Cutar Da Kai – Chapter Fifty-nine
by Aysha A Bagudo~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
Cafesu suka yi a lokaci ɗaya cikin tsananin farinciki da fad'uwar gaba tare da rungumesu tsam ajikinsu , samir na cewa "Masha Allah Kai kaga wasu kyawawan twins masu matukar kyau da tsananin kama da kai ?" murmushin gefen baki muradi yayi cikin sanyayyiyar muryarshi yace "wallahi na gani wannan idan wani ya gansu ɗauka zai yi ya'yana ne . yayi maganar a daidai lokacin dasu madu suka shigo falon gabadayansu banda kisna da suka baro tsaye a waje cikin tsananin tashin hankali da fargaba dawowar muradi dan ganinsa ya rikirkita mata tunaninta. . .