Kura a Rumbu – Chapter Twenty-six
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ko ba'a faɗa mun ba na san da wahala idan jini na bai hau ba, daƙyar na lallaɓa Al'amin ya yi shiru na goya shi kafin na fita samawa Bilal abin da zai ci. Bamu da komai da zai ciyu da safe ban da taliya. Ita na yi jollof da sauran miyar da ta rage na dafa masa baƙin shayi. Ya ringa kallon abincin kamar wanda na aje wa mugun abu kafin cikin faɗa faɗa ya shiga tambayar babu nama a gidan ne da zan dafa masa tsurar taliya ko me?
Haka. . .