Kura a Rumbu – Chapter Thirteen
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)Kasaƙe nayi ina kallon sa har ya fice daga kitchen ɗin lokaci ɗaya jiki na yayi sanyi lanƙwas kamar an watsa mun ruwan sanyi. A hankali na ajiye bowl ɗin hannu na na dafe drawer baya na da hannu biyu jin jiri na neman ɗiba ta. "Sam wannan ba Bilal bane, ba halin sa bane akwai wani abu da yake damun sa tabbas" abin da na furta a fili kenan cikin son ƙarfafawa kaina guiwa da kuma bawa kaina tabbacin ba cikin sani Bilal yayi mun wannan tozarcin ba. Nafi minti biyar kafin na tattara ƙarfin daya rage. . .