Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    Bayan sallar asuba Taj ya kira Kamal domin su yi sallama. Jiya basu sami haɗuwa a gida ba. Ya yi ta waya shiru Kamal ɗin bai ɗauka ba. Wanka ya yi ya gama shiri da sauri ya sake duba wayar. Abin mamaki Kamal bai bi kiran nasa ba. Da wahala hakan ke faruwa. Jikinsa sai ya bashi ko ba ƙalau ba. Abba ƙaninsa ya kira ko tunawa da lokaci bai yi ba.

    “Happiness ya fito sallar asuba kuwa?”

    Abba ya ɗan wartsake idanu “ya fito amma yau ya riga kowa baro masallacin. Saƙo ne?”

    “Ɗan leƙa min shi please.”

    Abba baya son fita don bacci ne sosai a idonsa ya ce “Ya Taj ya dai kamata ku rage wayar asubar nan. Kai kayi aure, idan shi ma ya yi wallahi za ku dinga samun matsala da matanku.”

    “Za ka tashi ko kuwa?” Taj ya ɗan ɗaga murya da ƙoƙarinsa na ɓoye yadda ya damu.

    Yana jin ƙunƙunin Abba har ya isa ƙofar ɗakin Kamal. Sallama ya haɗa da ƙwanƙwasawa.

    Da ƙyar Kamal ya iya buɗe jajayen idanunsa da su ka kumbura kamar wanda ya kwana yana kuka. Jikinsa gabaɗaya ciwo yake yi. Kansa kamar ana sara guduma saboda azabar ciwo.

    “Waye?” Muryarsa ta fito a dusashe.

    “Ya Taj ke nemanka.” Abba ya faɗa yana saita bakinsa da ƙofar yadda za a ji da kyau “na sanar dashi. Can I go back to bed now?”

    “Thanks” Taj ya ce da kulawa.

    Wayar Kamal ya sake nema. Yadda yaji muryarsa ya tayar masa da hankali. Amma Kamal ɗin ya tabbatar masa da mura ce ta kama shi da zazzaɓi.

    “Allah Ya ƙara sauƙi. Ko na bar tafiyar yau muje asibiti?” Hamdi ce ta faɗo masa ya yi murmushi.

    “Ka tafi kafin Amma ta sauka a garin nan duk mu shiga tara.”

    “Don Allah ka je asibiti dai. Bana so ana raina mura da zazzaɓi. Ciwukan gaske ne.”

    “To doctor.” Kamal ya zolaye shi.

    Suna gama wayar ya ɗauki ƴar jakarsa ta goyo (backpack) wadda ya sanya duka abubuwan buƙatarsa a ciki. Ƙananan kaya ya saka ya koma matashi sosai. Haramar tafiya ya yi sai ya tuna yadda Kamal ya damu kada Ahmad yaji babu daɗi akan halin da Salwa ke ciki. Lokaci ya duba akwai đan saura. Ya fito falo ya kira wayar Ahmad ɗin.

    “Yaya na shirya zan tafi.”

    Ahmad ya miƙe da sauri. Dama bai koma bacci ba tun sallar asuba.

    “Bari na zo na kai ka airport.”

    “Ka barshi. Zan sami adaidaita sahu.”

    Fitowa Ahmad ɗin ya yi. Su ka gaisa sannan ya miƙa masa key ɗin motar Kamal.

    “Incase ban sami dawowa akan lokaci ba, ina sa rai jibi motata za ta iso. In bawa mutumin numbarka sai ya kawota nan ya ajiye?”

    “Da ina zai kai?” Cewar Ahmad yana zura muƙullin a aljihun wando.

    Zama Taj ya yi ya buƙaci yin magana da shi na mintuna kaɗan.

    “Yaya akan Salwa ne.”

    Ahmad ya ɗan ɓata rai “ka cire lamarin yarinyar nan daga gabanka ka fuskanci matsalolinka.”

    “A’a Yaya. Idan da kara nima ƙanwata ce. Ba kuma zan so ta shiga irin wannan yanayin akan wani ba.”

    “Shin ka taɓa yi mata magana ko nuna mata alamun soyayya ne?”

    Ya kaɗa kai da sauri “a’a.”

    “To ka gani. Rigima ce kawai irin ta ta. Tun abin nata bai yi nisa ba na bata shawara taƙi ji. Ya take so ayi mata? Ana forcing soyayya ne?”

    Taj dai duk nauyin yayan nasa yake ji. Sai yanzu ya gane manufar Kamal.

    “Duk da haka ni dai ka rarrasheta. Allah Ya bata wanda ya fini. Mafi alkhairi.”

    “Kada ka damu. Dama a gidansu babanta ya yi mata miji. Amma kaga don fitina taƙi komawa gida. Wai tana jiran service kuma.”

    Dariya su ka yi su biyun. Ahmad ya kwantar masa da hankali. Da ace soyayya su ke yi yanzu ya gujeta shi ne zai zama rashin kyautawa. Amma tunda hakan bata taɓa faruwa ba babu mai ɗora masa laifi. Ahmad ya sako jallabiya ya kai shi airport tunda jirgin sassafe zai bi.

    *

    Yadda Amma taga rana jiya haka taga dare. Wajajen ƙarfe biyar ta sami labarin auren Taj daga wajen matar ɗaya daga cikin ƴan uwanta. Ba don shekaru ba da tabbas ƙaryata ta za ta yi. Ta dai daure su ka gama wayar. Yaya Babba ta fara kira ya ce mata haka ne. Ji tayi tamkar an kwaɗa mata guduma. Taj ya yi aure bata sani ba. Kuma har dare bai kira ba. Haka ta ƙarasa wunin ranar cike da fargabar kada mutan gidan su ji.

    Da taga Allah Ya taimaketa har bayan Isha babu wanda ya ce komai shi ne Daddy na gama cin abinci ta ce masa tana son zuwa Kano gobe.

    Kamar Anti jira take ta shigo falon a lokacin “Hummm, Maman Ihsan kenan. Kin gaji da ɓoye ɓoyen?”

    Gabanta faɗuwa ya yi amma ta dake.
    “Ɓoyo kuma? Wani abin ne ya faru?”

    “Kada ki raina min hankali mana. Za ki ce ba da saninki Taj ya yi aure bane? Ko kin zata bamu sani ba?”

    Anti ta faɗi da matuƙar ɓacin rai. Taci burin suruka da shi saboda ya haɗa dukkan abin so. Kyau, kuɗi, suna da kuma kyawawan ɗabi’u. Idan Anisa ta sami miji irinsa ta wuce raini a wurin kowa. A dangi ma sai an dinga bata girma na musamman.

    “Yadda ki ka ji maganar nan nima haka na ji ta. Kuma dalilinta nake son zuwa Kanon ma kenan. Babu wanda ya neme ni. Sai aure kawai naji.”

    “Ai in duk jikina kunne ne ni ba zan yarda ba. Yaudara ce dai an yiwa ƴata.”

    Ran Amma ya soma ɓaci ta ce “Ita Anisan ce ta ce ya yaudare ta?”

    Hankali kwance Daddy ya gama cin abincinsa sannan ya tsawatar musu.

    “Idan kuma ban isa daku ba sai ku fita ku ƙarasa.”

    Amma kwantar da murya tayi ta bashi haƙuri sannan tayi masa bayanin rashin sanin auren.

    “Idan haka ne kuwa kema bai mutuntaki ba. Kuma ya nuna bai san alkhairi ba.”

    Wani irin kallo Amma ta yiwa Anti. Bata son cigaba da rigima a daren nan amma take taken Antin so ta a cigaba da maganar har Hajja ta ji.

    Daddy sallamarsu ya yi akan su bar zancen zuwa washegari. Anti na fita ta koma ɗakinta inda ta sami Anisa a zaune da waya a hannu. Zuciya ta raya mata Taj take kira ƙila yaƙi ɗauka. Ai kuwa ta tashi ta nufi ɗakin Hajja tana kuka ta karanta mata ƙarya da gaskiya. Wani abin idan ta faɗa sai Anisa ta riƙe baki don mamakin yadda uwa take yanko ƙarya bisa son zuciya.

    “Damuwata yanzu yadda ta saka shi a ranta.”

    “Anti don Allah ki daina kuka. Ni wallahi na haƙura.”

    “Ai ba ke ki ka ce kina son sa ba tun farko balle haƙuri ko rashinsa ya zama a hannunki.” Hajja ta faɗi cikin fushi tana duban Anisa “har ni Jamila za ta yiwa haka? Maza kirawo min ita.”

    Cin mutumci babu irin wanda Hajja bata yiwa Amma ba. Da Daddy ya shigar mata shi ma ta haɗa dashi ta ƙare musu tas. Yau har gorin haihuwa biyu kacal sai da aka yi mata.

    “Saboda shegen son kuɗi da koyi da rayuwar nasara ki ka tsayar da ƙwayayen haihuwarki. Gashi nan wanda ki ka ɗauko a dangin ya nuna miki shi ba ɗan goyo bane. Don na tabbata da sahalewar ubansa ya yi auren.”

    Allah Yasa ita ɗin ma ba ƙyalle bace. Da maganganun su ka isheta fita tayi daga ɗakin. Hajja ta ce dama ta rainasu daga ita har mijin. Banda haka bai kamata tana yi mata magana ta fita ba.

    A wannan halin dai aka kwana ranar. Gidan duka babu daɗi. Anisa kanta ta sha kuka saboda ta dogara da cewa ko don alkunyar abin da gidansu su ka yiwa Taj, ba zai taɓa tsallake aurenta ba. Shi yasa da baya yi mata zancen soyayya bata wani damu ba. Aure ne dai za ayi kamar yadda Hajja ta alƙawarta mata.

    Da safe ma gidan babu wata walwala. Kowa kai kawo yake kamar ana tura shi. Ga tafiya Kanon da Amma ta so yi Hajja ta hana Daddy yi mata izini.

    *

    Taxi Taj ya shiga har gidan. Maigadi ya riga ya san shi saboda haka ba a tsaya sanar da mutanen ciki ba ya buɗe masa gate. Agogo ya kalla da ya isa ƙofar shiga gidan. Goma da rabi ta ɗan wuce. Sanin ba Amma bace kaɗai a ciki dole ya sanar da zuwansa don ayi masa izinin shiga. Wayarta ya kira tana gani ta taɓe baki, ɓacin ranta ya dawo sabo. Har kiran ya katse bata ɗauka ba. Ya kira yafi sau shida kafin ta daure ta amsa.

    “Ina jin ka.” Ta ce a kausashe duk da wani ɓangare na zuciyarta yaji daɗi. Ta tabbata tana ransa tunda ya yi asubancin zuwa gareta.

    Ya san za a rina. Ya kwantar da kai ya faɗa mata yana bakin ƙofa.

    “Yau kuma gidan sirikinka ne da ba za ka shigo ba?”

    “A’a, dama saboda naga safiya ce…”

    “Bana son gulma. Shigo ina falona.”

    “Tuba nake Amma.” Ya faɗi yana buɗe ƙofar.

    Abin da ya guda ne ya faru. Anisa da ƙannenta duka ya samu a falon suna breakfast kowacce da kayan bacci. Ba abin ya koma ba ya riga ya sako kai. Ɗauke ido ya yi daga kallonsu ya yi musu sallama. Aka rasa mai amsawa don kishi su ke taya yayarsu, sai ita Anisan. Mai binta ta banka mata harara. Ƙaramar kuma ta ja dogon tsaki.

    “Aikin banza.”

    Ko kallonsu bai yi ba ya wuce falon Amma. Uzurin ƙuruciya ya yi musu kawai. Kuma dai abin kunya ne ya biye musu. Yana ji suna ta tsaki. Ita kuma Anisa tana yi musu faɗan basu kyauta ba. Yana wucewa su ka yi rige rigen sanarwa Hajja da Anti zuwansa.

    A zaune ya tarar da Amma. Ita ma ko wanka bata yi ba. Komai nata a hargitse saboda rashin kwanciyar hankali.

    Jikinsa a sanyaye ya ajiye jakarsa a ƙasa ya zauna a gaban ƙafafunta.
    “Don Girman Allah Amma ki yi haƙuri. Wallahi ba da gangan nayi ba.”

    Rai na ƙuna ta ce “Kayi ne saboda ka nuna min irin nawa matsayin a wajenka?”

    “Ban isa ba wallahi. A gaggauce komai ya faru.”

    “Bayan ya faru ɗin kuma sai ka manta sunan da ka sanya min a wayarka balle ka kira ko? Haba Taj. Aure fa kayi. Nayi zaton ina sahun gaba cikin waɗanda ya kamata su sani ko da wacce irin gaggawa ya zo maka.”

    Shi ma ya san bai kyauta ba. A daren da Alhaji ya yi masa izinin auren ya dace ya gaggauta kiranta. Sai gargaɗin Alhajin ya tsaya masa a rai. Shi ya hana shi faɗawa su Inna. Idan ya kira Amma ya tabbata sai ta faɗawa su Inna. Ita ɗin sam bata tsoron Alhaji. Akan Taj ma sai ta ƙure take yi masa magana. Gudun kada ta ɓallo masa ruwa yasa shi kama bakin nasa. Bai ƙara tunawa ba kuma sai bayan sun kama hanyar gida da Kamal. Duka wannan bayanin babu lallai ita ko wani ya đauke shi a matsayin uzuri. Kawai ya yarda bai kyauta ba, ya bata haƙuri shi ne mafi a’ala.

    “Don Allah ki yafe min. Ki kuma saurari bayani na ko da ba zai gamsar dake ba.”

    “Baka da abin da za ka faɗa min Taj. Ka koma gaban iyayenka tunda dama na san burinka kenan. A nawa tunanin dai ko me zai faru ba za ka manta dani ba.” Tayi maganar da ƙwalla a idanunta.

    “Har yanzu Alhaji bai sakko ba. Su Hajiya ma basu san da auren ba sai bayan an ɗaura. Ke kuma gani nayi bai dace ba ace ta waya na fađa miki.”

    “Ban yi fushi ba. Ka dai koma Kanon tunda ka zama mijin aure. Allah Ya baku zaman lafiya.” Ta miƙe.

    “Amma ki yafe min mana don Allah.”

    “Ai nace raina bai ɓaci ba. In an tashi bikin ka daure dai ka faɗawa ƴan uwanka su Ihsan.”

    Da yaga dai rarrashin ba zai yiwu ba sai ya marairaice mata.

    “Amma na baki haƙuri kin ƙi. Ina son yi miki bayanin yadda auren ya zo ma ba ki son ji. So ki ke dole ki nuna min ni ba ɗanki bane. Banda haka ai ko gudun kada auren yaƙi albarka za ki sassauta min.” Hawaye yaga ta goge, ta kalle shi a raunane ya cigaba da magana “haihuwata ce fa kawai baki yi ba amma ina ji a jikina ko tsine min ki ka yi sai ta bi ni.”

    “Tsinuwar lafiya Taj? Kada na kuma jin wannan kalmar a bakinka.”

    Ya sake kwantar da murya “To ya kike so nayi? Fushinki ba zai barni naga hasken rayuwa ba.”

    “Allah Ya tsareka Taj. Zauna mu yi magana” ta ce a rikice. Bata son ganinsa a yanayi irin wannan ko kaɗan.

    Daga bayansu su ka ji muryar Hajja da basu san tun yaushe take tsaye a bakin ƙofar ba tana cewa.

    “Shegen baki kamar rainon cikin gari. Na rasa me yasa ba a taɓa cin galabarka a magana.” Ta nuna Amma “ke kuma da ya soma kalallameki sai ki bada kai bori ya hau. Da ɗan cikinki ne ya yi min haka wallahi ba zan masa da sauƙi ba. Ɗan riƙo dama ai ba ɗan goyo ba. Kayan aro bai taɓa rufe katara.”

    Bayan Hajja ashe harda Anti da su Anisa. Daddy ne kaɗai basu iya zuwa kai wa rahoton zuwan Taj ba.

    ‘Duk zan iya da ku’ Taj ya faɗi a ransa. Ya je bakin ƙofar ya riƙo hannun Hajja ya zo ya zaunar da ita.

    “Na ɗauka ko me zai same ni a waje idan na shigo gidan nan Hajja zan sami kwanciyar hankali. A wurin ɗanki na sami baban da bai taɓa ƙyamar sana’ata ko goranta min don mahaifina ya kore ni ba.”

    “Shi ne ka kasa yi masa alfarmar auren ƴarsa ba. Ko don ba Jamila ta haifeta ba?”

    Taj ya girgiza kai “kinga inda matsalar take ko? Komai nayi sai kun fassara saboda baku ɗaukeni ɗa ba. Da ace Daddy ne ya haifeni hukunci kawai za ku yi min da faɗa akan laifina na. Ba sai anyi ta zancen asalina ba.”

    Duk fushin Hajja bata san lokacin da tayi murmushi ba “Tajo kenan. Wannan baki dai ba na ubanka bane. Shi banda haɗe rai bai iya komai.”

    “Baki taɓa zuwa bayan magariba bane. Da har dariyar Alhajinmu sai kin ji.”

    “Wa yaga tarangahoma. Dariyar Hayatu ai tsorata mutane za ta yi.”

    Taj ya yi murmushi “wallahi Hajja ke kaɗai za ki taɓa min tsohona in share saboda kin isa. Kaka na ɗauke ki ba surukar Amma ba.”

    Kwashewa tayi da dariya. Ta bar Anti da Amma da mamaki.

    “Ɗan duniya. To ka gama kalallame mu. Sai ka faɗa min inda maganar ƙanwarka ta kwana tunda naji ance mahaifin amaryar ɗan daudu ne.”

    A take fuskarsa ta canja da furucin Hajja. Ta kalli Amma da mamakinta ya fi na Anti.

    “Kada ku ce min baku san ɗan daudu bane baban nata?”

    Amma ta kalli Taj tana neman ƙarin bayani a tsorace.

    Ɓoye ɓoye dama can ba halinsa bane. Balle kuma yanzu da ya riga ya yi aure. In ya rufe yau anjima ko gobe magana za ta fito. Saboda haka a taƙaice ya labarta musu yana aiki da Abba da kuma abin da ya faru lokacin auren Sajida har zuwa jiyan.

    “A taƙaice dai ba auren soyayya bane. Yarinya mai asali girɓatacce irin wannan dama sai dai auren alfarma.” Cewar Anti.

    Hajja kuwa cewa tayi “kakarta ce kawai ta yanke saƙa. Wannan kishi da ita ma ɓata lokaci ne Anisa. Kawai ki sa a ranki ke kaɗai ce.”

    “A’a fa Hajja” Taj ya katse musu hanzari kafin a kai matakin da zai faɗi baƙa.

    “A’a me?”

    “Ina sonta.”

    “Taj” Amma ta kira shi don ta san hali.

    “Am serious Amma. Ina roƙonku don Allah kada a sake tada zancen mahaifinta ko yanayin auren. Nema nayi ba bani aka yi ba. Please” ya kallesu ɗaya bayan ɗaya.

    For once sai jikin Hajja ya yi sanyi. Magiya Taj yake amma irin wadda mai yinta yake fata da tsananin burin samun biyan buƙata.

    Tashi Hajja tayi ba tare da tayi magana ba. Ta dai ƙarewa Taj kallo sai taji babu adalci idan ta cigaba da sanya shi a kwana.

    “Ina ɗan uwanka Kamalu”

    Taj ya dubeta girarsa a cure “yana gida.”

    “Idan ka koma ka ce ina nemansa. Shi sai ya zo su daidaita da Anisa idan bashi da wata.”

    “Hajja!!!”

    Anisa, Taj da Anti su ka kirata lokaci guda. Ta taɓe baki.

    “Ku bar Hayatu da halinsa. Ban taɓa ganin wanda Allah Ya azurta da iyali masu kyakkyawar mu’amala da ɗabi’a kamar nasa ba. Shi yasa nake kwaɗayin haɗa zuri’a dashi ba wani abu ba.”

    Bata jira jin me za su ce ba ta fita. Anti ma fita tayi da niyyar yiwa Daddy magana. Bata maraba da tumbling ɗin ƴarta da Hajja take yi. Ita ma Anisa bayansu ta bi. Sai dai kafin ta fita ta tsaya tayi masa magana.

    “Allah Ya sanya alkhairi Ya Taj.”

    “Nagode Anisa. Kuma don Allah kada ya zama reason na lalacewar zumuncinmu.”

    “Tun farko dama kayi min bayani. Babu wani abu. Sai mun zo ganin amarya.”

    Da ya rage su biyu a falon Taj ya kalli Amma “that went well right?”

    “I think so.” Ta bashi amsa da fatan hakan ne.

    Breakfast ta kawo musu. Bayan sun gama ya faɗa mata komai ds komai da ya danganci Abba da aurensa.

    “Yaron nan da a ɗan daba ka tashi sai an wahala da kai. Banda rigima ka rasa ƴar wanda za ka auro sai Simagade? Kai yanzu ka yarda Yaya Hayatu ba zai kawo matsala a gaba ba?”

    “Da Allah na dogara Amma. Bana son yin wannan tunanin saboda ban hango abin da zai rabani da Hamdi ba.”

    “Sunanta ya min daɗi fa. Hamdiyya. Ɗazu da ka faɗa har zan magana na kama bakina kafin Hajja ta zageni.”

    Cikin farincikin shiryawa da Amma ya bar gidan da yamma. Ta so ya kwana amma ya dage gara yaje hotel. Zaman nasa a ganinsa tamkar rashin kunya ne. Zai kyautu ya bawa mutanen gidan damar sake karɓarsa idan ciwon abin da su ke tunanin laifi ne ya ragu.

    ***

    A yau sha’anin biki ya ƙare. Kakan Safwan ya wakilta masu ɗauko amarya Sajida zuwa gidansa. Dama Umman Safwan ɗin bata da damuwa ko kaɗan. Babansa ne baya so. Bayan koke koken amarya da ƴan uwanta da kuma Yaya, gidan kakannin Safwan aka wuce da ita.

    Tsohon nan ya yi musu nasiha sosai da jan kunne.

    “Sai kun ji kon ƙi ji. Ku gani kuma ku ƙi gani sannan auren zai yi ƙarko. Musamman gareki jikata” Sajida ta kalle shi da jan ido “duk wanda ya sami dama a dangin nan zai faɗa miki magana son rai akan asalinki. Wannan ko ka hana wani sai ya yi. Saboda haka ki koyi kawar da kai. Inda ba za ki iya ba kuma ki kare martabar mahaifinki. Ina mai tabbatar miki da an kwana biyu zai bi jiki. Kowa zai haƙura matuƙar kun zauna lafiya. Kun bawa maraɗa kunya.”

    Safwan ne kaɗai ya iya yi masa godiya. Sajida kuwa in banda sharar hawaye babu abin da take yi.

    *

    Ana can ana ƙarasa guntattakin gyara a gidan amarya Zee ta fice daga ɗakin da Hamdi take yiwa turaren wuta ta koma wajen gate ta kira Taj. Yamma ce liƙis. Tana ta addu’ar samunsa a wayar. Tayi sa’a kuwa bugun farko ya ɗauka. Sai kuma ya kashe ya kirata.

    “Zee amarya.”

    Sake tsokanarta ya yi “to uwargida. Tun yanzu har an fara kishi kenan.”

    “Don Allah ka bari”

    Yanayin muryarta ba yadda ya saba ji bane. Shi yasa bai ja wasan ba ya nemi ta sanar dashi dalilin kiran. Muryarta rawa ta fara, sai kuma ta kama kuka. A haka ta faɗa masa maganganun da taji Abba yana faɗawa Hamdi jiya ba tare da sun san ta biyo su ba.

    Ashe tun shigowar Hamdi cikin gidan ta taso za ta tsokaneta akan me taje yi a waje sai taga Abba ya ja ta zuwa soro. Fuskarsa da ta gani da damuwa ita tayi sanadin binsu da tayi. Tana gama jin abin da ya ce tayi saurin komawa ciki.

    Jijiyar kansa tashi tayi sosai. Ɓacin rai ya rufar masa. Ya rasa dalilin da yasa Alhaji yake yi masa haka.

    “Ya Taj don Allah ka saketa ba sai tayi maka abin da zai ɓatawa Abbs suna ba.”

    “Yi shiru Zee. Maganar nan da wa kika yi bayan ni?”

    “Babu kowa.” Ta ja hanci.

    “To don Allah ki yi min alƙawarin riƙeta a ranki kin ji.”

    “Sakin fa?”

    “Hamdi ta zo kenan. Idan ku ka yi wasa ma duk sai ta riga ku haihuwa.”

    Wayar ta cire daga kunnenta saboda kunyar kalamansa. Kamar ya sani ya ce

    “Oh sorry, ƙanwa ce fa ke.”

    “Idan tayi maka laifin da zai sa ka saketa fa?”

    “Kada ki damu. Just focus on yourself. Ki gama karatunki ki kuma riƙe mutumcin aurenki. Ni da Hamdi in sha Allah anyi auren kenan.”

    “Tsoro nake ji kada babanka ya yiwa Abba wani abu.”

    “In sha Allah babu abin da zai faru. Ina son sister ɗinki. Zan kuma tsare mutumcinta da na duka family ɗinku.”

    Ya ɗauki lokaci sosai wajen kwantar mata da hankali. Sannan ya yi mata godiya da ta tunkare shi da zancen. Wayar Kamal ya nema da su ka gama don ya faɗa masa yaji a kashe. Ya yi ɗan tsaki. Tun asuba fa Kamal ba yadda ya saba yake ba. Komai daina yi masa daɗi yake saboda yana jin tamkar wani ɓangare na jikinsa baya tare dashi.
    Jirgin tara na safe ya yi booking ta waya kafin ya kwanta.

    ***

    Hannuwa da ƙafafunsa ya kalla hankalinsa ya sake tashi. A kumbure suke. Fuskarsa kuwa kamar an hura balloon. Magungunan jiya ya ɗauko yayi ta dubawa ko akwai wanda ya sha ba daidai ba amma babu. Gabansa ya dinga faɗuwa da tunanin me zai faru idan yanayinsa ya cigaba a haka. Babbar matsalarsa ma ita ce yadda zai samu ya bar gidan ba tare da kowa ya gan shi ba. Daga daren jiya zuwa yanzu ya fita hayyacinsa baki ɗaya. Wayarsa ya nema ya kunna domin magana da likitarsa sai yaji ana taɓa ƙofar ɗakinsa.

    Hankalinsa ya sake tashi da ya kalli kansa a madubi.

    “Waye?” Ya furta da ɗan ƙarfi.

    Shiru yaji babu amsa. Sai zura muƙullai da ake tayi a ƙofar. A gwaji na biyar aka buɗe ƙofar ɗakin wanda bai taɓa zaton akwai spare key ba. Idanunsa da ƙyar su ke buɗuwa saboda hasken fitilun waje da su ka shigo.

    “Abba? Bishir?”

    Fitilar ɗakinsa aka kunna gami da rufe ƙofar ɗakin nasa.

    “Kamal? Shaye shaye kake yi?”

    A gigice ya ɗago idanunsa da suke buɗewa da ƙyar saboda kumburi ya kalli wadda ke tsaye a kansa.

    “Umma?”=
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!