Son Rai – Chapter Twenty-two
by Aysha A Bagudo" hafsa kamar yadda kika ji na fad'a d'azu ,zan aurar da yesmin ga wanda yafi cancanta da rayuwarta ,bazan duba wata halaka, ko wani abu ba ,idan faruk din ne yafi cancanta zan bashi aurenta ,idan Kuma wani ne daban , shima haka ,fatana dai kiyi mata addua "
yana gama fad'ar haka ,ya yunkura yana k'ok'arin zare yatsun yesmin dake cikin nashi, ya mike tsaye idanunshi akanta ,har lokacin ganin da yayi mata manne a kirjin amininsa, yaki 'bacewa acikin kwayar idanunshi .
" Ita kuwa umma zaune kawai take a d'akin ,ta kasa motsawa, duk dai. . .