Kura a Rumbu – Chapter Twenty-five
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ina zaune a falon har Baba Jummai ta gama haɗa kayan ta tana kukan da nake ji kamar na tashi na shaƙe mata wuya idan ya so ta yi mai dalili. Ni da ta ke neman ta kashewa aure ai ni ce da kuka ba ita ba, akan na ce ta tafi tun da ita ta janyo ni ma aka ce na tafin shi ne ta fasa kuka wai na mata rashin kunya tana ƙoƙarin kare mun mutunchi na watsa mata ƙasa a ido. Ta shi na yi na goya Al'amin bayan da ta fito da. . .