Kura a Rumbu – Chapter Forty-seven
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)"Ashe baka da mutunchi kai mutumin banza ne ban sani ba? Ban taɓa zaton haka kake ba, ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan idon mu kana can kana zubar mana da mutunchi kana tozarta kanka; matan banza kake bi Bilal?"
Ya dafe in da ta mare shi ba tareda ya bari sun haɗa ido ba ya ce
"Ni wlh ba wasu mata da nake bi Hajja sharri kawai suka mun". Wani marin ta sake kai masa ya goce ta ce
"Yanzu kake da bakin kare kanka kenan? Ni zaka kalla ka ce sharri ake maka saboda ka. . .