Kura a Rumbu – Chapter Thirty
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Watan Al'amin goma sha takwas na yaye shi a kuma watan na samu wani cikin wanda ko kusa Bilal bai yi maraba da samuwar sa ba.
"Wai dama bakiyi komai na tsarin Iyali ba? Ni na zata hankalin ki zai baki da kiyi ba sai an tuna miki ba, kina kallon yanda abubuwa duke tafiya kuma kawai zaki kama ki wani sake yin ciki. To ni dai gaskiya ban so haka ba" Abun da ya faɗa kenan lokacin da na shaida masa ina da cikin.
Gaba ɗaya sai na rasa yanda zan fassara maganganun sa. Fassara ta kai. . .