Kura a Rumbu – Chapter Twenty-three
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Se bayan sallar isha'i Bilal ya shigo gidan lokacin ina wanka saboda kitso da lallen da bamu gama da wuri ba se lokacin. Leda na ga ni da kuma ƙaramin kwalin biscuit a ajiye, sai bayan da na shafa mai na saka kaya kafinna nufi falo muka gamu a bakin ƙofa yana shirin shigiwa dan haka na juya.
"Ga shi nan na suna ne se ki bawa waɗan da za su zo da safe" ya faɗa yana nuna mun kayan daya ajiye ɗin.
"Har yanzu baka ce komai ba na ɗauka ma ai ka manta gobe ne. . .