Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    A motar Nasir na ganshi, ya kame a ciki yanda kasan tasa. A raina nace kuɗi dai ze yi wa Bilal kyau dan kalarsu aka masa. Yanayin surarsa da irin kayan da yake sakawa ba zaka kalli gidansu kace daga nan ya fito ba. Yana son gayu, sau tari na kan raya a raina nan yake kashe kuɗin sa gurin siyan sutura da takalma haɗi da agogo masu tsada duk abin da samari sa’anninsa suke yayi zaka ganshi dashi hakan kuma yana burge ni duk da ba wadata ce dashi ba amma ba yanda za’a yi ka ganshi ka raina shi.

    A gaban motar nima na kame Inayah ta shiga baya muka tafi muna hirar mu gwanin sha’awa, ban tambaye shi in da zamu je ba shima be gaya mun ba har muka isa Goron dutse cikin GRA dake bayan matatar ruwa (WRECA). Na ringa kallon unguwar, a iya sani na banda kowa a gurin shima kuma bamu taɓa hirar wani nasu a nan ɗin ba, cikin wani da ke jere da gidaje hagu da dama muka shiga, gidaje uku ne ba kammalallu ba a ciki ɗaya ma kamar da mutane a ciki benen sama ne ba’a ƙarasa ba se fili da aka zagaye da alama ba’a fara gina shi ba. A ƙofar kangon dake ƙarshe layin ya tsaye dake layin baya ɓullewa, ya kashe motar muka fita na cigaba da kallon gurin ganin ya nufi kofar shiga gidan ya buɗe da muƙulli yasa muka bi bayansa se dai ban shiga ba na tsaya a waje ina kallon cikin gidan.

    “Ya kuka tsaya a waje? Ku shigo mana” ya fada bayan daya juya ya ganmu a tsaye. Se da na ɗan yi jumm ina kallon cikin gidan kafin nayi bismillah na shiga. Tsakar gidan bashi da girma sosai amma ze iya cin mota ɗaya ko ma biyu. Duk da ginin ba’a kammala shi ba amma yana yin tsarin yayi kyau. Akwai babbar ƙofa dake tsakiya tana kallon get, se kuma daga gefe can akwai wata ƙofar ƙarama. Ya buɗe babbar kofar ya shiga muka bishi, a cikin falon da ba’a yiwa fulasta ba ya tsaya yana kallona yace
    “Barka da zuwa gidan Bilal”. Se na saki murmushi, wato nan ne gidan da yake gina mana. Ya nuna bangon hagu in da ƙofa take yace
    “Bedrooms ne guda biyu kowanne da toilet, suna da girma nasan zasu ci kowanne irin saitin gado”. Seya matsa ya buɗe kofar dake bangon gabas yana cewa
    “Nan kuma kitchen ne da store”, waccen ƙofar ta waje kuma ɗaki ne da falo a ciki Master room kenan ina tunanin ko a faso da ƙofa ta nan” ya nuna mun ɗan corridor dake gefe yace
    “Saboda sauƙaƙa miki zirga zirga tsakanin nan da can ko dan yanayi na ruwa da sanyi”. Ni dai murmushi kawai nake kamar wata sokuwa. Ya buɗe ɗakunan muka leƙa har cikin toilets ɗin kamar yan da ya faɗa suna da girma sosai kam zasu ɗauki kaya har a samu gurin shimfiɗa carpet me ɗan girma. Har can part ɗin da yace nasa se da muka shiga, a nan naga ya aje buhunhunan sumunti da sauran kwanon da akayi rufi dukda saman gota ce se kayan toilet da sink na kitchen.Tsakar gida muka koma ya nuna mun ɗan filin dake kusa da part ɗin yace
    “Da nan gurin Hajja tace se ayi ɗaki tun da ga banɗaki a tsakar gida dama ko da zamuyi baƙi maza masu kwana”

    “Uhm” kawai na ce a raina ina lissafa ɗan abinda nake ganin ya rage a aikin ginin. Fulastar ciki ce dan an yi ta waje da ɗakuna guda biyu nawa, falo ne da kitchen suka rage se can ɓangaren sa.

    “Yau kin ga gidanki” ya faɗa bayan da muka zauna a mota. Nayi murmushi nace “guri yayi kyau sosai Allah ya sa rai aka yi wa”
    “Amin My Halims ai se ma an gama aiki an gwagwaje gurin da kaya yan kamfani kyansa ze sake fitowa” ya bani amsa na amsa masa da
    “Haka ne, to Allah ya nuna mana lokaci”. Shirun minti biyar ya gifta tsakaninmu ya ci gaba da tuƙi ni kuma na tsunduma tunanin abinda ya rage a aikin gidan yanzu wanda a gani na saura ne kawai tun da an yi me wuyar kammala ginin da rufi. Ni duk da yake ta zancen gini na zata irin ko linta be kai ba ashe ma ƙarashe ne kawai.

    “Yanzu kin ga abin da nake gaya miki na akwai sauran shiri a gaba na ko?” Ya katse mun shirun, se na kalle shi. Ya ci gaba da cewa
    “Ban siyi ko kwali ɗaya na Tiles ba. Ga gilasan winduna kin ga boggler kawai aka saka. Ban da ƙarashen fulasta sannan azo uwa uba wiring ɗin wuta da ruwa ga fenti dasu pop aikin fa ba ƙarami bane Halima”.

    Nayi kasaƙe ina sauraronsa, se da ya kai aya kafin nace
    “Allahn daya hore akayi wannan ze rufa asiri in sha Allah”
    “Haka ne” ya bani amsa daga nan be sake cewa komai ba har muka je unguwar mu. A hanya muka sauka ya wuce ina ɗaga masa hannu, se da na sake komawa gidansu Hansa’u cikin sa’a na tarar ta dawo nan muka zauna na shiga labarta mata yanda gida na yake.

    “Lallai Halima ba kunya kika bishi ganin gida ko?” Ta faɗa se na harare ta nace
    “Ji banza wai kunya. Kawai naje naga gidan ne wani abu da zan ji kunya lallai ma”. Seda Mama ta kira ni kafin muka fito ta rakani rabin hanya. Sau biyu cikin zirgilli na ina kusan gaya wa Mama zancen munje ganin gidan se Allah ya cece ni na canza maganar da wata. Abin na mintsili na, nayi kamar na gayawa Anty Labiba se dai nasan yanda take a cike dani tsaf zata haɗa ni da Mama se kawai na kama kaina na bar murna ta a ciki na. Bilal dai da ake ganin be kai ba gashi nan cikin hukuncin ubangiji ze yi abinda kowa se yayi mamaki ga dai gida nan na nunawa sa’a da nasan iya kar masu ƙaryar kuɗin dai suyi kamar shi ko wanda be kai shi ba kuma a unguwar yan gayu da na tabbatar ƙasa tana tsada a gurin.

    Shi ma a yanda yace filin na gadon sa ne ya adana gashi kuwa ya masa rana babu yanda masu gidajen kusa dashi da ma na nesa basuyi akan ya bar musu ba har musanyan ginannen gida aka bashi da cikon kuɗi duk yaƙi a cewar sa baze maida kamar sa ba kuma unguwar ta masa da irin tsarin rayuwar da yake so ya gudanar da iyalansa.

    Watanni uku suka shuɗe cikin wata shida na ranar auren mu data rage har sannan kuma daga ɓangare biyu nawa dana Bilal ba zan ce ga wani shiri da aka fara na biki ba. A gidanmu dai nasan Abba ya yiwa Mama magana akan abin da ya kamata ayi tace masa suna kan lissafi ne idan ta gama haɗa komai zata sanar masa ban sake jin sun tada maganar ba. Ina da abubuwan da nake so a mun daga kan zaɓin kayan ɗaki zuwa sauran kayan amfani se dai ban ga fuskar da zan sakowa Mama maganar ba. Anty Labiba ko yanzu ban ma isa na doshe ta da wannan zancen ba tun da ƙiris take jira dama ta samu nayi mun. A haka a ka fara azumi, na ƙudurce a raina har aka sallace ban ga an motsa ba to fa zanyi magana se dai ace nayi rashin kunya.

    A ɓangaren Bilal ma dai shiru ne, nayi zaton yanda nake cike da ɗoki shima hakan ce zata kasance dashi amma sam ba haka ba. Kullum yazo bashi da zance se na gini, ya rasa ya ze yi, kaza ya ƙara tsada se ya kashe kaza akan yin abu kaza kuma shi bashi dasu ko waya ya kira ko na kira shi zancen kenan har na fara gundura da jin sa daya fara akwai se in bashi uzurin zan yi wani abu na kashe wayar. Ban sake shan mamaki ba se wata rana daya zo bayan shan ruwa yake nuna mun ci gaban aikin da akayi a wayar sa se na ga babu banbanci da wancan zuwan da mukayi, fulasta kaɗai aka ƙarasa se wiring ɗin ruwa da yace anyi.

    Rai na ya so su, tun ku san sati ɗaya kenan Hansa’u take ta mun magana akan ya kamata mu fitar da anko in gaya wa Bilal ya bani kuɗi muje kasuwa. Nasan haka akeyi to amma tausayin sa da nake ji da yanda kullum yake ƙorafin gini ya hana shi sakat yasa nace bazan tambaye shi ba ƙarshe se Abba na tambaya da Mama ta ji ma tace ba yanzu ba in bari se bayan ƙaramar sallah tunda bikin ze kama bayan babbar sallah ne da kwana goma a lissafi. Ni ina ta tunanin ƙila ma an kusa gama fenti ashe shi tafiyar hawainiya ma yake yiwa aikin. Kasa daurewa nayi nace masa

    “Yanzu tsahon lokacin nan ashe babu abin da aka ci gaba a ginin nan? Yau fa sauran kwana casa’in da biyar ace ba’a ma ɗakko hanyar kammala gini ba balle a fara sauran hidimomin biki?” Se ya kalle ni yace

    “Wace irin magana kike yi haka Halima? Ashe ma baki yaba abinda nake yi ba kin san tsadar kayan gini kuwa a wannan zamanin? Karfa ki manta Halima ni nake yiwa kaina komai ba wani bane yake tallafa mun sannan hidimar nan ba iya tawa bace ba sanin kanki ne ga auren Naja ni zan mata kayan ɗaki bayan kuma albashi na kin san ba wata hanya ce dani ta samun kuɗi ba”. Nayi shiru saboda na hango gaskiya a cikin tasa maganar shima, ba shi da matallafi se Allah ga kuma hidimar ƙanwar sa kamar yanda yace ita ma abar dubace.

    “Shi yasa tun farko na guji a saka mun rana ba tare da na gama shiri na tsaf ba, kuma da aka je ma ni shakara ɗaya nace aka tashi aka sa wata shida bayan an san ba lallai na shirya a wannan lokacin ba” ya sake faɗa kamar cikin fushi. Se na kalle shi na ce
    “To me kake nufi yanzu?”
    “Ni babu abinda nake nufi kawai raina beji daɗin yan da kika raina ƙoƙari na bane har kina cewa wai duk tsahon lokaci babu abin da nayi”.

    Shiru kawai nayi ina kallon sa na rasa ma abin da zan ce har ya gama yayi shiru dan kansa. Haka dai ba daɗi muka yi sallama ya tafi, ko abincin da nayi niyyar bashi ban ɗauko ba shima kuma be tambaya ba, da asuba ma be kira ni ba har gari ya waye gurin ƙarfe goma se kuma duk naji na damu. Nasan dai ba wata magana na gaya masa da ya kamata ace ta masa zafi ba amma hakan nan na danne zuciya ta albarka cin son da nake masa na kira shi.
    “Raina ya ɓaci Halims, ya za ayi duk fafutukar da nakeyi akan naga nayi komai cikin rufin asiri amma kina rai nawa? Ke baki ga girman gidan bane ba kiga irin tsarin da aka ɗakko ba?” Ya faɗa bayan dana gama ban baki. Nace

    “Gaba ɗaya ka juyawa magana ta manufa ne amma ni ban raina ƙoƙarin ka ba kawai a nawa tunanin dai zuwa yanzu ko za’a ce da sauran aiki to ƙarashe irin wanda ma be zama dole ba. Kuma ni da zan baka wata shawara kaji, me ze hana ka mayar da hankali kawai ka gyara iya ɓangaren da zan zauna a ciki? Tun da dai mu biyu ne kawai a cikin gidan ko da ace ka gyara can ɗin ma ba lallai ace za’a yi amfani dashi yanzu ba. Kawai ka barshi ka tsayar da hankalin ka a guri ɗaya ina ganin ze fi”.

    Se yayi shiru kafin yace
    “Na yi tunanin hakan amma kuma bana son raini”
    “Wane irin raini kuma?” Nayi saurin katse shi, se yace
    “Ba zaki gane ba. Ki kwantar da hankalin ki za ayi komai kafin lokacin, naga alamar kin fini matsuwa fa Halims to ki cigaba da daurewa saura ƙiris ba zaki maimaita azumi a gida ba”. Na rufe fuska kamar ina gaban sa nace
    “Kasan bana son irin haka”
    “Surutun kawai, zaki yi baya ni ne duk ranar da kika shiga hannu yarinya” ya sake faɗa se nayi saurin datse wayar jin yana neman sakin layi da azumi a bakin mu. Shikenan muka shirya aka ci gaba da azumi kwanci tashi har satin sallah ya kama.

    Shakara biyar muna tare da Bilal be taɓa mun toshi ba har ga Allah wannan sallar na tsammaci ze yi tun da dai yanzu ai kusan na zama tasa za’a ce se dai shiru kake ji har sallah ta rage yan kwanaki babu wani labari. Ranar da ya rage kwana uku idi bayan an sha ruwa yazo kamar ko yaushe ina shirin zuwa gidan Anty Labiba zan kai mata saƙo daga nan na karɓo mana ɗinku nan mu ni da Mama. Tare da Bilal muka tafi, bamu jima ba muka dawo tun a hanya yake ce mun wai
    “Iye yar gatan Abba da Mama. Yanzu duk ledojin nan kayan sallar ki ne, ni ina nan ko rigar da zan saka naje idi bani da ita. Takaici yasa na masa banza har ya sauke ni a ƙofar gida, na shiga na aje kayan sannan na fito mu kan ɗan taɓa hira kafin yayi haramar tafiya, dubu uku ya bani yace gashi nan nayi kitso da lalle.

    “Na bawa Hashir sautun abaya, na ɗauka ze dawo lafin sallah se jiya yake ce mun wai jirginsu washe garin sallah ne kiyi haƙuri da wannan” ya faɗa bayan daya bani dubu ukun. Gashi dai ba wasu kuɗin azo a gani ya bani ba, a yanda nake tsaye ma ina da ninkinsu a jikina amma se naji daɗin kyautar tamkar wanda ya bani miliyan uku. Na ringa murmushi ina cewa na gode shi kuma ya basar wai akan 3k ai ba haka yaso ba in yi haƙuri da hakan kawai. Dana shiga gida haka na tarar da Mama ina dariya na bata kuɗin ta kalle ni ta kalle su da taji daga in da suka fito ina ga takaici ne ya saka ta dariya kawai tace ya kyauta. Washe gari tun da wuri na tafi gidan lalle kafin azahar an gama mun da daddare kuma naje gidan su Hansa’u ta yarfa mun kitso a nan naga abin arziƙin da Alhaji Bala ya kawo mata na toshi akwati guda harda kit kamar lefen bazawara ba abin da babu ciki tun azumi na tsakiya dama ya zo gaisuwar azumi nan ma ya kai musu sha tara ta arziƙi naji mata daɗi amma ba wai abun ya burge ni ba dan ni dai wlh da dai na auri dattijo kamar Alhaji Balan saboda kuɗi gara in ƙare a talauci tare da wanda nake so.

    Ranar idi haka na shaƙe kuloli saiti biyu da abinci, ɗaya na Bilal ɗaya na Hajjan su na bawa Aliyu ne Adaidaita ya kai musu Mama dai kamar yanda tace taga ikon Allah amma tunda me kawo abincin yace babu ruwanta a bar ni nayi yanda naso sadaka ce dole ta kama bakinta tun da dama ni nasha wahalar girka miya, wai na da tuwo kuma matar dake mana duk sallah ce ta zo tayi. Da yamma Bilal yazo, mutumin da yace beyi ɗinkin sallah ba se gashi da sabuwar kwalliya ba wadda ya turo mun hotunan idi da ita ba. Daya tashi tafiya nan ma a karon farko ya bani rafar yan naira goma sabbi yace na bawa Imam da Amirah barka da sallah Mama kuma na gaya mata jibi zasu zo gaishe ta da abokanansa.

    An ci sallah an cinye watan shawwal ya mutu har an shiga zulƙida ya raba a taƙaice ce dai ƙasa da kwanaki sittin a lissafin kwanakin ranar auren mu. Gidan Baba Salahu su Sauda da za ayi bikinmu tare suna ta shiru tu ni sun fitar da anko, sau ɗaya na yiwa Bilal zancen ina so zan fitar da ankon yace mun ya kamata kam na bashi tazarar sati ɗaya na ga ko ze mun wani abu amma naji shiru se kawai na share shi nayi amfani da kuɗin da Abba ya bani muka siyo Atamfa kala biyu, ɗaya ta kamu ɗaya ta yinin biki saboda rashin ta ido da na nuna masa se ce wa yayi
    “To ina na dinner kuma? Ko ba zaki mana dinner ba Halims?”

    A lokacin a wasa na ɗauki zancen mukayi dariya kawai ina ce masa “wannan ai hurumin ka ne, idan za kayi ko ana go be ranar ne ba zamu kasa samar da abin da yammata za suyi amfani dashi ba tun da kasan shi ankon dinner dama ba da yawa ake yin sa ba” ya ce
    “Shi kenan Allah ya kai mu lokacin na gaya miki har idan da hali babu abin da ba za ayi ba Halims ki na raina soyayyar da naki miki”.
    Ranar Alhamis aka aiko wa Mama daga gidan Baba Salahu akan ranar Asabar za a kawo lefen Sauda, ni se da naji aiken na tuna da batun wani abu a aure wai shi lefe. Ko da wasa bamu taɓa zancen da Bilal ba, be mun maganar ba ni ma ban masa ba ni hankali na duk ya tattare akan ya kammala gini shi yasa ma na manta da wani batun lefe ƙila. Bayan yaron ya tafi Mu’azzam yake ce mun
    “Ke kuma se yaushe za a kawo naki lefen? Ni wai Mama bikin nan yana nan kuwa dan ban ga ana wani shiri irin za a aurar da yar fari ba ko dama duk bula ce da ake nuna an fi son ta akan mu?”

    “Bana son sakarci Mu’azzam wane irin magana ne zaka ce an fi son ta akan ku?” Mama ta kwaɓe shi se ya ce
    “To yanzu dai ya maganar bikin akwai ko babu in san shiri na?” Wai se na ji Mama ta ce masa
    “Ga ta nan ai se ka tambaye ta ni ma ban sani ba”. Tsabar dariyar shaƙiyanci se da ya faɗo daga kan kujerar da yake zaune ya ce
    “Ai ko dai se dai a tambaye ta, kullum fa ina laɓe wa naji hirar da suke wlh Mama ki tashi tsaye da addu’a lamarin Halima fa kamar akwai saka hannu”

    “Wai Mu’azzam me yasa bakin ka bashi da saiti ne?” Mama ta sake faɗa yace
    “To wlh ita take forcing maganar auren nan mutumin nan kullum yazo uzurin safe daban na rana daban ina ji jiya yana ce mata wai ya siyi interlocks an je ɗakkowa motar tayi accident duk sun farfashe kiji fa wata jahilar ƙarya ko a gidan uwar wa ma yake ginin oho dan dai ban ga in da aka nuna a unguwar su aka ce na sa ne ba”
    “Tashi ka bani guri Mama” ta kore shi ya fita yana surutansa se da ya maido ƙofar falon ya rufe kafin Mama ta kalle ni tace
    “Saura kwana nawa ya rage biki ne Halima?”
    “Kwana hamsin da uku Mama” na bata amsa kai tsaye, ta girgiza kai tace
    “Madallah, kwana hamsin da uku amma shiru babu wani motsi daga gidansu yaron nan shi be ce komai ba iyayensa ma basu ce komai ba ko kuma kun ɗaga ranar ne bamu sani ba?”

    “Ai suna ta ci gaba da shiri ne Mama mu ne anan har yanzu ba’a fara komai ba” na faɗa kai na a ƙasa. Tayi murmushin daya fi kama da yaƙe tace
    “Haka ne, to Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya. Ki shirya kayan ki cikin satin nan zaki koma gidan Labiba kafin lokacin bikin”. Baki na tunzura gaba nace
    “Gaskiya ni Mama ki barni nayi zama na a nan kin san dai Anty Labiba yanzu ta canza ba wani so na takeyi sosai ba”. Banza ta mun, ta wuce ɗaki ina mita amma kuma dana zauna nayi tunani nan na gano ƙila gyaran amare za a fara mun shi yasa tace na koma can dan na san Mama da kunya hali na ne ma yake sakata magana in ba dan haka ba ba wani shiga sabgata take yi sosai ba. Nan da nan na fara haɗa kaya da yamma nace mata zan tafi tace Aa na bari se gobe haka ko akayi washe gari da azahar nayi ƙaura zuwa gidan Anty Labiba.

    “Ni kam Halima ko kin ce masa kin yafe lefe ne babu labari? Sannan na zata zuwa yanzu ai ze ce azo a ga gida ko saboda musan irin tana din da zamuyi” Anty Labiba dake kallo na ta faɗa. Ina danna waya ta na ce
    “Ban san san da zasu kawo ba Anty, gida kuma akwai sauran aikin da ba’a ƙarasa bane shiyasa amma nasan da zarar an gama ze yi magana aje a gani gidan ai ba wani wahalar jere zeyi ba” nan na shiga wassafa mata yanda tsarin gidan yake. Tayi shiru kawai tana kallo na kafin tace

    “Kin je kin gani kenan” na kalle ta jin kamar ta rafko ni se na wayan ce nace
    “Haba dai. A waya dai kullum idan yazo yake nuna mun duk abin da a ka yi”. Tayi shiru kamar ba zata ce komai ba har na fidda ran zata sake magana kafin naji tana cewa

    “Amma kina ganin wannan hanyar da kika bi me ɓillewa ce Halima?” Na kalle ta na ce
    “Wa ce hanya kenan Anty?”
    Gyara zama tayi ta fuskan ce ni da kyau tace
    “Halima, ita mace da kike gani abu kaɗan ke in ganta rayuwar ta haka nan ɗan abu kaɗan ke sakata a taskun rayuwa. Dace ko rashin dacen abokin zama wato miji abubuwa ne masu matuƙar tasiri a rayuwar ya mace. Gidan aure shi ne aljannar duniyar mace, idan tayi da ce na ƙwarai ta rabauta haka nan idan ta kuskure shikenan rayuwarta ta shiga walagigi ita da samun nutsuwar duniya se dai idan ubangiji ne ya ƙaddara mata wata rayuwar bayan jarabtar data faɗa”.

    Aje wayata nayi na fuskan ce ta dakyau nace “Me kuma ya faru Anty?”
    “Babu abin da da ya faru Halima. Ima tunatar dake ne abin da ya kamata ace a shekarun ki kin fahimta amma naga kamar baki sani ba ko kuma kin manta. Shin na tambaye ki Halima, tun da kike ki taɓa ɗaga hannu kin roƙi ubangiji zaɓi cikin tarayyar ki da Bilal kuwa? Kin taɓa yin istikhara kin nemi aga jin ubangiji cikin al’amarin ku?”

    Shiru nayi ina kallon ta lokaci ɗaya kuma jiki na yayi sanyi tiɓis. Tayi murmushin tace
    “Nasan amsar ki Aa ce”
    “Wallahi ina addu’a Anty ke ma ai kin sani” na katse ta se tace
    “Ban ce bakya addu’a ba ce miki nayi akan lamarinki da Bilal kina neman zaɓin Allah eh ko a’a shikenan amsar, ko da yake idan ma kina yi ba zaki taɓa fahimtar abin da ake haska miki ba saboda kin ri gada kin sakawa zuciyar ki shi ɗin shine alkhairin naki”.

    “Wallahi Anty ina addu’a, kullum nayi sallah se nace idan da alkhairi cikin tarayya ta dashi Allah ya tabbatar mana” na faɗa tamkar zan saka mata kuka se tace
    “Na yarda. Halima, lokuta da yawa mukan take gaskiya cikin sani mu kai kan mu ga halaka. Muna runtse ido daga gaskiyar da take gabanmu mu ringa hangen gabanta ko bayanta sannan idan an samu aka si muyi kuka muce ƙaddara ce. Tabbas rayuwar mu gaba ɗaya tsararren al’amari ne amma dukkan musulmi ya yarda da tasirin addu’a mun kuma yarda addu’a tana sauya mummunar ƙaddara zuwa kyakykyawa ko kuma ta sassauta muninta.

    Ki sani ko da ace kina addu’a muddin a zuciyar ki akwai abin da kika rigada kika ƙudurce shi ne matsayar ki ai ba zaki ma Allah wayo ba. Idan abun Alkhairi ne lafiya lau ubangiji da zuciya yake amfani se ya baki, idan ma ba alkhairi bane tun da har a ranki baki yarda ubangiji ne me bayar wa kuma ya hana ba kika saka wani ƙulli se Allah ya barki da iyawarki, ba zan yi katsalandan cikin al’amarin aure ba domin sirri ne amma zan sake gaya miki ki nemi zaɓin Allah da zuciya ɗaya Halima. Allah ya sani ban ji a jiki na tarayyar ki da Bilal alkhairi bace be kuma nuna wasu alamomi da zasu ƙaryata tunanin mu akan sa ba. Kiyi amfani da ɗan lokacin daya rage miki Halima kiyi tunani kuma kiyi addu’a, kar ki bari so ya rufe miki ido ki kai kanki in da zaki ƙare rayuwarki kina nadama. Cutuwarki bake kaɗai zata shafa ba har da mu dan Allah Halima ki yiwa kan ki gata tun da sauran lokaci ki haƙura da yaron nan. Barin Bilal ba fitar numfashi daga gangar jikin ki bane, kin rayu kafin wanzuwar sa yanzu ma idan ki ka barshi babu abin da ze same me ki se alkhairi Halima. Amma shawara ce ban miki dole ba” Anty Labiba ta ƙarasa maganar muryar ta tana karyewa se ta miƙe tana share hawaye ta shige ɗaki, haka take tana da saurin karaya abu kaɗai ke fito da raunin ta. Na bita da kallo har ta shige ɗaki ta maido da ƙofa kafin na lumshe idanuwa na ina tariyo maganganunta ina kuma fassara su tare da aje kowacce a muhallin daya daveyda ita.

    Yanzu aka fara tafiyar.
    Shin kun hango sarewa a lamarin Halima kuwa? Zata yarda ta bar Bilal kamar yanda makusantan ta suke fata?
    Me nene haƙiƙanin matsayin Halima a gurin Bilal? Shin ya ɗauke ta tamkar yanda ta ɗauke shi ko kuwa dai hasashen da ake mata akan sa gaskiya ne?
    Allah shi yasan karatun bebe, haka kuma Allah shi kaɗai yasan gaskiyar dake zuciyar Bilal dan gane da Halima, shin So ne da gaske ko kuwa akwai wata boyayyar manufa da be bayyana?
    Ana zaton wuta a maƙera, Bilal fa ze iya bawa maraɗa kunya cikin tafiyar nan ku dai ku kasance tare da alƙalami na domin warwarewar duk wani zato da zargi da yake yawo tsakanin zukatanku.
    *MASU ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*

    Note
    error: Content is protected !!