Kura a Rumbu – Chapter Twelve
by Maryam Farouk (Ummu Maheer)"Idan har izini na kike nema ban yarda ba, ko da yake ai kin saba yin gaban kanki. Kiyi duk yanda kika so Halima lokacin ki ne dama kika samu". Abinda Bilal ya gaya mun kenan bayan dana same shi akan maganar posting ɗina zuwa garin Bauchi. Duk yanda kuma naso da ya zauna muyi magana ta fahimta yaƙi, ƙarshe ma barin mun part ɗin yayi gaba ɗaya ya tafi can part ɗin sa da falon kaɗai muke amfani dashi ina jin sa a daren ya gyara ɗakin tun da dama da hado da komai a ciki ya. . .