Kura a Rumbu – Chapter Forty-two
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)A yayinda muke shirin kammala wannan littafi idan har kin san kina karantawa ba tareda kin siya ba kiyi ƙoƙari ki sauke nauyi domin babu lallai in yafe haƙƙina 🙏🏽🙏🏽
Cike da ƙaguwa da zancen ya ce
"Yanzu dai Umma wanne ake so a ciki? Lefen ko kuma kuɗin za'a bayar ko ayi mata kayan yanda tace?"
"To ai ni ba na ce ba, kaga ita Nuratu dai kayan tace tana so to ita ya kamata ka tambaya itama kaji wanne tafi so" ta bashi amsa sai ya girgiza kai ya ce
"Ai na gaya miki yanda. . .