Kura a Rumbu – Chapter Fifteen
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Ban tanka masa ba na shiga tattare kayan dake ajiye dana gama kuma na wuce ɗakina na kwanta, nayi mamakin ganin ya biyo ni, nayi lamo a kan gado ina sauraren sa har ya gama uzure uzurensa na bacci kafin ya kwanta a baya na tare da jana jikin sa yana cewa
"Nasan ba bacci kike yi ba juyo na baki barka da sallah" nayi masa banza duk yanda yake ya mutsani da son se na biye masa na dake daya gaji ya sake ni ina jin sa yana tsaki har baccin gaske ya ɗauke ni. Washe gari nayi zaton. . .