Kura a Rumbu – Chapter Fourteen
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Afuwan kun jini shiru. Wadanda suke cikin comment section group na bayar da uzuri.
A ɗarare na ƙarasa yinin cike da taraddadin yanda zamu kwashe da Bilal idan mun koma gida. Se da akayi magriba ya turo mun text a waya in fito mu tafi. Jikina ya sake yin sanyi, haka nayi sallama da Hajja da sauran yan gidan su tana ta mun godiyar abin arziƙi da tace an kawo musu daga gidan mu cikin azumi ga kuma turmin atamfa dana kai mata dama yanzu kuma na kaiwa mejegon itama Atamfa da wani lace cikin ɗinkunan biki da aka. . .