Search
You have no alerts.

    Hannu tasa ta karbi jaririyar tareda mannata a jikinta,wata irin tsagwaron ƙaunar yarinyar ne ya jiyarci tsakiyar zuciyarta,tareda muradin kareta a ta kowacce fuska.
    Idanuwanta ta sauƙe akan jar fuskar jinjirar,wadda yake ɗauke da ƙankanin kyau mai tafiyar da duk mai kallonta.
    Hancinta babu makawa kowa yakalleta yaga na ubantane,sai bakinta kuma data biyo irin na mahaifiyar ta ɗan ƙarami,motsashi take a hankali tana neman inda zataji abincinta ya isa gareta,wanda hakan yasa ainihin Cute feature ɗinta fitowa fili.
    Boyayyan murmushi Daneji tayi ganin halittar yar tata farincinkinta tareda gode ma Allah daya azurtata da itah.
    Maman ta buɗe na hannun dama inda yarinyar take,tareda ƙokarin saka mata a baki da taimakon iya mai ganye wacce take tsaye a kanta.
    Saida taga yarinyar takama nonon kafin tabi bayan Inna laari zuwa wanke kayan data bata.
    A hankali take jan ruwan nonon cikin rashin iyawa zuwa cikin bakinta,yayinda ita kuma Daneji ta tsareta da ido,ko da wasa ta gagara ɗauke idonta daga kanta.
    Idonta ne yafara motsawa alamar zai buɗe,wanda hakan yabata mamaki matuƙa,yarinyar da aka haifeta yanzu tana shirin buɗe ido,kawar da hakan tayi a ranta ganin daƙin da duhu,sannan kuma idan aka buga larasi da ƴaƴan zamani hakan bakomai bane.
    “Daga haihuwarki yau har kina ƙoƙarin buɗe idonki,lallai kina da wayo sosai t……….”
    Tsaida maganar tayi a ƙasan maƙoshinta,ganin launin idon dayake kallonta,ba baƙi ba ko kuma mai ruwan ƙasa ƙasa ba,da ake samun wasu yaran sukan zo dashi,nata launin idon shuɗine ne siɗik,kaman ba idanuwan bil’adama ba,duk wanda yarinyar takalleshi da idanuwan idan bayyi jarumta ba zai iya jefarta yagudu,saboda yanda suke ɗauke da wata haiba a cikinsu,da ko babban mutum bazai samu ba.
    Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce ta jiyarci danejin a karo na ba’a adadi,ganin irin halittar da ƴar tata take ɗauke dashi,wanda tayi amanna tunda take bata taba ganin irin ta ba a rayuwarta.
    Duk yanayin buɗe idon kaɗan kaɗan take irin na jarirai,amma hakan bazai hana mutum gano abinda yake tattare da yarinyar ba.
    Runtse idonta tayi na wasu mintina kafin tasake sauƙesu akan ƴar,wacce zuwa yanzu ta rufe idanuwan da alama tayi bacci a bakin nonon. Cireta tayi a hankali,ta sake lullubeta a cikin zanin da take,kafin ta maidata wajen da take kwance ɗazu..
    Tashi tayi tafara gyara ɗakin tareda ɗauko kayan dazata saka,har sannan jikinta a sanyaye yake na abinda tagani,a jima kaɗan ta kalli wajen da yarinyar take,a jima kaɗan ma ta kalleta,abin ya tsaya mata a rai takasa fitarwa.
    Tana cikin hakanne malm Ahmadu ya shigo ɗakin kaman an jehoshi,labarin sauƙarta lafiya ya risƙeshi a waje.
    Kai tsaye wajenda take ya nufa tareda ɗaukota ya rungume a jikinsa da rawar jiki.
    Sumbatarta yafara ta ko’ina kafin yafara yimata ƙiran sallah a kunne.
    Itadai Daneji tana tsaye da tsintsiya a hannunta bata ce komai har yagama rawar jikin.
    Ɗagowa yayi ya kalleta da murmushi akan fuskarsa yace.
    “Mashaallah nayi mata huɗuba,sannan kuma nasaka mata sunnan mahaifiyata MARYAMAH”
    “Allah yaraya ta bisa imani,sannan kuma Allah yasa halin mai sunanta ya bita”
    “Ameen ya Allah,kema Allah yayi miki albarka yabaki lafiyar shayarwa”
    “Ameen kasake yiwa Addah laari godiya da ƙoƙarinta a gareni”
    “Shikenan”
    Kafin dare yayi mutane ƴan uwa da abokan arziƙi suna ta zuwa ganin Ƙaruwar haihuwar da akayiwa malam Ahmadu,wannan su shigo wannan su fita.
    Har ƴan uwan su inna laari ma saida sukazo daga ƙyauyensu,Amma babu wanda yazo akace daga bangaren mai jego,duk da kowa yasan ƴan uwanta basanan amma abin yayi mata ciwo sosai,rashin danginka a kusada dakai abune mai ciwo matuƙa.
    Da daddare saida Daneji tasha kukanta ta ƙoshi na rashin danginta,babu wanda zai zauna a gunta daga bangaren yan uwanta,sai dole yadikon su malam akan ce wata tsohuwa tazo yi mata zama.
    Gashi yanzu tafara tara dangi itama nata na kanta,shin wa zata nunawa Ƴar ta a matsayin danginta zuwa gaba,ko kuma haka zata tashi batasan kowa nata ba,wanda itama tanada yaƙinin nangaba zata iya mantasu idan lokaci ya tafi.
    Har akayi kwana uku da haihuwa babu wanda yagane cewar idon Jinjirar bana mutane bane,sai iya daneji ce kawai tasani,har yanzu kuwa babu wanda ta faɗawa,kullum fargabarta shine idan mutane sun gano mai zasuce gameda hakan.
    Abinda yafi bawa Daneji mamaki shine idan har ita datake bata nono tagane ƙalar ƙwayar idanunta inaga mai wanka kumafah inna laari,tana da tabbacin Inna laari taga abinda tagani gameda yarinyar,amma ko kaɗan bata nuna tagani ba,ko kuma bata gani bakai?
    Ita kaɗai take tambayar kanta take bata amsa a ranta,abinda yashare mata tantama shine,lokacin da jinjirar ta shaƙi sabulu ta buɗe idonta kuma akan idon inna laari,amma batayi mamaki ba ko kuma nuna alamar zata sanar da wani abinda tagani.
    Duk abinda take bata kulada Daneji tana kallon sanda taga idon yarinyar ba,hakannne yakara tabbatar mata ba lokacinne kallonta na farko ba a gameda lamarin,tasani tunda farko,boyewa kawai takeyi,to miyasa?.
    “Addah Laari shin bakiga wani abu a tattare da yarinyar nan ba wanda ba irin na mutane ba?”
    “Nagani mana,ƙwayar idonta ba kalar ta mutane bace,saidai babu yadda Allah baya halittar sa idan yaso,shi yayi nufin yaganta hakan,dan haka babu mai ja da ƙudurarsa”
    “Hmmm hakane kam,nayi mamakine da kika gani amma bakice komai ba”
    “Uhm mai zance Daneji,saina bi duniya nayi ta yaɗawa ƴar mijina an haifeta da wani irin ido?ribar mai zanci akan hakan,innayi hakan nima ai kaina na tozarta ba kowa ba,sannan ya mutane zasu kalleni kenan,idan Allah yayi kwananta ta fita kowa ma zai gani,fatana shine Allah yasa mutane su gane halittar Allah ce itama kamar su,karsu nuna ƙyamatarsu gareta”
    Maganar da inna laari tayi baƙaramin faranta ran Daneji tayi ba,sai ta nemi kashi hamsin na fargabar halin da yar tata zata shiga ta rasa,yazamana itama tasaka a ranta cewar Allah ne mai halitta,kuma shi yayi nufin ya ganta a haka ba kowa ba.
    Ranar suna gadan gadan aka hau abinci da yanke yanken kaji,bayan tunkiyar da aka yanka na aƙiƙa.
    Mutane an ciki gida maƙil,a lokacinnne kowa yashaida yarinya taci suna Maryam,mahaifiyar malam Ahmadu.
    Bakinnan kaman gonar auduga,kowa rana yasan malm Ahmadu yana cikin farin cikin marar misaltuwa.
    Duk abinnan da ake Daneji kaffah kaffah take da Maryam,wanda tafara ƙiranta da BOMBEE,saboda kar mutane sugani su tsegunta,ana tsaka da taro kowa yaɗauka a ƙirƙiri abinyi na gulma.
    Dan haka sai itada inna laari suka haɗa baki akan yarinyar bata lafiya,kowa idan yazo saidai ya kalleta daga nesa,itama data rufa musu asiri wuni tayi tana bacci.
    Bayan anyi taro an watsen makwanta su larai suka tsayah aka gyara gidan tareda su,kafin bayan magriba sukayi mmusi sallama suka nufi nasu gidan.
    Dare yayi gari yafara shuru Bombee tace batasan kwanciya ba,dawa Allah ya haɗata idan bada kuka ba.
    Tun tanayi Daneji na rarrashinta har abu yafara fin ƙarfinta,dan shiɗewa take muryarta har dunshewa take dan Kuka.
    Shikansa malm Ahmadu take ɗakin inna laari yayi sawu yakai sau uku,kl yaushe idan yazo sai yace tabata tasha,tun tana ce masa taƙi karba har ta rabu dashi.
    Ruwa ta ɗebo a kofi tana tofi tana shafe mata jikinta,tunda ta kula babu zazzabi a jikinta,sannan cikinta bai kumbura ba bareta ce ciwo yake mata.
    Haka tayi ta shafe ta da ruwan addu’o’i,sai kuma tayi sa’a tafara sauƙe ajiyar zuciya lokaci lokaci,can wajen asuba tayi ƙitt kaman an kashe rediyo.
    Ida tai Daneji yanda taga rana haka taga dare,ga gajiyar bikin suna,sa’arta ɗaya ma Ba sallah zatayi ba ko girki,dan haka da rana ta samu damar rama baccin.
    Wasa wasa an kusa shafe wata ɗaya dayin suna,kullum babu fashi sai Bombee ta kwana tana ihu,idan asuba kuma tayi tai shuru kaman ruwa ya ɗauke.Tun abun suna ɗaukarsa kukan jinjirai har abun yafara sakasu dasa ayar tambaya. Bangaren Daneji kam harta fara mantawa da wani baccin dare yanzu.
    Bankaɗa labulen ɗakin tayi zata shiga ta fito daga wanka,turuss tayi a bakin ƙofar ganin malm Ahmadu rike da Bombee a hannunsa yana kallon idonta,ita ma kallonsa take da shuɗayen idanuwan nata na yara,kana kallon kan fuskarsa zaka hango tsagwaron mamaki da kuma irin mutum yaga abu a karon farko.
    Ɗago fuskarsa yayi ya sauketa akan Daneji wacce ta shigo daƙin jikinta yana ɗigar da ruwan wanka.
    Saurin sunkuyar da kanta tayi bata bari sun haɗa ido ba,dan babu alamar wasa a idanuwannasa,tambaya ya jeho mata kai tsaye.
    “Fatima menene wannan?”
    “Idanuwanta ne”
    “Dama haka suke tun farko,kokuma yanzu sukayi?”
    “Haka take dasu aka haifeta”
    “Meyasa kuma ina matsayin mahaifinta baki taba faɗaminba,kenan da bangani ba shikenan harsai ta girma ta fita naji a bakin mutane kome,idan kuma hakan ciwone kika barta dashi ya wuce gaban kwatance fah,yakike ganin za’ayi,kullum ina faɗamiki banason wannan shuru shurunnki,zai iya kaiki ga aikata danasani”
    “Kayi haƙuri banason ka shiga damuwane idan ka gani,sannan bansan ta yanda zan sanar dakai ba,na faɗawa addah laari ma tafaɗa maka tace baruwanta”
    “Eh baruwanta mana,ke kinga laifinta a ciki,tazo ta faɗa ace dama Allah allah take ya faru ta faɗa? Maza saka kayanki mutafi wajen maganin gargajiya da kuma na nasara,wannan abin ai bana zama bane,waya sani ma ko bata gani ke baki sani ba,inaga ma yanada alaƙa da kukanta da daddare,ko ciwo ma suke mata”
    “Tana gani fah dasu”
    “Taya kika san tana ganin”
    “Idan nasaka mata haske ina tafiya dashi tana bin hasken”
    “Ni ban yarda da wannan zancen ba,maza shirya mu tafi asibiti a ji shin mai yake damunta”

    Sadi-Sakhna ce
    ƴar mutan jama’are

    ____********_____

    *BAƘAR AYAH*

    _BOOK1_

    Labari/Rubutawa:SADI-SAKHNA
    [ _Ƴar mutan Jama’are_ ]

    *WATTPAD*
    Https://www.wattpad.com/user/SAKHNA03

    *AREWABOOKS*
    https://arewabooks.com/u/sadeesakhna

    ______________****_______________

    Note
    error: Content is protected !!