Kura a Rumbu – Chapter Fifty
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Turus yayi yana bin falon da kallo zuciyarsa tana ƙara gudu, shiga yayi ciki da kyau har sannan yana ƙoƙarin gane abinda yake faruwa. Ƙofar ɗakin Halima ya tura, nan ya tarar da gurin shima tamkar falon babu ko tsinke anyi shara da alama ma har mopping akayi. Sakin ƙofar yayi ya matsa ya buɗe ta ɗayan ɗakin da yake mazaunin nasa; a nan ne ya tarar da kaya zube a ƙasa wanda kallo ɗaya ya musu ya fahimci nasa ne.
Ɓacin rai haɗi da baƙin ciki suka kamashi lokaci ɗaya, fita yayi daga nan ya. . .