Rayuwa Da Gibi – Chapter Twenty-one
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Na ɗan taƙin lokaci ƙwaƙwalwarsa ta so ƙullewa har ma ya faɗi abin da bai yi niyya ba. Cikin sa’a sai ya tuno abin da ya tanadi faɗawa duk wanda ya ganshi a wannan yanayin. Murmushi ya yi mata sannan ya ɗaga hannuwa da ƙafafunsa yadda za ta gansu sosai.
“Mene ne wannan Kamal? Me ya same ka kake irin wannan kumburin?” Ta ƙarasa inda yake tana tattaɓa shi.
“Allergy ne Umma. A haka ma kumburin ya sauka sosai.”
“Subhanallahi” ta matsa hannunsa na dama “akwai zafi?”
Kai ya girgiza mata. Ya zauna ya shirga mata bayanin ƙanzon kurege wai allergy gare shi kuma har yanzu likitan bai gano mene ne jikin nasa baya so ba.
“Anya ya san aikinsa kuwa? Me yasa baka je wurin yayarka ba?”
Gaban Kamal ya faɗi da tsoron kada Umma ta matsa masa akan zuwa wajen Yaya Kubra. Ita ce babba wajen Mama kuma sananniyar likitar ɓangaren lalurorin mata. Yana zuwa wajenta asirinsa zai tono.
“Ita da take gynae? Wannan ba ɓangarenta bane.”
“Amma ai ba za ta kasa sanin likitan da ya dace da kai ba a asibitin Malam (AKTHA) ko? Ni dai bari nayi mata waya. Wannan kumburin ya bani tsoro. Har wani baƙi naga kayi.”
“Kai Umma, idonki ne.” Ya wayance.
Da ƙyar ya hanata kiran yayar tasu. Ya tabbatar mata likitan da yake gani ma ƙwararre ne. Harkar allergy wani zubin sai an wahala kafin a gano mene ne jiki baya so har yake reacting irin haka. Baiwar Allah sai ta yarda da zancen nasa. Ta kira masa Abba ta ce ya zo ya kai shi asibiti.
“Amma me ya sa ka ɓoye mana? Jiya ina kallonka kafin ku fita wajen sirikin Taj da Innarku ka shige kitchen ka watsa magani. Kuma yau kowa ya ce bai sanyaka a ido ba. Shi ne tsoro ya kamani. Ko ƙwaya ka fara sha.”
Halin ciwon da yake ciki bai hana shi dariya ba.
“Abin da ban yi da ƙuruciya ba Umma?”
“Yo Allah na tuba shaye shaye lokaci gare shi? Kai dai kawai Allah Ya kare ku da sauran zuri’ar musulmi. Zamanin ya zo da hanyoyin ɓata tatbiyar tsofaffi balle kuma matasa masu jini a jika.”
Tunaninsa na yadda zai je wajen likitarsa cikin sauƙi ya sami solution. Umma ta sa Abba ya kai shi asibitin. A hanya kafin ya ƙarasa ya tura mata saƙo ta bashi amsa. Roƙonta ya yi da sirranta lalurarsa a gaban Abba.
Da taimakon Abba ya iya shiga asibitin. Dauriya da ƙarfinsa sun soma ƙarewa. Wata Nos tana ganinsu ta hanzarta kiran likitar wadda dalilinsa ma ta fito don yau ranar hutunta ce.
Wata kyakkyawar matashiya ce ta fito sanye da baƙar abaya da ƙaramin hijab. A fuskarta gilashi ne mai ɗan kauri dake taimakawa ganinta. Madaidaicin tsayi gareta amma kuma she is a bit chubby. Sai dai ƙibar ba mai yawa bace. Ɗakin taimakon gaggawa tasa aka shigar mata da Kamal aka kwantar akan gado.
Abba ya gama tsorata da yanayinsa. Yana ganin ta farke sirinji cikin sauri ya ce “Doctor kinga jikin nasa duk ya rikice kafin mu ƙaraso. Don Allah ki gane mene ne ba ya so sai mu kiyaye.”
“Ɗan bamu wuri” ta ce idanunta akan Kamal. Patient ɗinta mai ɗan banzan taurin kai.
Hankali a tashe Abba ya fita. Ya shiga fareti a wajen yana addu’ar a shawo kan matsalar da wuri.
Yana fita Mubina ta rufe ƙofar emergency ɗin ta shiga bawa Kamal taimakon da ya kamata. Kimanin minti talatin kafin jikin nasa ya fara daidaita. Ya buɗe ido a hankali ya sauka cikin nata.
Ranta a ɓace yake sosai. Kallon da tayi masa ya sanya shi murmushi. Ya đaga hannunsa guda ba wanda take yi masa ƙarin ruwa ba ya kama kunnensa.
“Sorry.”
“Ya kake so nayi da kai? Ni a rayuwata babu abin da na tsana kamar ɓoye ɓoye.”
Ya ɗage gira ɗaya “a taƙaice dai kin tsaneni.”
Shan kunu tayi “ban ce ba.”
“Don Allah ki yi haƙuri.” Ya tashi zaune “Zan iya tafiya?”
“Jikin naka…”
Sallama aka yi, kafin ta amsa Alhaji ya turo ƙofar ta buɗe gabaɗaya su ka shigo tare da Abba. Kai idan kaga fuskar shi sai ya baka tsoro. Hannuwan babbar rigarsa sun sauko amma yau ya manta da wani matsayi. Ɗansa kawai yake son gani.
“Me ya same ka?” Ya kalli Dr. Mubina “Doctor me ya same shi?”
Kamal bai bari tayi magana ba don ya kula ganin Alhaji ya kiɗima ta.
“Allergy ne Alhaji.”
“Kai ne likitan?” Ya sake dubanta idanunsa na daɗa firgita ta “ina jin ki.”
“Allergy ne kamar yadda ya ce.”
“To an gano mene ne jikin nasa baya so domin a kiyaye?”
“A’a, muna dai kan…”
Kafaɗarsa Alhaji ya riƙe “Kai tashi. Visar ina da ina gareka yanzu da ba su ƙare ba?”
Mubina taga yadda bakinsa ya kasa tattaro amsa saboda sanin kafiyar Alhajin.
“Don Allah ka ɗan ƙara mana lokaci Alhaji. Lifestyle changes muke ta gwadawa. In sha Allah a hankali zamu gane trigger ɗin.”
“A hankali fa ki ka ce doctor. Jira zan yi har sai wani mummunan abu ya same shi?”
“Kayi haƙuri. Rashin bamu dama yana daga cikin abubuwan da ke sa a dinga ganin kamar bamu san aikinmu ba.”
Yadda ta tare shi kai tsaye ta bashi wannan amsa sai ya sanya shi murmushi. Yana son mutane masu confidence.
“Ya sunanki ne?”
“Mubina…Mubina Sa’id Kibiya.”
Fuskar Alhaji washewa tayi. Shi ne harda dariya irin tasu ta manya.
“Ikon Allah. Ke ƴar wajen Marigayi Dr. Sa’id ce?” Ta gyaɗa kai a hankali “kai masha Allah. Ƙasar nan ba ƙaramin rashi tayi ba. Arewa tayi rashin jajirtaccen likita. Allah Ya masa rahama.”
Idanun Mubina da ƴar ƙwalla ta ce “amin.”
Sakin jiki Alhaji ya yi su ka gama magana ya ce ya bata damar yiwa Kamal dukkan abin da ya dace domin samun sauƙinsa. Ya ƙara da cewa baya so ta sallame shi a yau. A kumbure gaɓoɓinsa su ke duk da a haka Abba ya ce wai ya saɓe. Fita su ka yi da Abban zai raka shi. Kamal kuma Mubina ta ce lallai ya koma ya kwanta.
“Ai dole na. Idan na koma gida yau ba za mu ƙare da daɗi ba.”
“Gaskiya yana son ka.” Ta faɗi tana murmushin yadda uban ya nuna kulawarsa akansa.
“Ai baki ga komai ba. Sai ƴarsa na labour room ake gane waye Alhaji. Wallahi in dai ba baya gari ba da shi ake zaman asibiti daga lokacin da yaji an tafi haihuwar har a fito da baby.”
“Kun ji daɗi. Shi ne kake ɓoye masa halin da kake ciki?”
“Duk tsaurinsa yana da mugun rauni akan ƴaƴa. Sanin matsalata alhalin babu abin da zai iya yi min damunsa kawai zai yi.”
Haƙura Mubina tayi. Ta kula da indai izinin Kamal take jira babu wani cigaba da za a samu wajen binciken sama masa waraka. Zaɓi guda ya rage mata. Za kuma tayi amfani dashi in sha Allahu.
Bata tashi ƙara sanin wane irin gida ya fito ba sai da taga matan gidansu da ƴan uwansa suna ta tururuwar shigowa. Ɗakin ba ma zai ɗauki rabinsu ba domin kuwa harda jikoki. Wannan yasa ta tunani akan hanyarta ta gida. Yanzu a ce duk yawan nan nasu babu wanda jininsa da na Kamal ya zo daidai?
***
Taj bai tashi sanin a asibiti Kamal ya kwana ba sai da safe. Da fari ya yi niyyar komawa gidan Amma domin su gaisa da Daddy. Sai ga wayar Naja tana sanar dashi labarin da ta samu daga gida. Ya duba wayarsa babu wanda ya kira shi. Jinjina kai ya yi ya ɗauki jakarsa ya fita. Allah Ya taimake shi bai haɗu da ɓacin rana ba. Jirgin ya tashi akan lokaci. Kai tsaye asibitin ya wuce daga airport. Ya samu ana ta rikici a bakin ƙofa tsakanin wata nos da ƴan uwansu mata. Ta tare ƙofar ta hana mutum biyar shiga. Na ciki su bakwai su ma tayi tayi sun ƙi fitowa. Ana ƙorafin sun yi yawa a ɗakin, su kuma sun ce babu wanda ya isa yasa su fita daga wajen ɗan uwansu.
“Ga wani ma nan ya shigo. Shi daga wani garin ma yake.” Autar gidan ta faɗi a tsiwace.
“To ko ma dai waye zuwa za ku yi ku fita. Idan ba haka ba zan sanar da na gaba dani. Doka ce ba a son a wuce mutum uku a ɗakin mara lafiya.” Nos ɗin ta ce da takaicin waɗannan mutane. Bakiɗayansu kamar masu kan dutse. An rasa mai lallaɓata ta haƙura ko kuma yasa baki su fita.
Wata ma cewa tayi “ku sallame shi mana. Muma yayarmu likita ce. Allah na tuba don dai ƙarin ruwa da allura wanne ne ba za ta iya ba?”
Ran Nos ɗinnan ya ɓaci matuƙa. Idan an zo ita za a yiwa faɗan barinsu a ɗakin. Da taga Taj ne ma ta ɗan saki rai. Ta san dai duk yadda za ayi namiji daban yake da mata.
“Kai ma ɗan gidansu ne?”
Caraf wata mai tsohon ciki ta ce “Baki ga kama da mara lafiyan ba?”
“Don Allah ka faɗa musu su ragu. A bakin aikina nake. In kowa bai min magana ba wallahi likitarsa sai tayi. Ta ce baya buƙatar hayaniya.”
“Ya Taj barni da ita. So take ta nuna mana ta fi mu son ɗan uwanmu. Ba fa surutu zamu yi ba.”
Kamal ba jin an ambaci Taj ya yi hamdala. Shi ma sun ƙi sauraronsa. Kansa har ya fara ciwo. A tunaninsu allergy ɗin ne shi yasa su ka dage. Basu san halin da yake ciki magana ma dauriya kawai yake yi ba.
“Happy. Don Allah kasa su bi dokar asibitin. Ni kaina doctor ɗin ba za ta barni ba idan ta gansu.”
Nos dai tana jin sunan da aka kira Taj daga waje da wanda mara lafiyan nan ya kira shi, bata san lokacin da ta ce “Happy Taj? Kai ne mai HappyTaj don Allah?”
Ƴan bani na iyan gidan Alh. Hayatu ne su ka amsa mata. Harda mai cewa da ta ɗauka su ɗin local mutane ne take son wulaƙanta su.
“A bakin aikina nake.” Ta nanata musu.
Da laluma da rarrashi Taj ya samu su ka bi tsarin asibitin. Da mutum bibbiyu aka dinga shiga ana fita. Nos ɗin tayi masa godiya bayan kowa ya tafi ta barshi ya shiga shi kaɗai. Abin mamaki yana zama ya kira sunan Kamal sai yaji shiru. Ɗaga kansa ke da wuya yaga ashe bacci ne ya ɗauke shi. Saurin bacci ba ɗabi’ar Kamal bace. Kuma bai fi minti biyar da raka ƴan uwansa waje ba don ya tabbatar sun tafi. Ya yi tsammanin zai dawo su yi hira ma tunda yaga kamar jikin da sauƙi. Hankalinsa sai bai kwanta ba. Anya allergy ne kawai? To ko kuma allurar bacci aka yi masa? Shi kaɗai ya dinga saƙe saƙe a ransa har Mubina ta shigo.
Haɗuwar farko ta jinjinawa soyayyar dake tsakanin ƴan uwan biyu. Lokacin Kamal ya tashi har Taj ya bashi labarin yadda su ka yi a Abuja. Ya ɗora da mitar me yasa ya zama na ƙarshen sanin bashi da lafiya. Cacar bakinsu su ka yi aka daidaita. Sai ga Kamal kamar ba shi ba. Jikinsa ma yayi ƙwari sannan kumburin duk ya sauka.
“Zan sallameka amma akwai magunguna da zan sabunta maka. Don Allah kada kayi wasa dasu.”
Tashi Taj ya yi ya ce “Idan akwai a pharmacy ɗinku ki bani na siyo kafin mu tafi.”
“A’a ka barshi kawai” in ji Kamal
“Ba duka za a samu ba.” Ita kuma ta ce da sauri.
Murmushi Taj ya yi, amma a zuciyarsa yaji rashin yarda dasu. Zargin nasa bai sami ɗorewa ba da yaga da gaske Mubina wata kulawa ta musamman take bawa Kamal. Daɗi ya kama shi. Wannan karon da alama za a dace, Kamal zai daina gudun matan da yaga yana yi.
“Bari na baku wuri ku ƙarasa maganan. Na san ba komai na patient ya kamata wasu su ji ba.”
“Har akwai abin da ya shafeni wanda bai kamata kaji ba?” Kamal ya faɗi yana ɗauke kai daga hararar da Mubina take masa.
“In ta faɗa ka sanar dani. Bari na duba ko Bishir ya zo.”
Ficewa ya yi ya barsu. Mubina ta sami sakewar ƙara sanar dashi dokokin da ya kamata ya kiyaye.
“Me yasa ya fita?”
“Ya zata akwai wani abu tsakaninmu. Bai san ni yanzu soyayya ko sadakarta aka bani zan mayarwa mai ita ba.”
Murmushin zuci kawai Mubina tayi. In zai ɓoyewa kowa ita ba zai yaudareta ba. Tana da saurin karantar mutane. Tun farkon zuwan Kamal asibitin ta fahimci ya kamu da sonta. Sai dai bayan ya gama faɗa mata alamomin ciwonsa da aka yi gwaji ta sanar dashi lalurar shikenan komai nasa ya sauya. Soyayyar da take gani ƙuruƙuru ta koma yaƙin neman lafiya. Da ya gane da wuya lafiyar ta samu sai ya zama mai mugun sadaukarwa ga duk wanda yake mu’amala dasu. Musamman wannan ɗan uwan nasa Taj. A halin da ake ciki za ta cigaba da adana soyayyarta ta mayar da hankali wurin ganin ya sami lafiya. Bata son ta bari komai ya shiga tsakanin aikinta a kan samun sauƙinsa.
***
Bayan kwana biyu da sallamar Kamal ya wartsake har ya koma shagonsa. Sai lokacin Taj ya sami sukuni da nutsuwa a ransa. Kullum yana tunanin Hamdi amma damuwar Kamal ta ishe shi. Daɗinsa ɗaya da ya koma gidan Ahmad Salwa ta tafi Bauchi. Hankalinsa kwance ya soma fafutukar neman gida don Inna ta faɗa masa bikinsa ba zai ɗauki lokaci ba. Yawancin fitar da Abba su ke yi ko Bishir. Bai fiye neman Kamal ɗin ba saboda yana ganin hutu ya kamace shi ba taya shi neman gida ba. A cikin kwanakin kullum yana waya da Abba. Abban ya so zuwa duba Kamal amma da ta tuna yadda su ka yi Alhaji sai ya haƙura kawai ya kira shi. Yaya har fushi tayi. Ta nuna masa rashin dacewar hakan. Shi dai haƙuri ya bata da ƴan dabarun wayo har ta daina zancen.
Yau alhamis ta kama kwana shida da ɗaurin aurensa. Ya sami sabon gida a sharaɗa self-contain daidai me sabon aure. Mama ce ta bashi shawarar kada ya ce sai ƙaton gida. Gara ya mayar da hankali wajen gina filin da su ka saya shi da Kamal shekara biyu da su ka wuce.
Shirye shiryen biki yana ta kankama. Iyayen basu saka rana ba sai sun ci ƙarfin shirinsu. Masu haɗa lefe su Yaya Hajiyayye kuma an taso Taj a gaba ya kawo size ɗin underwear ɗin Hamdi. Ya gama zille zillensa ta biyo shi har office a Happy Taj ta saka shi a gaba.
“Kirawota a gabana ka tambaya.”
“Na ce miki fa zan tambaya yau ɗinnan na turo miki.”
“Ai na gaji da gafara sa. Kai ko irin abinnan na angwaye da an ɗaura aure su fara damun amarya da fitina da alama baka iya ba”
Kunya kamar ya fice ya bar mata office ɗin.
“Haba Yaya Hajiyayye. Sai kace wani ɗan is**. Kunyarki ma ta kama ni.”
Dariya tayi sannan ta ce “Ka kira yanzu nima jirana ake yi in faɗa.”
Ido ya zaro “wa da wa za ki faɗawa? Wannan ai tonon silili ne. Kowa sai ya san girmanta saboda Allah? Sirri ne fa.” Ya yi kicin kicin da fuska.
Yaya Hajiyayye me zata yi kuwa banda dariya.
“Sirri manya. Ba dai naji ance weekend za ka kaiwa su Hajiya ita ba? Tana cire mayafi zan aunata tas da ido wallahi.”
“Zan fasa kawota.”
“Ka ma isa?”
“To umarnin zan bata kada ta yarda ta cire mayafi…kai, hijab ma za ta saka.”
“Kayi ka gama. Telan da zai yi mata ɗinkunan biki ma ranar zai zo aunata.” Ta ce tana kallon idanunsa.
“Tela kuma?” Ya ambata kamar yau ya fara jin kalmar “Dama har yanzu ana wannan jahilcin Yaya? Na zata yanzu mata ke auna kansu su bawa telan idan ma namiji ne.”
Ganin ta same shi a hannu ta cigaba da kunna shi.
“Ɗinkunan maza ai sun fi na mata kyau. Sun san duk wani lungu da saƙo da za su auna saboda shape ya fito.”
Abu ya yi tsamari. Taj harda gumi don takaicin yadda idanunsa ke nuna masa Hamdi a gaban wani ƙato yana gwadata. Mantawa ya yi da girman yayar tasa ya ce,
“Wannan dai kafurci ne ƙaɗa’an. Kamar ba a zuwa islamiyya a garin nan?”
Ta gimtse dariyarta da ƙyar “mu ne kafiran kuma yau Taj?”
“Allah Ya baki haƙuri” ya ce yana kumbure kumbure.
Dariyar da take dannewa sai da ta fito. Tayi mai isarta ta ce to lallai a yau ɗinnan take so ya tura mata kafin ƙanwarsu da ta tafi UK da mijinta ta dawo nan da kwana uku.
Tunda ta tafi yake tunanin yadda zai tambayi Hamdi. A ganinsa mai baki amma yana da kunya. Ga amaryar tasa ita ma gwanar tsiwa. Ƙarshenta daga tambaya ta fassara shi.
*
A unguwar tasu ya yi Isha tare da Abba. Ya jira shi ya sanar da Yaya zuwansa sannan ya shiga su ka gaisa.
“Kwana biyu mun tada kai tsaye. Naji kana ta yawon neman gida.”
“Yiwa kai ne Yaya.”
Abba ta kalla don bata daina fushin zuwa dubiya ba “Kamal bai yi fushi damu ba ko?”
Shi da ya san komai a bakin Zee ya riga ya fahimci Abba tsoron zuwa yake kada su haɗu da Alhaji. Nuna mata ya yi babu komai tunda ba jimawa ya yi ba. Kwana ɗaya ne.
“Allah Ya ƙara masa lafiya.” Ta tashi ta ce “Me za ka ci a ɗora maka? Yau abincin ana magariba da kowa ya ci aka bayar saboda zafi. Abbanku kuma ya ce a ƙoshe yake bamu ajiye masa ba.”
Shi da ba wata surukuta yake yi da su ba sai cewa ya yi zai ci indomie. Abba ya miƙe saboda sabo zai tafi kitchen ɗin.
“Girkin matarsa zai ci. Don Allah zo ka tafi ka watsa ruwa ka huta.”
“Au…haka ne fa” ya furta yana jin kamar ya faɗawa Yaya gaskiya. Baya son su fara jindaɗin kasancewa tare bayan ya san auren ba mai ɗorewa bane.
Dariya su ka bawa Taj. Yaya ta ce ya jira yanzu za ta turo Hamdi.
*
Tana jin takun Yaya ta gyara filo ta kwanta. Dama tunda taji muryarsa ta san sai an nemeta. Ba kuma son ganinsa take yi ba. Abubuwa uku ke damunta. Haushin abin da Alhajinsa ya yiwa mahaifinta da wa’adin da ya basu, sai kuma rashin nemanta da ya yi na tsayin kwanakin nan. Na ƙarshe kuwa kewarsa ce da ta mantar da ita rashin son girkin da yake yi. Ranar da taji Kamal ne babu lafiya dai tayi masa uzuri amma sai taƙi kiransa ta kira Kamal ɗin.
“Tashi kafin ranki ya ɓaci.” Yaya ta kai mata duka a cinya. Ta tashi tana sosa wurin.
“Kina fa da zafin hannu Yaya.”
“Wuce ki ɗan gyara fuskarki ki je ki dafawa Taj indomie.”
“Indomie kuma? Ba ya iya dafawa ba? Ya tafi gidansu mana.” Ta turo baki.
Hannu Yaya ta kai za ta ɗalle bakin ta gudu.
“Bana son rashin ɗa’a Hamdi. Kuma saura idan kin je ki kasa gaishe shi. Mara kunya kawai.”
Yaya na fita tayi saurin cire kayanta ta saka riga da wando na bacci ta ɗora hijabin da ya wuce gwiwarta kaɗan. Fita ta zo yi Zee ta kama kiran Yaya.
“Zo kiga a yadda za ta fita.”
Saurin rufe mata baki tayi “gulma dai haramun. Ina ruwanki?”
“Babu ruwana amma dai a matsayina na mai jin maganar iyaye zan so ƴar uwata ma tayi hakan.”
Harara kawai ta gallawa Zee ɗin. Ta koma gaban ɗan madubinsu ta fesa body spray sannan ta shafa hoda da man leɓe. Dama niya tayi taje masa tana hamma ta ce bacci take ji.
“To uwar iya…haka yayi ko kuwa sai na cire hijabin?”
“Da yafi bada citta don wallahi har laɓe sai nayi muku.”
Hamdi ta tafa hannuwa “gulmawiya, shi yasa naga kin yi saving sunan Baballe da Sadiq a wayarki? Wato ɗan zuwan nan da yake yawan yi har ya kwance miki hadda. Kin manta kukan bakya so ɗin da ki ke yi.”
Zee taji kunya sosai. Sai ta cije don Hamdi ba za ta rabu da ita da wuri ba.
“So muke mu rigaku haihuwar da Ya Taj ya ce ku za ku fara yi.”
“Na shiga uku. Zee zancen haihuwa yayi miki? Da wa zai haihun?”
Zee ta ƙyalƙyale da dariya “Hamdiyya Habib mana”
Tana faɗin haka ta fice daga ɗakin. Hamdi ta gama jimamin maganar ta fito da ƙudurin fara cika umarnin Abba. Za ta cigaba da nunawa Taj bata son girki da ma wasu abubuwan da take jin za su taimaka wurin ɓata masa rai.
*
Danna waya yake su na chatting da abokinsa Wakili da su ka yi karatu tare a Indiya ta shigo. Sallamar nan ciki-ciki da gaisuwar.
Taj ya yi kamar bai ji ba yaƙi amsawa. Sai da ta shigo cikin falon ya ɗaga kai ya kalleta.
“A dinga sallama ƴan mata.”
Ta juya idanu “Ai nayi.”
“Banji ba.” Ya faɗi lokaci guda ya shagala da kallonta. A garajen fitowarta hijabi ruwan madara ta saka mara kauri. Da kaɗan ya wuce babu a jikinta. Rikita masa lissafi yaga tana neman yi ya wayance da cewa “ba za ki iya sallamar bane in tafi?”
Ta turo bakin nan “to Assalam alaikum.”
“To wa alaikum salam.”
“Guda nawa kake ci?”
“Me?”
“Indomie ɗin mana.”
“Oh, ki kimanta.” Ya gyara zama abinsa.
Tana son tambayarsa ko me da me za ta saka a ciki amma bata son yawaita yi masa magana. Fita tayi ya ajiye wayar da dama amfaninta rage masa kallon ƙurillar da yake yi mata.
Ita kaɗai ta kama tsaki da ta tuna yanzu ƙila fa duk yadda za ta dafa zai ji bata yi ba saboda sabo da girki. Yanke shawarar yinta normal kawai tayi. Ta ɗauko attaruhu da albasa za tayi grating amma bata san gejin cin yajinsa ba. Ƙarshe dai guda biyu ta saka da ƙaramar albasa. Ta raba jajjagen biyu sai taga kamar yayi yawa. Kaɗan ta saka ta dafa indomie ɗin dashi. Sai ta kuma soya wani da curry da ɗan maggi cikin mai daidai suyar ƙwai. Yana fara ƙamshi ta juye ƙwai uku da ta kaɗa a kai. Ƙamshinsa har falo. Ta kawo cucumber ta yanka rabi a zagaye ta jera a gefen plate ɗin mai ɗan zurfi kaɗan ta tsakiya. Indomie ɗin tana ƙarasawa da sauran ruwa mara yawa ta juye sannan ta rufe kanta da ƙwan. Yadda bata son ci da sanyi shi yasa tayi gaggawar kai masa.
Tana ajiye tray ɗin ana ɗauke wuta. Taj ya kunna torchlight ɗin wayarsa ya hasketa tayi saurin rufe ido.
“Hamdi da zuciya ɗaya kika dafa min dai ko?”
“Me ka gani?”
“Wuta aka ɗauke. Kin san mu a India yanzun nan sai mu fassara abu.”
Murmushi tayi don ta fara gano tsokanarta yake da zancen Indiyan nan.
“To Shah Rukh Khan. Da me ka fassara ɗauke wutar?”
Taj ya haɗiye abincin da ya kai bakinsa ya ce “Da lokacin waƙa cikin duhun dare mana. Muna bin bango muna rawa.”
Toshe bakinta tayi ta kama dariya. Abin nasa azimun. Wai bin bango. Ganin ya tsura mata idanu amma bai fasa cin abincin ba shi ne ta ce.
“Bin bango kamar wasu ƙadangaru.”
“Kin ci sa’a yunwa nake ji da na tashi na gwada miki yadda ake yi.”
“Bana ma son sani” ta zare wayar fitila daga inda aka jona chaji ta kunna. A take haske ya wadata a falon. Ta buɗe fridge ta ɗauko ruwan sanyi ta ɗauko da kunun ayan da Yaya ta haɗa da rana.
Ta kawo gabansa ta ajiye a gefen tray ɗin sannan taje ta kawo kofuna guda biyu ta dire masa. Kujerar nesa dashi taje ta zauna
“Nagode” ya ce bayan ya gama. Abincin kaɗan ya rage.
Hamdi ta kalle shi da wutsiyar ido “banlbu daɗi ko? Ba irin haka ka saba dafawa ba?”
“Ke dai ki ce kina son in yaba miki. To nayi. Yayi min daɗi sosai.”
Bata yarda dashi ba “duk iya girkinka?”
“Girkina daban, na matata Hamdiyya ma daban. Zan dinga taimaka miki a kitchen amma ba kullum ba. Ina son in dawo gida kamar kowane namiji in ci abincin da matar gidan ta dafa.”
Yana lura da yadda maganarsa tayi mata daɗi. Ba dai ta son nunawa ne. Shi kuwa indai tana da kunnuwa to ba zai fasa faɗin maganganun da za su yi tasiri a zuciyarta ba. Tashi yayi ita ma ta miƙe.
“Bari na ƙarasa gida na huta kuma.”
Tray ɗin ta duƙa ta ɗauka ya ce “na faɗawa Yaya ranar asabar zan zo mu je gidanmu.”
“Gidanmu ko gidanku?” Ta ce a tsorace.
“Saurin me kike yi? Gidan iyayena ba gidana ni da ke da ƴaƴanmu ba”
Ya ƙare maganar yana kashe mata ido.
“Sai da safe” tayi masa fuskar shanu. Hira dashi tana yi mata daɗi amma biyewa zuciya ganganci ne.
“Oh, don Allah ɗauko min underwear ɗinki na sama da na ƙasa ana son ganin size.”
Tray ɗin hannunta ta kusa saki da taji me ya ce. Bata ankara ba taji hannuwansa sun damƙi nata. A karo na biyu su ka ji wannan yanayin da ya bambanta da in sun taɓa kowa. Zame nata hannun tayi ta bar masa tray ɗin.
Taj ya ce “yauwa yi sauri. Kuma don Allah wankakku.”
Wata uwar harara da ta banka masa ba shiri ya ajiye tray ɗin a inda ta ɗauka.
“Ai gaskiya ce. Naji an ce ƴan mata maimaici su ke na sati biyu ko ma fi kafin su wanke.”
Kamar za tayi kuka ta ce “Don sharri? To ba zan bayar ba. Idan ma bokanka ne yake so kace masa na hana. Ya turo aljanu su satar masa.”
“Dare ne dai kuma babu wuta. Ki cigaba da kiraye kirayen abubuwa. In su ka zo…” ya faɗi a hankali yadda zancen zai shigeta.
Ai kuwa bayanta ta kalla da sauri ta ɗan matso kusa dashi. Tausayi ta bashi. Duk tayi wiƙi wiƙi da idanu.
“Yayata ce ta ce na tambayeki fa.”
“Size ake tambaya ai. Ya za ka ce in baka?” Hamdi ta ce da mamakin irin nasa tunanin.
“Don kada ki faɗa min ba daidai ba. Nafi son komai accurate.”
“To ba zan bayar ba. Ka kamanta yadda ya dace.” Ta ɗora hannuwa a ƙugu.
Taj ya san bata da masaniyar shigar da tayi. Da bata yi wannan tsayuwar a gabansa ba.
“Don’t dare me Hamdi. In ki ka yi wasa da hannuna zan kamanta.”
Da sauri ta koma bakin ƙofar falon har tana tuntuɓe saboda gigitar kalamansa.
“Matsoraciya.”
“Naji.”
“Za ki turo size ɗin ko in sa Zee ta ɗauko min na tafi dasu?”
Zai aika ta sani yanzu. Tunda ya iya faɗa mata zasu riga haihuwa ai komai ma is possible yanzu.
“Zan turo.” Ta ce a hankali.
“Good girl. Sai jibin ko?”
Kada azo tafiya ya ce su biyu kaɗai shi yasa ta ce masa da Zee za su je. Shi kuma ya ce a’a don yanzu matar aure ce. Sai ta ce to da Halifa.
“Haka kawai sai in ɗauke ki da ƙato a mota?”
Hamdi ta ɓata rai “Halifan ne ƙato?”
“Yanzu duk duniya daga Abba sai ni sai Alhajina ne kaɗai normal maza a wajenki. Sauran kowa ƙato ne.”
“Kaima ƙaton ne kuwa.”
“Mijin ƙatuwa ba.”
Dariya yake yi da yayi maganar. Sai gata tana murmushi. Fushi dashi ma da alama ɓacin lokaci ne. Sai da safe ya yi mata ya tafi. Ta tattare kwanukan ta tafi kitchen tana wankewa hirarsu na dawo mata. Da ta gama gidan tsit yayi mata. Yau ko inji Halifa bai fito ya kunna ba da aka ɗauke wuta. Bata san Yaya ce ta hana ba. Wai ƙarar za ta dami Taj.
Ƙaramin table ɗin da ta ɗora masa tray taje ɗaukewa sai taga wayarsa. Ta ɗaga ta juyata a hannunta. Dole masu iphone su ke jin kansu. Wayar a hannu ma daban take. Abba ta yanke shawarar bawa da safe don da alama yau sun yi baccin wuri.
Kimanin rabin awa da tafiyarsa taga kira daga wani suna an sa Anti Zahra. Sai da aka kira na biyu sannan ta ɗauka. Muryarsa taji ta saki ranta. Ya ce ta ajiye wayar zai zo ya karɓa washegari.
“Zan bawa Abba ya taho maka da ita.”
“To nagode. Goodnight.”
*
Famfo iya famfo Mami ta yiwa Salwa. Tunda ta koma gida da ramar kwana biyu amma kamar tayi jinya hankalin Mamin ya tashi. Ta kira Ahmad ta ƙare masa tanadi. Harda kiransa wanda baya kishinta.
“Aure kuma tunda tana so ko uban naku bai isa ya hana ba.”
“Mami kin fi so ta kai kanta inda ba a sonta? A ƙarshe ta dinga fuskantar wulaƙanci.”
“Rufe min baki. Matan gidanku sun gama cinye maka zuciya baka iya taɓuka komai. Arziƙin Taj kai kana da rabinsa ne?”
“Kowa rabonsa yake ci Mami. Don Allah ki daina biyewa Salwa.”
Cikin faɗa tayi masa tsawa “Salwa za ta dawo. Ina so ka yiwa Alhajin naku maganarta don na san yana ƙaunarta. Ita wadda Taj ɗin ya aura na riga na samu bayani akanta. Bata da wani abin nunawa balle ta kara da jinina.”
Ta inda take shiga daban da inda take fita. Ran Ahmad ya gama ɓaci da su ka gama wayar. Yana jiran dawowarta ya nuna mata kuskuren sanya Mami tayi masa irin wannan faɗan.
Bayan Mami ta gama dashi kan Salwan ta koma tana yi mata nata faɗan na rashin ɗaukar shawararta. Kissa ba ƙaramar makami bace a wajen mata.
“Ki bari sai kamar shaɗayan dare ki kira shi ki gigita shi da kalamai masu daɗi.”
Sunkuyar da kai tayi tana murmushi.
“Ki nuna masa yafi kowanne namiji ba tare da kin zubar da ajinki ba.”
Sai da ta gama kwasar huɗuba sannan ta shige ɗaki. Ta gama komai da wuri ta zauna jira. Shaɗaya da kwata na dare kuwa ta doka kira wayar Taj.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
