Kura a Rumbu – Chapter Sixteen
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)*Nayi kuskuren rubutu a page 13, ajizanci ne, abinda ke raina daban abinda alƙalamina ya rubuta daban. Ina fatan zaku mun uzuri*
Na ringa juya zancen Farisa a raina bayan ta tafi har sanda Bilal ya dawo sau biyu ina buɗe baki da niyyar tambayar sa gaskiyar abin da ta faɗa mun se na kasa daga ƙarshe na tattara zancen na watsar har ina ganin baike na dana yarda da maganar tata har na saka a raina. Ta ya ma haka zata yuwu? Kawai dai haɗa guri ne irin na Farisa amma kuma idan tayi ƙarya. . .