Rayuwa Da Gibi – Chapter Five
by NadminMASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
Manyan gidan a wannan rana basu ga bambancin dare da wuni ba. Kusan babu wanda ya runtsa tsakanin maigidan da matansa. Abin da yake faruwa baƙo ne a wurinsu. Basu saba da rigima ba sai gashi dare ɗaya ana gab da samun gagarumar ɓaraka.
Ita dai Inna daga sallar asuba ta fake da ɗora kunun karin kumallo ta sauko. Bata zame ko ina ba sai ɗakin Mama. Akan sallaya ta sameta idanu sun kumbure. Jikinta a mace ta fita ta kira Umma da Hajiya su ka dawo ɗakin tare. Kai a ƙasa ta labarta musu ainihin yadda su ka yi da Alhaji jiya.
“Ni wallahi ba da wata manufa nayi maganar ba. Na tashi gidanmu babu ƴan uba amma tsakanin yayyena sai babba ya kau ta hanyar aure ko barin gari sannan mai bi masa yake ɗaukar ragamar gidan. Ban san gudun kada a gaba yaran nan su sami raunin zumunci a dalilin haka ni zai jawowa matsala ba.”
Umma ta kalleta babu wannan fara’ar ta kodayaushe
“To amma me ki ka gani a gidan nan da yasa ki tunkarar Alhaji da zancen? Cikinmu wata ta canja miki ne kuma ta nuna saboda kusancin Alhaji da Taj tayi haka?”
“Ko kusa. Nayi masa magana ne kawai akan ya dinga nuna sauran ƴaƴan musamman Ahmad da Kamal da su ke manya kamar yadda ya nuna shi.”
“Maganar girkin fa?” Umma ta sake tambaya don ita so take a warware komai.
“Yadda ba ku ɗauke shi laifi ba nima ban ɗauka ba. Wallahi ko kusa ni ban yi masa zancen da ya shafi haka ba. Ba gashi a ranar girkina ya yi miyar ba?”
Wata tambayar Umma ta so yi Mama ta katseta.
“Ni ban sakawa raina komai ba. Jiya Hajiya ta ƙara min nasiha akan idan muka bari wannan maganar ta girmi haka to zaman gidan nan zai daina yiwa kowaccenmu daɗi. Saboda haka zance ya wuce.”
Inna sai godiya da farinciki. Bata fita daga ɗakin ba sai da su ka koma wata hirar ana ta dariya. Da rana su ka kira Taj cikin lumana su ka rarrashe shi akan ya yar da wannan buri don ba mai yiwuwa bane. Mama tayi masa nasiha sosai akan yiwa iyaye biyayya.
“Ka cigaba da bin Alhaji kasuwa ranakun da babu makaranta amma daga yanzu tsakaninka da kitchen sai hange. Don Allah kada ka bari zancen nan ya koma tasowa a gidan nan.”
Nuna musu ya yi kamar maganar ta mutu, ashe suma tayi.
Shi da Kamal sun kammala sakandire suna da shekara goma sha shida da sakamako mai kyau. Alhaji kamar ya zuba ruwa a ƙasa ya sha ranar da su ka kawo takardunsu. Dama tuni ya tura Ahmad ƙasar India inda yake haɗa degree ɗinsa a fannin Computer Science. Zaɓi ya basu tsakanin Dubai, India ko China. Burinsa su zaɓa cikin ƙasashen da su ke cibiyar kasuwanci.
“Alhaji mun fi son zuwa wurin Yaya.” Cewar Taj.
Kamal ya yi Taj wani irin kallo sannan ya ce “ni dai Dubai.”
Kallonsu ya yi a tsanake. Da wuya zaɓinsu yake bambanta. Bai kuma saka ran samun haka ba ta ɓangaren karatun da zai rabasu na ƴan shekaru.
“Anya kuwa Happy da Happiness za su iya rabuwa na shekara huɗu? Ku dai sake shawara ku zaɓi waje ɗaya.”
Kamal ya kalli Taj da sanyin jiki. Ya ɗauka sun gama magana akan za su zaɓi Dubai. Burinsa ya koyo larabci banda karatun da za su yi. Sannan idan da faraga ya sami wani balaraben malamin ya danɗaƙi haddarsa da kyau ta ƙara zama. Kuma lafiya ƙalau Taj ɗin ya amince har da cewa shi ma zai yi. To me ya kawo wannan sauyi?
Alhaji bai ce musu komai ba amma ya fahimci akwai matsala tsakanin yaran. Sai bayan kwana biyu ya kira kowannensu gefe don jin me yake faruwa. A yadda ya fahimta zaɓinsu bai zo ɗaya ba. Kuma kowanne yana so ɗan uwansa ya bi ra’ayinsa. Kamal sai daɗa kwaɗaitawa Taj koyon larabci yake. Shi kuma duk da yana so amma haka kawai zuciyarsa tafi kwantawa da India. Sulhu ya yi musu da alƙawarin kowa zai sami inda yake so.
Harka ta kuɗi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci an gama yiwa kowa cuku-cukun samun gurbin karatu har ana shirin tafiya. Iyayensu mata su ka sha kuka kamar lokacin tafiyar Ahmad. Ƴan uwansu hatta na gidan miji don an fara aurarwa a gidan duka aka haɗu a filin jirgi wurin rakiya.
Alhaji da kansa zai kaisu makaranta. Dubai su ka fara zuwa saboda karatun Kamal saura kwanaki a fara. Ya biya komai ya tabbatar ya yi settling sannan su ka wuce India. Ahmad ya taho Mumbai ya tarbesu su ka rankaya Hyderabad tare. Gari daban za su zauna da Taj amma haka ya zauna da shi aka gama komai. Bayan sun raka Alhaji filin jirgi ya sake bin Taj har hostel ɗin makarantarsu, Osmania University ya tabbatar babu matsala sannan ya wuce makaranta.
***
Washegari Taj ya fita ganin gari. Karatunsu sai nan da kwana goma masu zuwa. Yana cikin yawo ya ci karo da wani katafaren ginin gidan abinci na alfarma. Mutanen dake shige da fice a wajen ba za su ƙirgu ba. Murmushin takaici ya yi. Ina ma iyayensa sun bashi goyon baya. Da watarana idan Allah Ya albarkaci nemansa zai iya mallakar wuri irin wannan.
Baya tare da yunwa amma yana son ganin wurin. Musamman kitchen da masu girki. Wurin shiga ya lura layi ake bi. Gashi ginin hawa biyar ne amma ko ina ka kalla tunda zagaye yake da gilas kana hango cikowar mutane. Da kansa ya haƙura da shigar ya kama zagayen ƙayataccen ginin yana mai son ganin iya faɗinsa. Ƙamshin girki mai tada kwantacciyar yunwa gami da muryoyi da ƙarar kayan kitchen yaji yana cikin tafiya. Da sauri kuwa ya manna goshinsa da gilas ɗin wajen yana ganin yadda ake kai kawo a wani makeken kitchen cikin tsari duk a ƙoƙarin ciyar da kwastomomi. Zuciyarsa a take ta soma harbawa. Yaji saukar nishaɗi da farinciki a ransa. Bai san minti nawa ya kwasa yana bawa idonsa abinci ba sai da yaji an taɓa kafaɗarsa an yi magana da yaren punjabi, guda cikin yarukan ƙasar.
Da sauri ya juya yaga wani ɗan dattijo sanye da t-shirt da wando ya ɗaure ƙugunsa da apron mai tambari da sunan gidan abincin. Kansa wata irin hula ce kamar ta wanka amma ita mai laushi ce. Ana amfani da ita domin hana zubar gashi cikin abinci. A shekaru a ƙiyasin idonsa zai yi sa’an Alhajinsa.
Daburcewa Taj ya yi ya matsa baya a tsorace yana cewa “I’m sorry. Sorry. Sorry.”
Hanyar komawa yake nema don tsoronsa ɗaya kada mutumin ya haɗa shi da security a ce me ya kawo shi nan.
Murmushi mutumin ya yi ya ce “hungry?” Don dama ita ce tambayar da ya yi masa da farko.
“Come inside” ya umarce shi da yaga yana neman guduwa.
“Am sorry Sir. Please. I won’t come again.” Ya ce zuciyarsa na faman lugude a ƙirjinsa.
Ko sauraronsa mutumin bai yi ba ya riƙe hannun ƙofar da ya biyo ya fito zai koma. Buɗewarsa ke da wuya wani jibgegen mutumi ya tare ƙofar ya yi magana da yarensu yana kallonsa.
Dattijon sai ya amsa da turanci yana yiwa Taj kallon in kuma ka musa babu ruwana. Nunawa ya yi ciki za su shigo da shi sannan ba laifi ya yi masa ba.
Ƙuttt ya haɗiyi yawu sannan kamar mai taka iska ya bi su ciki. Ƙofar na rufewa gabansa ya sake faɗuwa. Sai dai duk wannan tsoron ya kau lokaci guda da ya ƙarewa kitchen ɗin kallo na kurkusa. Aiki kowa yake yi da sauri-sauri ga magana ana yi wadda ya fahimci karanto odar masu jiran abince ce ko bada umarni. A gefe guda kana iya ganin wasu suna ta jere plates ɗin da aka gama haɗawa a wani abin turawa za a fita da shi. Ga masu girki sun duƙufa suna yi. Wuta da mai da cokula sai chuu…chauuu su ke. Ganinsa ya ƙare akan masu yanke yanke kamar inji. Wasu su na yanka albasa, caras, da ma nau’ikan kayan lambun da bai taɓa gani ba. Wani haɗaɗɗen murmushi ya saki sai ga ƙaton mutumin ya dawo da tray shaƙare da kwanukan abinci.
“Eat.”
Mutumin tsoro yake bashi amma duk da haka ya faɗa masa gaskiya “Am not hungry.”
“Taste our food and we talk, okay?”
Juyawa ya yi yaga dattijon farko ne ya yi magana. Musu ma wuri yake samu. Karɓar tray ɗin ya yi babu shiri ya zauna a inda aka nuna masa. Ƙamshin abincin ya tafi da tunaninsa. Shinkafa ce da kaza. Ga kuma wani haɗin albasa, cucumber da tumatir da wani ganye mai tsami tsami da daɗi kamar kunne zai fita. Wani ɗan kwano mai zurfi a gefe kuma miyar naman sa ne wanda ya dahu ya yi luguf. Sai wani abu kamar bread ko gurasa mai faɗi. Abu ɗaya ya kula shi ne babu cokali. Ya ɗaga kai ya tambaya dattijon nan shi kuwa ya ce masa.
“We eat with our hands here.”
Taj ya gyaɗa kai ya miƙe yace zai wanke hannu. Sink ya nuna masa ya wanko ya dawo. Yana zama ya yi Bismillah ya fara ci. Miyar ya ɗauka zai zuba a shinkafar da wani ɓangaren nata ya yi jaja-jaja, wani fari-fari, wani kuma yellow. Mutumin ya nuna masa ai gurasar nan ake ci da miyar. Shinkafar kuma ya zuba salad ya dinga haɗawa da nama. Ya tambayi sunan abincin aka ce masa chicken biryani ce da kuma chappati da beef curry (miyar).
Tunda ya saka hannu bai cire ba sai da abincin ya rage ɗan kaɗan. Yana ture plate kawai yaji mutanen kitchen ɗin suna ihu harda masu rungume juna. Ashe duk sun ankara da tsayuwarsa tun farko. Shi ne ogansu mai wurin ya shigo da shi. Farincikin fuskarsa a matsayinsa na wanda su ke da yaƙinin ranar ya fara cin abincinsu ne yasa su murna.
Sai da kowa ya nutsu aka cigaba da aiki sannan mutumin ya tambaye shi sunansa da dalilinsa na leƙensu.
“Kenan kana son girki” ya tambaye shi da turanci bayan ya yi masa bayani a taƙaice.
“Sosai.”
“Ka taɓa yin makarantar girki ko ka koya daga wani professional?”
“A’a.”
“Muna da makarantu a nan inda za ka iya yin degree.”
Taj ya yi murmushi da ya hango fuskar Alhaji idan ya je gida da kwalin degree a fannin girke girke. Sanar dashi ya yi cewa karatu zai fara kuma banu damar canjawa.
“Idan ka tabbata kana da ra’ayi ni zan iya koya maka a nan. Ka je ka duba tsarin karatunka. Ranakun da baka da aji ka zo nan kayi aiki.”
Baki ya buɗe da tsananin mamaki.
“Aiki?”
“Baka so ne?”
Da sauri ya ce yana so. Ya dai yi mamakin samu ne kafin ya nema.
Ƙaton mutumin nan ya sakar masa fuska ya ce.
“Dukkaninmu a haka yake ɗaukar mu aiki. Ra’ayin yi kawai zai gani daga gareka sai ya ɗauke ka yaronsa. Wurin nan nasa ne. Idan ka bada himma tabbas za ka ji daɗi. In kuma yaga baka da ƙwazo a wata ɗayan farko zai sallame ka.”
Kamar wasa daga wannan rana Taj ya fara karatu kuma yana zuwa koyon aiki a ROYAL CUISINE. Abin farinciki shi ne kasancewar dattijon da ake kira Paaji (ɗan uwa ko yaya) musulmi. Yawancin ma’aikansa musulmai sun fi yawa ma. Komai na wurin halal ne. Sai da ya yi wata guda cur babu abin da ake koya masa a kwana ukun da yake zuwa duk sati sai sanin sunaye da amfanin kayayyakin abinci da kayan ƙamshi (spices). Hancinsa ya aikatu don ko abu na kama da ɗan uwansa idan bai tantance ba maimaici za ayi ta yi. Wasu abubuwan kuma a ido su na kama amma a zahiri ɗaya nada amfani ɗayan kuma guba ne. Dole suma sai ya gane bambancinsu don kada a bashi a kasuwa ya cutar da masu sayen abinci.
Bayan nasararsa a wannin fanin kuma aka koma koyon ɓare tafarnuwa da yankanta ƙanana. Kan kace meye wannan hannunsa ya cika da plaster. Irin wannan yankan na mugun sauri ake so ya iya. Da ƙwararre a wurin aka haɗa shi. Daga nan aka koma albasa. A haka, a haka ya ƙware a yankan kayan lambu da kayan marmari. Yankan nama ma zaman kansa yake. Sai da ya koyi haɗa mince meat ko babu na’ura da wuƙa kawai da ƴar muciya. Shekara guda ko mai ba a taɓa bari ya soya ba sai da ya zama zakara a fannin ƙananan ayyukan da su ne ƙashin bayan kowane girki.
Bayan an dawo hutu wanda yaje gida ya yi da kyakkyawan sakamakon ƙarshen shekara ta farko aka kai shi gaban wuta. Zo ka ga farincikinsa da na abokan aikin. Mutane ne ƴan asalin garin Punjab masoyan duk wani abu na farincikin al’umma. Su dai ayi nishaɗi a zauna lafiya. Shi yasa Taj ya saje cikinsu. Happy Taj su ke kiransa tun ranar da ya yi skype da Kamal su ka ji yana kiransa Happy. Da yake anfi samun ƴan ƙabilarsu mabiya addinin musulunci a Pakistan, shi yasa Paaji duk inda ya sami ƴan uwansa musulmi yake basu aiki. Taj da wani Uygur Chinese (wata ƙabilar musulmai a China) Aynur kaɗai ne baƙi.
A cikin shekara ukun farko Taj ya ƙware a girke girke da dama na yankin Asia. Banda na Indiyawa an koya musu na Larabawa da duk wani yankin Asia da su ka yi fice ta fannin abinci. Duk kuma wannan badaƙala ko sau ɗaya Ahmad bai taɓa sani ba har ya gama ya koma gida. Taj ya ci karensa babu babbaka ya haɗa riba uku a zaman nasa. Bai manta da ƙudurinsu na bitar hadda ba shi da Kamal shi yasa ya shiga wata makarantar ƙarshen mako da ake yi a masallaci. Kamal ne kaɗai ya san me yake ciki kuma ya bashi goyon baya tare da nanata masa mahimmanci barin abin a matsayin sirri.
A kwana a tashi ba wuya a wajen Allah. Taj da Kamal sun ƙarƙare karatunsu a cikin shekara uku da ƴan watanni. Kowanne akwai taron convocation da za ayi a makarantarsu. Kamar yadda aka fara kai Kamal, ranar nasu taron ta zo sati uku kafin na su Taj. Alhaji sai ya ɗauki Hajiya da Umma su ka tafi Dubai. Satinsu biyu a can su ka koma gida tare da Kamal ɗin. Bayan kwana huɗu ya juya da Ahmad, Mama da Inna zuwa India.
***
Gagarumar gasar girki ce Culinary Academy of India ta saka domin samun zakarun da za ta bawa tallafin yin karatun degree na tsahon shekara uku a fannin Catering Technology and Culinary Arts. Makarantar reshe ce ta Jami’ar da ya kammala wato Osmania University. Kuma ɗalibanta ta buɗewa gasar masu ra’ayin girki waɗanda ba ƴan asalin ƙasar ba. Paaji na samun labari ya saka shi a gaba a gaban kwamfutar restaurant ɗin nasu ya cike komai online. Abokan aikinsu su ka yi ta murna domin da fari har ya soma yi musu sallamar komawa gida da zarar an yi convocation.
A kwana biyar za ayi komai a gama. Taj bai san da tahowar su Alhaji ba kamar yadda Kamal bai san ya shiga gasa ba. So ya yi ya yi surprising ɗan uwan nasa. Wanda kuma da ya faɗa masa zai gargaɗe shi da tahowar tasu. Duk wayarsu da gida ana ta ɓoye masa don an san ba ƙaramin farinciki zai yi ba idan su ka zo. Tahowar Ahmad kawai ya sani saboda zai zo registration na masters tunda ya gama bautar ƙasa.
Sun iso ƙasar awa guda kafin a shiga gasar a rana ta huɗu wadda ta kasance alhamis. Zuwa yanzu team ɗin Taj da aka haɗa da wani banufe ɗan Nigeria mai suna Wakili su ne su ke jan ragamar muƙami na biyu. Wasu wa da ƙani ƴan Indonesia kuma a sahun farko. Wayarsa Ahmad ya kira ya faɗa masa sunan hotel ɗin da su ka sauka.
“Yaya ka daure ka ƙaraso Uma Nagar cikin Culinary Academy.” Ya ce da farincikin isowar ɗan uwansa.
Don dai yau ɗaya yana ganin ba komai bane idan an sani. A tunaninsa nasararsa ta karatun da Alhaji yake so za ta sa ya bashi damar cika nasa burin.
“Me ake yi?”
“Gasar girki na shiga.”
Gefe Ahmad ya matsa hankali a tashe.
“Ashe ba ka da hankali Taj? Tun yaushe Alhaji ya soke maganar nan?”
Da yanayi na ban tausayi Taj ya ce “Yaya ina so wallahi. Domin neman amincewarsa na dage sosai a makaranta. Kana ganin yanzu ba zai sauko ba tunda nayi karatun da yake so?”
“Baka da hankali.” Ahmad ya sake faɗi yana jin zufa na karyo masa.
Duk abin da yake yi hankalin Alhaji dake magana da su Inna yana gare shi. Sauke wayar daga kunnuwansa ke da wuya yaji ya ce masa,
“Me ku ke ɓoyewa da har za ka tashi ka dawo nan?”
“Babu komai Alhaji. Ya ce min baya hostel ne.”
Rashin gaskiya ya gani ƙarara a fuskar ɗan nasa shi yasa ya ce,
“Kai ni inda yake!”
MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE
