Kura a Rumbu – Chapter Eighteen
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Haka rayuwa taci gaba da gangarawa; yau fari gobe baƙi. A yanzu da nake lissafa watannin aure na goma sha biyar da Bilal shekara ɗaya da wata uku kenan, tabbas a zaman da mukayi nayi karatu da yawa tattare da halayen sa waɗanda a baya ban san su ba. Babban abinda na fara naƙalta da Bilal shine mutum ne me son abinsa. Tabbas Bilal nada son abin sa kuma ya kan iya rufe ido ya cima koma wanene mutunci har idan ya shiga gonar sa, idan yayi wani abun se na shiga mamakin ta yanda har muka. . .