Ba kya tausayina? Allah I am sick. Amma dai kawo. Zan rama idan na warke.”
Yana shanyewa ko magana bai yi mata ba ya miƙa mata wayarsa bayan ya buɗeta.
“Kira min Happiness. Kaina…”
Hankalinta a tashe ta kira.
*
Tun dare bayan gidan nasu ya watse, ƴan uwa duk sun tafi Kamal ya soma jin jikinsa yana neman dawowa. Ya sha magungunansa ya shige ɗaki ya rufe ƙofa. Rashin kuzarin dake tattare da ciwon gami da ciwon jiki da wahalar numfashi ya soma ji. Ya dinga juye juye akan gado har Allah Ya kawo masa bacci. Da gari ya waye ya ɗan ji sauƙi amma ba sosai ba. Ya lallaɓa ya tafi boutique ɗinsa ya shige office ya kwanta. Idan yana gida damunsa za ayi da tambayar ko lafiya. Nan kuwa yaransa ba za su neme shi ba sai ya zama dole indai ba da kansa ya fito ba.
Yana kwance cikin ciwon nan ne Hamdi ta kira shi. Ya sani sarai ciwon wasa ba zai sa Taj nemansa ba. Haka ya tashi ya lalubi muƙullin motarsa. Kafin ya kai ƙofa amai ya taso masa. A cikin office ɗin ya fara da ƙyar ya ƙarasa toilet. Tun yana yi a tsaye sai da ya yi zaman dirshan a ƙasa. Kusan minti sha biyar kafin yaji dama-dama ya tashi yasa tissue ya goge duk inda ya ɓata a office ɗin sannan ya fita. Wayar Taj ya kira domin yaji jikin tare da bashi haƙuri akan rashin fitowa da wuri.
“Ya naji muryarka a shaƙe? Allergy ɗin ne? Me ka ci?” Taj ya manta da ciwonsa ya tashi zaune da kyau.
“Ƙwarewa nayi. Baka ganni ba harda amai saboda tari.”
Komawa Taj ya yi ya sake kwantar da kansa “ai kaƙi jin magana akan shan abu kana surutu.”
“Ba za ka yi min sannu ba to?”
“Sannu ba don halinka ba.”
Kowannensu ya yi maganar cikin dauriyar ciwo. Su ka yi sallama Kamal ya cigaba da tuƙi. Yana son faɗawa Taj lalurarsa amma mene ne amfanin sanya shi cikin damuwa?
Da nasa ciwon ya ƙarasa gidan Abba ya ɗauke shi. A soro ya yi sallama da Hamdi don ya ce turarenta hijab ɗin da ta ɗora ma bai hana shi mara lafiya ji ba.
“Allah Ya baka lafiya.”
“Amin.”
“Za ka kirani idan kun gama da asibitin?” Tayi magana tana kallon ƙasa.
“Dole na. Ko don na baki haƙuri.”
“Haƙurin me?”
“Wanka da shirin tarbar maigidan da ki ka yi mana. Ni kuma nazo na haɗaki da jinya. Maimakon na yaba miki da kyau tunda babu kowa a gidan. Mtswww, Allah ban jidaɗi ba.”
“Allah Ya shiryeka.” Ta tura shi.
“Ya shiryemu dai Hamdi. Ni dake idanunmu iri ɗaya ne.”
“Wane iri?” Ta tambaya don bata gane ba.
“Zan miki bayani a gaba.”
Motar Kamal ya shiga su ka tafi asibiti aka yi masa allura da bashi magani. Bai ga komai a tattare da Kamal ba domin ya daure sosai yana danne nasa ciwon saboda yadda yaga Taj.
***
Da wuri Yaya Kubra tayi clearing schedule ɗinta ranar litinin. Ta tabbatar bata da sauran aiki na gaggawa a asibitinsu sannan ta fita domin ganawa da Dr. Mubina. Hankalinta a ƴan kwanakin da su ka gabata sam ba a kwance yake ba. Tana dai daurewa ne kawai saboda kada kowa ya gane. Ta dai sakawa Kamal ido fiye da koyaushe. Duk wani motsinsa tana bi. Zuwanta biyu Happy Taj ma tana siyayyar dole duk don ta sami ganinsa. Bata son kiransa ta ɗora masa wahalar zuwa gidanta ko asibiti.
A reception ta bada katinta ta ce don Allah a miƙawa Dr. Mubina idan tana nan. Matar ta karɓa ta duba.
“Tun ɗazu ta ce idan kin zo a nuna miki inda take. Bismillah.”
Babu mamaki ko kaɗan a tare da Mubina da zuwan Yaya Kubra. Wannan yasa da ta shiga office ɗin ta ce ,
“Allah Yasa ban ɓata miki lokaci ba. Naga kamar jirana kike.”
“Na san yanayin aikin. Ina da niyyar jira har zuwa dare ko za ki zo.” Ita ce amsar da bata sannan su ka gaisa.
Yaya Kubra ta ɗora ledar kwalin maganin akan tebur tana fuskantarta.
“Na sami saƙonki. Amma mene ne dalilinki na breaking doctor-patient confidentiality? Laifi ne babba kin sani.”
Murmushi Mubina tayi “domin mu ceci Kamal kamar yadda ki ke tunani. Sannan ban karya doka ba. Magungunan ba a same su a nan ba shi ne nayi masa order daga India. Da su ka iso ni bana nan ina wajen conference a Ghana. Za ki iya duba date ɗin. Na kira shi bana samu. Kuma ban san numbar kowa nasa ba, sai sunanki da na asibitinki. Shi yasa na tura.”
“Kema kin san dai ba zan yarda da wannan zancen ba.”
Mubina ta dage taƙi bari fuskarta ta nuna ta san bata kyauta ba. Dags ƙarshe dai ta ce,
“Tura miki kawai nayi. Ban san za ki buɗe ba.”
Dariya Yaya Kubra tayi. Da alama babu yadda za ayi ta kama wannan matashiyar likitar da laifi.
“Ki yi min bayanin ciwon Kamal baki da baki ba abin da nake zargi daga magani ba.”
“Ƙoda ce. Duka biyun. Idan ciwon ya sake tashi sai dai mu fara dialysis. Shekara guda kenan yana fama. Kusan duk wani magani da na sani mun gwada. Amma they are barely functioning.” Mubina ta faɗi da rawar murya.
Jikinta har yafi na Mubina rawa Yaya Kubra ta ce “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Doctor kun taɓa shawarta yi masa transplant?”
“A nan matsalar take. Ya ce min shi kaɗai ne mai rhesus negative blood group a gidan. Dalilin da yasa yaƙi sanar da kowa kenan.”
“Wannan ai ba dalili bane. Ya ma aka yi shi kaɗai yake da negative? Wane blood group ne?”
Yaya Kubra tayi maganar cikin hawayen da bata san ya sauko ba. Ita da ta zo da niyyar jin ko kidney stone ko wani infection. Bata zata abin ya kai haka ba. Kamal, Happiness ɗinsu da ciwon ƙoda wadda take gab da daina aiki gabaɗaya.
Kukan da ita Mubina tayi a lokacin da ta hanga taga kamar mafita ta ƙarewa masoyinta, shi yayarsa take yi.
Abin da yake faruwa babba ne. Ƙoda ba abar sayarwa bace. Sannan ko a cikin gidan su mutum ba fa kowa ne zai iya yarda a cire tasa a bawa wani ba. Duk da tana da yaƙinin da wuya aje da maganar gida ba a sami kaso fiye da saba’in a shirye da su bayar ba. A ina za su sami ƙoda? A dangi?…abin da kamar wuya. Sannan zancen cigiya ma bai taso ba. Hukumomin tsaro da na lafiya basu yarda wani ya saka kuɗi ya sayi wani ɓangare na jiki ba. Faruwar haka zai sa mutane su dinga sayar da organs ɗinsu da zarar sun shiga matsala da ma abubuwa daban daban marasa daɗi da za su iya biyo baya.
“Ki kwantar da hankalinki mu yi magana doctor.”
A gigice Yaya Kubra ta ce “ta ina hankalina zai kwanta? Iyayenmu duka na tabbata jininsu positive ne. A ina ya sami negative don Allah?”
Bayanin wannan ruɗani Mubina tayi mata kamar ba likita ba don hankalinta na neman gushewa. Da gaske likitoci kamar kowa in lalura ta waji nasu ce su ma ba sa ji, basa gani. Group ɗin jini daban kamar yadda ta sani guda huɗu. A, B, AB da O. Sannan yana ɗauke da wani sinadari da ake kira rhesus. Idan akwai sai wannan blood group ɗin ya zama positive (+), idan kuma babu sai ace negative (-). Abin mamakin shi ne da group ɗin jinin da rhesus ɗin duka a wajen iyaye ake gada. Uwa za ta iya zama A+, uba kuma O-, sai su haifi ɗa O+. Ya gaji group a wajen uba, rhesus a wajen uwa. Wannan shi ne normal. To a case ɗin Kamal an wayi gari shi kaɗai ne yake ɗauke da jini rhesus negative. Wannan yana nufin ɗaya daga cikin iyayensa yana ɗauke da alamun rhesus negative ɗin a ɓoye. Tunda kowanne abu na jikin ɗan Adam ana samu daga uwa da uba a tare, wanda yafi ƙarfi ya nuna kansa (domimant gene). Ɗayan kuma ya zama a ɓoye (recessive gene). To wannan ɓoyayyen zai iya bayyana a jikin ƴaƴan da za su haifa a matsayin mai ƙarfi. A taƙaice dai ɗaya daga cikin iyayen Alhaji ko Hajiya suna ɗauke da rhesus negative gene. (Batul ba likita bace. Wannan bayani na samu shi ne bisa bincike da nayi. Idan yaci ƙaro da ƙa’idar likitanci don Allah ayi min uzuri. Littafin fiction ne dama.)
“Allah Sarki Kamal. Nagode Doctor. In sha Allah zan yi cigiya a family ɗin Hajiya. Don da ace daga ɓangaren Alhaji ne tabbas Kamal ba zai kasance shi kaɗai ne mai wannan blood group ɗin ba.”
“Cigiya kuma? Doctor Kubra please ki duba abin a matsayin likita. Anya ya kamata ki fara bin dangi kina neman mai bashi ƙoda?”
“Zuba ido zan yi ciwo ya cinye shi? Me yasa ki ka faɗa min in ba don haka ba?”
“Saboda mu nemi mafita amma ba da garaje ba. Cigiya zata iya zama laifi a shari’ance. Musamman idan mai bayarwar ya nemi a biya shi.”
Duk ta inda Yaya Kubra ta ɓullo sai Mubina tayi mata nuni da illar hakan. Iyayensa ya kamata su sani. Shi kuma Kamal yaƙi amincewa saboda a ganinsa tayar musu da hankali zai yi. Ga ciwo, ga kuɗi amma babu mai iya taimakawa. Damuwar da za su shiga sai ta ninka ciwon nasa.
“Da na sani Taj na faɗawa.” Mubina ta ce da taga Yaya Kubra ta manta da dokokin aikin nasu. Yadda zai sami lafiya kawai take nema.
“Rufa mana asiri. Gara kowa yaji akan Taj. Ina miki rantsuwa da sai yafi Kamal jinya. Those two are like one soul in two bodies.”
Da ƙyar Mubina ta sami kan Yaya Kubra. Sun tsayar da magana akan cewa za ta zo ranar next appointnent ɗinsa. Daga nan sai su san abin yi kuma.
***
Yadda Mami ta so ko ana muzuru ana shaho haka Alh. Mukhtar maigidanta kuma uba ga Salwa yake yi. Ta zauna ta kalallame shi da ƙarya da gaskiya aka son da Salwa take yiwa Taj.
“Mu ne da alhakin sama mata farincikinta. Idan ba haka ba Allah muna gab da rasata.”
“Ni uban mace ki ke so in kira tsohon mijinki in roƙi ya sa ɗansa auren ƴata? Da hankalina fa.”
Ɗaure fuska tayi “to sai ka barta ciwon so ya kasheta ai.”
“Ki gaggauta kiranta ta dawo gida kafin ranta ya ɓaci wallahi.” Har wani haki yake don ɓacin rai. Rainin hankalin Mami ya yi yawa.
Juyawa ya yi zai fita tayi saurin jefa layarta ta biyan buƙata a baki ta tauna. Kamar an tsayar da ƙafafunsa ya tsaya cak.
“Nace ka kira Alh. Hayatu ka san yadda za ka yi dashi ya amince a aurawa ɗansa Taj Salwa.” Ta faɗi da izza.
“To. Yanzu ko yaushe?”
“Zauna ka kira yanzu.”
Zaman ya yi ya ɗauko waya. Ta miƙa masa wayarta mai ɗauke da numbar Alh. Hayatu ya kwafa ya yi dialing.
“Assalamu alaikum”
Ta jiyo muryar tsohon masoyinta abin begenta har yau. Sake tauna layar tayi ta zarewa Alh. Mukhtar idanu. Jiki na rawa ya amsa sallamar tare da gabatar da kansa.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
