Rayuwa Da Gibi – Chapter Fifteen
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Rashin wuta da ake fama dashi ya hana Hamdi sayen naman yin meatpie da ake sayarwa a shagon Abba kullum. Har ta haƙura da cinikin ranar saboda da ta saya a daren ko ta soya zafin da ake zai iya canja mata ɗanɗanonsa idan ta haɗa. Sai Abban ya kira ya ce ko da yamma ne idan tayi Halifa ya kawo saboda ana so. Sai aka yi rashin sa’a Haiifan bai dawo daga makaranta da wuri ba. Ita kuma tana tsoron yin kwantai.
“Yaya zan kai masa da kaina.”
Izinin tafiyar tayi mata sannan tayi mata kwatance yadda za ta gane. s
Sau ɗaya ta taɓa zuwa tun dawowarta. Adaidata ta samu har can. Shagon a bakin titi yake a gefen wata plaza. Tana sauka ta matsar da kayanta gefe sosai ta kira Abba kamar yadda Yaya ta ce tayi idan ta iso. Kira huɗu, wayar tana ta ringing babu amsa. Gashi taƙi jinin a dinga kallonta. Madaidaiciyar cooler ɗin da ta sako meatpie ɗin mai hannu biyu ta kinkima ta ƙarasa.
Wurin a cike yake Masha Allah. Mutane suna ta kai kawo ana ta sayen abinci. A bakin ƙofa ta kuma tsayawa ta kira Abba. Wayar ko shiga bata yi ba wani ya fito ya ganta.
“Ahhh, wannan dai duk yadda aka yi ɗiyarmu ce don ga kama nan. Ƴan mata shigo daga ciki. Aunty Simagade yau ana ta fama da baƙi.”
Gaban Hamdi ya yanke ya faɗi. Da ganin mutumin Abba zai girme shi. Duk da dai bleaching ya caɓalɓala masa fuska fiye da ta Abban. Ya wani sha jallabiya da ɗaurin ƙirji. Kansa kuma ya yi ɗaurin ture ka ga tsiya da ɗankwali irin zanin.
‘Me ya kawo ɗan daudu wajen nan?’ Ta yi wa kanta tambayar cikin yanayin ƙuncin rai.
Ashe kallo yana ciki. Tana sanya ƙafafunta wani irin baƙinciki ya turnuƙeta. Akwai kwastomomi da yawa a ciki. Amma fa a yau dandazon ƴan daudu sama da huɗu ne su ke ta karakaina wajen ɗaukar odarsu da kawo musu abinci. Muryoyinsu da taƙi jini sun cika ko ina. Sai shewa ake ana yiwa juna shaƙiyanci. Ita kuwa waige ta kama yi tana son hango mahaifinta.
*
Ubangidan Abba a birnin Jedda lokacin da yake ganiyar daudancinsa ne ya zo Kano. Ƴar Ficika ake kiransa saboda ƙanƙanta da ƙwarewa a iya shege. Duk wani mai ji da hayaƙinsa idan ya gamu da Ƴar Ficika a Saudiyya dai sai ya sauke kai. Clicks da connections na fitina babu irin wanda baya haɗawa. A lokacin da suke tare da Abba ya so ƙwarai ya sanya shi a hanyar da kowa yake bi ya yi kuɗi. Sai ya fahimci Habibu ba komai ne a gabansa ba illa girki. Shi dai a tura shi gaban murhu ya haɗa abinci. Ƙaryar mutum ya ce ya taɓa ganinsa a wani waje sama da wurin girki ko cin abinci. Ƴar Ficika sai ya tsaya masa. Ko a bayan idonsa wani ya nemi yiwa Abba wayo ya sanya shi a gurguwar turba sai ya ci mutumcin mutum. Lokacin da Baba ma yaje wurinsa, da Abba zai dawo Ƴar Ficika ne ya biya masa rabin kuɗin jirgi.
Bayan dawowarsa gida babu abin da ya sake haɗa shi da kowa cikinsu. Ya tattare wannan shafin rayuwar tasa ya watsa a shara. Yaran da suke aiki a ƙarƙashinsa kaf babu ɗan daudu. Maza ne kawai masu ra’ayin girki a dalilin rashin wata sana’ar. To yau kwana uku kenan da Ƴar Ficika ya nemo Abba. A kamen takari aka watso su gida shi da wasu yaransa. Gashi girma ya kama shi amma zuciyar nema bata mutu ba. A nan gida Najeriya kuma bashi da ido da ƙafa kamar Saudiyya. Yana neman abin yi ne ya haɗu da wanda ya san inda Abba Habibu yake. Shi ne aka kawo shi har gidan abincinsa.
Abba bai ɓoye masa sabuwar rayuwar da yake yi ba. Ƴar Ficika yaji ya kwaɗaitu da samun darajar da ya rasa a wajen danginsa. Shi da yaransa babu wanda baya fuskantar ƙyama daga ahalinsa. Godiya ya yiwa Abba ya ce kuma zai buɗe gidan abinci. Yana fata zai taimaka masa.
“Ɗan halak baya manta alkhairi. In sha Allahu zan maka iya ƙoƙarina.”
“Idan babu damuwa zan so ganin yadda salon kasuwar take a nan. In zai yiwu ma kawai lokacin tafiyarka sabon restoran ɗin sai na karɓi wurin nan.”
Abba bai yi ƙasa a gwiwa ba ya kira Taj ya sanar dashi. Shi kuma jin taƙaitaccen tarihin Ƴar Ficika da tsoron da Abba yake na kada ya komawa rayuwarsa ta gidan jiya sai ya amince.
“Idan mai laifi ya so tuba yana da kyau a bashi dama. Rashin yin hakan na taimakawa wajen sake dulmiyar dasu cikin ayyuka marasa kyau.”
Taj ya ce “haka ne Abba. In ya rasa samun aikin da zai bashi halal zai koma ya nema daga haram ko yaya take.”
Da wannan shawarar Abba ya amince masa. Shi kuma saboda jindaɗi ya ce zasu dinga tayasu aiki duk lokacin da su ka sami lokaci tunda ba su da abin yi. Shi ne fa su ka zo yau. Girki harda wanda Abba ya manta. Yaji daɗi domin yau kasuwar ta buɗe fiye da kullum. Ya alaƙanta nasarar da kyakkyawar niyyarsa ta taimako. Don bai manta wulaƙancin da ya sha ba sanda ya dawo. Da wanda ya gani a dalilin neman wurin kafa sana’a da ya rasa wancan.
*
“Kai, kai, kai…Tabarakallah.”
Hamdi ta waiga baya ta haɗa ido da wani ƙarmasasshen mutum da ita kanta ta fi shi tsayi. Kanta ya yi yana murmushi kamar zai rungumeta. Kafin tayi baya Abbanta ya janyeta gefensa. Ƴar Ficika ya cigaba da murmushi yana kallonta.
“Wannan ma taka ce?”
Yaronsa da ta haɗu dashi a waje ne ya bada amsa.
“Aiwa, baka ga kama ba? Anti Simagade an dasa kyakkyawar shuka tayi fure mai ƙamshi.” Ya faɗi yana lanƙwaya hannu da juya idanu.
Wani irin ɗaci ya dinga kai komo a wuyan Hamdi. Da ƙyar ta yiwa Abba biyayya ta gaishe da mutanen da ya gabatar a matsayin abokan sana’arsa a Saudiyya.
“Cewa za ka yi mu iyayenta ne. An riga an zama ɗaya. Za ku yi ta ganinmu har sai mun saba.”
“To” ta ce da gatsali ta kuma juya ko coolar bata ajiye ba tayi waje.
Tana fita hawaye ya wanke mata fuska. Wannan wace irin rayuwa ce? Ta ɗauka Abba girki da abubuwa na siffar mata kawai yake yi. Me zai sa ya mu’amalanci mutane irin waɗannan? Don sai da ta gansu ne ma ta gane me ake nufi da asalin ɗan daudu.
“Hamdi”
Sarai taji kiran da yake mata amma ta ƙara sauri. Kafin ta ƙarasa titi ta dire coolar a gabanta ta ɗagawa wani adaidaita sahu hannu. Kafin ya gama tsayawa ta faɗa ciki su ka yi gaba.
Abba ya kalleta ya juya ya kalli Ƴar Ficika da ya biyo shi.
“Ba dai ganinmu bane ya ɓata mata rai ba?”
Murmushi ya ƙaƙalo “ahh haba dai. Sauri take yi.”
Ƴar Ficika ya murmusa “ko kai a gabana ka ƙarasa girma fa Habibu. Ta yaya zan kasa gane abin da na saba gani?”
Cike da jin nauyi Abba ya faɗa masa yadda a baya bata ma son nuna shi a matsayin uba. Yana ganin babu mamaki yanzu wannan abin da tayi yana da nasaba da tunaninta na komawarsa ga ɗabi’ar baya.
“To ko mu daina zuwa? In ya so lokacin da ka bar nan ɗin sai mu dawo?”
Allah Ya sani kamar ya ce eh, to amma nauyi da tunanin me zai je ya dawo a rayuwar su Ƴar Ficika sai ya ce a’a. Yau kaɗai da ya haɗu dasu ya ga wani irin farinciki da annashuwa a tare dasu. Sun sake suna ta aikin abin da su ka fi ƙwarewa wato girki. Har sai da ya yi tunanin me yiwuwa tun dawowarsu babu wanda ya sami tarba mai kyau da mutuntawa sai yau.
***
Hamdi tayi kuka tun daga hanya har gida. Da ƙyar ta iya labartawa Yaya abin da ta gani. Abba na dawowa kuwa Yaya ta kawo zancen ita ma nata ran a ɓace.
“Yaya Habibu ka sani cewa bahaushe na cewa abokin ɓarawo shi ma ɓarawo ne. Yanzu duk wanda ya ganka da mutanen nan zai yi maka kallon irinsu.”
Da laluma ya dubeta “Jinjin juya baya ba nawa bane ga wanda ya nemi taimakona. Duka duka yaushe muka sami wannan rayuwar bayan haɗuwa da yaron nan Taj? Ko har kin manta cin zarafin da aka dinga yi min akan neman shago? Duk unguwar da naje sai su ce kada yaransu su yi koyi dani basa so.”
“Naji kuma duk na fahimta. Amma hanyoyin samun lada ai suna da yawa. Shigowar mutanen nan rayuwarka a wannan lokacin da kake neman tada ƙimarka a cikin mutane gaskiya ba zai haifi ɗa mai ido ba.”
Ta sake faɗi cikin fushi. Duk yadda ya so ɓullo mata taƙi amincewa. Tsayuwa ya yi akan bakansa shi ma. Yau dai ɗaya zai yi abin da yake jin ya dace ko ba zai faranta ran iyalinsa ba.
“A bar maganar nan. Indai Ƴar Ficika ne, ba zan kore shi ba.”
“To ai shikenan. Allah Ya kyauta ɓacin rana.”
***
Yadda Salwa ta matsawa Taj da waya da messages a duk wata kafar da zai gani, haka Anisa ma take yi. Gashi dai basu san da zaman juna ba amma kowacce ta matsa lamba.
Ita Salwa banda ƙawa har Maminsu ta san irin soyayyar da take yiwa Taj. Da fari ta nuna rashin goyon baya saboda ɗan tsohon miji ne. Sai da taji ta kuma ga waye Taj a wani bidiyon girkinsa a youtube da Salwan ta nuna mata tayi mubaya’a. Matashi ne mafarkin duk wata budurwa. Burin duk wata uwa da take son ƴarta da arziƙi. Ko da wasa girkinsa bai zo ranta ba balle ya dameta. Yana da kuɗi kuma ta san asalinsa. To me ya rage?
“Kada ki yarda ya manta dake. In ya tafi ki dasa kanki a cikin rayuwarsa.”
“Ta yaya? Ko sau ɗaya bai taɓa nemana ba da kansa.”
Mami tayi dariyar manya “wannan ai duk ba wata matsala bace. Ke ki dinga bibiyarsa. Gaisuwa safe, rana da dare. Ƴan abubuwan nan namu na mata ku baku iya ba. Sai a zauna sakato ana jiran namiji ya yi komai.”
Salwa ta sunkuyar da kai “Mami idan mace tana bin namiji fa wulaƙanta ta yake yi.”
Taf…taji saukar duka a kafaɗa. Rai a ɓace Mami ta ce “banda shashanci dama ai ba da soyayya za ki bishi ba. Kulawa kawai. Ko kissar ma sai na koya miki?” Ta harari ƴarta.
“Na fahimta Mami.”
“Ko ke fa.”
Da haka Salwa ta kafa masa ƙahon zuƙa. Waya da saƙwanninta babu wani abu da zai bada ita har yasa Taj gudunta. Yayana sama Yayana ƙasa ne dai. Gaisuwa, bibiyar ayyukansa da yi masa fatan alkhairi. Tun yana sharewa har dai bisa shawarar Kamal ya soma amsa mata a mutumce.
“Ba’a san inda rana za ta faɗi ba. Ka daina wulaƙanta duk mai nuna damuwarsa a kanka.”
“Kada ta sa rai ne Happiness.”
Dariya Kamal ya yi “kai ma kamar wani ɗan yaro in kayi wani abin. Ai yadda ta zo maka a ƙanwa haka za ka je a matsayin yaya. Tunda baka so ta bijiro da zancen soyayya sai ka toshe ƙofar.”
“Kamar ya?”
“Ka dinga bata labarin wata a matsayin budurwarka. Wataran ka ce ma tana gaisheta.”
Girgiza kai Taj yayi kamar yana gaban Kamal ɗin “ba zai zama cin fuska ba kuwa?”
“A ƙanwa fa tazo maka. Kuma dai kayi mata hannunka mai sanda taƙi ɗaukar haske. Ba sai ka bita ba kawai a tafi a haka. Ya dai fi akan ka dinga shareta wanda za ta fassara a matsayin wulaƙanci.”
A haka suke ta tafiya. Ya Taj da ƙanwarsa Salwa.
A ɓangaren Anisa kuma bai san wane tudu wane kwarin aka bi ba sai ji ya yi Amma ta tado masa da zancen ko za su fara haɗa lefe kafin su koma gida.
“Lefe kuma? Na wa?” Ya tambayeta kai tsaye babu mamaki a tare dashi.
“Kada ka raina min wayo Taj. Ya ku ka yi da Anisa?”
“Anisa kuma?”
Amma ta ɗaure fuska “Allah idan na sake magana ka ce min ‘kaza kuma?’ Sai ranka ya ɓaci.”
“Yi haƙuri Ammana.” Ya yi mata murmushi.
Mayar masa tayi sai kuma ta sake shan kunu.
“Ka san sau nawa Daddy yana yi min maganarku? Sai dai nayi ta kame kame saboda ka ƙi cewa komai.”
Yadda su ka yi da Anisa da Hajjo ya faɗa mata.
“Ni na zata mun gama magana tunda ta fahimceni.”
Yanayin Amma duk babu wani kuzari ta ce “Maganar da aka fara daga sama ai a can ya dace a ƙare ta. Me yasa ba ka faɗa min ba?”
Ya yi shiru. Ba zai iya ce mata yaga kamar tana so ba shi yasa ya kasa sanar da ita ba.
Anti da kanta tayi mata waya tana cewa wai ta kira tayi mata murna ƴarta ta sami miji. Anisa da Taj sun daidaita.
Da murna Amma amsa mata da “cewa zaki yi na cigaba da tari. Allah Yasa damu za ayi.”
“Amin amin” Anti ta amsa da farinciki.
Da su ka yi waya da Daddy ma zancen kenan. Har yana cewa idan su ka dawo da kansa zai yiwa Alhaji magana. Ƙudurin Taj na aure bayan ya koma gida ba abin a kawo ido a zuba masa bane. Dole su za su yi nasu ƙoƙarin a yanzu da Taj ya zama successful su mayar dashi gaban mahaifinsa.
Ya gama tsare tsaren hanyoyin da zai bi domin bawa Alhaji haƙuri ya janye fushinsa. Wanda hakan ya yiwa Amma daɗi sosai. Shi ne ta tayar masa zancen shi kuma ya nuna ba haka aka yi ba.
“Ni yanzu ya kake so in yi Taj?”
Ta ma rasa ta inda za ta ɓullowa lamarin. Idan ta nuna bata so a yanzu da maganar ta fito daga bakin kishiyarta da mijinta kowa ita zai zarga. Za a ce ita ce bata so. Sannan ga dukkan alamu ma dai gadar zare Hajjo take neman ko ma a ce ta ƙulla mata. Kuskure guda zai sa a ce tana gudun ƴar kishiya. Ko kuma a gorantawa Taj rufin asirin da aka yi masa. Ta san Hajjo sarai. Idan abu bai tafi yadda take so ba to mutum ya shiga ɗari ba ma uku ba.
“Kasan me nake so da kai?”
Ya girgiza kai “ko mene ne zan yi miki Amma.”
“Kada ka nuna musu komai ta waya yanzu. Don Allah ko da wasa kada kayi abin da Anisa za ta sami maganar da za ta kaiwa Hajjo. Idan mun koma gida sai ayi maganar a gaban kowa. Yanzu ko me zamu yi a waya babu mai fahimta.”
Ko da Daddy ya zo lokacin da za ayi mata send-off party na retirement basu nuna komai ba ita da Taj. Lafiya lafiya yake waya da Anisa su gaisa. Idan bata kira ba sai ayi sati biyu bai nemeta ba. Bisa shawarar Anti da Hajjo da su ka kitsa wancan zance na amincewarsa duk da Anisan bata so haka ba take yawan kiransa ko ta tura saƙo ta whatsapp.
Wata gomq sun ƙare kamar ƙifta ido da buɗewa. Duk wani shiri na komawarsu gida ya kammala. Catering services ɗinsa na Happy Taj ne dai bai rufe ba. Duk lokacin da buƙata ta tashi zai iya komawa ya yi aikinsa ya dawo gida.
Zuciyarsa a ranar da za su tafi tana cike da ɗokin sake ganin Hamdi. Ba tare da saninta ba, duk wasu abubuwa musamman wanda su ka shafi samari yana sani a wajen ƴan uwanta. Zee akwai surutu. Ita ke faɗa masa irin abin da Hamdi take yiwa samari idan sun zo.
“Ni fa ina ganin kamar akwai wanda take so” ta taɓa faɗa masa watarana.
Murmushi yayi shi kaɗai da ya ji muryar Hamdi tana cewa Zee “gulmammiya, yau kuma faifaina aka buɗewa Salman Khan? Ki gama Yaya tayi mana shari’a don ba yarda zanyi ba.”
Zee ta diririce, wayar da bata gama ba kenan ta tashi tana bata haƙuri.
Ita kuwa kaza huce kan dami tayi. Mutumin nan na Abuja da bata san sunan shi ba ta riga ta cire shi a rai, tana kuma jin haushin yadda ya jirgata ta hanyar nuna kamar ya damu da ita.
***
Dogon tsaki mai madda da gunna Ummi ta saki a lokacin da Iyaa take duba katunan bikin Sajida da Yaya ta kawo da kanta.
“Allah Ya shiryeki Ummi. In Allah Ya so ba zan taɓa aibata ki da bakina ba balle ki fi haka.”
“Me kuma nayi? Yanzu mutum bai isa ya yi tsaki ba sai an fassara shi?”
Tashi Iyaa tayi ta bar falon. Idan ta zauna tabbas za ta ƙare da dukan Ummi da duk abin da ya zo hannunta. Haka su ke ta fama tun bayan dawowarta daga makaranta. Ummi ta kangare fiye da tunaninsu. Maganar aurenta da aka sa ran yi da ta gama makaranta tabi ruwa. Mijin dama na gida ne. Duk shaiɗancinta tana masifar son sa kamar rai. Zancen duniya da baya ɓuya sai gashi mahaifiyarsa da su ke ƴan maza zar da Baba Maje sannan ƴar mace da namiji da Iyaa ta zo har gidan neman ƙarin bayani.
Yayinda Ummi take ta tsula tsiyarta a makaranta bata taɓa tunanin akwai idon sani da za su iya kawo zancenta gida ba. Sai gashi a hawan hawa maganar bullying ɗinta da haura katanga tana bin samari yawo ta dawo. Maganar ayi ƙarya ko kwaskwarima ma ba za ta yiwu ba. Dole su ka faɗi gaskiya da roƙon rufin asiri.
“Maganar nan ba za ta taɓa fita daga bakina ba in sha Allahu. Amma fa aure babu shi Fisabilillahi”
Baba Maje ya kalli ƴar uwarsa, sai dai bai ji haushinta ba sosai. Ko shi ne zai iya yin haka.
Washegari ya mayar musu da kuɗin aurensu. Kayan kuma su ka ce a barsu. A ranar babu wanda ya runtsa a gidan. Ummi kusan hauka tayi musu tuburan. Kuka da magiya harda barazanar tana son auren.
“Kowa ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa. Ke ki ka haƙawa kanki wannan ramin. In kina da hankali sai ki canja tsarin rayuwarki don gujewa maimaici.”
Tana gunjin kuka ta ce “yanzu Baba akan ɗan daudu da ƴarsa ka gwammace rayuwata ta zama haka? Baka barni nayi jarabawa ba sannan auren ma ka kasa hana a fasa shi?”
“Ɗan daudun ne kuma yake ta fafutukar ganin kin koma makaranta ba.” Ya ce da faɗa “amma da yake kin daɗe kina taɓa mutumcin mutane Allah Yana yi miki talala yanzu ai kin ga ishara. Duk ƙoƙarinsa abu yaƙi ci yaƙi cinyewa. Ni kuma da hannuna ba zan sake kai ki wata makarantar ba.”
Gidan da su ka barta basu tsira ba. A hankali ta tsiri fita yawo. Idan ta dawo ayi faɗan, dukan da nasihar duk a bayan kunnuwanta. Shafawa idanunta toka kawai tayi tana abin da ranta yake so. Cikin watanni kaɗan ta ɗashe fata ta koma fara tas. Ga magungunan da take sha na supplement masu ƙara wasu sassan jiki. Halittarta duk ta sauya ta koma wata daban. Duk inda ta ratsa maza ke bibiyarta suna kashe mata kuɗi. Wayo da dabara irin nata yasa taƙi yarda ta bada kanta. Amma fa tana bari su fanshi wahalarsu ta hanyoyi daban daban. Hukuncin faɗa da duka ya ƙare. Sai nasiha da addua tsakaninta da iyayenta.
Halin da ta shiga yana ci wa Abba da Yaya tuwo a ƙwarya. Gani su ke kamar sanadiyarsu rayuwar ƴar aminansu ta gurɓace. Yayinda su Baba Maje kuma su ke ganin dubunta ce ta cika. Halayen da take ɓoyewa su ka bayyana. Ba don abin da ta yiwa Hamdi ba da haka za ta yi ta ha’intarsu ƙila har gidan miji tana rayuwa biyu ba a sani ba.
Ummi ta sake ɗaura ɗammarar watsa rayuwar Hamdi a duk lokacin da nata auren ya tashi. Kuma tsakin da tayi ba komai ya janyo ba sai takaicin lokacin ramuwarta da bai yi ba.
***
Kimanin sati uku kafin bikin Sajida aka gama komai da ya dace a HAPPY TAJ. An kashe kuɗi domin ƙawata wajen yadda zai janyo mutane. Taj da Abba da kansu su ka dinga yiwa mutane gwaji idan sun zo neman aiki. Banda yaran Abba, sai da su ka ƙara mutane masu ayyuka daban daban a kitchen ɗinsu. Girki, wanke wanke, serving abinci, waiters, cashiers da masu yin fruit juice, mocktails da icecream. Gabaɗaya kitchen ɗin maza ne. Sannan ya nemi inda za su dinga sayen kayan abinci. Komai ya tafi cikin tsari. Ƙannensa Bishir da Abba su ya damƙawa ragamar tabbatar da kayan buƙatar kitchen ba za su yanke ba. Sun daidaita da masu kayan masarufi na kasuwa akan wannan. Spices kuma na recipe ɗinsh za su dinga haɗawa saboda haka raw ɗin kawai su ka nemi mai kawowa. Dankali da kayan miya kuma fresh masu kyau da tsafta daga wajen ƙawar wata sister ɗinsu Rumanatu mazauniyar Jos (08065530483) za su dinga saya. Ya zamana dai babu inda su ka bari haka nan.
Masu naman tsire ko gashi su ma interview da gwaji aka yi musu. Iyawa kaɗai bata da garanti sai an duba tsaftar mutum da ingancin kayansa. Haka kuma aka yi a ɓangaren kayan fulawa. Saboda kawai Taj yana son ɗaukar Hamdi sai ya ce bakery ɗinsu mata za a saka.
Application babu kama hannun yaro. Da ƙyar su ka zaɓa don babu laifi a Kano akwai masu sarrafa fulawa daban daban da kayansu suke da inganci. Wata ƙanwarsa da ta dinga zuzuta masa ƙawarta Zahra wadda aka fi sani da Donutfairy (08065156303), dole yace a nemota. Ya ɗanɗana doughnut, banana bread da youghurt ɗinta. A take ya nemi signing contract da ita tunda matar aure ce. Aka ƙayyade adadin abin da za ta dinga kawowa kullum da farashinta.
Ɓangaren Kamal ma boutique ya tashi sai wanda ya gani. Garden da wurin wasan yara duka an gama zuba ma’aikata. Ranar Juma’a aka yi sauka domin kore kowanne shaiɗanci da neman albarka daga Allah. Sai kuma aka sanya sati mai zuwa a matsayin ranar buɗe restaurant ɗin. Anyi ta sanya talla ta gidajen yaɗa labarai da shafukan sada zumunta. Akwai discount ga mutanen da za su zo a wannan rana. Ga kyaututtuka na yara domin za su yi gasa da wasanni.
Garin Kano ya ɗauka. Ko ina ka zaga ana jiran ranar buɗe Happy Taj.
*
Gidan Alh. Hayatu ya hargitse da shiryawa wannan rana. In ka duna status da stories ɗin ƴaƴa da jikokin gidan ds su ka tasa, gabaɗayansu abin da su ke ɗorawa kenan. Sai kuma hoton Taj sanye da wasu fararen kaya na girki ya riƙe irin kaskon nan na zamani mai ɗan zurfi da dogon mariƙi a hannu ɗaya, sai kuma cokalin juyawa a ɗaya hannun. Harɗe hannuwansa ya yi dasu irin yanayin tsayuwar Black Panther idan sun yi alamar Wakanda Forever. Yayi matuƙar kyau da kwarjini a hoton. Ƙaryar mutum ya gan shi ya danganta shi da mace. Murmushin fuskarsa yafi komai tafiya da hankalin mai kallo.
Yadda ake ta shiri da farinciki a gidan Alh. Hayatu, haka ma su Sajida su ke ta murnar wannan ɗaguwar daraja da mahaifinsu zai samu idan ya fara aiki a Happy Taj. Har anko Abba ya yiwa ƴaƴansa. Yaya kuwa nata kayan sun fi nasu tsada ma. Kowa ya yi murna banda Hajiya Hamdi. Gani take ba a rabu da Bukar bane an haifi Habu. Abbanta zai baro local ƴan daudu su Ƴar Ficika, ya koma hannun international ɗan daudu wai shi Taj. Ita dai da tana da iko da ta hana shi wallahi. Har mamakin yadda kowa na gidan yake ƙaunar Taj ɗinnan take yi.
***
Komai nisan dare gari zai waye. Bayan shafe shekara guda da ƴan watanni, gobe ne ranar da za a buɗe Happy Taj.
Tunda aka saka rana Hajiya, Mama, Umma da Inna duk kawaicinta su ke roƙon Alhaji da ya yi musu izinin zuwa. Amsar da ya basu ita ce ba zai hana kowa fita ba amma idan sun tafi kada su dawo. Mama da Inna har kuka su ka yi. Ya ce ai bai hana su ba. Kowacce tana da damar zuwa amma tabbas bai yarda su dawo gidansa. Hajiya ta kai ƙararsa wajen Yaya Babba sai dai dattijon ya ce ba zai ƙara yiwa rayuwar ƙanin nass katsalandan ba. Har yau yana ganin laifinsa ne korar Taj da Alhaji ya yi.
Suna ji suna gani ƴan uwansu da na mijinsu da ƴaƴansu duk zasu amma ya yi musu shamaki. Walwala da farinciki sai su ka yiwa gidan kaɗan.
Taj bai fasa sanar da Alhaji duk abubuwansa ba kamar yadda Amma ta koya masa. Saboda haka duk wani abu da ya danganci restaurant ɗinnan tamkar dashi ake yi. Har hotuna da bidiyo yake tura masa. Bidiyon ƙarshe da aka yi kamar film na minti ɗaya da rabi shi yafi komai ƙayatarwa. An bi ko ina a wurin daga gate har ƙurya. Ga ma’aikata da shi kan shi CEO Taj cikin farinciki suna ta aiki a wajen. Ya kwanta tun wajen tara na dare sai ya kasa bacci. Kewar ɗan nasa tayi masa wani irin kamu. Ya yi kusan awa biyu yana juyi a kwance ƙarshe ya tashi ya ɗauki muƙulli ya fice.
Kowa ya yi mamakin fitarsa a wannan lokacin. Kamal zai bi shi Hajiya ta hana.
“Wallahi kewar Taj yake. Ku rabu dashi. Bashi da aiki sai kallon waya. Rannan da kunnena naji muryar Taj a wannan bidiyon da yara ke yawan kunnawa. Tunda girman kai ya hana shi dawo dashi gida sai ya yi ta wahala shi ɗaya.”
“Hajiyarmu yau da kanki?” Abba ya faɗi da mamaki. Don ita bata da zafi kamar sauran matan.
“Fita idona ni.”
Ta koma ɗakinta ta kwanta. Sauran matan ma duk su ka watse. Inna ce da ta shiga ɗaki ta dinga addu’ar Allah Ya daidaita lamura tsakanin uba da ɗan.
To dai Alhaji bai zame ko ina ba sai Happy Taj. Shi da ya jima bai yi tuƙi ba ko a jikinsa yau. Ga dare amma haka ya fito ya tsaya a bakin gate ɗin. Ya kalli ginin da wani irin pride yana jinjina kai. Tabbas yana cikin farinciki. Taj bai lalace yadda ya zata ba. Kuma a yau ya ɗauki sama da mutum ashirin aiki da kuɗin halalinsa.
“Allah Ya yi maka albarka” ya furta a zuciyarsa.
Ya kai hannu ya dafa gate ɗin. Jiniya har ta fara wiii, wiii sau biyu sai ɗif ta ɗauke. Alh. Hayatu ya sake dafa gate ɗin a karo na biyu yaji shiru. Addu’a sosai ya karanta ya tofa a jiki sannan ya koma mota ya tafi.
Taj dake ciki yana ƙarasa wasu cike ciken takardu ya share ƙwalla bayan tafiyar Alhajin. A gaban kwamfuta yake aikin inda take nuna masa ko ina da taimakon cctv. Yana ganin zuwan Alhajin ya ajiye aikin gabansa. Zuciyarsa ta shiga wani irin bugu mai tsanani. Ya tashi zai fita sai kuma ya fasa. Yana gudun kada zuwan nasa ya janyo wata matsalar tsakaninsu. Shi ya kashe jiniyar alarm ɗin tsaro da Alhaji ya taɓa gate ɗin. Yana ganin ya tafi ya fito ya ɗora hannunsa a inda ƙiyasinsa ya nuna mas Alhajin ya saka nashi ya sumbata. Wannan abu ya sanya shi farkawa da wani irin farinciki, jindaɗi da annashuwa washegari.
*
Amma da iyalin gidanta harda Hajjo a Kano su ka kwana. Da misalin ƙarfe biyu da za a buɗe gate ɗin ita da Anti da ƴaƴansu suna sahun gaba. Iman ɗinta dake Lagos ma ta zo da ƴaƴanta. Ga Anisa da Anti takanas tasa aka kira mai kwalliya ta gyare mata fuska. Ita kanta wani irin nishaɗi take ji a zuciyarta. Idan Allah Ya bata Taj, sai tafi kowa murna.
Ya Ahmad ma da iyalinsa suna kan layi. Anti Zahra da su Hayat an sha ado kamar za su biki. Salwa kuwa musamman Mami ta aiko mata da sababbin kaya daga Bauchi. Light make up tayi amma ba yadda za ayi ta wuce lafiyayyen namiji ya kasa yi mata kallo na biyu.
A cikin wani adaidaita sahu dake fake a wurin kuwa Hamdi ce take cika tana batsewa. Sajida da su Zee sun fito suna tsaye a bakin gate. Yaya kuwa duk yadda Abba ya kaɗa ya raya taƙi zuwa. Wai abin yara ne. Sai dai shi da ya santa yafi kowa fahimta. Har kullum bata fiye son su fita lokaci guda ba. A ganinta suna zubar da darajar ƴaƴansu ne. Uba ga yadda yake, ita kuma tun ƙuruciya har da girmanta ba a rasa yaran dake kwaikwayon tafiyarta. Sai ta zaɓi ɓoye kanta a gida don kawai ta tsira da mutumcinta.
Yau Abba har fushi ya yi amma taƙi. Wurin sana’arsa da take sa ran samun ɗaga darajarsa bai dace da ita ba. Yaran nasu basu san wainar da ake toyawa ba. Da Hamdi ba za ta taɓa yarda ta fito ba. Su duka suna ƙaunar Yaya kuma basa jin kunyarta.
“Ya Hamdi ki fito mana” Halifa ya dawo ya kuma kiranta don shi baya fushi. Su Zee ne su ka gaji da jiran ta sauko su ka yi tafiyarsu.
Da ƙyar ya samu ta fito. Haka kawai da su ka isa gate ɗin ta fara jin yanayinta ya sauya. Ita da bata son zuwa sai farinciki ya ziyarceta har tayi murmushi bayan ta saka ƙafarta a ciki. Tunda ababen hawa basu shiga saboda cikowa, a hagunta Salwa ce take shigowa, a damanta kuma ba tare da ta kula ba Anisa ce da su ka taɓa haɗuwa a Abuja watannin baya.
“Assalam alaikum wa rahmatullah”
Muryar Taj ta karaɗe wurin ta speaker a daidai lokacin da su ke shiga.
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
