Search
You have no alerts.
    The Den of Novels
    Chapter Index

    ~TRUE LIFE STORY~

    *PAID BOOK*

    *AYSHA A BAGUDO*

    *MASI ƁUKATAR A TALLATA MUSU HAJOJINSU ZA SU IYA TUNTUƁARMU TA LAMBOBIN 07045308523 MUN GODE*
    bismillahirrahmanirrahim

    Muryarta a dake tace “bawan Allah kayi hakuri ni din matar aure ce fa” wani irin kallon raunin wayo yayi mata sannan ya gyara tsayuwarsa tare da zube hannuwansa duka cikin aljihun wandonsa yana wata irin dariya har ya neman d’aga murya , cike da matsanancin tsoro ta matsa baya da sauri haɗe da rike hannun d’anta gam dan ba karamin tsoro ya bata ba , a zahiri ake iya hango tsananin tashin hankalinta waige waige ta soma yi tana neman hanyar guduwa ciki zolaya yace “dakata ! dakata!! mana Karki gudu dan duk inda kika shiga a kasar nan wallahi sai na zakuloki matsawar kina cikin garin nan na mallakawa zuciyata ke “.Yayi maganar hankalinsa kwance yana nuna ta da ɗan yatsansa yayinda idanunshi ke tsaye kyam akanta yana mata wani irin kallo yana cigaba da dariyar da yake dan shi karya ya dauki maganarta …

    “a matukar tsoroce ta dubeshi kamar zatayi kuka tace “dan Allah malam ka daina kallona haka wallahil azim ni matar aure ce har ma da yara biyu …” ta karasa maganar idanunta na ciccikowa da ruwan hawaye .
    Cak dariyar dake kwance akan fuskarshi ta ‘bace zuwa mummunar ɓacin rai sannan yayi shiru yana kare mata kallo sama da kasa zuciyarsa na wani irin tsalle da bugawa , sam bazakace matar aure bace komai na jikinta irin na yammata ne hatta shigar jikinta yammata dayawa suna yi irinta yayi maganar acikin ranshi “oh my goodness ya furta a fili yana dafe goshinsa ,”amman ko waye wannan mutumin daya aureki ya cuceni ya cuci rayuwata ya gama dani kalar matar dana dade ina nema na aura wayyo Allah naga samu naga rashi tawa ta sameni a fili yayi maganar yana Kallonta da narkakkun idanunshi , hankalin kisna ya sake tashi ita ba maganarsa tafi daga mata hankali ba zuwan ahlinta tafi jin tsoro dube dube ta soma tana addur kar Allah ya kawo Aliyu ko ya samir guri, numfashi ta sauke saboda babu alamunsu hatta su anty zee bata ga kyallinsu a gurin ba dan haka ta sanyawa jikinta natsuwa tare da gyara tsayuwar ta ,bangaren Aliyu kuwa gabad’aya ya manta da wata halitta kisna suka zo tsabgar gabansa kawai yake yana gwadawa areef takalma , duk wanda ya daukar masa sai ya d’aukarwa aryan ..”

    Mutumin ya lumshe idanunshi yana jin yadda zuciyarsa ke tafasa akan jin abinda ta faɗa masa yanzu ,cikin murya mai cike da kasala ya cigaba da fadin “gaskiya gaskiya wanda ya aureki ya kassara min rayuwa , ina ji ajikina koma waye ya aureki baya sonki sai dai kasancewar mata nada raunin zuciya zaki iya son shi dan baku san mutanen da suka dace da rayuwarku ba …”bata san sanda dariyar maganarsa ta subuce mata ba tayi murumushi tana toshe bakinta da hannuta, aryan ya d’ago kanshi ya kalleta ya sake maida idanunsa akan mutumin dake tsaye ,”kin san wani abu”?ya tambayeta yana tsareta da idanunsa ,taki cewa komai saboda qirjinta dake bugawa da sauri “idan ace ni na aureki bazan Iya barin ki fita ko’ina batare dani ba, irin kulawa da soyayyar da zan baki sai kin ce na rage yayi yawa zan lalla’ba…..” saurin katseshi tayi ta hanyar fadin “dan Allah ka wuce tare da mijina muke fa idan ya gamu komai zai iya faru “.ya zaro ido waje cike da mamaki “shine ya barki haka gaskiya hasashena ya tabbatar gaskiya, wallahi baya sonki “hasashenka bai tabbata gaskiya ba ni dai dan Allah ka rufa min asiri ka bar bibiyata hakan zai iya haifar min da babban matsala da mijina wanda bazan so faruwar haka ba “.

    “shikenan ya zanyi da rayuwata zanyi duk yadda kuke so sannan zanyi addu’ar Allah ya kawo tsautsayin da mijinki zai sakar min ke na aureki cikin kankanin lokaci dan bana son a dauki lokaci batare dana mallake ki ba yayi maganar tare da mika mata badir din kudin kasar “ga wannan ki sha ice cream ke da boy taki amsa tace ” bana bukatar haka daga gareka , sannan ba Ameen ba akan addur da kayi yanzu saboda ina tsananin son mijina duk runtsi bazan so rabuwa dashi ba ..”
    Tabe baki yayi kawai yana Kallonta sannan ya mika wa aryan hannu alamun yazo gareshi aryan yayi saurin makale kafad’a ,”har yanzu jikina yana bani baki da aure sai dai musamman zan sa a binciko min komai naki ina tabbatar miki nan da wani lokaci zan san komai akanki ya kamo hannun aryan da dabara ya daga shi sama yana masa wasa “ya sunanka boy “? Aryan daya jishi a sama yana yawo daman abinda yake so kenan ya wangale masa baki yana cewa “aryan …” “Wooooowwww nice name ” aryan kace auntynka ta fad’a min gaskiya kada ta wahalar da zuciyata idan kuma bazata amince min ba ta bari mu zama friend’s daita ….. “.”wayyo Allah na shiga uku shikenan kasani a matsala ta furta a matukar tsorace sakamakon idanunta daya haɗu dana Aliyu dake tsaye “dan Allah ka rufa min asiri ka sauke min yaro kuma ka bar gurin nan yanzu tayi maganar kamar zatayi kuka a hankali mutumin ya sauke aryan domin ganin wanda ta kira da sunan mijinta ….”

    A natse idanunshi ya sauka akan Aliyu daya soma takowa da kyawawan zara zaran yatsun kafafunsa masu matukar kyau cike da jarumta irin na karfaffan namiji mai tattare da natsuwa da haiba zuwa inda suke tsaye ,yayinda kisna dake tsaye qirjinta ya cigaba da bugawa da matsanancin karfin gaske hankalinta yayi mugun tashi take gumi ya shiga tsatsafo mata a goshinta da sansar jikinta ,ta tsura masa narkakkun idanunta da suke a matukar tsorace domin son tabbatar da yanayinsa ,
    Irin na d’azu zai yi musu ya sharesu ya basar kamar bai ga komai ba ko kuwa zai yi magana ne a matsayinsa na mijinta “?yana daf da k’arasowa inda suke wayarsa ta soma ringing kafin ya d’auka kiran ya katse a hankali ya ciro wayar daga gaban aljihunsa ya duba ganin mai kiran ya soma neman layin yana cigaba da daga kafafunsa yana ciza gefen lip’s dinsa yayinda hannunsa daga ke cikin aljihun wandonsa dan tunanin maganar da zai fadawa mr birsat dake bukatar zantawa dashi ta musamman a gobe ..”

    Ta daura laulausan tafin hannunta akan goshinta ta goge gumin dake tsatsafo mata zuciyarta na rawa yayinda har wannan lokacin tana cigaba da kallonsa jikinta na wani irin rawa , tana kallonsa ya soma wayar bata ji yace komai ba illa “to shikenan naji zamu yi magana later cikin tsadaddan turancinsa ya cire hannusa cikin aljihunsa ya riko hannu areef dake tsartsarfa yana biye dashi ,bakinta na rawa ta dinga furta kalmar ” ka wuce ! Ka wuce dan Allah !! Allah ya gani bata so Aliyu ya ganta ba saboda gudun tozarcinsa da wulakancinsa dan tasan duk abinda zai yi dan tozartata yana so saboda baya kaunar ganinta cikin farinciki sai dai babu yadda zatayi yanzu aikin gama ya gama sai ta jira taga sakamakonta , mutumin ya kallesa ya ganesa sarai realwan Aliyu muradi ne da suka haɗu d’azu nan take ya shiga wasi wasi acikin ranshi anya kuwa gaskiya ta faɗa masa? tunda ganin idanunshi suka yi karo dashi babu wanda yayiwa d’an’uwansa magana ko nuna alamun sun san juna idan kuwa har mijinta ne ta yaya zasu haɗu da juna batare da sun nuna alamun su din ma’aurata bane ? “ganin Aliyu yana ƙoƙarin nufo inda suke yasa jikinta ya sake ɗaukar kyarma gumi ya sake wanke mata jiki wani irin tashin hankali ne ke sake kawowa gangar jikinta ziyara a hankali ta cigaba da maimaitawa mutumin kalmar “ka rufa min asiri ka tafi dan girman Allah, amman ko gezai yaki tafiya ya tsaya kyam kamar mashi yana jiran karasowarsa yaga mai zai yi ,” dan tabbas idan matar aurensa ce dole ne ya dauki mataki ……”

    Sunkuyar da kanta kasa tayi tana kallonsa ta kasan idanunta , yana takowa qirjinta na luguden bugawa da matsanancin karfin gaske, saurin fixge hannu aryan tayi ta rike gam a hannunta ganin yana cigaba da karasowa “momy look at papa ……sororo mutumin yayi kar dai gaskiya ta faɗa masa ita din matar aure ce ,matar ma ta Aliyu muradi ,gaskiya ta cancanci ta kasance matarsa sun dace matuka, tana da kyau sosai kamar yadda shima yake da tsananin kyau na bugawa a jarida daman irinsu sai irin wadan nan matan masu tsananin kyau kamar su sukayi kansu …”

    yana gama k’arasowa ya fixge hannu aryan a hannunta ta d’ago idanunta a gigice ta kalleshi ,hanunusa ya mika baya tunaninta marin mutumin zai yi dan haka tayi saurin durkushewa kafin ya gama dashi ya dawo kanta ga mamakinta sai gani tayi ya riko hannu samir ya zagaye kanta dashi tare da mika masa hannu aryan suka juya suka soma ƙoƙarin barin gurin ,wani wahalallen numfashi ta sauke ta mike tsaye a firgice “da alamun kina matukar son wannan dan wasan kallon ba dai mijin aurenki ba ? ” ki duba kiga yadda ya nuna ko in kula akanki babu mutumin da zai ga matarsa ta sunah tsaye da wani reaction d’insa bai canza ba kina son maso wani wannan da shafukan sadarwarsa hotonsa dana wata buduwar ne wanda ake rade raden zai aureta me yasa zaki ‘batawa kanki lokaci akan mutumin da bai sonki kuma bai damu dake ba ki bawa yusif modibo dama ya zamo abokin rayuwarki zan kula dake da duk abinda na mallaka a duniya zan baki .. ..”
    “Enough dan Allah ka dameni da surutunka na banza shasha kawai sai wani zuba kake kamar fanfo babu class babu aji babu mannes ,” kasani koda ni din ba matar aure bace bazan taba kula ka ba saboda baka daga cikin tsarina tana gama fadar haka taja tsaki ta barshi tsaye ….”
    Bayanta yabi da kallo a ransa yace duk abinda zakiyi sai dai kiyi amman bazan hakura ba sai na mallakawa zuciyata ke “..

    Jiki a sanyaye ta k’arasa inda suke wanda zuwa lokacin numfashi ma da kyar take fitarwa “lafiya me ne ne ka wani fixge hannu yarona a hannuna ai ba kai kadai ka haifeshi ba tayi maganar cike da dakiyar zuciya Aliyu ya buɗe baki zai fara magana cikin sanyayiyyar murya Samir ya dakatar dashi dan haka ya juya a fusace ya tsaya nesa kaɗan dasu “wato daman kina da wata manufa a cikin ranki shiyasa kika ce a fito dan ki samu damar kula maza ko “? tsayawa tayi kawai tana masa wani irin kallon ,ya kalleta kamar zai ɗauketa da mari saboda kallon raunin hankalin da tayi masa “wuce muje gida “kayi hakuri dan Allah yanzu fa muka fito inji cewar aunty zee “lafiya kisna mai ya faru yayanki ya dauki zafi haka “?”Babu komai tayi magana muryarta can kasa hawaye na zubo mata ita ba fadan da yayi mata ne yafi damunta ba kamar yadda Aliyu ya wulakanta aurensa dake kanta “tabbas yanzu ta sake fahimtar Aliyu bazai sota ba “me ye babu komai ki faɗa mata wani kato kika kula da aurenki saboda bakinsa darajar kanki ba yana faɗa yana kara d’aure fuska nan take kisna ta sake tsoronta motar da suka zo daita ya nuna mata duk abinda Samir yake faɗa mata yana shiga kunnen Aliyu amman ko ajikinsa bai nuna ya damu ba dan shi ko yawo zatayi tsirara tayi ba zai damu ba bare kula wani kato …”

    A hankali su aunty zee suka karaso gurinsa tun daga nesa take kallon Aliyu so take ta fahimci reaction d’insa akan kisna amman taga babu alamar haka hasalima wasa da yaransa yake ya daga ariyan sama ya daga areef”Hannu areef ya rike aryan na saman fad’ansa ya nufi inda ya paka mota ya shiga ya sanya aryan a gabansa ,su aunty zeey suka shiga mota ya ja , gabad’aya hankalin kisan yana kan Aliyu dake zaune yana tuki “ya Allah ka taimakeni ka nuna min hanyar da zan shawo hankalin mijina gareni …

    Gudu yake sosai akan titi duk maganar da Samir yake masa yana bashi hakuri akan abinda kisna tayi bai ce uffan ba haka zalika bai waigo inda yake zaune ba yana karaasowa get din gidan ya danna hon da karfi mai gadi ya taso da sauri ya bude masa get ya sanya hancin motarsa cikin haraban gidan madadin ya karasa inda aka tanada domin ajiye motoci sai ya tsaya a tsakiyar gidan ya fito ya nufi kofar parlou’n gidan Samir ma ya fito da sauri ya biyo bayansa Aliyu na kokarin hawa step samir ya shigo yana masa magana “ina son na kasance ni kaɗai i will see you later samir , samir ya gyada kai ya zauna akan doguwar kujerar parlou’n yana furzar da iska mommy dake zaune tace “wani abu ya faru ne da kuka fita “?

    Girgiza mata kai yayi “babu komai momy ya fada mata haka dan kwantar mata da hankali “karka min karya fa samir ? babu komai mommy idan akwai ai zan faɗa miki “Allah yasa ta fada hk tana jiran shigowar jikokinta a guje suka shigo suna kiran sunanta “granny ta ware musu hannuwanta “oyayo sannuku da dawowa me kuka kawo min my dear”? “Ni yunwa nake ji inji cewar aryan yayi magana yana yatsuna fuska tare da shafa ciki Samir ya kalleshi “babana ban da karya fa duk cire ciye da kuka yi amman kace yunwa kake ? Turo masa karamin bakinsa yayi yana sake kwabe fuska mumy tayi murmushi Tace “karku damu yarana I have oredy cook delicious for you ta fada tare rungumesu ajikinta “really granny ? “sure my grandchildren’s babu abinda ban muku ba “yeeeeeeee suka soma tsalle suna sake rungumeta a daidai lokacin da kisna da aunty zee suka shigo hannunsu rike da kaya “iyeeee kunga yan gatan granny areef ya mike ya amshi farar ledar da Aliyu ya siyo musu takalma ya dawo gurin mommy “granny I want to show you something ya bude ledar takalma suka zubo masu yawa “papa ne ya siya mana nida aryan “iye lallai papa na ji daku ,aryan ya cire takalmin dake sanye da ƙafarsa ya matso ya dauki guda daya acikin wanda aka siyo “ki samin granny ina son nasa sabon takalmi ” ka bari zuwa gobe kaji my sweet heart ya kwasa takalman da gudu ya hau sama shima areef ya kwashi wasu ya bishi a baya “sannu da gida mommy aunty zee da kisna suka hada baki .”

    “sannuku kun sha yawo “wallahi ai kasar akwai tsari gasu da dogayen riguna da kananan kaya ai ina ganin sai na sake komawa tayi maganar tana nuna samir da baki ya juyo ya kalleta “aikuwa sai dai ki nemi mai kai ki dan duk kwananki nan zamuyi busy “haka zaka daure ka kaita “Allah mommy kina shagwa’ba yaran nan da yawa ya fadi haka tare da mikewa ya fita domin gabatar da sallah , Kisna ta mike” bari nayi sallah nima nazo na daura mana girki “huta abunki mamana na dafa muku had’ad’d’en girki kala dabam dabam “thats why I love you mommy ta kai mata pick a kumatu ita kuma mumy ta shafa kanta ..”

    Sama ta hau zuciyarta cunkushe da bakincikin nuna ko in kulan da Aliyu ya nuna mata lokacin daya gatan da wani kato wannan abu ya bala’i taba mata zuciya tana kan step ya sauko sanye cikin wasu kayan kunnensa manne da waya yana magana kasa kasa “,okay ka fito da marcende kawai yana ganinta yayi saurin ɗauke kanshi , idanunta ta lumshe tare da sake bashi hanya qirjinta na bugawa cikin natsuwa ya raba ta gefenta yana sake janye jikinsa dan kar jikinsu ya haɗu kamshin turarensa dake tashi ne ya cika mata hanci da zuciya hakan yasa ta ɗan ji sanyi acikin ranta har taji kashi dari na ɓacin ran daya haddasa mata kashi goma ya kau a cikin zuciyata , ta gefen idanunta take kallonsa har ya gotata sannan ta cigaba da tafiya , kofar fita ya nufa muryarsa a ƙausashe yace ” mommy zan ɗan fita amman ba jima zanyi ba zan dawo “
    “Muradi ……”Mommy ta kira sunansa ya juyo tare da tsurawa momy idanunsa da suke a rikici sun yi jawur tamkar garwashin wuta bama zaka taɓa cewa farare bane sannan cike suke da matsanancin maseefa ya kasa amsawa mumy illa tsura mata ido “amman naji kacewa Samir zaka huta ina kuma zaka yanzu da alamun ma akwai abinda ke damunka , murmushin gefe baki yayi mata wanda yafi kuka ciwo yana girgiza mata kai alamun babu komai, bata fuska tayi “karkawa mommynka karya mana zaka iya k’arasowa ka faɗa min damuwarka koni na taso na sameka”?murmushi ya sake yi yasan komai zai yi mommy Sai taso tasan abinda ke damunsa ko abinda zai fitar dashi a daidai wannan lokacin yasan yadda mommy take matukar sonshi bata haɗa shi da komai ba a rayuwarta , uwa ce data amsa sunanta shi kuma yana tsananin sonta zai iya mallaka mata komai daya mallaka a duniya koda kuwa rayuwarsa ce koda kuwa ba itace sila inganta rayuwarsa ba ,bashi da wata uwa kaf duniya data wuce ta, itace uwarsa itace ubansa itace komai nasa k’arasowa yayi ya zauna kusa daita ya kamo hannuwanta duka cikin nashi aunty zee na ganin haka ta mike tsaye “uhmmm bari na bawa uwa da d’a guri ta nufi sama mommy tayi murmushi “gara ki tashi kam .

    bakinsa ya kai daidai kunnen mommy yayi mata magana a hankali , murmushi ne ya sake bayyana akan fuskarta ta ja kunnensa ya ɗan saki qara mara sauti yana kai hannunsa kan na mommy “ashhh mommy akwai zafi fa “kabi a hankali muradi bana son kana damun kanka dayawa Allah ya tsare min kai sai ka dawo amman karka dade sannan karka yi abinda zai …..” Hannunsa ya d’aura a saman bakinta “mommy babu abinda zai faru kin rigada kin min addu’a ya mike ya fito zuwa haraban gidan yana waya “okay na gane unguwar ,no karka damu zani ni kaɗai ya katse kiran ya karasa inda direbansa ke jiransa har ya bude masa murfin gidan baya amman yaga ya bude gaban mota ya shiga direban ya karaso da hanzari ya bude mazaunin direba ya shiga ya tada motar mai gadi ya wangale musu get din gida…
    Jingina bayansa yayi da kujerar motar da yake zaune , zuciyarsa na wani irin zafi da tuttukin bakincikin mara misaltuwa ,shi kadai yasan yadda yake jin kanshi da zuciyarsa da yake jin kamar zata kama da wuta, runtse sexy eye’s d’insa yayi yana dukan cinyarsa da hannunsa daya “ina muka nufa ne boos”? direba ya tambayesa yana dubansa *”madinaty* ya bashi amsa a takaice ….”

    Zaune a bakin gado aunty zee ta iske kisna ta rafka tagumi yayinda aryan da areef ke guje guje a dakin ta karaso ta zauna a gefenta tana dafa kafad’anta “me yayi zafi kisna komai yayi zafi fa maganinsa addu’a “.
    Naunauyen ajiyar zuciya ta sauke tana lumshe idanunta “zuciyata aunty zee ina jin ajikina bazan dade a duniya ba na kusan mutuwa dan Allah ko bayan raina ga ….
    “dan damuwar datayi miki yawa ne yasa kika fadi haka bai zama lallai damuwar tayi sanadin barinki duniya ba ,idan Allah ya ga dama kina cikin damuwa zai rayaki na tsawon shekaru abinda zakiyi shine addu’a Karki gaji da kaiwa Allah kukanki “ina addu’a sosai aunty har na fara ga…” “Karki gaji ,ba’a gajiya da addu’a kisna , Allah na amsa addu’armu sai dai ana jinkirtawa bawa ne amman kisawa ranki duk abinda kika roki Allah ya amsa wai ma meye abun damuwa yanzu “?
    “Damuwata da bakincikina aunty zeey Bai wuce yadda ya Aliyu ya nunawa mutumin nan ni din bawata tsiya bace agurinsa alhalin na sheida masa ni din matarsa ce wallahi dana san wannan wulakanci zai min dana ce masa ni din ba matar aure ba kai dana ma bishi mun wuce gidansa ……….

    Aunty zee ta kwashe da dariya har da rike ciki “ai kuwa da kin haukata ya Aliyu kinsa wani abu ?Kisna ta girgiza mata kai “sai kin fada min ” wallahil azim yaji mugun haushin ganinku tare da wannan mutumin Samir ma yaji haushi bare shi mai mata “karki faɗa min haka aunty zee dan ba yarda zanyi ba ” kinsan Allah ko ki yarda ko Karki yarda Aliyu yaji haushi ya dai ki nunawa ne dan karki ɗauka ya damu dake “yaushe ne zai damu dani aunty wallahi na gaji dashi zama dashi ya fita raina banki ya sakeni ba ……”? Tayi maganar hawaye na gangaro mata “karki fidda sautin kukanki kinga yara suna gurin nan shiru sukayi gabad’aya yayinda kisna ke kokarin maida kukanta “nasan yadda kike jin wannan situation din da kike ciki sai dai bani da abinda zan faɗa miki daya wuce ki zauna da mijinki lafiya ki ci-gaba da ƙoƙarin janyo hankalinsa shiyasa ma na siyo miki kananan kaya domin ki dinga sakawa kina daga masa hankali” .
    “Wannan mai zuciyar dutsen ai ina fada miki ko tsirara zanyi yawo a gabansa bazai taba nuna ya ji wani abu ba bare wasu kaya , na dai sawa jikina naji dadi “karki gaji kisa tun bai damuwa zai zo ya fara nuna sha’awarsa tunda shi ba dutse ba “kai aunty bazan iya ba fa Kuma bazan cigaba da miki alkwari ba at any time zan iya barin rayuwarsa dan wallahi na gaji dana mutu nayiwa yayana hasara wallahi gara na bar rayuwarsa ,na dawo rayuwarsa ne dan na gyara kuskurena amman yaki bani dama sai faman wwulakantani yake , me ye amfani dawowata ?
    ” da amfani sosai bazaki gane ba sai nan gaba abinda nake so da Ke ki kara hakuri ki bar maganar rabuwa wai bana ce miki ma’aikun rahma na tsinewa matar dake neman saki daga mijinta ba kema fa kinsa furta hakan haramun ne shiru Kisna tayi kirjinta na buga ita fa ta kudurcewa ranta zata sanarwa mumy tana bukatar rabuwa dashi gara ta rungume rayuwar ƴaƴanta ” bari naje na bar yayanki shi kadai gashi banyi sallah ba Kisna ta sauke ajiyar zuciya “Okya shikenan nima bari nayi sallah na sauko an bar mommy ita kadai …”

    Sai wurin karfe goma da minti goma shabiyar Aliyu ya shigo gidan yana haki kamar wani zaki ,suna zaune gabadayansu akan dinnig table suna cin abinci kallo ɗaya yayi musu ya dauke kanshi ya haye step momy na ganin yadda ya shigo ta biyo bayansa da sauri kallon kallo suka bi juna dashi batare da sunce wa juna komai ba kisna kuwa kasa cigaba da cin abinci tayi duk taji komai ya fita akanta kawai ta cigaba da bawa areef zuciyarta na tsinkewa saboda hukunci zuciyarta yayinda aunty zee ke bawa aryan abinci , kasa zama kisna tayi ta biyo byn mumuy domin son aiwatar da kudirin ta ..”

    A tsakiyar dakin mommy ta iskeshi yana ƙoƙarin cire rigar jikinsa jin motsin shigowa dakin yasa ya juyo yana zare rigarsa ya saura daga shi sai farar vest da dogon wando a hankali ya shiga fifita da rigarsa yana furzar da iska mai zafi daga bakinsa yayinda hannunsa daya ke rike da kugunsa sai zufa yake yi ,jijiyon kanshi duk sun mika sun yi rudu rudu tamkar wanda ya shiga fagen yaki ” bana ce kabi komai a hankali ba me yasa zaka ………”shigowar kisna ya katsewa mumy hanzari ,kisna ta karasa shigowa jikinta a sanyaye idanunta na kanshi a kallon da take masa ta fahimci yana cikin tsananin damuwa “to me kuma ya sameshi”? tayi Maganar akasan ranta tana takowa inda jug din ruwa yake ta tsiyaya a glass cup ta karaso inda yake yana fidda numfashi ta mika masa kin amsa yayi sai da mommy tasa baki sannan ya amsa sai dai ya kasa kai cup din bakinsa yana jin tamkar ya saki cup din kasa ,babu zato babu tsammani suka ga ya matse glass cup din a hannunsa take cup din ya soma tarwatsewa ruwa da fasassasun glss suka yi kasa kisna da momy suka tsura masa ido hankalinsu a tashe cikin tsananin tashin hankali mumy ta rike hannunsa tana furta “menene haka muradi zaka kashe min kanka ne kalli yadda …ai ganin jini ya fara diga yasa mumy yin shiru tare da rudewa cikin tsananin soyayya ta tsinka masa marin da sai data ji saukansa a zuciyarta kana da sauri ta yaga gefen zaninta, kisna ta matso kusa dashi tana kokarin taba hannunsa ya dakatar daita da hannunsa sannan ya runtse idanunshi gam dan baya son ganinta bai ji zafin marin da momy tayi masa ba illa gyara tsayuwarsa da yayi cike da jarumta, ahankali ya dinga motsa labbansa yana furta kalmar “kiyi hakuri momy kiyi hakuri ….” “karka sake cewa zakayi wani abu kaji na faɗa maka ka manta da komai “no mommy “no I can’t “,wallahi mommy abinda Kika faɗa min nayi banyi wani abu dana san ba daidai ba “.muryarta a raunane tace “mommy me yasa mesa dan Allah kice masa ya dinga sawa zuciyarsa salama ya dinga bin komai a hankali idan wani abu ya sameshi ban san yadda su aryan zasu ji ba …….”
    “har ke kanki zakiji babu dadi dan duk abinda ya samu uban ya’yanki ya sameki “a hakan da bai daukeni da daraja ba , bai san mahimmancina ba ,sannan bai damu da damuwata ba tayi zance a zuci “shima kuma bazai so wani mummunar abu ya sameki ba amatsayinki na matarsa kuma uwar ya’yansa inji cewar mumy , aliyu ya sake runtse idaunshi yana ciza gefen lip’s d’insa da karfi mumy ta kamo sa ta zaunar dashi akan kujera “karka sake min irin wannan ganganci dan rayuwarka nada matukar muhimmancin gareni ta kalli inda kisna ke tsaye “kin wani tsaya kina kallon mu ki je dakina ki dauko min akwatin first aid ,juyawa tayi a sanyaye ta bar d’akin ko cikakken second biyar bata yi ba ta dawo ta ajiye ta sake fita dan dauko tsinyaya ta gyara gurin ta cigaba da tsayuwa tana kallonsu dan ko tace zata taimaka masa bazai yarda ba
    mumy ta bude laulausan tafin hannunsa gabanta na wani irin faduwa ,shiru tayi tana kallon raunin daya ji ,tausayinta ya kamata taji kamar ta cire ciwon ta dawo dashi jikinta wanke masa hannu tayi da hydroxy da auduga, tana wanke raunin tana duba ko kwalba ya shiga naman hannunsa .
    Bayan ta gama ta rufe akwatin ta janyo kisna tare da zaunar daita gefenta bayan kamar minti goma ” kisna taga gara ta aiwatar da nufinta tunda gasu tare , ta kira sunan mumy a hankali “mumy ina neman wani alfarma agurinki saboda kece mutun ta farko a duniya da kike son zamana da ya Aliyu tun ada can baya har zuwa yanzu ,sai gashi har yanzu babu wani cigaba a rayuwar aurenmu.
    “da cigaba mana me yasa zaki ce haka “? Mumy tayi mata tambayar a dan kufule dan yaji haushin maganarta “allah babu wani cigaba mommy saboda har yanzu ya Aliyu bai daukeni a matsayin matarsa ba me zai hana mu saukakawa juna ya sawakemin idan zaki wuce na biki mu koma tare dan wallahi zuciyata ta gaji da wannan zaman idan kuma hakan bai samu ba wata rana labarin mutuwa zai riskeku a lokacin da kuke tsananin bukatata ta karasa maganar hawaye na gangaro mata mumy ta damki tsintsiyar hannunta jikinta na rawa numfashinta na barazanar daukewa “ki kwantar da hankali mumy Allah rabuwar mu zai fi kwantar miki da hankali zucoyoyinmu zasu fi samun natsuwa Allah ya raya mana su Aryan “abinda ta faɗa gaskiya ne mumy nima ina iyakacin kokarina naga cewar na manta baya na inganta relationship din sake tsakaninmu amman na kasa idan dai har zai yiwu mu sawakewa juna …….”
    “Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un ” mumy ta shiga furtawa jikinta na tsananta rawa …”

    Inshallahu ku saurari 14 zuwa an jima

    Mmn sudais
    💗💗💗💗💗💗
    CUTAR DA KAI
    💖💖💖💖
    💗💗💗💗💗💗

    Note
    error: Content is protected !!