Kura a Rumbu – Chapter Twenty-four
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)A ƙaramar akwati na zuba mana duk abun da na san zamu buƙata a yinin, Baba Jummai ta goya Al'amin tana tsaye tana jiran na yafa gyale na da na ajiye a gefe. Zama na yi a gefen gado ina rarraba ido kamar wadda ta yiwa sarki ƙarya, ta kalle ni ta ce
"Ya kuma kika zauna? Tun da dai an kaiwa maƙwaftan nan abinci se ki tashi mu tafi kuma su ce zasu shigo yinin suna".
"Baba ban gayawa Bilal ba" na faɗa ba tare da na kalle ta ba,
"Naga abinda ya ishe ni. . .