Son Rai – Chapter Twenty-nine
by Aysha A BagudoWata irin kulawa ta musamman Dr jamil ke wa yesmin , Komai tare suke yi da Dr jamil ,duk abinda take so shi yake mata ,fita ne dai baya barinta zuwa koina ,sai dai ta zauna ita kad'ai a gida .
duk kulawar da Dr jamil ke bawa yesmin hakan Bai sa ta daina jin kwad'aicin da take ciki ya raguwa ba ,kullun tunanin gida ne aranta ,dan haka ta dinga Allah Allah suje Kano ..
"Yau Koda ya dawo daga aiki, ya ganta shiru zaune babu wata alamar tayi farinciki da dawowarsa, asalima ko kallon inda yake bata yi ba. . .