Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-two
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Da farko da taji ƙarar wayar cikin baccin da ya fara ɗaukarta tsorata tayi don ta manta da ita. Niyyarta ta barta ta gama sai ta kashe, ko waye ya kira da kansa. Ita ba mai son amsa wayar mutane bace. Wani kiran ne ya sake shigowa immediately bayan na farkon ya katse. Ta daure ta wartsake idanu ta kalli sunan mai kiran SALWA B. Wani irin tunani ne ya shiga karakaina a ƙoƙon ranta. Meye ma’anar B ɗin? Bichi, Bunkure? Ba dai brother bane tunda sunan mata ne. To ko dai baby yake nufi? Ko bestie? Haba! Zuciyarta tayi wani irin kumburi ta taso mata har wuya. Harda wani ɗaci-ɗaci kamar ta tsotsi flagyl. Mantawa tayi da maganarsu da Abba a karo na biyu yau ta amsa kiran ido rufe. Garin sauri harda _record_ ta danna a rashin sani da ta mannata a kunnenta.
“Ya Taj na tasheka ko?”
Salwa tayi magana da sassanyar murya da ta sha kwaskwarima domin yin tasiri a zuciyar wanda ake yiwa.
“Ayya ba shi bane. Ya manta wayar ne.” Hamdi ma ta mayar da zuƙaƙƙiyar murya.
Ba shiri Salwa ta zabura ta tashi zaune daga kwanciyar da tayi. Da ta gama shirin yadda za ta dinga mirginawa hagu da dama saboda daɗin murya da hirar da za su yi da Taj.
Gabanta na faɗuwa ta ce “Wace ce ke?”
Tana buɗe murya normal, Hamdi ta gane wannan wayar ba ta ƴar uwa bace. In ma ƴar uwar ce to tabbas cousin ce.
“Suna na Hamdiyya.” Ta ce a kunyace “manta wayar ya yi a wajena ɗazu.”
Tsakin Salwa taji wanda ya yi mata ciwo matuƙa kafin ta ji ta ce,
“Wai ƴar gidan ɗan daudun da ya aura last week ce?”
“Laahhh, ashe kin sanni.”
Hamdi ta amsa da sauran fara’a a muryarta kamar gaske. Bata so tayi saurin kwafsawa kuma ya kasance Salwan ƴar gidansu ce.
Cikin huɗubar Mami harda kada ta ragawa yarinyar da ya aura. Tunda ance musu sakandire ta gama sun tabbatar babu wayo da wayewa a tare da ita. Tsorata ta da nuna mata ita ɗin ba komai bace zai taimaka sosai wajen samawa Salwa ƴanci idan ta shiga gidan Taj.
“Da alama kina da rawar kai. To amma ba zan hana ki ba. Lokacinki ne. Ki dai sanya a zuciyarki cewa nan ba da jimawa ba wadda ta fi ki son Taj za ta shigo rayuwarsa.”
Hanci Hamdi ta ja kamar mai shirin kuka “Anti Salwa nayi muku laifi ne har ku ke son bashi wata daga aurenmu? Ita wadda za ku bashi ɗin bana jin ta kai ni son shi. Don dai bamu haɗu bane da kema sai kin yaba min. Tarbiyya da iya kula da miji duka ɗan daudu da miskiniyar da su ka haife ni sun koya min.”
Amsar Hamdi ba ƙaramin tayar mata da hankali tayi ba. Kai tsaye ta faɗa mata magana ta rama wadda tayi mata. Tana so ta ce mata ita da kanta za ta auri Taj amma gani take faɗin hakan zubar da aji ne sai ta gimtse fuska cike da takaici.
“Ni ba ƴar gidansu bace.”
“Ikon Allah. Kuma naga ya yi saving sunanki da Sister Salwa? Cousin ɗinsa ce ke kenan?”
“Sister Salwa???” Baƙinciki ya mamaye zuciyar Salwa a lokacin da take nanata kalmar “haka ya rubuta?”
“Uhm, da capital letters.”
Tsanar Hamdi ta sake ruruwa a zuciyarta yayinda ta bata amsa.
“To ko ma dai mene ne kada ki saki jiki don ba zan zauna da kishiya ba.”
“Lahhhhhhh, ko ke ce wadda ta suma ranar aurenmu?”
Salwa ta haɗiyi yawu da ƙyar saboda jin da alama suna da yawa masoyan nasa “suma kuma? Shi ya ce miki akwai wadda ta suma a kansa?”
“Ba ke bace kenan.” Hamdi ta faɗi da rashin damuwa “Allah Sarki. Kada ki damu fa. Ni bani da matsala ko ya ce zai ƙara aure don na san a danginku dole a bashi wata. Tunda na samu na shiga sai dai in ce Allah Ya bawa mai rabo sa’a. Mu kwana lafiya.”
Katse kiran tayi ta ajiye wayar a kusa da tata tana murmushi. Za ta so ganin idanun Salwan nan. Irin yadda taji tana sauke numfashi da tana bata amsa ya kusa sanya ta dariya. Ta riga ta san mahaifinsa baya sonta. Abba kuma ya faɗa mata mahaifiyarsa tana maraba shi yasa ma ta nemi ganinta. Duk da haka ba sakin jiki zata yi ba. Dole dama ta sa rai da ganin wulaƙanci kala kala kafin ta bar musu danginsu. Ko banza dai bata bari an ƙuntata mata ba ta ce a ranta tana faɗaɗa murmushinta. Zee ta kalla tana ta sharar bacci. Ina ma idonta biyu. Yau da sun mannawa wannan cousin ɗin hauka. Don Zee dake sakandire ma ta fita sanin irin waɗannan abubuwan. Zamani na turawa, na baya suna zuwa da wayo da dabarun da waɗanda su ka gabacesu basu taɓa sani ba. Bata san lokacin da tayi bacci ba saboda yadda abin duniya ya dameta daga baya. Shin ƴan mata gare shi ko kuwa a dangi ake son aura masa daidai da shi? Zuwa gidansu jibin nan kuwa shawara me kyau ce?
Da kuka Salwa ta kwana. Ba kuma na auren Taj ba wannan karon. Yadda yarinyar da ta raina ta ɓata mata rai ba tare da ta rama ba ne yake damunta. Wai bata da matsala ko zai sake aure. Kenan ma alfarma za ta yi mata ta bari a aurota.
Ƙwafa tayi “sai zaman gidan Taj ya gagareki indai ni ce.”
***
Da Abba zai fita kamar yadda ta faɗawa Taj ta bashi wayar. Ya dubeta da kyau ganin fuskarta shar babu damuwa a tare ds ita.
“Hamdi kada ki manta da maganarmu. Bana son abu ya yi nisa Alhaji yasa a ɗora miki zawarci mai ciwo. Gara ma ace ba kya son shi zai fi miki sauƙi.”
“In sha Allahu Abba” ta faɗi tana mai sunkuyar da kai don ta san jiya dai bata wani taɓuka abin kirki ba.
“Garin yaya ya manta wayar?”
“Ina jin daga aljihunsa ta fito. Sai bayan tafiyarsa na gani.”
“To shike nan. Ki kula dai. Sai na dawo.” Tsayar da ita ya yi kafin ta koma ciki “wannan hijabin Hamdi gaskiya ko dai ki haƙura dashi ko kuma kada ki yarda wani baƙo ya ganki da shi.”
Da sauri ta kalli jikinta “Abba wani abin ya yi?”
“Ki duba madubi.”
A dawo lafiya tayi masa a soron da su ke tsaye su biyu sannan ta koma ciki. Hannu ta ɗora a ka da ta ƙarewa kanta kallo. A haka fa ta fita wurin Taj jiya. Da ta tuna an ɗauke wuta ne ma ta sami nutsuwar kama aikinta na yau. Zee ce da girki idan ta dawo daga makaranta. Ita kuma wanke wanke da shara. Halifa kuma kullum shi ne da wankin banɗakuna da sharar tsakar gida zuwa soro da harabar gidan. Duk wanda ya san gidan Abba ya shaide su da tsafta. A kansu Anti Labiba ta ƙara gane cewa babu wata ƙwaƙƙwarar alaƙa tsakanin talauci da ƙazanta. Kowanne zaman kansa yake yi.
*
Yana cire lock ɗin wayar abin da ys fara gani shi ne (save – discard) na recording call. Ya san da wuya Hamdi ta iya yin kira da wayarsa tunda yatsansa ne mabuɗin wayar. Amma wa ya kira shi ta ɗauka har su ka kwashi waɗannan mintuna suna magana? Saving ya yi sannan ya shiga call log. Nan ya tarar da missed calls ɗin Salwa kafin wanda aka ɗauka.
Da saurinsa ya nemo recording ɗin ya shige office ɗinsa ya kunna. Shi kaɗai ya dinga dariya. Hamdi bata da dama. Ta kuma burge shi. Bata cikin irin ƴan matan nan da su ke zama a taka su son rai su shiga ɗaki su yi kuka. Nishaɗi fal zuciyarsa. Salwa ce ma yaga dacewar ya taka mata burki kafin ta kai su ga ɓacin ran da wani zai ji su. Kiranta ya yi kamar tana jira ta ɗauka. Ƙin magana tayi gudun maimaicin abin da ya faru jiya. Sai da ya yi sallama ta saki rai ta amsa ta gaishe shi.
“Kin kirani jiya ashe. Hope ba matsala bace?”
“Eh wallahi.” Ta gyara zama tana murmushi “babu wata matsala. Kira nayi kawai mu gaisa. Faɗa maka tayi na kira?” Ta ƙarashe maganar a hankali.
“No, missed calls ɗinki na gani. Sai kuma naga alamun kun yi magana da Babe ɗina har na kusan five minutes. Lafiya dai ko?”
Wai Babe? Siririn tsaki tayi kuma yaji. Ba don yana son a yau ya daƙile komai nata ba da ya ajiye wayar.
“Na ce lafiya ko?”
“Naga kwana biyu baka nema na ne.”
“In ce miki me Salwa? Muna gida ɗaya nayi aure ki kasa yi min fatan alkhairi.”
Tsayar da zuciyarta tayi wurin daina kwana-kwana a kansa.
“Ohhh, wai har kana saka wannan a jerin aure Ya Taj? Ba ance babanta ɗan …”
“Yes, ɗan daudu ne a da. And one of the most wonderful people alive today. Mamanta kuma is physically challeged. Polio ya yi affecting posture ɗinta sosai.”
“Ta faɗa min jiya” ta ce don bata ga amfanin maimaitawar ba. Mutane irin waɗannan mene ne abin tinƙaho dasu? Idan iyayenta ne za ta yi bakin ƙoƙarinta wurin guje musu don ma kada ace ta san su.
“Ina sake faɗa miki duk da na fahimci kin sani ne don ki gane cewa duka waɗannan abubuwan da wasu ke gudu ni su ne su ka sa Hamdi ta zama the most special girl alive. I love her Salwa. Bana kuma son duk wani makusancina ya dinga ganin kamar wannan abu ya isa dalilin da zai rageta a matsayin mace. She is everything I want.”
“Kirana kayi ka ci min mutumci saboda ina son ka? To my face ka ke faɗa min kana son wata?” Salwa tayi magana da rawar murya.
“To your ears dai. Amma in kina so zan maimaita miki in mun haɗu. Ba ke kaɗai ba kuma, duk family ɗin Maitakalmi, babu wanda zan ragawa akan mutumcin matata.”
Iya wuya ran Salwa ya gama ɓaci. Za ta iya rantsuwa basu taɓa wata doguwar hira da Taj a waya ba idan ta kira shi kamar wannan. Saboda ƴar gwal ta kai masa gulmar wayarsu ta jiya.
“Abin da Yaya Ahmad ya ce Alhaji da bakinsa ya gaya masa wata uku ya bawa babanta ya kashe auren don ka koma gida. Na san akan mace ba za ka zaɓi dawwama a haka ba” Ta faɗi kai tsaye don da alama kukan ba zai kaita ko ina ba “Ya Taj zamu yi aure kuma za ka bani haƙuri akan wulaƙanta soyayyata.”
Ita ta fara kashe wayar ta barshi da wani irin sanyin jiki. Bai taɓa zaton yayan nasu zai ɗauki sirrinsa ya faɗawa ƙanwarsa ba. Kowa matsayinsa daban. Maganar da ko Kamal bai samu ya faɗawa ba saboda rashin lafiyarsa. Su Innarsa da Amma da sisters ɗinsa duk basu sani ba. Shi ne zai sanar da Salwa? He felt disappointed and betrayed. Tun farko abin da ya yi ta gudu game da ita kenan. Tunda baya so dole yayan nasu ya sami ɓangare guda da zai fi tausayawa. Sai ya musgunawa ɗayan kuma? Duk da haka ya ƙudurce ajiye abin a ransa har ya gano yadda aka yi taji zancen.
Bayan sun kammala wani emergency order na taro an fitar da abincin ya tafi wurin Kamal. Mutumin da kullum idan ya shiga shagon nasa har mita yake masa na rashin hutu yau a zaune ya same shi yana gyangyaɗi. Ya kan ce masa mene ne amfanin ƴan zaman shagon dake nuna kaya da waɗanda ke wurin biyan kuɗi. Shi kaɗai ya yi nan, ya yi can. Sai gashi hayaniyar kwastomas bata hana shi baccin ba. Yana zuwa hannu ya kai ya taɓa wuyansa da goshi. Abin da ya farkar da Kamal ɗin da sauri don ji ya yi kamar an ɗora masa ƙanƙara. Tsigar jikinsa har tashi tayi ya buɗe ido a firgice.
“Happiness kaji jikinka kuwa? Tashi mu koma asibiti” Taj ya ce yana kai hannu gefe ya ɗauko masa wayarsa.
Hamma Kamal ɗin yayi “bacci ne fa. Bari na shige ciki na kwanta” ya nuna nasa office ɗin.
“Kada ka raina min hankali mana. Bacci ne yake kawo zazzaɓi? Muje don Allah.”
Wasa ya mayar da maganar ya ce “Sai dai in kai ka. Dama na faɗa maka yau ɗanin motarka zanyi. A adaidaita sahu ma na taho saboda son banza.”
“In ka bari mu ka je asibiti Allah zan yarda mu yi musanye. Saboda na san kai mayenta ne na saya.”
Wani irin kallo Kamal ya yi masa. Taj is just selfless akan duk abin da ya shafi Kamal. Abubuwan da ya yi masa iyayensu basu sani ba ba za su ƙirgu ba. Ciki harda bashi jarin da ya gina boutique ɗinnan. Ya rufa masa asiri a lokacin da Alhaji ya bashi miliyan goma yaja jari. Allah Ya haɗa shi da ƴan damfara su ka wanke shi. Abu kamar rufa ido. Ya shiga ƙuncin rashin sanin yadda zai tunkari Alhajin. Kawai sai Taj ya ce ya sayar da filinsa da su ka saya tun da daɗewa. Filin da Mama take jira a fara gini. Filayen biyu su ka kama miliyan shabiyar. Ko ƙwandala Taj bai karɓa ba duk yadda ya so hakan. Ya kuma so ayi rubutu idan ya samu zai biya nan ma Taj ya ce kyauta ce. Baya fatan har abada a sake tada zancen.
“Tashi mana”
Muryar Taj ta dawo dashi daga duniyar tunani. Miƙewa ya yi cikin dauriya ya ce masa mura ke son kama shi. Shi yasa yake zazzaɓin.
“Ni kuwa sai nake ganin kamar kana ɓoye min wani abu Happiness. Kwanakin nan kamar fa baka nan. Komai ni kaɗai nake yi.”
“You are married Happy. Ya kamata mu fara rage wasu abubuwan. Da banyi tunanin ba sai da Abba ya ankarar dani.”
Taj ya taɓe baki “yanzu zancen Mal. Sule har wani abin ɗauka ne?”
“Ai kuwa dai ya fi mu gaskiya. Nan gaba kaɗan sai kaji ana Malama hide my ID. Brother ɗin mijina kullum suna tare. Ko unguwa zamu sai ya kira ɗan uwansa. Bamu da wani lokaci irin na mata da miji saboda ya kankane komai. Don Allah a bani shawarar yadda zan ɓullo musu ba tare da mijin nawa yaji haushi ba.”
Dariya sosai Taj ya yi.
“Kamal mai malaman ig. Wato har salon tura saƙon ka iya. Daɗinta dai ba Hamdi bace za ta yi wannan. Daga ji Doctor ce ta fara ƙorafi. Tell her I’ll make myself scarce in kun yi aure. Ayi soyayya lafiya.”
Daga nan sai zolayat juna. Kamal ya dage va zai je asibiti ba wai yunwa ma yake ji. Cikin Happy Taj su ka koma. Kamal ya yi odar shinkafa da gasasshen kifi. Kamar yadda Taj ya koyo, yawancin abincim Asia duk da hannu ake ci. Masu zuwa ko sun so gayu suna fara ci sai kaga an yi yadda yake a hoto da bidiyo da suke a lungu da saƙon wajen ana ci da hannu hankali kwance.
“Kawo masa kaza” Taj ya ce da waiter ɗin.
“Ban gane ba. Ka dai sanni da kifi ko?”
Wani article Taj ya nuna masa sannan ya tura masa a waya. A ciki anyi bayanin yawancin abincin dake kawo allergy. Akwai gyaɗa da dangoginta. Kifi, kayan da aka sarrafa daga madara, ƙwai, kantu da kayan fulawa.
“Za ka daina cin duka. A hankali sai mu dinga gwada ɗaya muna gani. Wanda a kansa reaction ɗinka ya dawo kaga mun san shi ne. Nima zan daina ci don ma kada ka ce mugunta na shirya maka.”
Yawun bakin Kamal ɗaukewa yayi. Ya shiga damuwa amma dole ya mayar da ita dariya. Sam baya jindaɗin ɓoye ɓoyen nan. Amma yanzu da zarar sun sani ƙarshen duk wani farinciki na gidansu ya ƙare. Baya son ya zama silar daina walwalar kowa akan lafiyar da kuɗi kawai ba za su iya saya masa ba.
Abincin da yake masa ɗanɗanobda magani saboda rashin jindaɗin abin da yake yi ya dinga tutturawa harma yafi Taj ci.
***
Office ɗin an rubuta Dr. Kubra Hayatu a jiki. Wani private asibiti ne mai tashe na mata da yara da su ka buɗe ita da ƙawayenta biyu. Wurin yana samon mutane fiye da zato saboda ƙwarewar aikinsu musamman akan mata. Zaune take tana harhaɗa wasu takardu kafin ta fita don ta gama shift ɗinta taji bugu a bakin ƙofar. Umarnin shigowa ta bayar inda wani matashi ya shigo ya gaisheta. Ƙaramin kwali da aka yi wrapping ya miƙa mata.
“Ban sayi komai ba. Bana tsammanin delivery.” Ta ce masa.
“Ance na wani Kamaluddeen Hayatu ne amma ke ake so ki fara gani.”
“Wa ya aiko ka?” Ta tashi tsaye.
“Idan kin duba ciki za ki gane. A tashi lafiya”
Fita ya yi kafin ta sake yin magana. Ta ɗauki kwalin taji babu nauyi sai ɗan girma. Ta jijjiga taji abu kamar magani. Buɗewa tayi da sauri sauri. Sunayen magungunan da hotunan dake jiki su ka sa ta kusa yanke jiki ta faɗi.
“Kamal? Innalillahi wa inna ilaihi raji’un.”
Waya ta ɗauka za ta kira Alhaji. Har ta shiga sai tayi saurin katse kiran. Duk yadda aka yi likitarsa ce ta turo saƙon. Kuma da alama hakan yana nufin tana son ganawa da ita domin tayi mata bayanin da ya dace. Kiran Alhajin ne ya biyo bayan nata. Ta ɗaga wayar a firgice.
“Doctor yaya? Haihuwar Nabila (ƙanwarta mai ciki) ce ta tashi?”
“A’a Alhaji. Kira nayi mu gaisa kuma sai network ya katse kiran.”
Kwantar da hankali ya yi su ka taɓa hira sannan ta tashi. Kao tsaye asibitin da Kamal ya kwanta ta nufa. Aka sanar da ita Dr. Mubina sai litinin za ta zo. Nambar wayarta ta nema a reception ɗin aka sanar da ita bata ƙasar ne. Ta tafi Ghana amma ranar lahadi za ta dawo. Haka nan ta tafi cike da zulumi da fatan gaggawar zuwan litinin ɗin.
***
Wato ƴan gidan Alh. Hayatu gwanaye ne wajen son shagali. Duk abin da zai sa su taru a gida komai ƙanƙantarsa basa raina shi. Daga su har ƴaƴansu. To iyayen ma dai ba a barsu a baya ba.
Akan maganar zuwan Hamdi sai ka rantse bikin ne ya taso. Mama ce ta kira Yaya ta nemi izini tunda har yanzu a gida take. Bayan sun gaisa ta gabatar mata da kanta.
“Suna na Haj. A’i kuma Mama a gida.”
“Allah Sarki Hajiya. Da fatan kuna lafiya.”
Da jindaɗin yadda Yaya ta tarbeta Mama ta ce “Alhamdulillahi. Allah Yasa Taj ya yi muku ɗan bayanin gidan namu.”
“Sosai. Ya ce Hamdi surukarki ce ke da ɗayar maman tashi ta Abuja.”
“Ƙwarai kuwa. To muna bada haƙuri tunda mace ita ya kamata a bi. Yanayin gidan namu ne Masha Allah. Muna da yawan da in muka zo za sai ƴan unguwa sun fara tunanin ko biki ake baki gayyace su ba.”
Yaya ta kama dariya. Da alama barkwancinsu Taj ba a ƙasa su ka ɗauka ba.
“Allah da gaske. Shi yasa mu ka ce gara ta zo. Kuma dai idan zuwan zamu yi Inna ba za ta bi mu ba. Ai kin san wacce ce Inna a cikinmu ko?”
Yaya tayi murmushi “na gane.”
Mama ma dariyar tayi “tunda anyi auren ya dace mu san juna ko yaya ne. Ina fatan zuwan nata babu takura.”
“Wace irin takura kuma ku da abar ikonku? In Taj cewa yayi ta tafi kenan ai sai dai mu bita da addu’a.”
Da girmamawa gami da mutuntawa su ka gama magana. Taj zai ɗaukota bayan azahar.
***
Abba ya yi mamakin shigowa gida ya sami Yaya ta taƙarƙare tana gogewa Hamdi jiki da ragowar dilkan Sajida.
“Allah ƙadiran ala mayyasha’u. Khadijatul Kubra yau ke ce da wannan aikin? Lallai Sajida rakiya tayo a gidan nan ga ƴar so nan kin saka a gaba” ya kalli Zee dake gefe tana fifita garwashi “kema ƴar rakiyar ce ko za ayi miki?”
Kunya ta kama Yaya ta tashi ta koma cikin falo. Hamdi da Zee su ka yi ta dariya. Da ƙyar Hamdi ta yarda ake yi mata. Wai cikin mutane za ta je. Bata son a rainata ta. Zee ma nata kwaɓin yana gefe. Ita kuma sai yau Baballe zai zo. Cinikin motoci ya kai shi Kwatano tun bayan auren. Yaya ta ce gara a ga ƴaƴan nata a yanayin da duk hassadar mutum sai dai ya kushe a zuci. Sai gashi Abba na sakota a gaba ta gudu.
Falon ya bita “dawo ki cigaba da kankareta kada mijin ya zo a barshi jira.”
“Kankara kuma don Allah kamar wata faso?” Ta faɗi tana ƴar harararsa cikin wasa.
Ƴaƴan da irin wannan abu ba baƙonsu bane su ka tattara su ka barsu a falon. Zee ce taƙarasa mata ita kuma ta yiwa Zee ɗin.
“Wai amma gyaran jiki kamar za a kai mu yau?” Cewar Zee da su ka sanya turaren wuta cikin lulluɓin ƙaton zani kowacce ta zauna akan kujera.
“Ke dai muyi kawai in ba kin shiryawa mitar Yaya ba. In taji haushi sai ta hanamu zuwa gidan Ya Sajida gobe.”
“Kin tambaya ma kuwa kamar yadda ta ce? Ni fa na rasa ma me zan ce. Haka kawai yanzu shige ds fice na sai in bin wani bayan a gidanmu nake” cewar Zee.
“Na ma manta da tambayar. Zan dai gwada. In na kasa in rubuta a text.” Shawarar ta yiwa Zee. Ita ma a text ɗin za ta rubuta.
Suna idar da sallar azahar Yaya ta umarci Hamdi da yin wanka ta shirya. Jinkirin fita na ɗaya daga cikin abubuwan dake saurin kawo saɓani tsakanin ma’aurata. Ita dai nata to ne. Tana kaffa kaffa don sun gama shirya irin dabdalar da za su yi gobe da Sajida. Ga tanadin hira da neman shawara kowacce tana son ji daga babbar yaya.
*
Biyu da kwata Taj ya iso. Ƙememe Kamal yaƙi rako shi. Har cewa ya yi to wa zai shiga da ita gidan tunda shi a waje zai tsaya. Kamal ya ce masa in sun iso ya kira shi. Haka nan ya tafi yana mita. Sai da Hamdi ta fito ya shiga shi masa albarka.
Yana zaune a falo yana zubawa Yaya santin kunun ayanta da duk sanda zai zo sai ya nema tayi sallama. Ya juya a hankali su ka yi sa’ar haɗa ido. Da ido kawai ake gani lallausar shaddar da ya saka wadda aka yiwa ɗinki irin na matasan zamani. Ruwan toka ne kamar kullum an ƙaranta adon. Very classy and elegant. Bai saka hula ba sai gyaran fuska da ya yi.
Ita kuwa cikin ɗinkunansu na bikin Sajida ne ta saka guda da ya kamata su sa ranar ɗaurin aure. Riga da siket ne mai adon ja da shuɗi mara turowa ne a jiki sai baƙi. Fuskarta yau ya fara ganinta da kwalliya irin wannan. Light make up. Komai cikin tsari babu hayaniya. Tayi ɗaurinta a karkace kaɗan ta ɗora shuɗin mayafi daga rabin ɗanƙwalin. Hannuta da lallen biki ya fara tafiya ta sanyawa abin hannu a ɗaya. Ɗayan kuma agogo ne na silver.
“Gara ku tashi kada yamma ta same ku ko?” Yaya ta ce da taga kallon yaƙi ƙarewa. Taj ya ma manta inda yake da alama. Ita kuma Hamdi sai juya awarwaro take.
Da ya fita ta fara binsa sai taji kamar ta zura da gudu. Tsoro ya shigeta har zuciyata tana gudun famfalaƙi. Bakin wata mota da duk rashin sanin motocinta ta san wannan ta kai duk inda ake so ta kai. A idonta dai jeep ce tunda tana da tudu. Fara ƙal da tambarin BMW a jiki.
Buɗe mata ya yi ta shiga sai ta daina ganin hasken rana sosai. Gilasan masu duhu ta kalla ta ƙara jin wannan tsoron. Ƙamshin daɗin da motar take fitarwa zai iya mantar da mutum a ina yake. Taj na zama a mazaunin direba ta kama kanta. Ɗan waigen ƙauyancin ya ƙare. Ya tada motar ya kunna AC sannan ya fara ribas.
“Ɗan tsaya.”
Hamdi ta faɗi tana ɗora hannu a ƙirji.
Burki ya taka da hanzari “Me ya same ki?”
Idanunta har sun tara ƙwalla ta ce “Gabana ke faɗuwa wallahi.”
“Saboda me? Haɗuwa da ƴan gidanmu?”
Ta girgiza kai da dukkan gaskiyarta ta nuna shi.
Yana son honesty ɗinta. Juya kan motar yayi domin su hau titi ya ce
“Kin dai san ko ina satar mutane ba zan saci jinin Abbana ba ko?”
Tana jindaɗin yadda yake girmama mahaifinta sosai. Amma da yake bakin baya shiru sai cewa tayi “na sani ko ka fara yau. Ka zo da mota a rurrufe ba a gano ciki ta waje.”
“Ƴar ƙauye zan ce miki ko matsoraciya? Amfanin wannan tint ɗin ga irinmu shi ne yanzu misali idan naji ya kamata…” ɗauke ido ya yi daga titi su ka kalli juna.
“Ya kamata me?”
“Will you let me kiss you idan mun dawo? Ko yanzu in sami wurin parking?”
“Ya Taj???” Idanunta su ka firfito.
“Na’am. Ashe kin san suna na. Na zata Salman Khan za ki ce. Har na tanadi waƙarsa da zan miki.” Ya yi maganar yana dariya.
Bakin tsiwa ya mutu murus. Ya ɗan kalleta yaga hannuwanta kawai take kallo. Shi da ya tsammaci ta bashi amsa.
“Hamdi? Yaya? Zazzaɓin ne yau ma?”
“Uhmm” ta gyaɗa kai harda shafa wuya da goshi.
“Ki ce in tanadi maganin maleriya da thypoid ranar da za ki tare kawai.”
“Allah da gaske nake. Jikina babu ƙwari ma.” Ta ɗaga hannu ta sake shi yaraf.
“Kinga mun kusa zuwa gidan. Ki rufa min asiri yanzu don za ki haɗu da ƴan jarida masu tambayar tsiya. Akwai ƴan bugun ciki ma waɗanda za ki iya faɗa musu duk hirar da muka yi yanzu ba tare da kin sani ba.”
A tsorace ta ce “da gaske?”
“Da wasa” ya furta a hankali yana yi mata murmushi.
A bakin gate ɗin wani ƙaton gida taga sun tsaya. Ya ɗaga waya ya kira Kamal ya ce masa sun iso.
Tsoron nan bai barta ba ta ce “ba za ka shiga ba?”
“Alhaji bai yi min izini ba.” Ya amsa mata da murya mai rauni.
Tausayinsa ya mamaye zuciyarta har taji kamar tayi masa kuka.
“Kada ki ɓata min kwalliyar nan tun kafin na biya kuɗinta don Allah.”
“Ni ba don kai nayi ba” ta ce da tsiwar nan.
“Mala’iku suna jin ki dai.”
Da sauri ta ce “Astagfirullah.”
Bata ankara ba ya yi abin da tun shigowarta motar yake muradin yi. Hannunta mafi kusa dashi ya kama ya sarƙe yatsun ya lanƙwashe su.
“Wa ki ka yiwa kwalliyar? Suna ji dai kada ki manta.”
Tsuke baki tayi tana jin yadda ɗumin hannunsa ke shigarta. Ita kam ta shiga uku. Wannan aure ta son ya ɗore….Allah na tuba ta faɗi a zuci.
“Hamdi?” Ya ɗan matsa hannun.
“Kai na yiwa” murmushi ya soma yi ta ƙara da cewa “amma dai Yaya ce ta tilasta min nayi.”
“Allah Ya biya Ya mafificin alkhairi. Now can I ki…”
Bata bari ya gama magana ba ta sanya hannu ta toshe masa baki.
“Kaga fa Ya Kamal ya fito.” Ta kalli gate ɗin a firgice.
Dariya ta bashi ya cire hannun nata ya riƙe shi da ɗaya hannun.
“Idan ya ƙaraso sai na ce ya tayani roƙonki. Kinga fa a waje za ki barni for God knows how long.”
Kamal har ya ƙaraso. Ƙwanƙwasa gilas ya yi ta ɓangaren Taj. Shi kuma ya zuge gilas ɗin ƙasa.
“Happiness taƙi yi min sallama kamar bata san iyakata nan ba. In ta shiga ciki sai sanda suka ga damar sako min ita.”
Sunkuyar da kai tayi don har lokacin hannuwanta suna cikin nasa. Tana ja yana sake riƙewa.
Kamal dariya yayi kawai “Mrs Happy haka za mu yi dake?”
“Shi za ka zaɓa?”
“Da me kike tunani? Ya zaɓeki a kaina?”
“Naga wai ni ce ƙarama” tayi kicin kicin da fuska.
A take Kamal ya canja sheƙa.
“Happy buɗe mata. In ka kaita gida sai ku yi sallamar a can.”
“To wallahi tayi alƙawari a gabanka” Taj ya sha kunu da ya yi maganar.
“Ki yi mu shiga kinji. Su Umma ke su ke jira.”
“Nayi.” Ta faɗa don idanun ƴan uwan su biyu sun hanata sakat.
Sama Taj ya yi da gilas ɗin ya kai hannunta guda bakinsa ya sumbata. Hamdi ta rasa inda za ta tsoma ranta don kunya.
“Gidanmu ba irin wanda ki ka saba bane Hamdi. Duk inda ake da yawa komai is possible. Don Allah idan an ɓata miki rai ki fara faɗa min kafin su Abba. Zan baki haƙuri a madadin ko waye. Kin ji?”
Murmushi tayi har zuci. Ta ɗan matsa hannunsa dake cikin nata sannan ta fita.
Kamal na buɗe gate da su ka shiga ciki taji wata murya da ta so ta gane tana yi masa magana.
“Ya Kamal basu iso bane?”
Hamdi ta bi inda ya kalla da ido. Budurwa ta gani tayi kwalliya ta fitar hankali. Tayi kyau tamkar wata amarya.
“Salwa? Saukar yaushe?” Ya ce babu wani jindaɗi a tare da tambayar.
“Ɗazun nan na iso. Ina zuwa gidan kuma naga Anti Zahra za ta taho wai yau amaryar Ya Taj za ta zo gaishe da su Hajiya.”
“Gata ku gaisa.” Ya faɗi yana kallon yadda shigarta gabaɗaya ta saɓawa sanin da ya yi mata a baya.
“Sannu amarya.” Ta ce tana yin gaba “bari naje na taya Ya Taj hira kafin ku fito.”
Kashewa Hamdi ido tayi wanda Kamal bai lura ba. Ta wuce su ta buɗe ƙaramar ƙofar gate ɗin ta fita. Komai ya nemi tsayawa Hamdi da ta tuna yadda su ka yi a waya. Sai da Kamal ya kirata sau biyu taji ta bi bayansa tana tunanin hanyar da zata bi ta nunawa Salwa tayi kuskuren shiga gonarta.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
