Kura a Rumbu – Chapter Twenty-one
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ina ɗaki, hayaniyar yan dubiya duk ta cika mun kunne, tun da Anty Amina ta tambaye ni abinda za'a dafa da rana na nuna mata shinkafa da mai wanda su kaɗai suka suka rage mana a gidan, ina ganin Hajja ta shiga kitchen ɗin na fito na barsu. Ta biyo ni ɗaki tana tambaya ta sauran kayan girki nace mata iya abinda muke dashi kenan, zata yi magana Anty Aminan ta jata waje shikenan nayi zamana a ɗakin ban sake fita ba suma kuma babu wadda ta sake leƙa ni. Da yaron yana gurin su ma aka. . .