Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    Duk nazarin na ban hango abin da take ganin na rashin dai dai ba. Rashin yi mun kyauta ne aibun sa ko kuwa rashin kammala ginin da be yi ba da kuma zancen lefe? A cikin ukun sune abin da nake ganin Anty Labiban take emphasizing se dai ni a ganin ta wannan ai ba komai bane ba. Bilal nake so ba abun hannunsa ba. Iya kar ƙoƙari yana yi gurin ganin ya kammala in da ze ajiye ni kuma ba a ɗaura auren nan an ga be yi mun lefe ba balle su ce wani abu. Ni duk wani lefe da wasu bidi’o’i basa gabana duk da dai ba zan ce bana so ba amma tunda nasan wanda zan aura bashi da ƙarfin yi shi yasa ban sawa raina ba sanin kuma masu shirya mun a gida ba yin al’amarin suke yi ba shi yasa kwata kwata ban sa a ka ba. Ko ankon yammata na kamu dana fitar saboda naji Mama da Aminyarta Hajiya Rakiya suna maganar ne shiyasa har na saka ran Maman za tayi taro.

    Ban cewa Anty Labiba komai ba itama kuma ganin na ci gaba da sabgogina ba tare da na ce mata komai ba yasa ta fahimci amsar ke nan ina kan bakana ba gudu ba ja da baya. Allah ya gani tayi bakin ƙoƙarinta gurin haska mun tun da kuma na runtse ido abin da ya rage kawai su bini da addu’a ne, Allah ya saɓa tunanin su akan Bilal ɗin. Shikenan ta aje komai ta shiga yi mun gyara irin wanda ya dace da budurwa kuma yar gata kama ta.

    Biki nata matsowa, tun da na koma gidan Anty Labiba sau ɗaya Bilal yazo a waje kuma muka tsaya yace sauri yake yi be zauna ba tun ranar kuma se dai muyi waya. Idan na masa ƙorafi yace aikin gini ne da sauran shirye shirye suke hana shi zuwa har ya rage saura kwana ashirin da biyar ranar Hansa’u tazo ta sakani gaba akan dole na kira Bilal ya basu kuɗin sallamar yammata ko kuma ita ta kira shi da kanta. Kira biyu na masa be amsa ba se ya mun text akan suna seminar ne ze kira ni. Se na mayarasa da text ɗin akan Hansa’u ce take so za suyi magana ina jiran sa. Har aka yi sallar isha’i muna zaman jiran kiran sa ko ya zo amma shiru daga ƙarshe ta tafi bayan da mukayi faɗa dan tace yana sane yaƙi zuwa ni kuma na kafe akan be gama abin da yake yi bane. Ko minti biyar bata yi da tafiya ba kuwa se gashi ya kira ni. Se da na gayawa Anty Labiba kafin na fita, ya ringa kallo na yana yaba kyan da nayi.

    “Amarya kin sha ƙamshi. Kin ga yanda walwalinki yake haske ido kuwa Halims menene sirrin?” Murmushi kawai nayi na wuce ciki ya bi bayana ya na cigaba da zugani. Se da na aje masa ruwa da lemo yana ta bin duk motsi na da ido kamar ze cinye ni ɗanya, har na zauna ya kalle ni yana shafa cikin sa yace
    “Yanzu fa muka gama ko gida ban je ba na taho dan nasan kina jira na”. Se da na kalle shi sama da ƙasa, ƙananan kaya ne a jikinsa baƙin wandon da army green ɗin riga short sleeve. Sumar kan sa ta ɗan taru haka gashin fuskar sa da alama ya kwana biyu be yi aski ba ga ƙamshin turaren sa ya baibaye ko ina ni dai be yi mun kala da wanda ya wuni a gurin aiki ba. Cikin gida na wuce dan na fahimci maganar tasa yunwa yake ji. Se da yaci ya ƙoshi ina kallon sa ya sha ruwa kafin ya washe baki yace

    “Kin san Allah, ni fa idan bake kika bani abinci ba sam se dai kawai naci amma bana ƙoshi”. Nayi murmushi kawai se ya sake cewa
    “To Hansa’un? Babbar Aminiyar mu Allah dai yasa ba tayi fushi ba”
    “Ai ta tafi gida ma” na bashi amsa a gajarce, se ya fito da ido yace
    “Haba dai? Ai na ɗauka ta dawo nan da zama itama har se an gama biki shi yasa ko da naga nayi magriba ban gama ba ban damu ba tun da kuna tare”.
    “Ka ji ka da wata magana fa, bikin saura kwana 25 shi ne zata dawo nan da zama tun yanzu?” Na bashi amsa ina kallon sa se yace
    “Au haka fa, kin san saboda zumuɗi gani nake kamar sati biyu ne ya rage”
    “Ban ga alama ba” na bashi amsa kai tsaye se yayi shiru yana kallo na. Haɗe fuska nayi na ci gaba da cewa
    “Dama zuwa tayi akan maganar shirin biki da abun da za muyi na yammata shi ne tace na kira mata kai ka sallame su”.

    “Hajiya Hansa’u kenan iyayen rigima, wace sallamar yammata kuma se kace wasu yara ko yammatan ƙauye?” ya faɗa yana wata dariya me kama da ta rainin hankali. Se kawai na tsaya ina kallon sa jin abin da yace wai kamar yara ko yammatan ƙauye, me yake nufi kenan?
    “Kin yi shiru kina kallo na” ya faɗa yana kawo hannunsa fuskata na goce nace
    “Ban fahimci abin da kake cewa bane, a ƙauye ne ake bada sallamar ƙawaye?”

    “Ni dai gaskiya rabon da naji an bayar da wani kuɗin yammata tun san da Abdulhadi yayi aure da muka je can garin ƙawayen amaryar nan suka sa mu gaba wai se mun basu kuɗin party” ya faɗa. Se kawai nayi shiru ina jin sa yana ta zuga zance shi kaɗai ni kuma ina danna wayata. Sallamar Anty Labiba ce ta katse shi. Ya zamo daga kan kujera kamar gaske ya shiga gaishe ta ta amsa fuska ba yabo ba fallasa kafin ta fara magana
    “Dama na tambaye ta zancen gida dan muna so mu ga guri saboda musan awon labule da sauran abubuwan da zamu mata se take cewa bata sani ba, ga lokaci yana ta matsowa bama so a shiga hidimar biki bamu sallami gidan amarya ba”.

    Kamar in toshewa Anty Labiba baki haka na ringa ji sanda take maganar, na kalli Bilal yana ta mutsu mutsu kamar wani mara gaskiya se naga kamar harda zufa yake yi duk kuwa da garin babu zafi. Anty Labiba tayi shiru tana kallon sa bayan ta gama magana tana jiran jin amsar sa amma be ce komai ba se satar kallo na da yake yi ni kuma na sadda kaina ƙasa se ta miƙe ta kalle ni tace
    “Duk yanda kuka yi ina jiran ki” ta fice ta bamu guri. Gani nayi yanayin fuskar sa ya canza, zuciya ta ta tsinke amma na dake na saurara naji ze ce wani abu dangane da maganar data masa amma naji shiru se ma kallon agogo da yayi ya ɗauki muƙullin sa daya ajiye kan center table ya kalle ni yace
    “Dare ya fara yi Halims bari nazo na wuce ko?” Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Mamaki yasa kawai na bishi da kallo na kasa cewa komai. Yayi murmushi yace
    “Babu rakiya? Ko baki gaji da kallo na bane na zauna?” Cikin ɗari ɗari nace
    “Baka ce komai ba akan abin da Anty Labiba ta faɗa”. Murmushi ya sake yi mun yace
    “Na ji mana Halims, cewa tayi ai duk yanda mukayi ki gaya mata. Na zata duk abin da ake ciki kin sani me yasa baki gaya musu ba da har zaki bari yanzu ta titsiye ni? Me kike nu fi kenan Halima? So kike a ga gazawa ta ko me? To yanzu ai se hankalin ki ya kwanta tun da kin tozarta ni” ya faɗa sautin sa a ƙasa se dai yanayin kalaman da kuma yanda ya kira ni da Halima kai tsaye mai makon Halims yasa na fahimci ransa a ɓace yake.

    “Yanzu kuma me nayi? Wace irin magana kake yi haka dan Allah meye abin tozarci a nan?” Na faɗa ina marmar da ido, gaba yayi yana cewa “Na gaji sosai bacci kawai nake so nayi zamuyi magana daga baya kawai”

    Yanda kasan ya ɗaure mun baki haka na tashi na masa rakiya zuwa ƙofar falon ya tafi, ɗaki na wuce na kwanta bayan na kwashe kayan da yayi amfani dasu. Anty Labiba bata ce mun komai ba kamar yanda ni ma ban ce mata ba, haka Hansa’u data ki rani da safe kan ya mukayi nace zan kira ta shikenan bata sake tada maganar ba tun ranar kuma Bilal be zo ba a waya ma sau ɗaya ze kira ni da safe ko da yamma da mun gaisa ze kashe ko da na ɗakko magana ze bani uzurin yana abu shi kenan se washe gari kuma ze sake kira. A haka muka shafe kwana goma, idan ka ganni baka buƙatar a ce maka bani da nutsuwa saboda yanda jiki na ya nuna. Dama ba wani auki ne dani ba, ba tsahon kirki kuma bani da kiɓa, ɗan gyaran da Anty Labiba take mun da kunun alkama da madarar da dake ɗura mun suka sa na fara kumari yanzu kuma bani cikin nutsuwa ko abincin ma se naji yunwa na neman kayar dani nake ci ita kuma ta saka mun ido bata ce mun yi bata ce mun bari. Randa aka kwana takwas da zuwan Bilal ne ma da ta ganni na zauna na zubawa guri ɗaya ido ina tunani shine har ta mun magana tace

    “A banza zaki kashe kanki Halima mu zaki yiwa asara tun da dai gashi ƙiri ƙiri ya nuna miki baya yi idan kina da hankali ya kamata ki cire shi daga ranki. Dama yau nake niyyar in tambaye ki in gayawa Mama yanda akayi saboda kar su cigaba da shirin biki a banza ko kuwa dai in kama kaina kar in shiga abin da babu ruwana?”

    Se na kalleta a birkice nace
    “Me zaki gaya mata kuma Anty?”
    “In gaya mata na tambaye shi zancen gida tun da ya tafi be sake dawowa ba mana ita ai me hankali ce idan taji haka zata fahimci in da zancen ya dosa, dama dai na gaya mata ta dakata da duk wani shiri dangin Abbanki ne dai suke ta shirin su dan ma dai dama bikin ba na ki ke kaɗai bace abin haushin baze musu yawa ba” ta bani amsa. Se kawai na fashe da kuka, ta saki baki tana kallona can tace

    “Dukan ki nayi ko zagin ki Halima da zaki saka mun kuka?”

    “Ya yake so nayi Anty? Me zanyi Bilal ya gane irin son da nake masa?” Na faɗa cikin matsanan cin kukan dake fitowa tun daga ƙasan raina. Na yarda son Bilal jarabawa tace babu kuma wanda ze fahimci yanda nake ji har shi kansa kuwa. Kamar zata share ni ta wuce se kuma ta zagayo ya zauna gefe na tare da jana jikin ta nan kuwa na sake samun sararin yin kuka yanda nake so. Cikin tausasawa ta shiga yi mun magana tana cewa

    “Halima har se ya buɗe baki yace baze aure ki ba kafin ki fahimci kurman baƙin da yake miki? Halima ko a littafin hausa kin taɓa jin labarin neman aure irin naki? Aure fa za a yi na yar mutum ba wai yar tsana ba amma ace ƙasa da wata ɗaya ba ango ba dangin sa ba babu wani ɓangare da suka nuna murna ko zumuɗin su akan abin da ze faru a ina kika taɓa ganin an yi haka?
    Ki ture duk wasu al’adu ace ba dole bane basu yi ba amma Halima muhalli yana cikin sharuɗan da se sun samu kafin aure ya ƙullu, a ina ze ajiye ki? Ko kuwa dama lasisi yake nema a gidan ku zaki ci gaba da zama bayan an ɗaura muku auren ko yaya? Yau idan haya ze kama biki ƙasa da sati uku yaci ace ya samu har ya nuna guri an san me za a saka miki. Kwana nawa ina miki magana akan ki tuntuɓe shi? Yanzu da na masa magana da kaina gashi ya nuna miki zahirin da kika kasa ganewa ko kuma da be fito miki a mutum ba ba auren ki yaron nan ze yi ba ki godewa Allah da be samu galabar lalata miki rayuwa ba ki haƙura ki barwa Allah zaɓi Halima”.

    “Bilal yana so na kuma aure na zeyi Anty. Ta yaya za ayi ya turo iyayen sa a saka mana rana har idan ba aure zeyi ba? Kuma zancen gida na gaya miki gini yake be ƙarasa ba ni muna magana ya kuma tabbatar mun kafin ranar biki ze gama komai gajen haƙuri kawai kika yi kika masa magana gashi yanzu kin saka ransa ya ɓaci, yaƙi ya zo a waya ma sau ɗaya yake kira na kuma bata ko bari muyi doguwar magana ze kashe idan ma har ya ce ya fasa ɗin ai ke ce kika jawo ba wai a karan kansa yayi ra’ayi ba” na faɗa cikin kuka. Yanda tayi shiru tana kallo na ta tabbatar neman hanya mafi sauƙi da zata huce takaici ma takeyi ta rasa, se na miƙe ina cewa
    “Ni gidan mu kawai zan tafi, dama ai so kike yi ya fasa aure na shiyasa idan ba haka ba ai ina ji har Mama se da tace ki rabu damu ai ni ce zan aure shi tun da naji na gani kowa nasa ido ne” na wuce ɗakin da nake ina ci gaba da kuka haɗi da zazzaga mata rashin kunya. Kaya na na shiga haɗa wa a akwati waya ta dake jikin caji tayi ƙara jin ringing ɗin Bilal yasa na saki kayan hannu na na wuce gurin wayar da sauri na ɗaga.

    Kamar ko da yaushe a kwanakin nan muryarsa cikin sanyi ya amsa gaisuwar da nayi masa kafin yace
    “Amm kina wani abu ne Halima?”
    “Ba abinda nake yi, wani abu kake buƙata nayi maka? Ko abinci kake so?” Na faɗa cikin zaƙuwa. Ina jin sa ya sauke ajiyar zuciya kafin yace
    “Ina so na ganki ne, akwai maganar da nake so mu tattauna me muhimmanci idan babu damuwa”
    “Wace irin damuwa kuma? Yanzu zaka zo ko se da daddare?” Na amsa shi, se yayi ɗan jimm kafin yace
    “Ke zaki zo ki same ni idan zaki iya amma”. Shiru nayi na kusan minti ɗaya ina juya maganar a raina, abin da Anty Labiba ta faɗa mun yanzu akan na godewa Allah da be lalata mun rayuwa ba ya faɗo mun a rai se nayi saurin korar maganar daga raina ina bawa kaina tabbacin Bilal ba ze taɓa yaudara ta ba ba kuma wannan niyyar ta kawo shi guri na ba.

    “Karki takura kanki idan ba zaki iya ba babu damuwa dama magana ce akan abinda ya shafe mu mu biyu da nake ganin ya kamata mu tattauna amma zamu iya barin ta kawai idan baki da lokaci” ya katse mun shirun da nayi. Ban san sanda harshe na ya furta
    “A ina zan zo na same ka toh?”
    “Ina shagon Sani” ya bani amsa. Se na sauke ajiyar zuciya jin ba wani guri daban ya ce na same shi ba har na tsinewa shaiɗan ɗin daya fara kawo mun wasi wasi akan Bilal ɗin. Aje wayar nayi na shiga toilet da sauri na canza pad ɗin jiki na tare da wanke fuskata na fito na canza kaya. Dogon Hijab na saka da niƙab saboda munafukan unguwan mu. Dana fito ban tarar da Anty Labiba a falo ba se Amir ne ya tare ni yana tambayata me ya samu Momy ya shiga ɗakin ta ya tarar da ita tana kuka nace masa ban sani ba sauri nakeyi kuma ana jira na ne yaje ya bata haƙuri.

    A bayan gidan mu Chemist ɗin Abokin sa Sani yake, haka na ringa gyara niƙab ɗin fuskata harda canza tafiya dan kar a gane ni ce, na tarar da shi da Bilal zaune suna hira. Kallo ɗaya na masa na hango ramar da yayi idanunsa sun sake fitowa haka dogon hancin sa ya ƙara tsayi hatta da lips ɗin sa se naga sun bushe sun ƙara jaa alamar yana cikin damuwa ko bashi da lafiya. A taƙaice muka gaisa da Sani kafin ya fita ya bamu guri. Na sauke kaina ƙasa saboda yanda Bilal ya kafe ni da nasa idon da nake jin sun ƙara kaifi yau, sama da minti biyar muna zaune kafin a hankali ya fara magana yace

    “Kiyi haƙuri Halims be kamata ace na ɗauki fushi akan abin da ya faru ba. Bayan na dawo gida na nutsu na gane kun fini gaskiya se dai ina cikin wani yanayi da ni kaɗai na san wane hali nake ciki duk kuma wanda zan yiwa bayani be zama lallai ya fuskan ce ni ba”. Kallon sa nayi jin yayi shiru se yayi murmushi ya ci gaba da cewa
    “Tun farko shiyasa ban so aka saka bikin nan wata shida ba kuma kema na gaya miki, dalilin da ya saka bana ɓoye miki komai da nake ciki kenan Halims saboya tunani na duk abin da ya taso za kiyi mun uzuri” se na ɗaga kai na kalle shi yayi saurin cewa
    “Ban ce baki mun ba, wlh na sani kin yi ƙoƙari. Kin mun abin da ba kowacce mace ba kuma na yaba and i will for ever be grateful for that Halima. Ke ɗin kin nunawa duniya true love still exist, se dai har yanzu ban kai ba Halima. Nayi tunanin a wata shidan nan zan iya yin ƙoƙarin ganin ban baki kunya ba amma se yanzu na fahimci wautar da nayi gashi kuma lokaci ya ƙure mun balle na juya da baya”.

    Gaba na ya yanke ya faɗi baki ja har yana rawa na kalle shi nace
    “Ban gane ba, what are you trying to tell me Bilal what do you mean by lokaci ya ƙure balle ka juya baya?”

    “Relax Halima ba wani abu nake nufi ba” ya faɗa yana kama hannu na, se na fizge ina kallon sa se dai na kasa ci gaba da magana saboda yanda zuciya ta take wani irin bugu kamar zata huda ƙirjina ta fito. Wayar sa ya ciro daga aljihun sa yayi danne danne kafin ya miƙa mun, hannuna na rawa na karɓa na kalli screen ɗin. Video gidan daya kai ni a matsayin nasa wanda zamu zauna a ciki ne yake playing, seda na kalla daga farko har ƙarshe kafin na kalle shi muka haɗa ido dan shima ni yake kallo se ya karɓi wayar ya mayar da ita aljihunsa kafin ya haɗe hannu biyu ya dafe haɓarsa ya furzar da iska daga bakin sa kafin yace

    “Bayan da aka saka ranar auren mu munyi magana da Baba Liman ya kuma kira gidan su yaron da ze auri Fadila akan suyi haƙuri a ƙara ranar auren su zuwa wata goma amma suka ƙi yarda akan in dai ba wata shidan da suka yanke ba se dai a mayar musu da kuɗin su kawai ya haƙura ya fasa auren ta. Na gaya miki Halima ni zan yi mata komai na aure, babu abin da baki sani ba a kaina tun da mahaifin mu ya rasu duk wata ragama ta yan ɗakin mu ta dawo kaina. Yayyenmu tun da muka samu saɓani dasu lokacin rabon gado shike nan suka zare hannun su daga komai daya shafe mu ko sanda nace babu damuwa a bar zancen auren mu a wata shidan na ɗauka su Yaya Alhaji ze yiwa Fadila kayan ɗaki ne se da kuma biki ya taho da Hajja tayi musu magana suka ce ai an raba gado an bawa kowa nasa dan haka ba abin da zasu mana..”

    “Bilal ka faɗa mun kai tsaye me kake nufi ko me kake so ayi yanzu dan Allah tun baka janyo zuciya ta ta buga ba” na katse dogon sharhin daya ɗakko wanda babu abin da nake fahimta a ciki. Shiru yayi ina kallon yan da abin wuyan sa ke sama da ƙasa alamar magana na cikin sa ya kasa furtata kafin ya sake riƙe hannaye na biyu duk yanda naso na ƙwace be bani dama ba haka ya kafe idon sa cikin nawa yana murza zoben dake hannu na yace
    “Ina son ki Halima bana fatan na rasa ki amma a yanzu bani da halin auren ki”.

    “Dagaske Bilal dama yaudara ta kake yi ba aure na zaka yi ba?” Na faɗa cikin karyewar sauti. Se ya ƙara ƙarfin ruƙon da yayiwa hannaye na yace
    “Allah shine shaida ina son ki Halima dai dai da rana ɗaya ban taɓa niyyar yaudarar ki ba”
    “Amma da bakin ka yanzu kace ba zaka iya aure na ba, me yasa tun farko baka faɗa mun ba se da ka bari auren mu ya rage sati biyu?” Na faɗa ina fashe wa da kuka.
    “Nayi zaton zan iya Halima, na ɗauka zan samu yanda nake so kafin lokacin amma hakan yaci tura. Ta yaya kike zaton iyayenki zasu bani ke bayan ba ni da ko muhallin da zan ajiye ki?” Ya faɗa tamkar shi ma ze fashe da kukan. Kamar zan shiɗe nace
    “Shi kuma wannan gidan fa? Ko dama ba naka bane ƙarya kayi mun kace na ka ne?”

    “Gida na ne Halima amma wannan shi da kango ai basu da maraba ta yaya mutum ze shiga ya zauna a gurin da ko daɓe babu? Ki aje maganar wannan gidan a gefe kawai dan dashi da babu banbancin su kaɗan ne. Da ace ina da sararin da zan kama miki haya ma da wlh bazan damu ba amam bani dashi, a yanzu bani da wasu kuɗi a tare dani se wanda za a siyawa Fadila kujera su kansu basu gama haɗuwa ba dama sadakin ta ne na cika kuma na ranci wani abu ciki dashi na ƙarasa aikin fulasta ai kin gani sanda muka je iya waje ne da fulasta ba ayi a waje ba ko? Zaɓi biyu ne kaɗai ya rage mana Halima, ko dai a ɗaga auren mu wanda bana zaton iyayenki zasu amince tun da har sun ambata dama akwai wanda suke so su haɗa ki dashi a familyn ku kenan se dai na haƙura dake tun da bani da halin auren ki shikenan rayuwa ta tazo ƙarshe ban san wace alƙibla zan kalla ba idan babu ke a tare da ni”.

    Note
    error: Content is protected !!