Search
You have no alerts.

    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Kallon da Abba ya yiwa Taj na tsantsar ƙauna da girmamawa ne bayan ya gama mamaki. Ya miƙe tsaye ya kama hannun daman Taj da hannayensa biyu.

    “A duniya bayan iyayena da matata da kuma ƴan uwana da ba su guje ni ba da kuma ƙalilan cikin abokai, kai ne mutum na farko da jini bai haɗamu ba amma kullum burinka ka sanya farinciki a rayuwata.”

    Kamal samun kansa ya yi da girgiza kai saboda tsoron kada ya amince da ɗanyen aikin da Taj ya ɓallo.

    “Abba…”

    Kallonsa Abban ya yi yana murmushin danne ciwon dake cin zuciyarsa.

    “Kada ka damu Kamal. Ba zan taɓa zama butulu gareku ba. Na san duka abin da kake gudu. In sha Allahu ni Habibu ba zan bari son zuciya yasa na zama mai ƙara nesanta uba da ɗansa ba.”

    Daga Taj har Kamal ba ƙaramin tausayi ya basu ba. Taj ya rufe ido ya ce,

    “Abba, Alhaji ya daɗe da zare hannunsa a kaina. Auren Hamdi ba zai …”

    Kamal ya katse shi da hanzari “wallahi zai ƙara girman fushinsa a kanka. Haba Happy, ba ka tunanin su Inna ne?” Ya mayar da idanunsa ga Abba “ni zan auri Sajidan in sha Allahu. Laifin ba zai tattare akan Taj ba.”

    Abba jinjina zumuncin ƴan uwan yayi. Kuma bai bar zancen a cikinsa ba ya faɗa musu.

    “Lallai Yaya Hayatu ya iya haihuwa. Ko shaƙiƙan da su ka fito ciki guda ba lallai su yi zumunci irin naku ba. Amma ku tafi gida, nagode. Zan bawa Sajida haƙuri. Na san za ta yi min uzuri.”

    “Sai dai idan ni ne baka son bawa ƴarka. Ba auren taimako zan yi ba. Allah na fi shekara ina sonta.”

    “Har a yaushe ka santa?” Kamal ya tambaye shi don bai yarda da zancensa ba ko kaɗan.

    “Duka wannan bai taso ba. Ku je gida. Nagode”

    Abba zai shige gida Ƴar Ficika ya kamo shi da sauri. Duk sun manta dashi. Kwarwar da yake da ihu ma ba sa ji saboda mahimmancin abin da su ke tattaunawa.

    “Simagade….au Habibu ashe baka da hankali? Ya Allah zai kawo maka agaji a lokaci irin wannan ka nemi ka watsa mana ƙasa a ido. Ina mai tabbatar maka da cewa Sajida kai za ta ɗorawa alhakin rabata da farincikinta. Daga nan kuma bamu san halin da za ta shiga ba. Ni a tawa shawarar kawai ka bari su aure su duka.”

    “A’a Balarabe. Baka san komai akan yaran nan ba. Son zuciya a yanzu ita ce ƙiyayya mafi girma da zan nuna a madadin kyautatawar da su ke min.”

    Ƙofar gidansa ya ƙarasa da sauri don ƙirjinsa zafi yake. Sai dai ko rabin jikinsa bai samu shigewa ba ya faɗi a wurin. Ƴar Ficika aka sake samun abin yi. Ya ɗora hannu a ka zai cigaba da ihu, Kamal ya daka masa tsawa.

    “Kada ka kuskura ka sake tara mana jama’a. Yi sallama ciki ka yi min magana da Yaya.”

    “To, to” ya amsa kamar ba ɗan cikinsa bane ya yi masa tsawar. Yadda mata ke ruɗewa a irin wannan yanayin, haka nasa hankalin ya gushe.

    Da Kamal ya juyo bai ga Taj ba. Ya fara tunanin ko cikin gidan ya shige, don yanzu komai aka ce ya yi ba zai yi mamaki ba. Ya lura yana da taurin kai irin na Alhajinsu, sai dai kuma shi Taj ya haɗa da ɗanyen kai kamar wani ɗan ta kife. Idan ya san abu daidai ne to kawai damn the consequences.

    Horn ɗin mota yaji daidai ƙofar gidan. Ya leƙa Taj ya fito a lokacin.

    “Mu kai shi asibiti.”

    “Ai ka bari a faɗawa Yaya ko?”

    Bai ma yi wannan tunanin ba. Amma da yake ya san mahimmancin yin hakan sai ya gyaɗa kai. Salatin Yaya su ka ji su ka koma cikin soron.

    “Damuwa ce Yaya. Kada ki ɗaga hankalinki musamman tunda da mutane a ciki. Za mu kai shi asibiti.” Ɗaga shi su ka yi Kamal ya ƙarasa dashi motar. Taj kuma ya tsaya sakamakon maganar da Yaya ta fara yi.

    “Ƴar Ficika kuma ya ce…”

    Taj ya gallawa Ƴar Ficikan harara shi kuwa bawan Allah ya girgiza kai da sauri.

    “Wallahi ban faɗa mata komai ba.”

    “Me ku ke ɓoye min?” Ta tambaya hankalinta a tashe. Dama bata ga abin da zai ɗaga masa hankali ya faɗi ba. Bayan bikin nan shi ne babban farinciki da cikar burinsu.

    Gani su ka zasu ɓata lokaci sai kawai Taj ya ce Ƴar Ficika ya faɗa mata in sun tafi.

    “Amma don Allah ki bar maganar a wajenki kafin ya tashi mu san abin yi. Yanzu hankalin mutane ne kawai zai tashi.”

    “To, nagode. Idan kun je asibiti ka faɗa min. Sai na kira ƙaninsa ya taho.”

    Kana ganin yadda take magana sai ta baka tausayi. Da gani hankalinta ya kai ƙololuwar tashi. Tana dannewa ne kawai saboda mutanen cikin gidan.

    *

    Asibitin kuɗi Kamal ya kai su amma ba wanda ƴan gidansu su kw zuwa ba. Ana buƙatar file Taj ya buɗe musu na family. Aka shiga dashi ciki aka duba shi. Jininsa ya hau sosai shi da bashi da bp. Dole aka bashi gado ana jiran jikin ya daidaita. Drip aka saka masa da allurai sannan ya sami bacci.

    Zaman jiran Abdulƙadir ƙaninsa Taj da Kamal su ka yi a ɗakin. Kamal ya dube shi a tsanake.

    “Yanzu Happy duk abubuwanbda su ka faru da kai a gida ba su isheka ba? Kai da bakinka kake cewa za ka auri Hamdi. Auren ma gobe goben nan. Less than 24hrs. Har kana yiwa Abba ƙaryar sonta kake kawai don kafi kowa iya rigima.”

    “Allah da gaske nake ina sonta Happiness.”

    “Kai ɗin? Ya aka yi ban sani ba?” Ya tambaya don bai gaskata shi ba.

    Babu wani juya zance ya ce “Saboda nayi tunanin za ka ƙaryata duk wata niyyata ta janyo Abba Happy Taj. Infact bana tunanin da ka sani ko zuwan farko ba za mu yi gidan ba in ka san waye babanta.”

    “Lallai ka iya ganganci. Banda ɓoye min da kayi da kuma kana can tayi saurayi fa?”

    Taj ya yi murmushi “wallahi a next flight za ku ganni.”

    “Da ni na ce ina sonta fa?” Kamal ya yi tambayar idanunsa cikin na ɗan uwansa.

    “In sha Allahu ma Allah ba zai jarabcemu da son abu ɗaya wanda mutum ɗaya ya kamata ya so ba.” Ya haɗe kafaɗunsa don tsigar jikinsa tashi tayi.

    “Next time kada ka ɓoye min abin da ya kamata na sani.”

    Gira Taj ya ɗaga yana ƴar dariya ganin Kamal ya ɗauki zafi da gsske.
    “Bros, faɗa min gaskiya. Ba ka ciki ko? Kaga matar yara ce irina.”

    Fuska Kamal ya ɗaure amma da gani ya sauko “Ji min mutumin nan. To meye marabata da kai?”

    “Wata biyar mana. Kai fa kana cikin layin tuzurai.”

    “Baka da mutumci Taj. Ni ne tuzurun? Kai kuma teenager ko?”

    Taj ya gyaɗa kai yana dariya.

    “Banda ƙuruciya, teenager kamar ka ina zai kai budurwa kamar Hamdiyya?”

    “Inda ake kai matan…”

    “Ehemm. Ughhh” Abba ya yi gyaran murya da ƙarfi don ya katse hirar tasu haka. Yaga an kusa zuwa wurin da bai kamata kunnuwan uba su ji ba.

    Kan sa su ka yi suna tambayarsa jiki. Da sauƙi kamar yadda idanuwansu su ke iya gani. Ya ƙara yi musu godiya sannan ya roƙesu da su bar maganar auren nan haka. Allah zai bashi yadda zai yi da iyalinsa.

    “Idan Alhaji ya amince za ka yarda a ɗaura goben?” Taj ya tambaye shi kafin su fita. Shi ko a fuska bai nuna damuwa ba da Abba yake ta maganar su daina zancen.

    Shi dai Abba ya gama gajiya da zancen. Sannan ya matsu su tafi saboda so yake ya fice ya koma gida su shawarta da Yaya.

    “Me zai hana? Waye zai ƙi jinin Yaya Hayatu ko ma in ce zuri’ar Alh. Sule?”

    Jin wannan ya kwantarwa Taj hankali. Ya san Alhaji ba shi kaɗai bane shamakinsa. Shi kan shi Abba za a sha fama da shi.

    ***

    Salati Yaya ta fara yi kafin ta fashe da kuka. Zaune su ke a cikin wani ɗan falo ƙarami na ɗakin Abba. Ita da shi da kuma Baba Maje, Inna Luba mahaifiyarta da kuma ƙaninsa Abdulƙadir.

    Faɗan kukan Inna Luba ta fara yi mata kafin ta koma tausarta.

    “Indai ku ka nunawa yarinyar nan cewa kun karaya na tabbata ciwon da za ta ji sai yafi na fasa auren.”

    “Yaron nan ya cuce mu” cewar Abdulƙadir.

    “Na dai cuce mu. Rayuwar da na zaɓa ce ta zo tana bibiyar ƴaƴana” Abba ya faɗi da raunin murya.

    “In ka amince kuma kana jin Sajida ba za ta ƙi ba, yanzu zan kira Baballe ya zo gidan nan a rufe magana. Gobe ya auri ƙanwarsa bakin kowa alekum. Ko kuwa?”

    Abba ya nuna farincikinsa da godiya.

    “Zan so haka. Amma Maje ka tuna lallai akwai haƙƙi tsakaninmu da yaran nan. Aure ba a son yi masa shigar sauri. Yanzun nan sai ya jagwalgwala abin da ake son gyarawa.”

    Baba Maje ya dage harda cewa “indai ba kuma rowar ƴar za ka yi min ba ka amince kawai. Ba don ni na haife shi ba amma Allah yaro ne mai biyayya. Ina sa rai in Allah Ya so ba zai bamu kunya ba.”

    Yadda ya matsa ɗinnan sai Inna Luba ta ce a kira yaron. Ba a mayarda hannun kyauta. Kuma Allah kaɗai Ya san dalilin faruwar wannan al’amari.

    Cikin farinciki Baba Maje ya kira Baballe a gabansu. Allah Yasa baya nesa sosai ya ce gashi nan zuwa. Ita Iyaa da Siyama suna can wajen biki. Uwar baƙin hali kuma an tafi bikin ƙawa kamar yadda ta shirgawa Iyaa ƙarya.

    Kowa ya yi zugum ana jiran isowar Baballe. Baba Maje ya takura masa da waya saboda basa son ƴan biki su fara dawowa. An gargaɗe su lallai kada su wuce takwas a waje har amaryar.

    Baballe ya iso hankalinsa duk ya tashi. Irin wannan kira da wayar bai saba dasu daga mahaifinsa ba. Shi yasa ya dinga tunanin ko wani abu ne ya faru. Kafin ya iso sai da ya kira Iyaa yaji lafiyarta da ta Siyama. Ummi kuwa bata ɗauki wayar ba don kada a ce ta dawo gida. Sam ba ya raga mata akan halayen da ta tsiro musu da su a gidan.

    Tiryan tiryan haka Baba Maje ya labarta masa halin da ake ciki a gaban kowa. Wanda shi Abba ya so su keɓe. Don idan Baballe zai ƙi, ba zai ji nauyin idanuwansu ba.

    “Baba don Allah ko za mu koma soro mu yi magana” abin da ya ce kenan da Baban nasa ya matsa masa akan ya bada amsa.

    Gabansa sai da ya ɗan faɗi. Yaran yanzu ba a ci musu laya. Ya gama yabonsa shi ne yake son watsa masa ƙasa a ido.

    “Nan dukansu amsar da ka bani dole zan dawo musu da ita. Saboda haka gara ma kawai ka faɗa a gabansu.”

    “Baba don Allah” ya faɗi yana cije leɓensa na ƙasa. Shiru ba zai amfane shi ba a wannan lokacin. Shi yasa yake son faɗa masa dalilin da ya sa ba zai iya auren Sajida ba.

    “Ka je ka saurare shi don Allah. Share ire iren waɗannan abubuwan fa don mun isa su ne su ke zama dalilan yaji ko mutuwar aure. Allah Ya kiyaye.” Inna Luba ta faɗi tana nuna musu ƙofa.

    Ba don ya so ba ya tashi su ka fita. Ransa duk ya ɓaci don Baballe bai saba yi masa haka ba. Yaro ne shiru shiru mai sauƙin kai. Tsayinsu kusan ɗaya don ma shi shekaru sun ɗan durƙusar da shi. Fuskar Iyaa ma’abociyar fara’a ya ɗauko. Ga shi kyakkyawan matashi mai zuciyar nema. Banda aikin da ya samu ƴan watannin baya akwai shi da buga bugar neman halak. Bai san zama ko kaɗan.

    “Ina jin ka. Kada ka ce min budurwa gareka. Tunda ban san da ita ba, ba za ta zama silar da za ka watsa min ƙasa a ido ba.” Baba Maje ya ce a kausashe.

    “Ba haka bane Baba” Baballe ya ce a ladabce “ƴar uwarta nake so. Na ɗan jinkirta faɗa mata ne saboda wasu dalilai. Gaskiya ba zan iya aurenta ba alhali ina yiwa ƙanwarta so na aure.” Ya ƙarashe kai a ƙasa.

    Gumi ne ya tsatstsafowa Baba Maje. Ya dubi ƙofar cikin gidan.
    “Danƙari! To yanzu ya kake so nayi? Me yasa ku ke da zurfin ciki ne? Da na sani ko baka faɗa mata ba ai ba zan yi wannan karambanin ba.”

    “Idan zai bani ƙanwar sai ka sanar da su Kawu a ayi auren goben a madadin na Sajidan. Sai a jinkirta komai tunda ban shirya ba.” Baballe ya furta da hope ɗin baban zai amince.

    “Dama ko wace ai zan faɗa musu. Ni damuwata ma ita Hamdiyyan za ta yarda ne? Ko ka manta yadda su ka yi da Ummi a makaranta?”

    Da sauri Baballe ya ce “Zeenatu ce ba Hamdi ba.”

    “Wace Zeenatu kuma?” Baba Maje ya ce don kansa ya ƙulle.

    Baballe ya yi murmushi “Zee. Naga bata gama makaranta ba. Niyata zuwa ƙarshen shekara idan ta gama na san lokacin na ɗan yi tari. Sai na gabatar da kaina.”

    Kamar Baba Maje ya make shi don takaici ya ce “banza, kana can kana shiri wane zai shige tsakani sai dai kaji ana batun an kawo kuɗi.”

    Shi dai tunda yaga kamar ya sauko sai ya kwantar da hankalinsa. Ciki su ka koma tare. Kowa ya zuba musu ido. Baba Maje ya ɗan rissina kai na jin kunyarsu ya faɗa musu yadda su ka yi da ɗansa.

    “Alhandulillahi ai duk gida ne.” Cewar Abdulƙadir.

    “In kun amince dashi maimakon a fara kiran mutane ana cewa an fasa auren gobe, me zai hana a ɗaura nasu. In ya so sai ta tare bayan ta ƙare karatunta.”

    “Hakan ma ya yi. Bari su dawo daga wajen taron sai a faɗa musu.”
    In ji Inna Luba.

    *

    Banda gunjin kukan Zee babu abin da yake tashi a tsakar gidan. Sai da kowa ya watse sannan Inna Luba ta kira su har Halifa ɗakin Abba ta faɗa musu. Sajida ko uffan bata ce ba. Tashi tayi da mutuwar jiki ta koma ɗakinsu. Yaya za ta bita Abba ya hana.

    “Ki barta ta sami sararin yin kuka har taji sanyi a ranta.”

    “Ita kaɗai?” Ta share nata hawayen.

    “Wata damuwar tana buƙatar kaɗaicewa kafin zuciya ta karɓe ta. Idan tana buƙatarmu da kanta za ta neme mu.”

    Zee ya kalla da ta faɗa kan kakarta tana kuka kamar wadda za a zarewa rai.

    “Shikenan sai a fara yi min aure bayan ina da yayye?”

    Inna Luba tana shafa mata baya ta ce “Ja’ira. Ashe kukan ba na ƙin mijin bane. To ai da sauƙi. Yayyenki kuma ki sani kowacce lokacinta yana hannun Mahaliccinta kamar yadda naki yake.”

    “Mijin ma bana so Inna.” Ta ce tana ƙara sautin kukanta.

    “Bana son rashin hankali. Ihun da kike yi maƙota za ki tara mana ko me?” Yaya ta faɗi cikin fushi.

    Tana son Iyaa da Baba Maje a matsayin aminansu. Amma auren ne bata da tabbas a kai. Auren da aka yi ta soyayya ma gashi nan bai kafin ayi ya tashi. Ina ga wanda ya yi kama da cushe? Duk son su yi aure da take yi, bata so a wulaƙanta su.

    Hamdi ce ta riƙe Zee su ka koma ɗaki. A nan ta tarar da Sajida akan abin sallah. Kuka take yi amma babu sauti. Sai kwararar hawaye kawai. Sau tari ma’anar sunanta tana binta. Mutum ce mai yawan kai goshinta ƙasa wurin Allah.

    Zee daina kukan tayi ganin yayarta ta fita nutsuwa. Hamdi ta fita tayi alwala ita ma ta zo ta shimfiɗa abin sallah kusa da Sajida. Ganin haka ita ma Zee sai tabi sahu. Sun riga sun yi sallar isha tun ɗazu. Don lokacin shaɗaya ma ta kusa. Alƙur’ani kowacce ta ɗauka ta buɗe inda ya samu su ka fara karatu. Idan ka gansu abin tausayi kuma abin sha’awa. Yayinda ta ƴan uwan biyu ke nemawa kawunansu zaɓin Allah da sassaucin abin da ya tunkaro su, Hamdi su duka biyun take yiwa addu’ar zaɓin alkhairi. Tana fata kowacce ta sami aminci a ƙaddarar dake jiranta a gobe. Kuka kuwa idanuwansu ko gauta albarka.

    Duk wannan abu wayar Sajida vibrating take da kiran Safwan. Ita kuwa tayi alƙawarin sake haɗuwarsu ko jin muryar juna sai in sun haɗu bisa kuskure. Ba za ta ɗauka ba balle ace ta kasa haƙuri da wanda babansa ya zo har gida ya ci mutumcin nata uban.

    ***

    A ɓangaren Taj yadda abubuwa su ka kasance sai addu’a kawai. Roƙon Kamal ya yi akan ya kai shi gidan Yaya Babba ya ce babu ruwansa.

    “Ina son rabuwa da iyayena lafiya. Naga kai wannan is the last thing on your mind. Duk nasihar da nayi maka bata shige ka ba.”

    “Don Allah Abba bai baka tausayi ba?”

    “Ya bani, amma addua ce kaɗai taimakon da zan iya yi masa. Da za ka haƙura da auren Hamdi ni kuma nayi maka alƙawarin auren Sajida.”

    Haushin Hamdi da yake ji ya tuna, sai dai kuma wannan bai isa dalilinsa na haƙura da ita ba. Wannan tsiwar yake son ƙurewa da salon soyayyar da ya tanadar mata. Zafin kai kuwa ya yi imani da cewa bata kai shi ba. Zai gayyato ta cikin rayuwarsa su hau sama su faɗo tare. Barinta ne dai ba zai iya ba. Domin duka wannan rigimar tasu bata kama ƙafar son da yake yi mata wanda ya yi masa shigar farat ɗaya ba.

    Bari ya yi sai da Kamal ya bar gidan Ahmad sannan ya fice. Ya kusa isa gidan Yaya Babba sai kawai ya canja shawara. Taɓo mai adaidaita sahun ya yi.

    “Don Allah ka yi haƙuri. Kantin Kwari zani.”

    “Malam lissafin kuɗinka fa zai canja.”

    Taj ya zura hannu a aljihu ya zaro dubu uku sabbi fil ya bashi.

    “Ko akwai ciko?”

    Mai adaidaita ya saki murmushin da ya koma dariya.

    “Yallaɓai sai dai idan kuma sadaka za ka ƙara min akan wannan.”

    Taj dake neman taimakon Allah sai ya ƙara masa dubu biyu.

    “Idan mun je in jira ka ne Yallaɓai?

    “Da ka kyauta. Inda ka đauko ni zan koma.”

    *

    Alh. Hayatu na zaune a cikin ofishinsa dake hawa na biyu a katafaren ginin store ɗinsa mai suna Maitakalmi Enterprises dake kantin Kwari yaji ana ƙwanƙwasawa tare da sallama lokaci guda.

    Muryar wani yaron shagon ce wanda ya kasance ɗa a wajen wata da su ke ƴan maza zar da ita.

    “Kawu dama…”

    “Matsa na shiga” Taj ya ce da ɗan saurayin.

    Da sauri ya yi gefe, yayin da Alhaji ya tashi tsaye saboda gane muryar da ya yi.

    “Me ya kawo ka?” Ya ce da kakkausar murya.

    Yaron da ya nuna masa office ɗin don bai taɓa zuwa ba tunda aka yi ginin sai yau ya kalla. Cikin sauri ya rufe ƙofar ya bar wajen. Taj ya juyo ya kalli mahaifinsa sai kawai ya sauke gwiwoyinsa duka biyu a ƙasa.

    “Alhaji na zo neman izini da amincewarka ne.” Ya faɗi yana kallon uban.

    “Dama nayi wannan isar a rayuwarka ne?”

    Zuciyarsa dokawa take da ƙarfi saboda fargaba. Amma ya san cewa indai ya rasa goyon bayan Alhaji, ba zai taɓa auren wadda yake so ba.

    “Ka fi ƙarfin komai a rayuwata.”

    “Shi yasa ka zaɓi barina akan ka ajiye burinka?”

    Taj ya girgiza kai “baka bani zaɓi ba a lokacin da ka koreni Alhaji. Hukunci kawai ka yankewa kuskurena.”

    Zuciyarsa hasala tayi. Ɗan nasa ya fishi gaskiya. Wannan ne ya ɓata masa rai.

    “Rashin kunya ka zo ka yi min?”

    “Ban isa ba.” Ya ɗaga kai daga durƙuson da ya yi “aure nake so ka yi min gobe don Allah.”

    “Ka fara shan ƙwaya ne Tajuddin? Ni za ka tunkara da wasan kwaikwayo irin wannan?”

    “Ƴar wajen Habib Umar ce. Simagade na Soron ɗinki.”

    Yana gama magana ya rufe idanuwansa saboda jiran saukar mari daga Alhaji. Da yaji shiru na wasu daƙiƙu sai ya buɗe idanunsa. Abu na farko da Alhaji ya fara ce masa shi ne,

    “Me ka ke taƙama da shi ne Taj? Kuɗin da kayi ne kake jin ya isa ka kawo min zancen banza irin wannan?” Ya nuna ƙirjinsa “Ni? Ni za ka cewa kana son auren ɗiyar Habibu?”

    “Bana taƙama da komai Alhaji sai matsayina na jininka. Ka juya min baya a karo na farko amma Allah Ya tsareni daga faɗawa rayuwar da kake guje min. Ba yin kaina bane. Ba kuma isarka bace ko tawa. Albarka ce kawai daga Allah wadda na tabbata kullum kana roƙa min.”

    Kallon mamaki kawai Alhaji ya dinga yi masa. Yana kuma tuno kalaman Gwaggo na ƙarshe ƙarshe a gare shi da take cewa Taj tamkar shi ne a madubi. Yadda yake haka ya haifo ɗa irinsa. Duk lokacin da yake son taƙwara ɗansa, to ya fara bari shi ma duniya ta tanƙwara shi.

    “Shi yasa yanzu ma ka shirya saɓa min saboda kana jin komai zai tafi yadda kake so?”

    “Wannan karon ina jin tsoron idan ka barni kada na saɓawa Allah akan soyayya…”

    “Kai Taj ka kiyayeni. Ni kake faɗawa waɗannan maganganun?” Alhaji ya furta kansa na yi masa wani irin nauyi.

    “Ina sonta Alhaji.” Ya faɗa kai tsaye abinsa.

    “Ita ƴar Habibun?”

    “Eh.”

    “Zo ka zauna”

    Don dai shi tsayuwa tana neman gagararsa. Kan kujera su ka koma. Alhaji ya daɗe yana tunani kafin ya ce da Taj,

    “Ka tafi gida ka jirani.”

    “Gidan Yayan za ka zo?” Ya tambaye shi da wata irin murna don ya san ina yake nufi.

    “Gidana nake nufi Tajuddin. Ka je can ka jirani.”

    Godiya ya yi ya tashi ya fita. Sanin me Alhaji zai ce sai Allah. Shi dai buƙatarsa ita ce ya sami damar yin auren da zai fidda Abba daga kunya gobe da izinin mahaifinsa. Haƙuri ya bawa mai adaidaitan ya ce inda za shi ya canja. Mutumin ko a jikinsa tunda ya caski kuɗi.

    *

    Mutane sun kai biyar da Alh. Hayatu ya bawa aikin yi masa duk wani binciken da ya dace akan Abba Habibu. Kafin isha’i dukkanin bayanai sun riske shi. Tun daga zamansa a Lagos bayan ya yi aure har batun auren babbar ƴarsa da za ayi gobe. A duka bayanan yafi mamakin dalilin da yasa Taj da Kamal nemo Simagade. Da kuma aikin da Taj ya bashi. Share wannan ya yi ya kira mahaifin Safwan domin kuwa ya san shi duk da ba wai abokai bane. Shi kuma yadda yake mutunta Alhajin yasa ya faɗa masa auren nan fa babu da dalilinsa. A ƙarshe yadda ya fahimta wanda kuma da ƙamshin gaskiya a ciki, auren ragewa Habibu baƙinciki Taj yake son yi.

    Dariya ce ma ta kama shi. Wato ta wannan hanyar Habibu ya zaɓi ya dawo cikin rayuwarsa. Lallai zai nuna masa kuskurensa a lokacin da ya dace.

    *

    Gida kowa murna ganin Taj ya shigo kuma ya ce Alhaji ne ya yi masa izini. Inna harda kukan farinciki. A gidan ya yi Magriba sannan Kamal ya dawo. Yana ganinsa ya sha jinin jikinsa.

    “Wace tsiyar ka ƙulla?”

    “Alkhairi dai. Zancen auren Hamdi nayi masa.”

    A harzuƙe Kamal ya ce “ba ka da hankali ko? To wallahi yana da bindiga. Ƙarshenta ma harbeka zai yi.”

    Taj ya ƙyalƙyale da dariya. Kamal ba dai tsoro ba. In anyi magana kuma ya ce Taj ɗin ne matsoraci.

    Wuraren tara na dare Alhaji ya dawo. Yana hawa sama ya kira Taj. Bai nuna masa ya san komai ba. A gabansa ya kira Yaya Babba ya yi masa magana.

    “Ɗanka ne ya ɗauko aure bagatatan. Wasu matsaloli ne su ka taso da su ka sanya auren dole ayi gobe. Zan zo gidanka da safe kafin lokacin mu yi magana.”

    Yaya Babba farincikin jin Alhaji ya tsayawa Taj bai bashi damar zurfafa tambayoyi ba.

    “Kana iya komawa gidan yayan naka. In sha Allahu gobe za a ɗaura.”

    Godiya mara adadi Taj ya yi masa.

    “Ba sai ka faɗawa matana na ba domin ko Abu ba za ta baka goyon baya ba. Zan yi musu magana da kaina.”

    Duk da cewa a zuciyarsa yana jin kamar shigo shigo ba zurfi Alhaji yake masa, sanin cewa baya magana biyu yasa bai ji ko ɗar ba. Ya tabbata za ayi auren in sha Allah.

    ***

    Gidan Abba Habibu tamkar ba shi bane jiya da yamma ake ta hayaniyar shirin zuwa sisters’ eve. Yau shiru kamar babu mutane. Gashi dai ba a yi shelar me ya faru ba. Amma ganin ƴan biki babu walwala sai kowa ya sha jinin jikinsa.

    Banda ƴan mazan gidan Alhaji babu wanda ya san da maganar ɗaurin auren sai ƴan uwansa maza. Su duka mamaki bai hanasu haɗuwa a masallacin juma’ar da za ayi auren bayan an idar da sallah ba. Kamal ne ya bawa Taj sababbin kayansa masu babbar riga. Ya tuƙosu a mota zuwa masallacin. Sai dai jikinsa tamkar anyi masa duka. Gani yake akwai abin da zai biyo bayan wannan ɗanyan kai na Taj. Alhaji ba zai barshi ya sha ba.

    Ana idar da sallah Liman ya yi sanarwar ɗaurin aure kamar yadda aka faɗa masa. An fara da Abubakar Maje Garba (Baballe) da Zeenatu Habib Umar akan sadaki naira dubu hamsin. Masallaci ya đauki kabbara.

    Abba yana share ƴar ƙwallar farinciki sai yaji an taɓo shi. Yana juyawa damansa ya yi tozali da Alh. Hayatu. Ba ƙaramin ruɗewa ya yi ba kuwa.

    “Kwantar da hankalinka. Sunan yarinyar wajenka da Taj yake so za ka bani. Ina fata ka yi masa izinin aurenta.”

    Abba baki ba rawa ya ce “Yaya Hayatu…”

    “Kada ka damu. Nima short nktice da ya bamu ne ya hanani zuwa mu yi maganar. Ya sunanta.”

    “Hamdiyya.”

    Alhaji ya juya fuskarsa ba yabo ba fallasa ya faɗawa Yaya Babba. Shi kuma ya sanar da Liman. Nan aka sake sanarwa. An ɗaura auren Tajuddin Hayatu Sulaiman da Hamdiyya Habib Umar akan sadaki dubu ɗari biyu.

    A karo na uku sai ga wani tsoho an gunguro shi akan wheelchair. Ba kowa ne ya turo shi ba kuwa illa Safwan. A gaban Abba ya tsayar da kujerar. Ya ɗuka a kunyace. Tsohon ya dubi Abba da murmushi a fuskarsa.

    “Ni ne mahaifin Sabi’u. Kuma ni zan yiwa jikana waliyyi. Ina fata za ka haƙura da abin da ya faru jiya wanda bani da masaniya. Sai ɗazu yake cewa wai an fasa. Shi ne na kira Safwan ɗin ya yi min bayani.”

    Baba Maje ne akan gaba wurin cewa sun amince. Nan take Liman ya ɗaura aure na uku. Safwan Sabi’u Mamman da Sajida Habib Umar.

    Allahu Akbar
    Abba sakaya fuska ya yi cikin babbar riga yana kukan farinciki.
    MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE

    Note
    error: Content is protected !!