Son Rai – Chapter Twenty-five
by Aysha A Bagudo"Zuba masa ido kawai Dr jamil yayi yana cigaba da kallonsa zuciyarsa na harbawa , Shima abban yesmin din kallonsa yake, yana jin abubuwa guda biyu a lokaci day'a a kanshi farinciki da bakinciki .
bangaren Dr jamil Shima zuciyarsa cike take fal da tashin hankali bai ta'ba tunanin faruwar abinda ya faru a safiyar yau din ba ,yau tazo masa da abubuwa da yawa ,tashin hankali da farinciki mara misaltuwa " sai dai har lokacin zuciyarsa rawa take ,ya kasa tabbatar da abinda aminin nasa yayi masa "shin gaske ne marwa ta zamo Mata a gareshi ko kuwa kunnuwansa ne. . .