Son Rai – Chapter Fifteen
by Aysha A Bagudo....Yesmin na zaune ta zuba uban tagumi ,sai hawaye ke gangarowa bisa kuncinta , gabad'aya abun duniya ya isheta, duk ta rasa hanyar da zata bi ta had'u da Dr Jamil dinta ,bata san gurin Wanda zata samu cikekken address inda yake a maiduguri ba ,har mahaifinta ta tambaya cikin wayo da dabara ,shima yace " bai sani ba " me zatayi da address din ?
Kame kame ta dinga yi masa daga karahe sukayi sallama "
"damuwar da take ciki tasa karatu gagararta , tunanin barkatai kawai take ,Wanda ita kanta ta kasa barin kwalkwaluwarta tayi tunani day'a na iyayenta, ko Kuma. . .