Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    Ko sakan 30 ba ayi ba tsakanin fitar Salwa da shigarsu ciki Taj ya turo gate ɗin. Kamal ya yi mamakin ganinsa tsaye daga waje. Shi kuwa yafito shi kawai yake da hannu. Cewa Hamdi ya yi ta ɗan jira shi. Ko kallon Taj ɗin bata yi ba domin ranta a ɓace yake. Bata son yanayin da take jin zuciyarta a ciki. So take ko dai taga dawowar Salwa ciki ko kuma ita tayi hanyar gidansu.

    Kafin Kamal ya ƙarasa gate ɗin sai ga Firdaus. Ƴar wajen Yaya Hajiyayye wadda su ka gama FGC tare da Hamdi.

    “Anti Hamdiyya Habib Umar” ta kirata da ƙarfi cikin murna.

    Tana rufe baki sauran jikokin su ka firfito suna yi mata oyoyo. Abin ya bata mamaki don gaskiya idan ta ce ta sa rai da tarba mai kyau daga zuwanta tayi ƙarya. Ƙaruwa mamakin nata ya yi da Firdaus ta rungumeta.

    “Wai ashe matar Uncle Taj ce ke ban sani ba duk zamanmu a school. Ai da ko ruwa wallahi ba za ki ɗebo ba. Uncle Taj is my favourite.”

    Hamdi tayi murmushi kawai tana mai jin kunya. Firdaus ta ja hannunta su ka shiga ciki. Anti Zahra ta taso da sauri.

    “Ke matsa min. Ƙanwata ce. Ni zan kaiwa su Hajiya ita.”

    “To duk gidan nan dai idan aka cire Happiness kowa ya san nice ta gaban goshin Happy. So please allow me…” wata ƙanwarsu ta janyeta “sannu da zuwa Sis”

    “Meye haka jama’a? Ba babba babu yaro?” Umma tayi magana daga ƙofar ɗakinta. Kowa sai ya sami nutsuwa “Za ku barta ta zauna ne ko kuwa sai kun gama tsorata ta da wannan hayaniyar?”

    Sai a lokacin wata mai yawan murmushi ta zaunar da Hamdi akan kujera. Sai dai tana zaman ta zame jikinta ta koma ƙasa. Akayi akayi sam taƙi komawa kujerar. Ga mayafi ta sa ta rufe fiye da rabin fuskarta. A haka ta gaishesu. Umma da su Hajiya su ka fito su ma. Cike da kunya da ladabi ta gaishesu tamkar iyayenta. Aka tambayeta mutanen gida ta ce suna gaishesu. Bakin Inna kasa rufuwa yayi. Surukar tata tayi mata ta ko ina. Fargabarta ma ta ganin wata halayya da za ta nuna nakasun tarbiyya a tattare da zuri’ar Abba Habibu ta ɓace ɓat.

    Filin gabatarwa aka shiga inda Bishir ya nuna mata iyayensu da sunayensu. Sannan yabi ƴan uwansa ɗaya bayan ɗaya su ma. Haddacewar dai sai a hankali. A wajen ya nuna mata mata goma sha biyar. Sauran sun yi nisa. Ga jikoki gari guda. Su kaɗai sun ishi juna gayya.

    “Za a saka ki a family group. A hankali duk za ki gane mu.” Yaya Kubra ta faɗi.

    Tana cikin waɗanda Hamdi ta riƙe sunansu saboda kana kallonta kaga ƴar gayu ajin ƙarshe. Gashi ance likita ce. Ta lura dai duka gidan akwai wata kamanceceniya da ko baka san su ba za ka iya danganta su da juna.

    Kai ta gyaɗa har lokacin ta kasa buɗe fuskarta da kyau. Hira ce ta ɓarke kowa da irin tambayar da yake yi mata.

    “A kawo abinci kafin ku cika mata kunne don Allah.”

    “Hajiya ai so muke ta buɗe bakinta.”

    “Baki zai buɗe ne babu abinci?” Mama ta fatattaki jikokin ta ce su tashi su fara ɗauko kwanuka.

    “Yau bamu ci komai ba muna jiran amaryarmu. Me za ki ci?” Wadda tayi maganar ta fara buɗe food flask. Akwai fried rice wadda taji kayan haɗi da hanta, tuwon shinkafa da miyar agushi, waina (masa), coleslaw, pepper chicken, farfesun kayan ciki da kuma nau’ikan lemo na kwali da ruwan roba. Abu kamar taro, kodayake taron ne tunda yawa garesu.

    Kai a ƙasa ta ce “Na ƙoshi.”

    “Kada na sake jin zancen ƙoshin nan Hamdiyya. Don Allah ki saki jiki don a gida kike. Girkin yau dukkaninmu uwayenki sai da muka saka hannu.” Umma tayi magana tana hararar ƴaƴan nasu “daga cewa za ki zo gaishemu duk su ka baro gidajensu saboda fitina. Ai gashi nan kun cika mata ido ta kasa sakewa.”

    Dariya aka yi. Aka gama ajiye tarin kayan abinci kamar na biki sannan aka shiga zuzzubawa. Hamdi ta lura kusan sa’anni ake haɗawa a tray guda. Firdaus ta nace a haɗasu a tray guda amma fir aunties ɗinta su ka ƙi. Wai matar aure ba sa’arta bace. Basu san ita babu yadda za ayi ta ci abinci da kowa a zuwan farko ba. Kuma ƙila na ƙarshe.

    “Idan ba za ki iya ci su ba a zubo mana tare.”

    Wani irin shiru falon ya yi na wucin gadi kowa na kallon Inna kamar ba ita tayi maganar ba. Kafin kuma su kwashe da dariya suna hailing ɗinta. Harda masu karambanin ɗauko plate za su zuba musu.

    Da wani irin sauri Hamdi ta matsa tray mafi kusa da ita harda gyara murya ta ce “Bismillahir Rahmanir Rahim.”

    Waɗanda basu yi dariya da farko ba ma sai da su ka yi yanzu. Cikin ruwan sanyi Inna tayi musu maganinta. Inna ma murmushi tayi.

    Abinci ya yi daɗi. Ba don gidan surukai bane tabbas cin da Hamdi zata yi sai yafi wanda tayi na baƙunta. Su na ci ana kiran sallar la’asar. Ɗakin Mama aka ce a kai ta tayi sallah a can. Suna tafiya da Firdaus ne ta tambayi Salwa. Don duk abin da ake hankalinta bai bar kallon ƙofa ba.

    “Gidan nan kowa nada kirki Firdaus. Da ina shigowa na haɗu da wata ƴar uwar taku ma a bakin gate mu ka gaisa. Naga kamar ta tafi.”

    “Kai anya kuwa. Kowa na nan fa.”

    Ba don bata riƙe sunan ba ta ce “sunanta Salma ina jin.”

    “Salwa ko?” Sai kuma ta kalli matan dake zaune ta ce “Ina Anti Salwa ne? Sai yanzu na lura bata nan.”

    Cigiyarta aka fara yi ana kiran Anti Zahra ko ta san inda ta tafi saboda bata cewa kowa za ta fita ba. Ita dai jikinta sanyi ma ya yi. Dama tun a gida da ta rangaɗa wannan uwar kwalliyar hankalinta bai kwanta ba.

    “To ku kira ta mana. An duba banɗakuna? Ko bacci ya ɗauketa a wani ɗakin?” Cewar Hajiya.

    Hamdi ta tabbata ko ma mene ne babu hannun ƴan gidan nan, duba da yadda su ka shiga ruɗanin ina ta shiga. Firdaus ta ce musu ai Hamdi ta ce taga fitarta.

    “Tambayata sunan wadda su ka gaisa a waje tayi shi ne na kula ita ce bata nan.”

    “Da shirin fita ki ka ganta?” Anti Zahra ta tambayi Hamdi.

    Murmushi tayi don tambayar da take jira kenan dama.
    “A’a, cewa tayi za ta je wajen shi…”

    Yaya Hajiyayye ta ce “shi wa?”

    “Ke kuma komai sai anyi miki gwari gwari ne? Taj take nufi ko Hamdiyya?” Yaya Zulaiha ta tambayeta.

    Ta sake yin murmushi kawai. Kunyar inda take ba za ta sa ta bari Salwa ta sami biyan buƙata ba. Tayi kaɗan! A yadda tazo mata da raini da isa shi yasa za ta hana ruwa gudu matsawar da igiyar Taj a kanta. Ko sun rabu Salwa ta aure shi ba za ta ce ita ce sila har taji daɗi ba.

    “Ku kira min ita. Ko Kamal. Ta dawo ciki” Anti Zahra ta faɗi hankalinta a tashe.

    Yadda tayi yasa kowa kallonta da ayar tambaya. Sai ta wayance wai taga Salwan daga tafiya ta dawo ko abinci bata ci ba su ka fito. Nan kuwa tsoronta kada taje tayi abin da zai zubar musu da mutumci. Domin duk abin da Salwa za ta yi dole a danganta ta da Ahmad. Ita kuwa bata son abin da zai taɓa mutumcin mijinta akan wata shirmen soyayyar da babu aji a ciki.

    Kamal ɗin aka kira ya ce sun fita da ita da Taj amma ba jimawa za su dawo.

    “Ya za ku fita da ita babu wanda ya sani?” Umma da ta kira wayar ta tambaye shi.

    “Gamu nan Umma. Mun kusa gida ba in sha Allahu.”

    Sallah aka tafi yi. Wasu kuma suna ta aikin kwashe kwanuka. Masu aikin gidan dai za su aikatu da wanke wanke. Don ma ba da plate suke ci ba, haɗawa ake yi.

    Hamdi ta đauro alwala ta tada sallarta a inda aka shimfiɗa mata abin sallah.

    Shigarta ta kamala ta burge Mama. Taƙi jinin lokacin sallah ya yiwa mata a waje su dinga aron mayafi ko hijabi saboda nasu bai dace da tsayuwa gaban Allah ba. A ganinta rashin daraja addini ne yake sa mata fita da suturar da ba za ta musu sallah ba. Su kansu sun san hakan bai dace da tarbiyya da ma ɗa’a ga addini ba.

    Da ta idar sake gaishe da Mama tayi bayan ita ma ta idar.

    “Hamdiyya ina son mu yi magana. Matso kinji.”

    Gaban Hamdi ya ɗan faɗi. Ko faɗa mata zata yi ta fara shirin zama bazawara?

    “Ina fata kin san komai game da Taj yanzu da alaƙarsa da mahaifinsa?”

    “Na sani” ta amsa kai a ƙasa.

    Mama ta numfasa ta ce
    “Kullum burinmu shi ne ƙila idan ya tashi aure su daidaita. Sai Allah Ya ƙaddara masa aurenki. Wannan ma ya ishi mai hankali tunani.” Ta kamo hannunta ta riƙe “a halin yanzu mutumci da martabar mahaifinki da ta mijinki suna hannunki Hamdiyya. Hali da ɗabi’ar da za ki nuna mana ita za ta tabbatar da ɗorewar rigimar Alhaji ko kashe gobarar da ta tashi babu gaira babu dalili.”

    Jin an taɓo Abbanta ne yasa ƙwalla cika mata ido. Wani ɓangare na zuciyarta yana ƙara tunatar da ita laifin mahaifinsu ne da su ke fuskantar wannan abu daga ita har shi. Yayinda wani ɓangaren kuma yake kare Abba a matsayin đan Adam ma’asumi wanda ya cancanci duniya tayi masa uzuri idan ya bayyana tubansa.

    Da ƙaramar murya ta ce “Me ya kamata na yi?”

    “Na san ke yarinya ce amma tunda na ganki naji bani ds haufi akan zaɓin da Allah Ya yiwa Taj.” Mama ta faɗi tana yi mata murmushi “Alhaji yana son mutane jajirtattu. In kin kula yaran gidan nan kowa baki gare shi. To ƙuruciya su ke samun wannan ƙwarin gwiwa ta rashin gazawa daga gare shi. Saboda haka kada ki yarda ki zama sokuwa. Ko laifi aka yi miki yafi son ki gwada ƙwatarwa kanki ƴanci. Sai abin yafi ƙarfinki ya amince ki nemi wani. Abu na biyu kuma ki kasance a kodayaushe cikin nuna hali na kyakkyawar tarbiyya. Zan so ya gani kuma ya shaida cewa ƴaƴan Habibun da yake ganin ya kauce hanya ya sun cika ƴaƴa ta kowacce fuska. Na ƙarshe kuma ki so mahaifinki da mijinki. Ki nuna masa ke kina ƙaunarsu dasu da sana’ar da Allah bai haramta musu ba. Kina alfahari dasu kuma hakan bai rageki da zama ƴar da shi ko wani zai kasa ƙauna a matsayin suruka ba.”

    A rayuwa akan ce wanin hanin daga Allah baiwa ne. Hamdi ta fahimci haka a yau. A shekaru irin nata ko ma fi wata ba za ta gane mene ne ainihin abin da Mama take so ba. Saboda duka maganar a ɗan dunƙule take fita. Amma yau da gobe saboda tashi a gaban Abba yasa ta gane. Magana da iya zuba zance a wajen cikakken ɗan daudu yana daga cikin alamomin da ake ganesu ma. Ya rage nasa ne nesa ba kusa ba da ya gane yana daga cikin abubuwan dake saurin saka a gane tsohuwar rayuwarsa.

    A taƙaice Mama so take ita Hamdi ta saye zuciyar Alhaji da halaye masu kyau ta yadda zai gane Habibun da ya raina bai gaza ba wurin tarbiyyar ƴaƴansa. Sannan sana’ar Taj bata cikin dalilan da mutum zai yi fushi da ɗansa.

    Godiya tayi mata da alƙawarin kamantawa da yardar Allah.

    “In kin kula gidan nan babu ƴan ubanci tsakanin ƴaƴanmu. Duk da Alhaji ne ya ɗora mu akan turbar zaman lafiya to amma fa akwai ƙoƙari matuƙa daga Hajiya. Daga cikin irin zaman ne alhakin kula da kuma tarbiyar ƴaƴa maza ta dawo hannuna. Ba don Allah Ya tsare ba da tuni a sanadiyar korar Taj komai ya rikice mana. Ni kaina ina ɗorawa kaina laifi domin kuwa ni na ƙarfafa masa gwiwar girki. Fatana da raina da lafiyata in ga lokacin da Alhaji zai shigo da Taj ya damƙawa mahaifiyarsa.”

    Kowane gida akwai nasu kalar damuwar. Tana ganin kamar duk duniya sun fi kowa sai gashi gidan da tun shigowarta komai na jama’ar ciki yake burgeta su ma da nasu.

    Ɗakin Umma, Mama ta kaita. A nan ma babu kowa sai Umman ita kaɗai zaune akan abin sallah. Suna shiga Mama ta fita ta barta. Umma ta ɗaga hannuwa tana addu’a, Hamdi sai ta ɗaga ita ma har Umma ta kammala ta ce Amin.

    Umma ta zolayeta da cewa “Wato kin ji ina roƙa muku ƴan bibbiyu sau biyu a shekara shi ne ki ke ta cewa amin ko?”

    Kunya kamar ta nutse “Allah ban san ita kike yi ba.”

    “Janye Amin ɗin za ki yi?”

    “Eh” Hamdi ta faɗi da sauri, kunya duk ta ishe ta.

    “Yanzu addu’ar tawa ce ba kya so?”

    Sake daburcewa tayi ta ce “A’a ban janye ba. Yi haƙuri don Allah”

    Umma tayi dariya sosai.
    “Wasa nake miki kinji Hamdiyya. Zo ki zauna.”

    Ita ma kamar Mama da yi mata bayani akan gidansu babu ɓaraka ts fannin zamantakewa ta fara. Sai abin da ba a rasawa na zaman tare. Ko a cikin ƴaƴa tunda ba a raba siblings da ƴan rigingimunsu. Amma dai duk inda aka je aka dawo su ɗin tsintsiya ne masu maɗauri guda.

    “Hamdiyya don Allah ki riƙe mijinki riƙon da Allah Ya umarci bayinSa kinji. Ki bawa maraɗa kunya.”

    “In sha Allahu Umma.”

    “Na tambaye shi ya min rantsuwar ba taimako da rufin asiri kaɗai ya so yiwa mahaifinki ba. Auren yake so kuma ke ya zaɓa a matsayin abokiyar rayuwa. Saboda haka don Allah ki ji, ki ƙi ji. Ki gani, ki ƙi gani. Babu wata rayuwar auren da take ɗari bisa ɗari. Amma indai kun riƙe juna amana za a sami nutsuwa da rahamar da Allah Ya sanya a cikin aure.”

    Wani tunani ne ya ɗarsu a zuciyar Hamdi da Umma ta kaita ɗakin Hajiya. Shin matan gidan nan sun san shirin da mijinsu yake yi a kanta na raba aurenta da Taj ne? Amsar a bakin Hajiyan ta samo ta ba tare da ta tambaya ba. Ita ma kamar ƴan uwanta zancen da ta fara akan zaman lafiyar iyalinsu ne. Shekaru arba’in da ɗoriya suna gina ƴaƴansu akan turba mai ɓullewa. Ba za su taɓa maraba da abin da zai kawo rabuwar kai tsakaninsu ba.

    “Nayi imanin kin ji daga bakin mahaifinki cewa Alhaji ya bashi wata uku ya san yadda ya yi Taj ya sake ki. Haka ne?”

    Taurin zuciya irin na Hamdi sai ta kasa kuka. Idanunta ne kawai su ka yi jazur kamar gauta. Ta gyaɗa a hankali.

    Hajiya ta dafa kafaɗarta da kulawa “Inna ce kaɗai cikinmu bata sani ba sai kuma ƴan uwanku da shi Taj ɗin. Ko kin faɗa masa?”

    “A’a.”

    “Da kyau. Don Allah ki bar zancen a cikinki. Abin da nake so shi ne ki ginawa kanki matsugunin da babu wanda ya isa ya rabaki da shi. Kina ganin yadda ƴan uwansa su ka karɓeki hannu bibbiyu. Innarsa da danginta kuwa …” ta kasa ƙarasawa. Haƙiƙa wannan karon akan Taj yayyen Inna da ƙannenta da su ke duk maza sai ɓarin kuɗi suke yi.

    Takanas babban wan ya turo matarsa ta sanar da Hajiya cewa su za su yi komai na bikin. Kayan gida da Inna ta ce za ta yiwa Hamdi duk an ɗauke musu. Lefen da ƴan uwansa ke haɗawa kawai aka bar musu. Shi ma kuma akwai gudunmawa gagaruma daga garesu. Yadda Taj yake kyautatawa a gidansu da dangin babansa haka su ma can yake yi musu.

    Ita dai Hamdi zuciyarta tsinkewa ta sake yi. Bata yi ƙasa a gwiwa ba ta ce
    “Hajiya maganar mahaifi ba abar wasa bace. Musamman shi da suke da wannan matsalar.”

    “Hamdiyya addu’a nake so ki yi. Ki roƙi Allah ki kuma yi taki bajintar saboda muddin Taj ya fara sakin aure a tsukin lokaci irin wannan wallahi sunansa zai ɓaci. Alhaji bai san wannan hukuncin duka gidan nan zai shafa ba. Za a ce da gaske tunda ubansa ya kore shi ba mutumin arziƙi bane. Sannan ina mai tabbatar miki Innarsa ba za ta zauna ba. Don wannan karon a shirye take. Dama can wa’adin zaman ne bai ƙare ba amma da tabi ta ƴan uwanta da ta daɗe a gida.”

    “Subhanallahi” Hamdi ta faɗi cike da tsoro.

    “Ƙwarai kuwa. Idan Inna ta tafi kuma Mama…Haj. A’i da ki yi sallah a ɗakinta ma tafiya za ta yi. Saboda kullum gani take laifinta ne Taj ya tashi da son girki.” Ya dubi Hamdi da kyau “a yadda ki ka fuskanci gidan nan kina ganin ni da Umma za mu zauna? In kuma duka mu ka tafi yaya makomar shekarun da muka ɓata muna gina ƴaƴanmu akan soyayyar juna da zumunci?”

    Murya na rawa Hamdi ta ce “Hajiya aikin ya yi min nauyi.”

    “Ke fa mace ce. Kada ki bari na kuma jin wannan kalmar ta gazawa.”

    “Abbana…Yaya ma tana da lalura. Waye zai mutunta abin da zan yi?”

    “Ubangijin da Ya tayar dake a cikin zuri’arsu, Ya kuma kawoki cikin tamu, Shi zai dafa miki.”

    “To amma ta yaya zan yi abin da aka yi shekaru ba a samu ba?” Har a lokacin zuciyarta ta kasa ganin me su ke so taƙamaimai.

    “Mace na juya miji Hamdiyya. Mu dai namu ina jin a kan shi aka ƙare kafiya da taurin kai” Hajiya ta faɗi tana dariya. Hamdi ma murmushi tayi.

    “Duk ya bi ya ɓata mana yara da halin. Sai dai kawai na wani yafi na wani. Tunda Taj ya hana shigo masa gida ba iyalin Taj ba ina ganin yau da gobe yana ganinki da kyawawan halayenki zai gane ɗansa da baban naki da yake ƙi basu ragu da komai ba akan sana’arsu. Allah Yasa kin fahimceni.”

    “Na gane Hajiya. Amma…”

    “Za ki iya Hamdiyya. Wallahi ina jiye mana ranar da Abu za ta botsare a gidan nan. Mai haƙuri bai iya fushi ba. Komai na zaman lafiyarmu zai tashi a banza. Ƴaƴa ashirin da takwas idan kansu ya rabu yaya zamu yi?”

    Yau dai bata sani ba kuka ya kamata tayi ko dariya. Duk inda ta shiga magana ɗaya su ke yi mata. Ina ita ina ɗaukar wannan nauyin? Alhajin da ya raina mahaifinta bata jin za ta taɓa yi masa abin da zai burge shi har ya yafewa wani.

    Hajiya tashi tayi ta ce mata su je ɗakin Inna. Sun sameta da yawancin ƴan matan jikokin nasu. Zolayarta su ke son rai tana biye musu.

    “Ku zo ku fita.” Hajiya ta nuna musu ƙofa. Babu wadda tayi gardama sai Hayat ɗin Ahmad da ya dage ba zai fita ba.

    “Ƙyale shi Hajiya” Inna ta kalli Hamdi tayi murmushi “iyayenki na san duka sun gama yi miki nasiha. Nawa kawai tuni ne akan ki riƙe maganganunsu domin su ne iyayen Taj. Sai Amma dake Abuja. Ya taɓa haɗaku kuwa?”

    “A’a” Hamdi ta bata amsa

    “Ai ta ce tana tafe jibi. Ita ma ba za ta bari su yi haɗuwar wajen biki ba tunda an riga an ɗaura.” Ta nunawa Hamdi kujera “Zauna ba a rasa abin faɗa miki ba. Sai dai in kuma kara ce ba za ki yiwa Mama ba.” Cewar Hajiya ga Inna.

    Bayan ta fita Hamdi taji kunyar da tafi ta sauran ɗakunan. Innar Taj tana da wani irin kwarjini da cika ido.

    “Kina da zaɓin kalar kayan ɗakin da ki ke so?”

    Tambayar a bazata ta zo mata. Ta ɗaga kai daga sunkuyon da tayi.

    “A’a.”

    “Taso ki gani” Inna ta nuna mata waje kusa da ita akan makeken gadonta da tun shigowar Hamdi take santinsa a zuciyarta.

    Kasa tashi tayi sai da Inna ta maimaita maganar tare da umarnin lallai ta taso. A ɗofane ta zauna. Inna ta buɗe catalogue ta ɗora mata a cinya.

    “Buɗe ki zaɓi wanda ya yi miki. Sai kuma ki zaɓarwa mijinki.”

    Yawu ta haɗiya. Jikinta har wani rawa yake tana jin sanyi sanyi na ratsa ƙasusuwanta. Wannan fa ita ta haifi Taj. Da Yaya za ta ga zaman da tayi kusa da ita irin wannan ƙarshenta sai ta ɓallata.

    “Hamdi”

    Ita kaɗai ta kirata da sunan da ake kiranta a gida. Wannan yasa taji ranta ya đan sake.

    Inna ta cigaba da magana “kin shiga ɗakuna uku na surukai. Nan kuma ɗakin na mamanki ne. Don Allah ki ɗaukeni a matsayinta domin hakan ne kaɗai zai bani damar yi miki riƙon ƴar cikina.”

    Cikin rashin jindaɗi Hamdi ta ce “Ki yi haƙuri.”

    “Ba fushi nayi ba. So nake ki ajiye komai ki saurareni da kyau.”

    Hamdi ta miƙa mata hankalinta kacokan. Inna ta fara da yiwa Abba da Yaya addu’a da su ka haifi matar da ta auri Taj. Saboda ta jima tana tsoron kada aurensa ya tashi iyayen ƴar su fasa saboda korarsa da mahaifins ya yi. Abu na biyu kuwa fito mata tayi a mutum. So take Hamdi ta amsa sunanta na matar Taj ba tare da taji ɗar a zuciyarta ba.

    “Indai mijinki ne to ki manta da matsayinsa ki kama abinki a hannu. Na san komai da ƴan uwana su ke ɓoyewa game da sharaɗin da Alhaji ya bawa mahaifinki. Ni kuma in Allah Yaso Ya yarda kin shigo kenan. Allah ba zai bawa kowa damar ganin ƙarshen auren ba ballantana su cigaba da ɗora zarginsu. Hatta ƴan uwanki ina yi musu fatan samun nasarar zaman gidajensu. Abu ƙanƙani ne zai faru a ɗorawa babanku laifi. Idan kuwa ta ɓangarenki ne to da uba da miji duka a kunnuwanki za ki ji ana cin zarafinsu.”

    Darasi mai girma Inna ta ɗora mata, saɓanin su Hajiya da aikin da su ka bata ne mai girman. Akan shekarunta taji kamar an ƙara mata ashirin saboda yadda take ganin ba za ta iya ba. Amma kuma ta sami ƙwarin gwiwa sosai.

    “Taj yana son ki. Ki sa ya ƙara ƙaunarki Hamdi. Ki hana zuciyarsa sakat ta yadda aurenku ba zai sami tangarɗa daga yinsa ba don Allah.”

    Bayan ta gama ɗaukar karatun mai girma sannan Inna ta kira Firdaus ta ce su koma falo. A can aka cigaba da hira wadda ita dai amsarta bata wuce murmushi sai eh ko a’a. Tunanin da aka barta dashi yafi ƙarfinta. Abu guda ta fahimta shi ne matan gidan duka basa son auren nan ya mutu. Gashi Abbanta ya tsorata da barazanar Alhaji yana ta yi mata tuni.

    Cikin dabara aka sa Firdaus ta tambayeta size ɗin da taƙi turawa Taj. Da ƙyar ita ma ɗin ta sanar da ita. Sannan cikin ƙanen Taj wata ta aunata gwajin riga da siket da na doguwar riga. Sai gashi kafin magrib ta soma sakewa dasu. Naƙasun da aka samu bai wuce na rashin shigowar Kamal ko Salwa ba. Sannan ko sau ɗaya Taj bai kirata ba. Ta shaƙa tayi fam tana jiran ya tsikareta ta fashe.

    Ita ma Anti Zahra har fargabar zuwan Ahmad ɗaukarsu take yi. Ta san shi sarai. Laifinta zai fara gani kafin ya saukewa ƙanwar tasa kwandon masifa.

    ***

    Ikon Allah Taj da Kamal su ka gani yayinda Salwa ta soma kuka tun a bakin gate wai Taj yana wulaƙanta ta. Aka yi ta rarrashinta taƙi shiru saboda makirci. A dole Kamal ya ce ta shiga motar. Shi ne su ka tafi Happy Taj. Office ɗin Kamal dake cikin boutique ɗinsa su ka shiga. Ta sami wuri ta zauna tana goge ƙwalla.

    “Salwa tunda ku ke da Taj ya taɓa cewa yana son ki?”

    Shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta. Taj yaji a duniya yanzu babu abin da ya tsana kamar mace ta dinga wasa da yatsunta. Tsaki ya ja ta dubi Kamal.

    “Kana ganin abin da yake yi min? Meye laifina don na ce ina son shi? Ba fa cewa nayi ya saki yarinyar da ya aura ba.”

    “Ki dinga gyara kalamanki akan matata. Sannan kin fi kowa sanin cewa ba zan juyo ba. Ba yaudararki nayi ba so don’t give me that crap wai in haɗaku.”

    “Haɗamu ma bai taso ba tunda Alhaji ya ce…”

    “A wurin wa ki ka ji wannan maganar?” Ya tambayeta muryarsa a sama.

    “A wurin Yaya mana.” Ta bashi amsa tana tura baki.

    Kallonsu Kamal ya yi don bai gane komai ba ya ce “wace magana ce Happy?”

    A taƙaice Taj ya yi masa bayanin da bai yi ba saboda rashin lafiyarsa.

    “Bana jin Yaya zai faɗa mata.” Kamal ya faɗi yana kallonta “a ina ki ka ji?”

    Rigimar da Mami ta ce ta haddasa tsakanin Taj da duk wanda zai goyi bayan yaƙi aurenta ta tuna. Ta kuwa taɓe baki cike da raini.

    “Ina ruwanka? Kai dai burinka ba ya saki Hamdi ka aura ba?”

    Duka su biyu zabura su ka yi cikin ɓacin rai.

    “Salwa!” Kamal ya yi mata tsawar da a tunaninta ba zai taɓa iyawa ba saboda yafi Taj sanyin hali.
    “Ki kiyayeni wallahi.”

    “Idan naƙi fa? Ya Kamal na fa san kana son yarinyar nan. Ko ba abin da ya kwantar da kai ba kenan? Me yasa baka taɓa yin wani ciwon allergy ba sai da Ya Taj ya aureta? Wallahi zan iya dafa izu sittin baka da wani allergy.”

    “Kinga Salwa, kalleni nan” Taj ya yi mata magana yana cijewa don ta riga ta kai shi matakin da yake son taɓa lafiyarta. Wani abu da bai taɓa yi ba ko da wasa.

    Idanunta a bushe ta kalle shi. Bai san bata tunkari wannan rigimar ba sai da ta shirya mata daga gida.
    “Ina jin ka”

    “Zo ki tafi kafin wani cikinmu ya yi miki rauni.”

    “Please Taj kada ka biye mata. Ka bar zancen raunin nan kada wani ma yaji.” Kamal ya yi maganar da kana gani za ka gane yadda yake ƙoƙarin danne ɓacin ransa.

    “Za ka aureni Ya Taj. Allah kuwa…”

    Kawai ta sa kai ta fita. Bayan tafiyarta Kamal ya zo zai yi masa rantsuwar zancenta ƙarya ne Taj ya dakatar dashi.

    “Idan kana tunanin na yarda da zancenta har ina buƙatar ka wanke kanka to gaskiya akwai matsala tsakaninmu.”

    Murmushi Kamal ya yi “Allah Ya huci zuciyarka.”

    “Amma wane irin ciwo gareka Happiness?”

    Koda Kamal ya juya ya kalli Taj sai yaga babu alamun wasa a tare dashi. Allah Ya taimake shi ya fara ajiye magungunan allergy su antihistamine saboda rana irin wannan. Durowar magungunan ya buɗe ya fiddosu duka.

    “Ka ce baka yarda da zancenta ba.”

    “Daga cikin addu’ar da nake yawan yi mana harda kada Allah Ya haɗamu son abu guda da mutum biyu basa tarayya a kansa. Zancen ciwo kuwa ai rantsuwa tayi. Tunda tana sa gaba gabas zancenta zai iya zama gaskiya.”

    Ɗaya bayan ɗaya yabi magungunan ya dudduba. Pain relievers ne da wanda su ka danganci kwantar da abin da ya shafi allergy.

    “Allah Ya baka lafiya Happiness.”

    “Amin.”

    ***

    Tafiyar minti biyar a mota za ta kai mutum wani babban mall da ya yi shura a titin kafin a gina Happy Taj. Ƴan Kano da son sabon abu na yayi kusan kowa ka taɓa zai ce maka ya yi siyayya a Glory Mall. Wurin shaƙe yake da kaya na alfarma. Sannan akwai snacks irinsu shawarma, small chops, popcorn, ice cream da sauransu. Har event centre garesu a ciki. Wurin mallakar wani hamshaƙin ɗan kasuwa ne da ya damƙawa babban ɗansa alhakin kula da shi. Kuma a shekara biyu da rabin farko uban ya yi alfahari da ɗansa. Ciniki ake yi na bugawa a jarida.

    Komai ya soma taɓarɓare musu cikin abin da bai fi sati guda da buɗe Happy Taj ba. Idan kaya ake so boutique ɗin Kamal yana da na kowanne jinsi manya da yara. Abin da ya shafi abinci kuwa harda wanda mutane basu sani ba akwai a ɓangaren Taj.

    Kamar wasa su ka dinga tunanin ko irin abin nan ne na ɗokin sabon waje. Idan an kwana biyu abu zai koma normal. Sai aka yi rashin sa’a kasuwa da gaske take damawa da su Taj cikin albarkar Allah. Haka kawai mutane su ka fara janye jiki. Ciniki ya yi wani irin ja da baya mara daɗi. Alh. Usaini ya shiga gagarumar matsala da mahaifinsa. Inda rashin tawakkali yasa uban ya taso shi a gaba da muggan kalamai da tsoratarwa. Indai ciniki bai daidaita ba to ya kwana da sanin zai karɓe mall ɗinsa ne ya bawa wani daban cikin ƴaƴansa. Wannan abu ya yi matuƙar tayar masa da hankali. Ya shiga faɗi tashin hanyar dawo da martabar mall ɗinsu amma abu yaci tura. Har an kai wasu masu kai musu kaya sun fara janye jiki.

    A irin wannan yanayin na neman hanya kowacce iri ce Allah Ya haɗa Alh. Usaini da Ummi. Cutar hassada tayi mata lulluɓi tun daga kai har tafin ƙafa a lokacin da taji labarin auren Hamdi da mamallakin Happy Taj. Ranar harda kuka sai da tayi. Zuciyarta a cunkushe tana fama da takaicin yadda ƴar ɗan daudu ta sami miji irin Taj. Ta taɓa zuwa wajen da wani saurayinta. Yadda taga Taj ta san wadda ta fita ma bata isa ta aure shi ba, balle kuma Hamdin da bata kama ƙafarta a gayu da rufin asiri ba.

    Wani abin kayan haushin kuma jan kunne da gargaɗin iyayenta da yayanta akan ƙanwar Hamdi da ya aura. Ko kallon banza ta yiwa Zee ya yi alƙawarin canja mata kamanni.

    Ranar da ta haɗu da Alh. Usaini, cikin jin zafin auren Hamdi ta fito ds niyyar zuwa Happy Taj ta ɓata ta a gaban Taj. Sai da ta iso kuma ta rasa me ya kawo mata tsoro ta kasa ƙarasawa. Haka kawai ƙafafunta su ka kaita Glory mall. Ta je wurin snacks ta sayi meatpie da lemo ta sami wuri tana ci. Amma hankalinta gabaɗaya yana kan ginin Happy Taj.

    “Ki tafi can mana idan nan bai yi miki ba.”

    Kallonsa Ummi tayi za ta faɗi baƙar sai ta adana. Mutumin zai yi shekara arba’in da biyar. Ya sha shadda ƴar ubansu da ɗinki na alhazawan birni. Ga ƙamshi na waɗanda naira ta tsaga jikinsu ta zauna da kyau.

    Murmushi tayi masa “ba kallon son zuwa nake ba. Fatan abin da zai zo ya tayar da wurin gabaɗaya koda gobara ce nake yi.” Ta kashe masa ido.

    “Ko zan san dalili?” Amsarta tasa ya sami interest akanta.

    “Kaji daɗin kaini gaba? Allah Ya kiyaye.” Ta tashi tsaye.

    “Ko kusa. Nima burina kenan..” ya kashe mata ido yadda tayi masa.

    “Dalili?”

    “Sun kashe min kasuwar mall ɗina mana.”

    Zama ta koma tayi “nan wurinka ne?”

    “Eh. Amma yana fuskantar barazanar rufewa saboda su.”

    Dariyar mugunta Ummi tayi a zuci. Daga ranar su ka ƙulla ita da Alh. Usaini. Suna neman hanyar da za su nakasa Taj domin su gurgunta masa sana’a.

    A wannan rana ta asabar da Salwa ta fito daga Happy Taj cikin ɓacin rai, ta faɗa Glory Mall saboda akwai mai POS daga bakin gate ɗinsu. Tana jiran mutumin ya idar daga sallar la’sar a gefen ƴar container ɗinsa take waya da Mami. A ciki take zayyane mata duk fa abin da ta ce tayi ta gwada amma ƙarshe Taj yaci mutumcinta.

    “Ni dai Mami da kin barni naje masa a yadda nake. Na tabbata idan ina kwantar da kai zai dube ni.”

    Zaginta Mamin tayi ta ce mata kuma ta kwantar da hankalinta. Ta sanar da mahaifinsu ya ce zai kira Alhajin su yi magana. Tana da yaƙinin yadda Alhaji yake ragawa Salwa don mutumcin babanta da yake gani nw. Duk taurin kansa ba zai ƙi tayin ƴa ba. Musamman tunda ba son wadda Taj ɗin ya aura yake yi ba.

    “Kin nuna musu kin san baya son auren?”

    “Eh, kuma ban faɗa musu cewa waya naji Yaya Ahmad yana yi da matan gidansu yana sanar dasu ba. Har wani cewa yake su yi wani abu kada a raba Taj da wadda yake so. Ni ko oho.”

    “Ki daina yin komai. Da kansu za su nemi ki idan babanki ya yi masa magana.”

    Wayarta duka a kunnuwan Ummi da Alh. Usaini waɗanda su ka yiwa juna wani irin kallo gami da murmushi. Tana gama wayar Ummi ta matsa kusa da ita su ka gaisa. Sai ta nuna kamar ita ma mai POS ɗin take jira. Abin ka da mata in an haɗu. Hira a taɓa nan a taɓa can sai gashi sun yi exchanging number.

    Bayan Salwa ta ciri kuɗin ne ta fito Kamal ya kirata. Babu ja in ja ta faɗa masa inda take. Shi ne su ka ɗauketa don darajar Ahmad kawai. A hanya harda basu haƙuri wai ranta ne ya ɓaci. Babu wanda ya kulata a cikinsu har su ka isa gidan. Taj ya yi zamansa a mota.

    “Happiness ka turo min ita in kaita gida kafin magrib.”

    Salwa bata ce musu komai ba tayi wucewarta ciki. Ganin Kamal bai shigo ba ta tsaya ta goga hoda da lipgloss kafin ta shiga ciki. Hayaniyar mutan gidan taji daga ɗan korido ɗin da ake ajiye takalma kafin a shiga falon. Ta ƙara yin tsaki. Bata san za ta ƙi mutanen nan ba sai da taga yadda aka dinga kai kawo akan zuwan Hamdi. Yanzu kuma da alama hirar ma da ita suke yi.

    Sallama tayi ta shiga da wani irin farinciki a fuskarta. Bata sha wahalar haɗa ido da Hamdi ba don ita ma ɗin sallamar tasa ta ɗaga kai ta kalli ƙofa. Murmushin nasara ta sakar mata. Hamdi ta mayar mata. Daga ita har Taj ɗin sai ta fanshe wannan ɓacin ran da su ka sa ta wuni cikinsa.

    “Salwa ina ki ka je?”

    Ɗan firgita tayi domin kuwa Ahmad ne ya yi tambayar da kakkausar murya.

    “Da Ya Taj muka fita. Cewa ya yi na raka shi Happy Taj. Shi ne mu kaje harda Ya Kamal”

    “Bangane ba? Ya zai kawo matarsa kuma ya yi wani wajen. To da izinin wa ma ki ka fita?”

    Kafin ta bawa Yaya Zulaiha amsa Kamal ya shigo. Sai ta canja akalar tambayar.

    “Ko dai soyayya ku ke da Kamal?”

    Da wani irin sauri ya ce “Allah Ya kiyaye. Ina da wadda nake so.”

    Jama’ar falon su ka kama ihun murna. Harda masu cewa ko a dakatar da bikin Taj saboda dama indai da amana tare ya kamata su yi aure.

    Wannan amsa ta Kamal ta ɓakanta ran Salwa. Yadda ya faɗa tamkar wata abar ƙyama. Ahmad kansa sai da yaji babu daɗi. Anti Zahra ta kallesu su biyun. Idan Salwa ta cigaba da zama dasu za a iya samun matsala tsakaninsa da ƴan uwansa. Ko me za ta yi ita ma jininsa ce.

    “Ku tashi mu tafi” ya ce da Anti Zahra, bana son Magariba tayi min.

    “Kai Ahmad, kamar kana dawa? Don Allah ka zauna.”

    “Ai mun gaisa da ƙanwar tawa ko?” Ya yiwa Hamdi murmushi.

    “An kusa kira Yaya. So kake Ya Taj ya yi sallah shi kaɗai?” Bishir ya ce.

    Fin ƙarfi aka yiwa Ahmad. So yake kawai su shiga mota ya gamu da Salwa. A dole ya bi ƙannensa waje su ka tare cikin motar Taj abin tausayi suna hira.

    Aka sake tashi yin sallah. Hamdi ta koma ɗakin Mama. Salwa sai ta faki ido ta bi bayanta. Su Mama suna ɗakin Umma ana ta shirye shirye.

    “Washhh. Wannan zirga zirga Ya Taj duk ya tara min gajiya.”

    Ƙin kulata Hamdi tayi. Kowa yaci tuwo da ita ai miya ya sha. Darajar inda su ke yanzu yasa ta kama kanta. Amma ramuwa kam zata yi gwargadon abin da aka yi mata!

    ***

    Gayya guda aka rako Hamdi bakin gate da sha tara ta arziƙi. Har ta dinga jin wani iri saboda bata kawo musu komai ba. Yawancin kowa a bayan mota ya ajiye kyautarsa. Banda likitar gidan. Yaya Kubra a hannu ta damƙa mata wata baƙar pepper bag da aka rubuta Scentmania a jiki. Ƙamshi a take ya cika gaban motar tun ba a buɗe ba. Ya haɗe da sanyin AC sai ya bada wani irin ni’imtaccen yanayi.

    “Zamu yi waya in miki bayanin turarukan kinji. Mun kuma gode da wannan ziyara.”

    “Nima nagode sosai. Allah Ya saka muku da alkhairi.”

    Suna ta ɗagawa juna hannu aka rabu a mutumce. Daga nan kuma motar ta koma ta kurame. Taga ta zubawa idanu tana kallon gilmawar ababen hawa da fitilunsu. Taj ya kalleta yafi a ƙirga ya tabbatar da gaske shi ne bata son kulawa. Murmushi ya yi. Ya taɓa wayarsa wanda Hamdi ta gani da wutsiyar ido amma ta share.

    “Hello, Salwa…”

    Iya abin da taji ya ce kenan ta juya a fusace su ka haɗa ido. Wayar a gefe ya ajiyeta. Babu kuma wani abu da zai nuna mata wayar yake yi. Dariyar kamata ya fara sai yaga babu fuska sam. Ta tsuke baki kawai ta sake juyawa. Har wani numfashi mai nauyi ya kula tana saukewa. Gabaɗaya sai yaji ya kasa sukuni. Dama ya san za ta ji haushi. Amma ya yi zaton za ta jira bayani daga gare shi.

    “Mrs Happy”

    Shiru.

    “Hamdi” sunan nan har tafin ƙafarta take jinsa idan ya faɗa amma ko motsi bata yi ba.

    “Please ki juyo..” nan ma biris tayi dashi ” to kada ki ga laifina duk abin da ya biyo baya.”

    Gyaran murya taji ya fara ta taɓe baki. Wato zai fara yi mata daɗin bakin maza da take ji ….katse mata zancen zucin ya yi.

    “Dil ne yeh kaha hain dil se (my heart has said this to your heart)”

    “Innalillahi wa inna ilaihi raji’un. Banda waƙar India don Allah. Wallahi kunya ma nake ji. Bana son namiji yana…”

    “Mohabbat ho gayi hai tumse (I have fallen in love with you)”

    “Na shiga uku” Hamdi ta sanya hannuwanta biyu ta toshe kunnuwanta “ka bari don Allah zan saurareka.”

    “Meri jaan, mere dilbar (my life, my love).”

    “Ya Taj wasa nake. Ba ma fushi nayi ba…”

    “Mere aitbaar karlo (have faith in me)”

    “Happyyy” ta faɗi kamar tayi kuka wai yau ita ce miji yake yiwa waƙar india.

    “Jitna beqarar hoon main (how much restless I am)”

    Titi yake kallo abinsa yana sakin baiti. Ta rasa yadda zata yi dashi. Kawai sai ta kai hannuwanta ta cupping fuskarsa wanda ya sanya shi ɗauke wuta na wucin gadi.

    “Allah na haƙura.” Ta fada a hankali.

    Gefen titi ya gangara da motar ya ɗaga handbrake tare da canja giya zuwa ‘P’. Ya juyo su ka haɗa ido har lokacin bata cire hannuwanta daga fuskarsa ba.

    Shan kunu ya yi “Ki barni in ƙarasa. Ba ke nake yiwa ba.”

    Ita kuma ta marairaice masa
    “Don Allah kayi haƙuri to sai na fita.”

    Ƙwayar idanunta yake kallo sai ta rufe idon.
    “Can I have that kiss now?”

    Zame hannuwanta ta soma yi daga fuskarsa ya janyota gabaɗaya. Garin ya ɗorata a cinyarsa handbrake ya sauka. Motar ta ɗan yi gaba amma ba da sauri ba saboda giyar da ya canja. Rungume shi tayi ƙamƙam tana salati ta sanya fuskarta a tsakiyar ƙirjin shi.

    “Wayyo Allah Abbana…Yaya…”

    Bata san lokacin da ya sake tsayar da motar ba. Hannunsa đaya kawai taji a ƙasan haɓarta ya ɗago kanta sama.

    “Salwa bata da matsayi ko kaɗan a wajena kinji.” Kai ta gyaɗa a hankali.

    “Fitar da muka yi ba abin da kike tunani bane. Happiness ne yake ƙoƙarin fahimtar da ita ta haƙura.”

    “Ai na yarda.”

    “Akwai waƙa da ta dace da irin wannan yanayin.” Ya ɗage gira.

    “Kada kayi don Allah.”

    “Ke dai???”

    “Bana so.” Ta turo baki.

    “Hamdi.”

    “Na’am.” Ta ce tana mai jin nauyinsa don yaƙi sakinta balle ta koma mazauninta.

    “I love you.”

    Ƙasa ta so yi da fuskarta don kunyar yanzu tafi ko yaushe. Sai dai Taj yaci alwashin yau sai ya rage wani abu a kunyar nan ya tafi dashi gida. Shammatarta ya yi kamar zai yi magana taji saukar leɓensa akan nata. He was so gentle amma ya kashe mata jiki har ta sake narkewa a jikinsa bata sani ba. Rungumeta yayi a haka kanta a gefen kafaɗarsa kamar mai bacci. Shi kuwa wani irin contentment ya samu ds nutsuwa a zuciyarsa.

    Basu yi aune ba su ka ji ana ƙwanƙwasa gilas ḍin motar. Mutanen dake waje suna cewa ko lalacewa tayi ko kuma mai ita wani abu ya same shi. Kamar ƙifta ido Hamdi ta koma wurinta tana raba idanu. Taj ya kalli mutanen ya ga da wuya su fahimci matarsa ce idan su ka gan shi da mace. Kawai sai ya canja giya ya yi gaba. Shi da Hamdi su ka haɗa ido su ka kama dariya.

    _Uwargida….I see you! SonSo Sis Juwairiyya_
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!