Kura a Rumbu – Chapter Fifty-two
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke mu'amala da su balle makaranta.
Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa ganinta da wata. . .