Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
    “Ayyyyyyiririiiiiiiii. Allah mungode maKa. Hajiya Jinjin uwargidan Habibu namu asa goshiia ƙasa a miƙa godiya ga Sarkin sarakuna. Allah Ya kwashe miki ƴan matanki a sa’a guda. Wannan farar juma’a ta amare uku ce rigis. Sai a saurari zuwan ƴan dugwi dugwi iyalan Baba.”

    Ba kowa bane da wannan aiki sai Ƴar Ficika daga soron gidan. Yana gama magana kuma yaransa su ka amshe guɗar su na yi. Yaya fitowa tayi daga ɗakinta inda ta fake da shiryawa ta zauna rarrashin Sajida da Zee. Hamdi na gefe ita ma tana basu baki tare da taya su kuka.

    Anti Zinatu ce kaɗai ta san zaman me su ke a ɗakin. Ita ce ma ta tura musu Yayan domin wani ciwon uwa kaɗai ke iya maganinsa.

    Hamdi na jin muryarsa ta haɗe rai bayan fitar Yaya daga ɗakin.
    “Wai namiji kenan. Mtsewww.”

    Lulluɓi Yaya tayi ta fita soron. Ƴar Ficika ya wangale baki.

    “Sai muka ji abin arziƙi ko Jinjin? Allah Yasa abokan zamansu ne.”

    Ita ma takaicin ɗaga muryar tasa take yi. Ga zaƙin murya gashi bai iya tausasa harshe. Ta tabbata kowa na jinsu a ciki.

    “Da ka ɗan rage maganar saboda ƴan biki ba su san auren Zee aka ɗaura ba maimakon Sajida. Sannan kana cewa amare uku sai ayi zaton…”

    “Ba zato bane Jinjin. Ƴaƴan Simagade sun zama farinwata sha kallo. An so tozarta shi sai gashi Allah Ya aurar dasu lokaci ɗaya.”

    Yaya dai bata fahimci inda ya dosa ba. Gani take wani zancen yake haɗawa da wani. Sai kawai ta koma ciki. Aka yi ta tambayarta me yake nufi kuwa don duk sun ji.

    “Shirmen Ƴar Ficika ne. Shi da ko wurin ɗaurin auren basu je ba?”

    Rufe bakinta ke da wuya Halifa ya shigo gidan kamar an jeho shi daga sama. Haki yake da ƙarfinsa saboda gudun da ya sha ba na wasa bane. Tun daga masallacin juma’ar unguwarsu har gida. Tafiyar kimanin minti talatin. Ƙafafunsa sun yi buɗu buɗu.

    “Yaya! Yaya!!” Ya dinga ƙwala kira kamar makaho na neman ɗan jagoransa.

    “Kai Halifa lafiyarka kuwa?” Wata maƙociyarsu ta tambaye shi.

    “Ina Yaya?” Ya faɗi yana dariya.

    Banda Yaya, duk matan da su ke gidan fitowa su ka yi. Yana ganinta ya taho da sauri, sai kuma ya tsallaketa ya rungume Sajida.

    “Wai mene ne Halifa? Ka sanya mu a duhu” cewar Inna Luba.

    Murmushi ya yi yana duban ƴan uwansa.

    “Yaya an ɗaura. Duka su ukun an ɗaura musu aure.”

    Dafa shi Inna Luba tayi zuciyarta na bugawa.
    “Nutsu ka yi min bayani. Su waye su ka yi auren?”

    “Ya Sajida da Yaya Safwan.”

    Sajida ta bar jikin bangon da ta jingina tayi da sauri, ta rufe bakinta da hannu. Wasu zafafan hawaye suna sauko mata. Hamdi ta rungumeta tana cewa “Alhamdulillah.”

    Anti Zinatu ta ce “Mata biyu aka aura masa kenan? Naji ka ci mutum uku.”

    Ya murmusa da farincikinsa “a’a, sai Ya Hamdi da Happy.”

    Inna Luba ta ware idanu a tsorace “Hafi? Mutum ne?”

    Yadda yake murna kai ka ce shi ne angon mata uku. Gyarawa ya yi yadda za ta gane da kyau.
    “Ya Taj. Shugaban inda Abba yake aiki yanzu.”

    Cikin Hamdi wata irin ƙullewa ya yi. Taji ya saki lokaci guda yana neman tsinkata a gaban mutane. Duk da haka danne shi tayi da hannu biyu.

    “Kai ka san bana son wasa irin wannan. Wace Hamdin kake nufi?”

    “Wallahi ke ce Ya Hamdi. Babansa kawai muka gani ya cewa Abba yana nemawa ɗansa aurenki. Sadakinki fa dubu ɗari biyu. Cash in faɗa miki.”

    Daga inda ya yi rantsuwar ita Hamdin ta daina jin komai sai bugun zuciyarta. Wannan wane irin mugun wasa ne Halifa yake yi mata haka? Aure? Ita ce tayi aure kamar wata kayan wasa? Kuma wai da Taj. Waye ma Taj? Kamar ta san sunan.

    Sama-sama taji muryar da ko gane mai ita ba yi ba tana cewa “Ku riƙeta…Sajida kama hannun. A’a rungumota kawai kada ta kai ƙasa.”

    Luuu haka taji ƙafafunta suna narkewa su kaɗai za su kaita ƙasa. Kafin ta gama faɗuwa aka tallafota zuwa falo. Akan doguwar kujera aka kwantar da ita. Ana yi mata fifita. Daga nan ba za ta iya tuna me ya faru ba.

    ***

    Ƴan uwa da abokan arziƙi dafifi su ka yi wajen taya Abba murna a masallacin. Yadda al’amura su ka kasance maƙiyi ne kaɗai zai ce bai jidaɗi ba.

    Baba Maje baki har kunne shi da Baballe. Murna yake yi, ya sami damar kyautatawa amininsa bayan abin da Ummi tayi. Don tun daga lokacin shi da Iyaa su ka ja baya da iyalin Abba. Suna masu jin kunyar abin da ƴarsu tayi. Duk rashin son fita sai ya zamana Yaya ce mai ƙoƙarin zuwa. A yawan ziyarar da take kai musu ne Baballe yaga Zee ya ƙyasa. Ashe rabonsa ce bai sani ba.

    A ɓangaren Taj kuma inda mahaifinsa yake ya zauna tare da ƴan uwansa. Kawunnai ne na ɓangaren Alhaji shi kaɗai sai ƴan uwansa su Ahmad. Yadda ya hana Taj faɗawa su Inna tun jiya, haka ya tsallake ƴan uwansu maza da dukkanin abokansa.

    Mutane na ragowa ya tashi da sauri ya fita. Ƙaninsa Baba Amadu ya tare shi ganin sun nufi wurin motocinsu.

    “Haba Yaya Hayatu. Ba za mu tsaya mu gaisa da baban amaryar ba za mu tafi?”

    “Baka gane shi bane? Habibu ne fa. Meye abin gaisawa a nan?” Ya amsa a wulaƙance

    Daga nan gaban Taj ya faɗi. Su ka haɗa ido da Kamal kowannensu da tunanin da yake ransa. Yaya Babba kuwa haɗe rai ya yi.

    “Da alama akwai manufar da ta sanyaka amincewa auren nan bagatatan. Dama nayi mamaki da ka sanar dani jiya a ƙurarren lokaci. To amma saboda Taj ne shiyasa na zo don kada sai an zo ɗaurawa ka ce ka fasa don kawai ka muzanta shi.”

    Alhaji ya yi murmushi “bani da wata manufa. Auren fitar da ubangidansa a daudanci daga kunyar al’umma yake son yi kuma nayi masa don kada ma a sami bakin zagina.”

    Kallon tsananin mamaki Taj ya bi shi da shi. Bakinsa ya mutu. Tun ba a je ko’ina ba ya gane shigo-shigo ba zurfi Alhaji ya yi masa.

    “Alhaji don Allah ka tsaya” Ahmad ya roƙe shi don baya jindaɗin ganin manya su na sa’in’sa.

    “Kaima ban maka izini tsayuwar ba. Yanzu ku sai ku yi musabaha da mutum irin wannan?” Ya nuno Abba da yake tahowa inda suke da ƴan abokansa.

    Abin ban sha’awa babu ɗan daudu ko ɗaya. Dama su Ƴar Ficika ne. Shi kuma tunda a gabansa mahaifin Safwan ya ci mutumcin Abban sai ya ce shi da yaransa ba za su ɗaurin auren ba don kada a sake samun matsala.

    Bawan Allah bai san wainar da ake toyawa ba. Da ya iso hannu ya miƙawa Yaya Babba gami da rissinawa sosai cikin girmamawa. Har sai da Taj yaji wani iri.

    “Yaya barka da rana?”

    Fuskarsa shi ma a sake ya ce “Sannu Habibu. Shekaru da yawa. Gashi mun zama surukai.”

    Abba ya murmusa “ina ni ina surukuta da ku Yaya? Ƴa taku ce. Sai dai ace ta bar gida ta sake komawa gida.”

    Ragowar ƴan uwan Alhaji su ka ƙarbi musabaharsa saboda Yaya Babba ya buɗe musu hanya. Ransa fari ƙal ya sake rissinawa ya miƙa hannu ga Alhaji.

    “Yaya Hayatu …”

    Kallon da Alhaji ya yiwa hannun yafi ƙarfin a kira shi na wulaƙanci. Sai dai a ce ƙasƙanci. Domin ba ma da duka ƙwayar idon ya kalle shi ba. Duniya bai ga abin da zai sa ya kama wannan hannun da ya gama lalacewa da bleaching ba. Knuckles ɗin (gaɓoɓin yatsu) duka baƙaƙe ƙirin. Ragowar hannun kuma fari da ɗigo ɗigon baƙi.

    Yawu mai ɗaci Taj ya haɗiya ganin Abba ya shanye abin da aka yi masa tamkar babu komai. Hannun kawai ya mayar ya ƙara duƙawa.

    “Barka da rana.”

    “Kaga tashi don Allah. Bana son wannan ɗabi’ar taku ta gaisuwa kamar maroƙa.”

    “Alhaji” Taj ya kira sunansa da ɗan ƙarfi ba tare da tunanin komai ba sama da son ya tunatar da shi me yake aikatawa a gaban mutane.

    Ko kallonsa Alhaji bai yi ba. Yaya Babba ne ma ya yi masa alama da ya yi shiru kawai.

    Ba tare da nuna ɓacin rai ba Abba ya miƙe yana murmushi. Zuciyar Taj ta kasa jurar ganin wannan abu. Barin wurin ya so yi. Hannun Kamal a jikin babbar rigarsa ya hana shi motsawa.

    Alhaji ya ce “Ina son ganinka yau bayan Isha’i. Ai ka san gidana ko?”

    “Gaskiya ban sani ba. Amma ko Taj sai na biyo in sha Allahu.”

    Alhaji ya yi irin murmushin nan na ɓacin rai. Yana magana ciki ciki “na manta yanzu kai ne uban. To kada ku wuce Isha dai.” Ya kalli Taj “kai kuma kada ka manta dokar gidana a kanka. Da ishan ma don ni na kiraka ne.”

    Mota ya faɗa abinsa direba ya ja. Abba ya sake yin murmushi yana ɗagawa motar hannu tare da faɗin “Allah Ya kiyaye hanya.”

    Hannun nasa Taj ya sauke masa ya nuna masa Baba Maje “Abba kaje ga abokinka can ina jin kai yake nema.”

    Sai da ya tafi ƴan uwan Alhaji su ka soma bashi baki. Baki ma kasa motsawa ya yi saboda ɓacin rai. Ya dai dinga gyaɗa kai kawai. Yaya Babba ne ƙarshen yi masa magana.

    “Ina so ka sani cewa a musulunci iyaye suna da babbar daraja. Bana so abin da Hayatu yake yi maka ya zama sanadin da za ka mayar da martani. Domin idan kayi haka lallai kayi asara. Baka jidaɗinsa ba a duniya kuma a lahira ma ba za ka sami rangwame ba.”

    Godiya sosai ya yiwa Yaya Babban sannan su ka tafi.

    Ahmad na ganin babu sauran manyan ya ce masa “mu tafi gida mu san yadda za mu yi da matan gidan. Na san dukkaninmu ba za ta yi mana kyau ba. Ace kayi aure babu wadda ta sani.”

    Kafin yanzu da wannan tunanin Taj ya kwana. Amma ƙullin da Alhaji ya soma yi masa ya sa ya daina damuwa.

    “Baka ji yana yi min tuni akan kada na shigar masa gida ba?”

    “Ni kuma a ganina wannan shi ne lokacin da ya dace ka take wannan dokar ka shiga gidan. Rayukansu za su ɓaci. Sannan bana jin za su yarda su biyoka gidan Yaya. To a ina ka ke jin za ku haɗu har ka yi musu bayani na fahimta? Don ni ban hango sun amsa wayarka ba balle su saurareka” cewar Abba wani sarkin zuciyar.

    Bishir ɗan salihin cikin mazan ya ce “Ɗauko sun dai ya dace ayi su haɗu a gidan Yaya ko gidan Yaya Babba.”

    Agogo Ahmad ya kalla. Lokaci na ƙurewa kuma ba su sami matsaya ba.

    “Mu je gidana ayi shawara. Zan kira su Yaya Hajiyayye dukkaninsu yanzu a hanya. Idan ya so ko mu kaɗai ne sai mu je mu yi musu bayani.”

    Shi dai Taj bashi da ta cewa. Motar Kamal ya shiga Abba kuma ya ja motar Ahmad su ka tafi da Bishir. A hanya Ahmad ɗin duk wata yayarsu ta kusa da ta nesa ya kira ta ya sanar da ita. Bishir aka bari da kiran sauran. Duk wadda ta sami hali ta taho gidan Ahmad. Amma banda na cikin gidansu su uku. Idan aka kirasu dole a zargi wani abu. Yadda shawara ta kaya za su haɗu su je gida wuraren biyar na yamma.

    *

    Kamal na tuƙi ya ɗan kall Taj “Yanzu ka fahimci me yasa nace ka bar maganar auren nan Happy? A gaban jama’a kana ganin yadda Alhaji ya tasarma wulaƙanta Abba.”

    Kamar bai ji shi ba sai ya yi masa tambaya.
    “Me yasa idan na zo da abu baya bani zaɓi Happiness? Sai dai ya bari nayi sannan ya ɗauki hukunci mai tsauri a kai.”

    “Saboda baka tsayawa kayi hangen me zai je ya dawo. Har cewa nayi zan auri Sajida duk don ka haƙura da gaggawar nan amma ka ƙi.”

    “Ko bana son Hamdi ba zan yarda ka auri Sajida ba. Yadda ya sallama ni haka zai yi maka. Sannan kuma ya ɗora laifin naka a kaina.”

    Kamal ya haɗe gira “akan me zai ɗora maka?”

    “A dalilin kafi kowa kusanci dani mana.” Taj ya bashi amsa.

    Tunanin bai zo masa ba a baya sai yanzu. Tabbas da ya yi auren laifin su biyu Alhaji zai rabawa. Yana ma mamakin da ya ƙyale shi ya buɗe boutique a wurin Taj. Bai zaci zai sami goyon bayansa da wuri ba.

    Taj ne ya yi magana bayan dogon shirun da su ka yi.
    “Happiness, ba fa zan bari ya wulaƙanta Abba ba. Ni ban ga dalilin da zai sa mu dinga kasa yiwa mai tsohon laifi uzuri ba. Hakan zai iya sawa su koma ga laifin.”

    Tausayinsa Kamal yake ji. Sai dai kuma yana ganin kamar harda taurin kan Taj. Da zai sauke nasa kambun ya yiwa Alhaji biyayya da tuni an jima da wuce wannan wajen.

    “Na sani. Amma akwai hanyoyin samun lada da yawa sama da zaɓar wanin mahaifinka.”

    Idanun Taj sai da su ka yi ja kafin ya bashi amsa.
    “Baka ji me nace bane? Happiness, Alhaji bai taɓa bani zaɓi ba. He just pushes me away and gets angry when I comply (ingiza ni yake yi kuma ya yi fushi idan nayi yadda yake so). Auren nan ina faɗa bai wani ja ba ya amince min. In baka manta ba certificate kawai naje na nunawa Yaya Babba shi kenan ya koreni. Da cewa ya yi in zaɓi girki ko zaman gidansa kaima ka san ba zan taɓa barinku ba. Ba don Amma…”

    Zaro idanu ya yi waje ya shiga karanto Innalillahi hankalinsa a tashe. Ya kai hannu ya damƙi hannun daman Kamal dake riƙe da sitiyari tunda yafi kusa da shi.

    “Kamal…ya zan yi? Amma. Ya Rabbi.” Ya faɗi cikin tashin hankali.

    “Me ya same ta?” Kamal ɗin ma duk ya gama ruɗewa.

    “Ya za ta ɗauki zancen nan? Ga maganar Anisa. Kada hakan ya janyo mata matsala da Daddy.” Ya kuma faɗi, damuwarsa na ƙaruwa.

    Har su ka ƙarasa gidan Ahmad suna jimamin yadda za su tunkari Amma da zancen nan. Kamal ya ƙara tayar masa da hankali da ya ce ya tabbata cikin kawunnansu ba za a rasa wanda zai faɗa mata ba.

    “Kenan ba a bakina za ta fara ji ba? Shinenan. Na gama yawo.”

    Yadda ya marairaice Kamal dariya ya yi masa.

    ***

    Falon gidan Ahmad ya cika ya tumbatsa da ƴaƴan Alh. Hayatu. Duk wadda take cikin garin Kano ta na zaune a wurin.

    Yaya Zulaiha ce ƴa ta biyu a gidan. Ita ta karɓe girman daga hannun Hajiyayye don ta fi ta zafi. Ta yiwa Taj faɗa sosai.

    “Don kana son taimako bai dace ka dinga yin abin da zai cigaba da ɓata masa rai ba. Mahaifi ne fa.”

    Haƙuri ya bata da alƙawarin zai yi ƙoƙari a nasa ɓangaren yaga al’amura sun daidaita. Ya ƙara da nanata musu cewa abin ne ya zo akan gaɓa. Yana son Hamdi tun farkon haɗuwarsu. Ya yi haka ne saboda sanin halin mata tunda cikinsu ya tashi. Idan ta kuskure musu, tsaf za a goranta mata wata rana.

    Babbar yaya Hajiyayye tana jin an kashe wancan zance sai cewa tayi,

    “Ya maganar lefe? Ya kamata kafin a soma zancen tariya mu haɗa wanda zai fiddo darajar gidanmu.”

    “Kai jama’a, Ya Hajiyayye ana ga yaƙi kina ga ƙura. Wa yake ta lefe alhalin uwayen ango basu san anyi auren ba?” Wata yayar tasu ta ce.

    Duk sai su ka kama dariya. Hajiyayye dai ta fuske abinta ta ce a samo takarda tayi list. Tunda dai an riga an ɗaura auren sannan bata fatan ace saki ya biyo baya ai kuwa zancen lefe ya zama tilas. Ƴan son biki irinta su ka goya mata baya. Daɗi ya isheta domin ƙannen nata wani sa’in tamkar ƴaƴanta ta ɗaukesu.

    “Sai ka tambayar min ita size ɗin takalmi da undies. In su Mama sun bamu goyon baya da wuri kaga ba sai an yi wani jinkiri ba.”

    “Ya Hajiyayye ki bar min sayen undies ɗin. Jibi tafiyarmu UK da Abban Farouq. Kin san na ce miki sati biyu kawai za mu yi.” Wata ƙanwar tasu ta faɗi da zumuɗi.

    Taj ya rasa me ya kawo wannan zance a cikin mutane haka. Kunya sosai ta kama shi don bai taɓa tunanin yin irin wannan maganar da Hamdi ba. Da su ka farga da discomfort ɗinsa kuwa su ka dinga yi masa shaƙiyanci.

    ***

    Kamar kullum idan magana tana da mahimmanci a wajen Alhaji, ɗakinsa yake kiran matansa ya sanar dasu. A yanzu gidan nasa ya sha gyara mai kyau irin wanda ba a taɓa yi masa ba. Idan ka jima baka shigo ba sai ka kasa gane shi. Duk da cewa fasalin shi ne dai na da, amma an sabunta tsari da kaya yadda zai shiga sahun farko na kowanne maikuɗi. Saboda yanayi na girma, ya fitarwa kansa da wani ɓangaren ta baya inda ya yi sabon sashensa manne da babban falon ƙasan gidan. Saman ya barwa ƴan matan da basu yi aure ba da jikokinsa matasan mata dake yawan zuwa su kwana.

    Haka kawai Inna ta dinga jin faɗuwar gaba akan wannan kiran. Jikinta ya bata ba zai wuce akan Taj ba tunda ya zo jiya. Tana son sanya ranta yayi murnar ƙila an shirya tsakanin uban da ɗansa, amma kuma duhun fuskar Alhajin ya sare mata gwiwa.

    Haka su ka zazzauna har ya gama tsakurar abincinsa na rana sannan ya dube su.

    “Yau bayan sallar juma’a na ɗaurawa Taj aure da ƴar gidan Habibu Simagade.”

    Isashshen lokaci ya basu zancen ya zauna musu. Cike da fargaba da tashin hankali su ke dubansa. Mama tayi ƙarfin halin tambayar ko wani laifi ya sake yi.

    “Da farko dai yana aiki tare da Habibu saboda ya nuna min ban isa ba. Banda haka ko masu girki nawa ne a garin nan da har sai ya nemo Habibu?”

    “Alhaji ina ganin ire iren matakan da kake ɗaukarwa Taj ba za su samar da biyan buƙata ba. Shi fa ɗa komai shekarunsa indai yana da iyaye to fa yana buƙatar laluma da ja a jiki.” Cewar Hajiya.

    Cikin fushi da faɗa Alhaji ya ce “an ƙi a lallaɓa shi ɗin.” Sannan ya faɗa musu abubuwan da ya binciko da dalilin auren.

    “Yaron da yake da hankalin son fitar da wani kunya ne zai kasa gane dacewar ya kiyaye ɓacin ran mahaifinsa?”

    Umma ta ce “Kayi haƙuri. In sha Allahu za mu yi masa magana.”

    “Bakin alƙalami ya riga ya bushe tunda an ɗaura auren.”

    Sai da kowacce ta gama rarrashin Alhaji akan ya yafewa Taj shi kuma yana botsarewa sannan Inna ta dube shi ido cikin ido.

    “Yanzu da ka tara mu wane hukunci ka yanke masa.”

    Dukkaninsu sun girgiza da kalamanta da ma yanayin fitarsu. Babu wannan ladabin da kiyaye harshe da kowacce cikinsu bata isa ta ƙetare ba.

    “Abu? Da ni kike?”

    Ko gezau bata yi ba ta ce “Alhaji na gaji ne. Ina son sanin matsayarka ta uba kafin na sanar da kai tawa ta uwa.”

    Hajiya sai ta ɗan taɓata don tayi shiru. Ita kuwa ta kafe Alhaji da ido. Mamakinta ya hana shi motsin kirki. Da yaga da gaske take ne ya iya yin magana.

    “Faɗa min naki hukuncin. Ai kema kin isa da shi. Wata tara ai ba kwana tara bane.”

    Gyara zama tayi ta hakimce abinta domin a yau Alhaji ya gama kaita maƙura.

    “Tunda ka aurar dashi ni kuma in sha Allahu zan yi masa biki irin na ɗan da mahaifiyarsa take so kuma take alfahari da shi.”

    “Da kyau Inna Abu.” Umma ta faɗi cikin farinciki tana tafa hannuwa. Da Hajiya ta kalleta ta kaɗa kai tana dariya. Yau ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha.

    “Biki? Yanzu ke sai ki yi bikin ɗanki ya auri ƴar ɗan daudu? Auren da baki ma san da shi ba sai yanzu?”

    “Aure ka ce, halattacciyar alaƙa. Kuma da kake zancen ban san dashi ba ai ba laifinsa bane. Na yarda da tarbiyar da mu ka bawa ƴaƴanmu. Yaron nan bai taɓa yin wani abu gaba gaɗi kamar mara mafaɗi ba. Tunda har kai ne ka jagoranci ɗaurin auren na tabbata ba a hanya ka tsinci zancen ba.”

    “Haka ne” ya ce da wani irin disbelief. Wai yau Abu ce take kallon idanunsa tana faɗa masa maganganu irin waɗannan.

    “Na kuma jima da sanin cewa duk abin da zai yi yana turo maka saƙo ya sanar da kai.”

    Bai yi mamakin yadda aka yi ta sani ba
    “Shi ya faɗa miki ko?”

    “A wayarka na gani.”

    “Bincike kike min?” Ya ɗaga murya.

    “Ni na nuna mata” Mama ta bashi amsa ita ma yau da nata ƙwarin gwiwar.

    Inna ta dube shi bayan ya gama yiwa Mama nata kallon za ki gamu dani ɗin.

    “Abu guda nake nema daga gareka. IZINI. Duk wani abu da ya kama na bikin nan wanda zai fitar dani ko ƴan uwana…” ta nuna su Hajiya “daga gida ina roƙon ka sahale mana. Sannan ranakun taron su ma ka barmu mu je. A gidan nan kai amarya ne kaɗai uwa bata zuwa. Amma komai tare muke yi ka sani. Ko sisi ba na nema a wajenka. Alhamdulillah ina da abin hannuna na fitar da ɗana kunya.”

    “Ɗanki? Wai yau Abu kin sha wani abu ne?” Alhaji ya ma kasa yi mata faɗa saboda ta shayar dashi mamakin da bai taɓa zato ba.

    “Ɗana Tajuddin ba. Wanda a kansa na fara sanin daɗin zama uwa. Yaron da tsabar taurin kai irin nasa ya laƙaba min suna Inna tun da sauran ƙuruciyata.” ta faɗi cikin tuna baya da tasowar zazzafar ƙwalla “a wajen yi maka biyayya da son kyautatawa na dinga danne haƙƙinsa dake wuyana. To amma daga yau in sha Allahu an gama. Ba zan bari wata aƙida mara tushe tasa ya rayu da fushin iyaye biyu har ma rayuwar tasa ta kasa albarka ba.”

    Tana gama magana ta tashi za ta fita don hawayen da take yi ya hanata cigaba da faɗa masa irin damuwar da ta jima tana dannewa a zuciyarta.

    “Zainab.”

    Dakatawa tayi ta juyo su ka haɗa ido da Alhaji.

    “Ban yi miki izinin fita yin duka buƙatun da ki ka nema ba. Haka ma ku” ya kalli inda su Hajiya ke zaune suna murmushin jindaɗin wannan abu.

    Inna ta goge hawayenta ta kalle shi.

    “Samun izinin shi ne kaɗai abin da zai sa na yafe maka rabani da ɗana da kayi sama da shekara goma alhalin ba Allah Ya saɓawa ba.”

    Ficewa tayi ko kallon inda yake bata sake yi ba. Umma da Mama su ka bi ta. Hajiya da ta ɗan jinkirta tashi kallonsa tayi.

    “Tura ce ta kai bango Alhaji. Kuma ina mai tabbatar maka da cewa idan baka sassautawa Abu ba to wannan fito na fito ɗin yana nufin ta gaji da aurenka. Muma kuma ƙofa ta buɗe mana na daina shanye mulkin mallakar da kake mana. Ah to.”

    “Wai ni Gambo anya ba sauya ku aka yi ba?” Ya faɗi da gaske.

    Hajiya tayi dariya “ai na faɗa maka tura ce ta kai bango. Ka bar gani na shiru shiru. Wallahi da Kamal ka yiwa abin da kake yiwa Taj da gidan nan ba zai ɗaukemu ba. Ita kanta Abu har gulmar yakana irin tata muke yi da su A’i. Akan korar Taj da kayi kuma ta cigaba da zaman gidan nan akwai yayunta biyu da su ka fita harkarta. Kafi kowa sanin tana da gata. Mace tilo cikin maza shida! Babu yadda su Alh. Lurwanu basu yi ba akan za su ɗauko Taj daga wajen Jamila taƙi. Kawai don ta faranta maka. Amma kullum sakayyar da kake yi mata ba mai daɗi bace.”

    Ita ma ficewarta tayi ta barshi da tulin tunani da fargaba. Ba zai yaudari kansa ba. Tsoro ya mamaye shi da abin da ya faru yanzu. Idan ya matsa matansa za su iya barinsa babu waige. Idan kuma yayi sakaci gidan zai fi ƙarfinsa. Abu ɗaya ya rage. Ya dinga cizawa yana busawa. A yau dai dole ya busa don yana cizawar Abunsa za ta ɓalle. Matar da zuciya ta kasa tsufa daga yi mata soyayya tamkar yau ya aurota.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!