Cutar Da Kai – Chapter Fifty-six
by Aysha A Bagudo~TRUE LIFE STORY~
*PAID BOOK*
*AYSHA A BAGUDO*
da sauri afra ta fito suka kamata suna kiran sunanta "daman bata da lafiya ne afra. ?"granny ta tambaya cikin tsananin tashin hankali "eh tun shekaranjiya dai da zazzaɓi take kwana afra ta juya ta isa inda frigde yake ta bude ta dauko ruwa mai sanyi sosai suka shafa mata a fuska sai dai shiru bata motsa ba sai yatsun hannunta ne suka shiga karkarawa direban granny aka kira aka ɗauketa zuwa hospital , likitoci suka rufa akanta har washegarin daurin aure kisna bata farka ba koda musa da danginsa suka zo. . .