Kura a Rumbu – Chapter Thirty-three
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Banji komai dangane zaman da ya ce Hajja zatayi ba dukda nasan ba jituwa mukeyi da ita ba amma kuma abinda yake so ne kuma wanda zai faranta masa ni kuma burina a koda yaushe kenan. Har ya fita ya kirani a waya yace na shirya gashi nan dawowa zamu fita tare, da nace masa Al'amin fa kar lokacin tashin su yayi bana nan sai ya ce ai ba jimawa zamuyi ba dan haka nayi maza na canza kayana na shirya Sharifa ina jin horn ɗin mota na fita. Raina fes na kame a gaban mota ina jin wani. . .