Kura a Rumbu – Chapter Twenty-eight
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Washe gari da wuri na fara haɗa kayan mu dan komawa gidan Anty Labiba duk da jirgin dare su Mama zasu bi amma da wuri nake so na tafi can ɗin dan ko rakiya ba zan tsaya yi musu ba. Gaba ɗaya raina babu daɗi na tashi, na ɗauka Bilal zai sake kira na daga baya ko kuma da asuba amma shiru. Ina zuge akwatin kaya na Zainab ta shigo ta ce mun na zo na yi baƙi, na ɗora mayafin doguwar rigar yadin jiki na ina ƙoƙarin kawar da ɓacin ran dake kwance akan fuskata. . .